Gishirin Zaman Duniya Book 1 Mrs Bukhari

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   15 / 33

42K to 45K   out of 98.4K words

yasha jinyarshi, dan gabanshi tsattsagewa yayi. Ya kamata
fa ku hankalta da kyau mata.
Ajjiyar zuchiya na sauke, domun na gamsu da maganganun Dr, kuma ina tunanin abunda ya
faru kenan da su Aliyun, dan ni a daren lafiya lau muka rabu.
Dr ayi ha'kuri, Amarya ce, wata k'ila tasha abunda yai mata yawa ne. yanzu haka mai gidan
nata yana d'akin jinya a wannan asibitin. Amma wanne magunguna za'a d'aurata akai?
"mu na ta k'ok'arinmu dai a kwai tesses da mu ka yi, basu fito ba tukunna. An d'aurata akan
magani, da mayukan shafawa, yanzu jinyar raunin da taji zata yi, dan raunin da yawa."
godiya nai ma likita. na koma wajan Aliyu.
Kawu da Anas na gani a d'akin, sunyi tsaye akan Aliyu sun balbaleshi da fad'a. Isowa ta wajan
yasa, fad'an da kawu ya ke yi, ya dawo kaina. Har marina sai da kawu yayi, ya zageni ta uwa ta
uba. Gefe na koma kaina a 'kasa ina shirgar Hawaye. Ala tilas su ka tursasama Aliyu sai ya
tashi sun koma gida. Aliyu shi kuma yana ta k'ok'arin fahimtar da su Amma fur Kawu ya ki. Dole
muka ne mi sallama, mu ka koma gida.
Goggo ta balbaleni da ruwan fad'a, ta uwa ta uba itama tai mun.
D'akinta ta buk'aci Aliyu ya koma da zama, khadija kuma mai dambu ta tafi da'ita jinya gida.
Magunguna kala kala na gargajiya ake ta d'irkama Aliyu. jama'ar k'auyannan sai tururuwar zuwa
duba Aliyu su ke yi. Ni da Aliyu sai kallo, dan Goggo ta kafa ta tsare. Kullum wanzan yana zuwa
duba lafiyar Aliyu. magunguna dai yana shansu sosai.
*BAYAN WATA D'AYA*
har zuwa lokacin Aliyu jinya ya ke yi, amma dai jiki da sauk'i ya na ta warkewa.
kamar kullum yauma ina zaune a gaban Aliyu Goggo bata nan, ta je dubo khadija. hannuna ya
na cikin na Aliyu ina wasa da shi, shi kuma sai jawo ni jikinshi ya ke yi.
Ka yi hakankali, kar ka fama ciwonka fa." murmushi yai mun yace
"Ina kewarki ne sosai, kuma na yi na yi da Baba ta barni in koma d'akin ki, amma fur tak'i
amincewa."
Tsoro take kar mu keb'e mu famo ciwon da rashin hak'uri. Inka warke ai shikenan. Amma ya
kake jin jikin naka? yamutse fuska yayi, tare da yaye mun tsumman da Anas yake rufa mai.
Babu laifi ciwon na warkewa, har ya soma b'awo b'awo. Kuma nima akwai had'i na musamman
da na yi mishi, dan farfad'o mai da kuzarinshi, a islamic kemist na harhad'o gasu kamar haka.

man zaitun
man habbatus sauda
man tafarnuwa
man kwakwa
man rid'i
zuma farar sak'a
garin hulba
da man shi
sai garin b'aure
da
garin ruman
dukka na cak'ud'a waje guda, nake bashi babban cokali uku da safe kafin ya ci komai
maganine sadidan, wanda yake farfad'o da sha'awar d'a namiji, kuma ya ke k'ara masa lafiyar
wajan, har da ma k'arfi.
masha Allah dan muna ganin canji, dan in ina tare da Aliyu, yana jin feelings, kuma yana
nunawa, amma ba sosai ba. Babu wanda yasan wannan batun, wannan tsakaninmu ne kawai."

Gidan su Khadija
Goggo ce a zaune a falon mai dambu.
"Sai yaushe wai yarinyar nan zata koma d'akinta ne mai dambu? naga ai jikin fa da sauk'i, yaci
ace ta koma ai ko? amma kin mun shiru sabida Allah fa."
mai dambu ta b'ata fuska tace.
"Toh Asabe, ki bari wannan yaro ya samu ya warke mana, ba gara tana gabana ina ganin komai
ba. Kofa ta koma gidannan sai dai kawai ta yi zaman hak'uri, sabida yaronnan fanko ne."
wannan magana ta daki Goggo Asabe sosai, cikin zafi tace.
"Fanko fa ki ka ce mai dambu, har Aliyu ya kai matakin a soma yi mishi gori, sabida asirin jikin
naki 'yar ya karye ko? Da kyau, ai na jima da gane duk take taken ki, nason ganin kin hana
khadija komawa d'akinta. Da kyau Mai dambu, kuma kin ban mamaki, bayan da duk shawararki
nayi amfani har kika jefa mu a cikin wannan halin shine yanzu kike son zuk'ewa . mai dambu tace
"Amma Asabe ni kin ban mamaki ma da har kike tunanin wai khadija za ta komawa Aliyu.
Tsakani da Allah auransu bazai ci gaba ba, mahaifinta ma haka yace. Babu fa iyayen da zasu
amince akai 'yarsu, wajan mijin da bazai iya gamsar da ita ba. Ai aure baya yiwu ne sai da
lafiya. Ina fatan Allah ya bashi lafiya, ita kuma Allah ya b'ullo mata da wani mijin, tunda itama
tace bazata koma ba, babu mai yi mata dole kuma ehe"
"mai dambu kin cuceni, bazan fasa maimaita tsinuwa akan ki ba. kuma zaku gani, shi alhaki
kuikuyo ne, sharri kuma d'an aike ne, duk daren dad'ewa zai dawo maka. Za'a aiko ma da
khadija takaddarta."
"Asabe kenan har ya fad'amun sharri d'an aike ne? Ai ko yanzun ma aikenshi kika yi ya dawo
miki, itama Sadiyan ai rai gareta. 'yar d'an uwanki baki ji kunyar cutar da'ita ba, sai khadija ce
bazai cutar ba nan gaba, ai mugu shi yasan makwancin mugu.
Aranar dai saida Goggo Asabe su ka yi dambe da Mai dambu, suka tarama kansu jama'a da
k'yar mak'ota da kishiyoyin mai dambu suka raba wannan dambe na aminai.

Fita Goggo ta yi ta na kuka, a b'arayin Goggo Safiya ta ya da zango.

Sadiya
ina jikin Aliyu mu na ta hirar mu abun sha'awa, kamar kar Goggo ta shigo haka mu ke ji.
Bakinshi ya danna a cikin nawa. tsotsa ya ke yi tamkar ya samu Alawa, gam ya rik'eni, kamar
za'a kwace ni. Munfi minti goma a haka ni da Aliyu, sannan na samu na kwaci kaina da kyar.
Aliyu, tun jiya na ke son mu yi magana da kai, Amma ban samu damar hakan ba."
sake gyara mun zama yayi a gefenshi, muka sark'e hannayen mu a cikin na juna.
"Ina sauraron ki Sadiya ta, menene?"
Dama uhm juna biyu gareni. wata zabura Aliyu yayi, tare da sake damk'e hannuna.
"Da gaske ki ke yi Sadiya?"
Eh da gaske na ke yi, duk wani halamu sun nuna hakan, ga kasala, da yawan yin amai, kuma
abu kad'an da na yi sai in ji duk na gaji."
Rumgumeni tsam Aliyu yayi a k'irjina, yana wani murna mara misaltuwa
"Sadiya nagode, Allah yai miki Albarka, yanzu nine na kusa zama Abba? Allah na gode ma
daka azurta ni da samun rabo.
ni dai kaina na sunne a k'irjinshi, kunya na ta kamani.
d'agoni yayi, yana kallona.
"Me ki ke so in miki Sadiya?" Dubanshi nayi da kyau, duk ya wani rud'e sai lallab'ani ya ke yi."
Aliyu, so na ke yi, in dinga zuwa asibiti awo, sannan inaso in haihu a asibiti. Aliyu sannan dan
Allah kar a kai yarona almajirci dan Allah.
hawaye na soma zubarwa, dan bazan iya haifar d'a a cikina akai mun wata uwa duniyar ba.
bani da wannan juriyar d'a yafi gaban ai wasa da rayuwarshi. Sake rungumeni yayi yana
rarrashina.
"ya isa Sadiya ki dena kukan haka. na miki alk'awarin zaki je asibiti, kuma zaki haihu a asibiti,
dake da Babyn bazan so wani abun ya same ku ba. maganar Almajirci kuma, zan iya iya
k'ok'arina, dan ganin yaranmu sun rayu a gabanmu. Sadiya ina samun lafiya zan bud'e
makaranta. yarana a tsangaya ta za su yi karatun arabic d'insu. Kuma ina da tabbacin za ki
koyar da su boko. uhm haba maman twins." Dariya muka yi. na sake mak'alk'ale mijina

mrs Bukhari ce

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. ‍♀️*




1, *MU GANI A ƘASA...*
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*‍❤️‍
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya

0810 433 5144

Masu tura katin MTN

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* ‍❤️‍

Instagram links

https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Facbook group

https://facebook.com/groups/463653111781414/


Telegram links

https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk


*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google
za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
[8/14, 8:36 PM] Badiat Ibrahim: G Z D
MRS BUKHARI

35~36


"Wai yaya Asabe, lafiya? tunda kika shigo ki ke ta runtuma kuka. Kuma naga jikin Aliyu ai da
sauk'i sosai. Goggo Asabe tace.
"hmmm Safiya bari, mai dambu ce take so a raba Auran Aliyu da khadija, ki duba duk irin
hidimta musu da Aliyu yayi, wanne irin so ne ban nuna ma khadija ba, dama ita kanta mai
dambun? Har gori take yi, wai Aliyu bai da kuzarin iya gamsar da mace, Bacin duk khadijan ita
ta jefa shi a cikin wannan kaddarar." mamaki ne ya kama Goggo Safiya ainun, domun in ba dan
a bakin Goggo ta ji wannan labarin ba, toh da k'aryatawa za ta yi tsab."
"Yaya ita mai dambun ce ta ce hakan, ko kuwa har da mai gari?" majina Goggo ta share tace.
" mai dambu ta sanar dani, shima kanshi mai garin yace, Aba khadija takaddarta. duk irin kud'in
da Aliyu ya narka ma khadija a lefenta. Sannan kuma fa, sun kwashe adakar baki d'aya." Goggo
Safiya tace.
"Tunda haka su ka zaba, Yaya ni ina ganin a basu takaddar, tun kafin a yi rikici, kinsan mai
dambu ba mutunci gareta ba."
"Ni babbar damuwata shine, Aliyu zai rayu ne a cikin damuwar rashin magaji, ko dad'in Aure
d'and'anashi yayi kawai na d'an lokaci. Abun yana damuna Safiya. Duk da wanzan yana ta
k'arfafa mana guiwa akan hakan"
Sun jima su na tattaunawa, sannan Goggo ta koma b'arayinta.

Sadiya
Da sauri na fita daga jikin Aliyu, zuwa can gefe in da na saba zama. Goggo ce ta shigo, duban
Aliyu ta yi.
"Kai kuma lafiya kake dariya haka?" cewa yayi zauna Baba.
Xama Goggo ta yi kusanshi.
"Goggo Allah kenan mai k'arfin iko akan dukkan bawanshi, Allah ya k'addari zaki samu jika
daga gareni." Sororo Goggo take kallonshi tace.
"Banfa gane komai ba." Hannunta ya kama yace
"Baba Allah ya axurta Sadiya da juna biyu." Da sauri nai k'asa da kaina. Ina sauraron shin
wanne irin farin ciki Goggo zata bayyawa. Fashewar kukanta mu ka ji. Daga ni har Aliyu mun yi
tunanin kukan farin ciki ne. Ashe sab'anin hakanne."Shikenan ta faru ta k'are, zamu sake
cud'anya da Aisha ni Asabe, sai kuma yanda su ka yi da Aliyu." kuka ta ke yi sosai. mamakine
ya cika ni, take wasu zafafan hawayen bak'in ciki su ka shiga sunturi a kumatuna, gashi na na
kasa mik'ewa dan jikina har rawa ya ke yi, tsabar jin haushi. Aliyu kuwa ganin zubar hawayena,
duk sai ya rud'e ya rasa wacce zai rarrasa a cikinmu, Yace"
"Baba mu fa muka yanke k'auna da samun rabon d'a, sakamakon abunda ya faru da ni, ni na
zaci murna zaki yi Baba, a tunanina komai ya xo k'arshe." Tana kuka tace.
"Yanzu komai zai fara Aliyu, ita kanta Aisha sai da ta haifi Sadiya ne, boka ya bata nasarar raba
mu da d'an uwanmu. Bazan zuba ido haka ta faru da ni ba. Bana farin ciki da samun juna biyun
Sadiya, dan juna biyunnan barazana ce ta rasa gudan jinina." mik'ewa Goggo ta yi, tare da
shiga cikin uwar d'aki, a bakin gado ta zauna, ta shiga tunanin meye mafita, mai dambu ce ta
fad'o mata a rai, Amma sai ta tuna da irin yanda suka kashe baran baran, amma lallai ta k'udirin

niyyar zubar ma da Sadiya cikin dake jikinta, ko kuma ta tilasta mishi ya sake ta. Tabawa
k'awarta ce ta fad'o mata. wani murmushin mugunta ta saki."
Ni kuma, da kyar na samu na yunk'ura zuwa tsaye, dan duk wata lakar jikina, ta gaza ba ma
jikina sapot d'in daya dace.
Aliyu ne ya kira sunana a hankali, sai da tsigar jikina ta tashi.
Ahankali na juyo ina kallonshi, shima a cikin tashin hankalin yake, idanuwanshi su na dab da su
zubo da ruwa, sun kad'a sun yi jawur, tausayinshi ne ya kamani, duk ta dalilina ya kasa jituwa
da mahaifiyarshi. Ina ganin barin gidannan shine A'ala a gareni.
"Sadiya ki yi hak'uri kinji, kar ki sama kanki wata damuwar kinga ba ke kad'ai bace." runtse
idanuna na yi, nace.
Aliyu ka yi hak'uri bazan iya ci gaba da zama da kai a cikin wannan halin ba, Goggo bata sona,
yau na sake gasgata cewar har abada baza ta soni ba, bazata amshi jika daga gare ni ba. tafiya
zanyi."
A guje na fita a cikin d'akin. ina jiyo muryarshi da k'arfi yana kirana.
Da sauri Goggo ta fito daga d'aki, hawaye ta samu yana zubarwa. Tare da kung'urin tashi.
"Kar ka kuskura ka taka k'afarka daga cikin d'akinnan. Sabida k'anwar uwarka tana kuka shine
kai ma kake ta ya ta ko shanyayye? Aliyu ka ji kunya wallahi. Ina saninka ya tafi ne? an gama
birkita maka rayuwa da asiri, wama ya sani ko ba cikin ka bane ma, har kake wani b'are b'are.
Toh babu inda zaka fita ka bita. Tafi ruwa gudu, ta kaima duk uban da zata kaima k'arata. Inji
sammaci a kotu, tunda su 'yan boko ne, masu sanin hakkokin kansu.
Ina shiga d'aki na soma harhad'a kayana iyakar wanda zan iya d'auka. Hijabina na zura, fitowa
nayi tare da kulle b'arayin nawa. Hawaye kuwa ya gama wanke mun fuskata, ga wani
matsanancin ciwo da kaina ya ke yi mun. K'ofar baya na bi nai ficewata.
wajajen Azahar Babur d'ina ya sauke ni a bustop, motar dake kan lodin zuwa zamfara na shiga.
Na galabaita ainun, har amai sanda na yi. Ina zaune a motar nan shiru, ina tunano maganganun
Goggo da irin k'iyayyar da take yi mun ni da mahaifiyata. Yau ina ma Baban da ake magana ma
a kanshi? Babu ya kwanta dama, amma ace har zuwa wannan lokacin su Goggo baza su xubar
da makaman ya'kinsu da mahaifiyata ba. A ganina tsantsar son da zan nuna ma Aliyu shine in
fita a rayuwarshi ya samu daidaito da mahaifiyarshi, duk da akan daidai yake, amma mahaifiya
tafi gaban a dinga jayayya da ita, kullum tana cikin fishi da Allah wadai a kan ka. Girman uwa
yafi gaban misalin da za'ayi wasa da furucin da zata dinga fad'ama marasa dad'i, kullum a
hassale take da kai. Hakan sai ya tab'a maka rayuwa ta yanda baza ka samu albarka rayuwa
ba. Babban farin cikin ka yau shine, iyayenka ka yi duk yinka ka rabu da su lafiya." Idanu na
lumshe, motar mu kuma ta hau tafiya. wani nishin kukane ya taso mun, ina ganin nayi nisa da
Aliyu. Da kyar na sa harshe na danne kukan, sai wasu wahalallun hawaye ne su ka gangaro
mun, da sauri na sa hannu na share su.
Misalin k'arfe hud'un yamma motar mu ta shiga cikin tasha, inda ake lodi gari gari, sa'ar da na
yi, motar kano saura mutum guda su ke jira, ina shiga mota ta cika, mu ka d'auki hanya, sai
kano."

Aliyu
jagob ya zauna, kan shi har wani juyawa ya ke yi, kalmar da goggo ta fad'i game da cikin
Sadiya yafi gomai d'imauta shi, dolen shi ya cire kunya ya fayyace ma Goggo a yaya ya samu

Sadiya.
"Baba kar ki sheganta mun jini, wallahi Allah Baba, Sadiya na sameta a matsayin cikakkiyar
budurwar data tsare kanta, tai ma mijinta kyakkyawan tanadi, khadija ce ban sameta a hakan
ba ma. Amma na rufa mata asiri ko ita bata san da hakan ba, cikin nawa ne." kukan shi ya ke
son had'iyewa dan gudun kar Goggo tace, Sadiya ya ke yi ma. "Na ji ka sameta Budurwa. ka sani, indai jika daga tsottson Aisha zai samu, harko duniya ta
nad'e bazan k'aunace shi ba, nama gwammaci ace baka da d'a Aliyu. Son da kake ma Sadiya
ya wuce kimar da za'aimai kallon hankali, dubi fa yanda ka gigice dan kawai ta ce ma zata tafi,
tunda khadija ta koma gida sau nawa ka tambayeni ita, ko ita ba matarka bace? Ahir d'inka
dani." yaya Fatima ce ta banko cikin d'akin tana kururuwa, Goggo tace.
"Ina fatan ba dukan ki yayi ba? dan in dukan ki yayi, mai rabani da uwarshi Habi sai Allah." cikin
shesshek'a Fatima tace.
"Saki na yayi Baba, shikenan dama shekarun baya ya mun saki d'aya, yanzu kuma ya mun saki
biyu, ya rabani da yarana Baba."
Duk kurin Goggo sai da wannan mutuwar Aure ya jijjigata. D'akin ya d'auki shiru na fin minti
goma. Ko wanne a cikinsu da abunda ya ke sak'awa."
Tabawa ce ta doko sallama tare da shigowa a tare. Goggo ce ta amsa mata, Tabawa ta bi kowa
da ido"
"Lafiya ciwonne ya tashi ko yaya?" Goggo ta nisa tace."
"Ko d'aya, ita wannan sakinta mijinta yayi, shi kuma

15 / 33