Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
*GISHIRIN*
*ZAMAN*
*DUNIYA*
_Daga Al'kalamin_
_Badi'at Ibrahim_
( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)
GAWURTATTU BIYAR í ¾í´ší ¼í¿» TAKUN FARKO
Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace
ya ke bayarwa ga al'umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin zamantakewar
Aure.
Kashi na farko
Babi na 1~2
Shinfi'daí ½í³–
Kano 7/2/2010 gidan cike ya ke dam da 'yan Uwa da abokan arziki, wanda su ka amsa gayyatar
biki na, daga gari gari. 'Yan uwan mahaifina da su ka kasance su ne jigon bikin, kab 'dinsu sun
halarci wannan biki nawa. Daga 'bangaren maza a waje 'yan daurin aure kuma, Kawu
Sulaiman wan mahaifina shine mad'aurin aure na. An cika ma'kil a k'ofar gidan mu dan
gudanar da wannan 'daurin aure. Ni kuwa ina cikin kawayena da su ka kasance manyan mata.
Dan kab kawayena babu budurwa, daga matan aure masu yara, sai zawarawa. Kasancewar na
samu jinkirin aure. Shekaruna talatin da biyar a duniya. Daga gari gari a ka halarci wannan biki
dan na yi gayya sosai. Abokan aikina na asibiti ma duk sun hallara, kasancewata ma'aikaciyar
kiwon lafiya, bangaren anguwar zoma. Farin cikin da na ke ciki a wannan ranar bai da abun
misali. Sanye na ke cikin riga da siket na atamfar Soso, mai kalar green da wani ganye ganye
mai ruwan madara a jikin atamfar, na yi kyau sosai, sai busa kamshin turaren humra na ke yi.
Kawayena sai tsokana ta su ke ta faman yi. Aminiyata makociyarmu Amina ce ta shigo d'akin
da mu ke ni da kawayena ta na haki. Dubanta nai da mamaki nace.
Ke kuma lafiya ki ke ta haki kamar wacce jaki ya ka da ita?" Ba ta ce da ni komai ba, hannuna
kawai ta ja, tare da kirawo kawata Hadiza wacce ta zo bikina daga katsina. Fita mu ka yi zuwa
bayan gidan mu, in da akwai rangwamen taron mata. Ta ce da ni.
"Sadiya akwai fa gagarumar matsala a wannan karon ma." Murmushin ya'ke na yi, domun
zuchiyata har ta gama yi mun hasashen abunda amina ta ke so ta ce."
An fasa auran wannan karon ma ko Amina?" Murmushi na sa ke sakar ma Amina, amma cikin
zuchiyata ci take da wuta babababah. Hadiza ta ce.
"Amina dukkan mu ba yara bane. Ina tunanin kwakwalwarmu za ta iya shanye komai. Ki sanar
da mu abunda ke faruwa." Yawu Amina ta ha'diye ta mi'komun wata kalanda. Hannu nasa na
amsa jikina na rawa. A hankali na warware wannan kalandar. Abunda na gani shi ya tsananta
bugun da zuchiyata ta ke ta faman yi, take hawaye su ka gama wanke mun 'yar fuskarta.
Kalanda ce mai d'auke da hoton Ahmad mijin da zan aura yau, tare da kawata Fatima. Ko da
na duba date sai na ga the same date da nawa daurin auren yau. Amina na duba na ce. Ina ki
ka samu wannan kalandar Amina, Ahmad d'in dama soyayya su ke yi da Fatima ban sani ba,
tare zai ha'da ya aure mu ko kuwa ita ka'dai zai aura, ni ya fasa aure na?" Dukka Wa'dannan
tambayoyin a gigice na jeroma Amina, cikin dimuwa da tashin hankali mafifici. Sau uku ana
kawo sadaki na, ana fasa auran, sabida kawai na yi ilimin boko mai zurfi har ina d'aukar albashi
daga asusun gwamnati. Amina jiki a mace ta ce.
"Maman mu ce, ta je bikin jiya. Shine aka rarraba kalandar, yau da na zo sai na soma shiga
gida kafin in shigo nan, sai na tarad da mama bata nan, ta na nan gidan. A kan gadon ta na ga
wannan kalandar. Sadiya iyakar abunda na sa ni kenan." Lumshe idanuna na yi, ina jin son
Ahmad na ninka kanshi a zuchiyata. Na ce. Babu komai nagode. Koma mai Ahmad ya ke nufi ai zan ji zan gani, tunda yau ne daurin
auran, kuma ma yanzu. A wajan na barsu na shiga ciki, ina ta gauraye hanya dan ba na jin da'di
sam, zazzab'i me mai zafin gaske ya ke shirin kwantar da ni. Kwanciya na yi a d'akin da
kawayena su ke. Sai liyafar cin abinci da shan lamon kwalba su ke yi. Ni kuwa na zama kurma
sai duba siririn agogon fatan da ke manne a tsintsiyar hannuna na ke yi. Zainab kawata ta ce.
"Sadiya ta wajajen ina gidan da Ahmad zai sa ki ya ke?" Duban ta na yi a sanyaye na ce.
Ta wajajen D'orayi gidan ya ke, amma bansan layin ba gaskiya." Hadiza ta ce.
"Rabu da ita Sadiya, bayan anjima anjimannan tare da ita za mu je jere, ko wannan dinma mai
gidan na ki bai barki bane?" Ta jefa ma Zainab tambaya. Dariya Zainab ta yi tace.
"Ahh haba dai, shima bazai hana ba, ya fa san yanda mu ke da Sadiya. Shima ya na waje cikin
maza 'yan daurin auren ai." Ni dai sai bin su da kallo na ke yi. Kanwar umman mu ce Goggo
Hansatu ta le'ko d'akin da mu ke tace.
"Kawayen amarya da su wa da su waye za su je jere ? Dan Allah ku fito ga iyaye can a wajan
mota ku ake jira." Gabana ne ya sa ke sabon bugawar da sai da na runtse idanuna. Su Amina,
da Hadiza, da Zainab, ne su ka mi'ke tare da bin bayan Goggo Hansatu. Ni dai ina kwance ina
jiran tsammanin abunda zai je ya zo. Su Goggo su na wajan motar kayan da zata kai kayan amarya. Kawu Sulaiman da kawu Bala
ne, su ka iso wajan Motar. Goggo Safiya, da Goggo Mariya 'kannenshi ya ce da su. Su shiga
gida ya na da magana.
Bin bayan su, su ka yi zuwa cikin gidan 'dakin da ke zauran gidan, in da anan su ka sauka su
maza mazan. Sawa ya yi a ka kirawo Yaya Asabe Babbar yayarsu a mata, da kuma mahaifiyar
Sadiya, da kanwarta Goggo Hansatu.
Bayan duk sun hallarane, Kawu Sulaiman yace.
"Toh al'amuran daurin auran yarinyar nan komai ya jagule ya damalmale. Aisha kin cuce mu
da ki ka bar mana yarinya a gida harta ri'ka ta ri'ke. Ki ka k'i fur ki ba mu yarinyar nan lokacin
da 'dan uwanmu Adamu ya rasu. Amma Aisha ki ka yi fur ki ka hana, wai ke 'yar ki karatu za ta
yi, Adamun ya baki wasiccin ki bar yarinyar tai zurfin karatu. Toh yaro dai iyayenshi sun gama
bincike sun ce 'dan su bazai auri yar boko ma'aikaciyar gwamnati ba, 'yan bariki masu
budadden idanu. Shine ni da Bala wan mahaifin Aliyu 'dan gidan Yaya Asabe, mu ka yanke
shawarar a 'daura auran da shi Aliyun kawai 'dan wajan ki Yaya. Kuma Alhamdullah, Malam
Bala shi ya amshi Auren har da sadaki nera dubu uku ga su."
Yaya Asabe ta soma rabka salati tare da fashewa da kuka tace.
"Shikenan ni Asabe na shiga uku. Sai da yarinya ta zama 'yar duniyar da a Birni ma ta kasa
auruwa, sau uku wannan ne na hu'du ana fasa aurenta. Shine Bala za ka cuce ni ka Aura ma
K'usar Yaki ita? Aisha fa sai da ta tabbatar ta raba Adamu da kab danginsa da asirinsu irinna
mutan katsinawa, wacce iriyar azaba ce ba ta bamu ba, amma yanzu k'usar Yaki aka aura ma
Sadiya? Wallahi bazan yarda ba." Kawu Sulaiman ya ce. "Yaya ki yi hak'uri, ni kai na na ji abun. Kuma kinga Sadiya ta girmi Aliyu da kusan shekara
biyar. Goggo Safiya tace.
" Ai juya shi za ta yi, tai ta yi mai wayo. Ni na tabbatar sai abunda Sadiya ta ce da Aliyu. 'Yan
boko fitsararru da ba zaman aure su ke yi ba. Sun fi so a barsu sakaka sui ta cu'danya da maza
wai abokan aikinsu. Kawu Bala ya ce.
"Yanzu dai bakin alk'alami ya bushe, ni ne dai Wan mahaifin Aliyu kuma ni ne madaurin Auran
shi, ni kuma na amshi Aurannan domun a rufa ma Adamu asiri, shi da ya mutu ya bar baya da
k'ura. Yarinya ta yi kwantai kowa na gudun na shi ya aure ta. Asabe hak'uri za ki yi dan Allah.
Goggo Asabe ta ce. " yaronnan fa, da rana a kan shi. Daya dawo da wata d'aya za'ayi auran shi da Khadija 'yar
gidan mai gari, yarinya ga mai dambu Aminiyata. Wallahi aure kuma ba fashi." Kawu Sulaiman.
Ya ce.
"Wannan ba zai gagaraba yaya Asabe, yaro zai yi auran shi duk macen da ya ke son Aure."
Goggo Asabe tace.
"Shikenan yaya zan yi, cuta ce dai an riga da an cutar da ni. Yaro sai da ya zama mutum
tukunna, duk wata kadarata, da gadon da shi kan shi yaron ya samu, duk ya k'are a wajan
naiman ilimin addini shine har Madina. Amma zai dawo ya samu mummunan labari, wallahi
bazan yi wuyar renon Kusar yak'i, da gina shi, Sadiya ta hanani cin arzikinshi ba. Tunda
Adamu ya fa'di ya mutu, Aisha ita da 'diyarta ne ka'dai su ke amshe ku'din pension d'in nashi da
garatuti. shikenan na yi Allah ya sanya alkhairi." Cikin kuluwa da takaici Goggo Hansatu tace.
"An d'aura auran yarinya, babu wani shawara. Toh ya maganar aikinta da take yi na asibiti, daga
can kauyan za ta dinga tawowa ko yaya? Sannan ya yarinya zata rayu a maraya, wayayya, mai
ilimi, ma'aikaciya, sannan ita ba yarinya ba. Kawai a d'aura auranta da wani Wai shi Aliyu. Ai ta
na da hakki ya kamata aji ta bakinta, koma meye sai a yi daga baya. Sannan Sadiya ba yarinya
bace, ta girmi Aliyu nesa ba kusa ba, wanne irin zaman aure za su yi to? Aure ba soyayya,
kuma a kaita kauye shikenan a dur'kusar da rayuwarta, ba za'a barta ta amfanar da al 'umma
da ilimin data karanta ba? Wai me yasa ake ganin illa ne mace ta yi ilimin boko ta yi aiki, dan ta
kare martabarta ta mace, da martabar k'asar ta. Mu gidanmu 'yan boko ne, kuma dole Sadiya
za ta ci gaba da aikinta." Kawu Sulaiman yace.
"Ke dakata Hansatu, wannan ba huruminki bane, ko Aisha bata isa ta tanka mun ba kan batun
Sadiya. Domun ni ne uban Sadiya, duk duniya bata da gatan da ya wuce mu. Yarinyar nan
zumunci mu ka yi ma, har aka ba ma shi Aliyun domun naga anan taki auruwa, ga shi sai girma
take yi, shakaru takatin fa da biyar ai ta gama tsofewa a gida. Maganar aiki ma ajjiyeshi za ta
yi, mu abunda muka sani shine 'd'akin mace shine darajarta. Mu daraja mu ka ne ma mata."
Yaya Asabe ta cabke cikin daga murya tace.
"Zancan kauye kuma da kuke yi, ai Adamu daga wannan kauyan ya fito kuma Aisha ta aureshi
ta raba mu dashi, ko san zuwa ganin gida ba yayi. Itama dole ta je ta yi zaman aure." Goggo
Hansatu za ta yi magana Aisha ta d'aga mata hannu, dole ta yi Shiru, zuchiyarta na yi mata
k'una. Cikin raunin murya tace.
"Yaya sulaiman Sadiya 'yar ku ce, kuma kune gatan ta. Ni ba ku da matsala dani, Allah ya
sanya albarka a wannan auran, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a gare mu baki d'aya." Ta
na kai wa nan ta fice a d'akin. Goggo Hansatu kuwa ba karamin rikici su ka yi da su Goggo
Asabe ba. Har sai da 'yan Uwa aka shiga zancan sannan fa aka yi sulhu. Kawu Sulaiman yace. "Safiya ina ga kuje ku tafi kai kayan Sadiyan ko? Kawayen ita Sadiyan suna wajen motar su
na jira. Hansatu kuma ki kirawo ta ku tafi tare. Barayin Dauda daya gina zai sa amaryar sa nan
da wata biyu shi
Za ku yi ma Sadiyan jere in yaso shi Dauda ya gina wani. Kui maza rana na yi." Goggo safiya
ba ta ce komai ba ta bi umarnin Kawu Sulaiman. Goggo Hansatu ta dubi kawayen amarya
tace.
"Toh
Su waye 'yan kwana domun in fa mu ka je acan za'a kwana waje ba kusa ba?" Hadiza ta ce.
"Ai ina ga ni ka'dai ce zan kwana, sai Amina ko?" Zainab tace.
"Gaskiya kam ni kam sai dai gobe ma bi ayarin 'yan budar kai mu zo ganin d'akin amarya."
Goggo Hansatu ta yi ma su Hadiza jagora cikin motar da za su ta fi. Da ita sai Goggo Safiya, sai
Hadiza, da Amina. A gaban mota kuma daga direba sai Anas wan Aliyu. Motar su Goggo
Hansatu na gaba. Motar kaya na biye da su a baya. Mahaifiyar Sadiya na dakinta, hawaye kawai ta ke ta faman sharcewa wa. Hankalinta yai
matuk'ar tashi, shin wacce rayuwa Sadiya za ta yi a kauye, gashi an aura mata miji yaro,
maganar aikinta kuma fa, shin karatun da su ka da'de suna wahala domun samuwarshi, yanzu
gashi ya samu har ta kai matsayin ma'aikaciyar asibiti, shikenan dangin mahaifinta sun dakatar
mata da cikar burinta da manufarta kan karatun d'iya mace?.
"Ya Allah kai ne ubangijin kowa da komai, ya Allah ka saukar ma da Sadiya nutsuwa da
dangana, ya Allah ka sa aurannan na ta ya zame mana alkhairi, ya Allah ka raba Sadiya da
makiyanta masu son ganin bayanta, Allah ka kawo mata sauyin alkhairi." Sauke hannayenta da
ta 'daga tayi, ta na zubar da hawaye. Ta rasa dalilin da yasa dangin mijinta su ka tsane ta. Dan
kawai ta zama 'yar boko kuma ma'aikaciyar gwamnati. Shin shi ilimin Mace laifi ne, ko kuwa
kasancewarta ma'aikaciya zunubi ne?" Mi'kewa ta yi, ta share hawayenta. Cikin dakewar
zuchiyata ta tura d'akin da Sadiya take a kwance.
Sadiya
Idanuna na runtse domun har zuwa lokacin a cikin fargaba da taraddadin abunda ka je ka zo
na ke. Bansan me ke faruwa ba, kuma bansan a wanne matsayi na ke ba a yanzu, matar auran
da igiyoyi uku su ka rataye rayuwarta, ko budurwar da ta gaji da kwanciya a gado ita ka'dai,
cike da matsananciyar sha'awa da shaukin jin dumin mijin halali a tare da ita?" "Sadiya!!! Ki sa me ni a d'aki yanzu." Juyawa ta yi ba tare da ta ji amsar da zan bata ba. Jiki a
mace tamkar kazar da ta taka wu'ka haka na mi'ke.kawayena su kuma sai aikin zolayata su ke
yi. Wai tun kamun a kaini har na riga da na karaya. Da dariyar ya'ke kawai na bisu. Ahankali na
dinga ratsa jama'ar biki ina bin sawun mama. Kallon da jama'ar bikin su ke bi na da shi, sai na
lura ya wuce gaban misali. Take zuchiyata ta shiga kokawar fitowa da k'arfin tsiya.
*Mrs Bukhari Ibrahim*
*GISHIRIN*
*ZAMAN*
*DUNIYA*
_Daga Al'kalamin_
_Badi'at Ibrahim_
( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)
GAWURTATTU BIYAR í ¾í´ší ¼í¿» TAKUN FARKO:
Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace
ya ke bayarwa ga al'umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure.
Wannan Labari true life story ne, duk abunda na rubuta, abune daya faru a zahiri, sai d'an
k'alilan dana canja, kamar sunaye, da sauransu. Ku bini a sannu, akwai d'umbun darasi sosai.
Kashi na farko
Babi na 3~4
Da sanyin murya na yi sallama a k'ofar 'kuryar 'dakin mama. Ban ma jira amsar sallamar da na
yi ba, na kutsa kai kawai. Idanu ta zuba mun, ta na ko'karin karantar yanayi na. Kaifin tsinin
idanuwanta ne ke mun yawo a jikina. Zuchiyata ta shiga cikin taraddadi. Domun bansan meke
wanzuwa ba, jikina ya na ba ni babu lafiya. Gwauron numfashi mahaifiyata ta sauke ta ce da ni. "Sadiya! Ga waje k'araso ki zauna, domun ni da ke inaso mu tattauna sosai." Hantar cikina
tana kakkarwa na k'arasa in da ta nuna mun da manuniyarta. Zama na yi, kai na a k'asa, jikina
kuwa sai bari ya ke yi. Takowa ta yi, ta zauna ta na fuskantata."
"Sadiya" ta kira sunana da babbar murya."
"Kinsan irin power d'in da dangin mahaifi su ke da shi, kinsan irin rawar da su ke takawa?"
Cikin daurewar kai na dubeta, sam ban yi zaton jin wannan Kalmar da ga bakinta ba. Lumshe
idanu na yi, ina tunanin dangin Babana sun ci mutumcin mama ne kamar yanda su ka saba. A
sanyaye na ce. "Dangine da su ke jibantar al'aumara, kuma sai da su komai ke iya gudana. Da amincewarsu
komai zai iya faruwa, domun da uba ake ado, su guma dangin uba. In ba mahaifi da su zaka yi
ado. Amma mama......" Hannu da d'aga mun halamar bata son jin tambaya. Mu'kut na ha'diye
tambayata. "Sadiya! Ahmad iyayenshi ba su amince mishi ya auri 'yar boko ba. A sakamakon haka ya fasa
auranki." Nunfashi naja tamkar wacce aka zare ma rai haka na kasance na wucin gadi, ji na yi
kalmar da mama ta jefomun tamkar bulalace wacce ta zane rayuwata tai mata dukan da baza
ta iya boruwa a gaba ba. Iya so ina yi ma Ahmad, Allah shine masanin tsantsar son shi da ke
raina. Wasu dun'kulallun hawaye ne su ka fashe a kumatu na. Ta ke zazzab'in da ya ke ta
shirin kada ni ya samu nasara, har wani turirin zafi ne ya ke busowa daga jikina."
"Amma dangin mahaifinki da su ka fini iko da gadara akan ki, ba tare da sun girmama