Gishirin Zaman Duniya Book 1 Mrs Bukhari

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   30 / 33

87K to 90K   out of 98.4K words

yi tare da saurin
mik'ewa. Ficewa na yi daga d'akin ina kukan da hawayena ya ke 'kok'arin makanta ganina.
Da Innah na ci karo, kuka na fashe mata da shi, ba wani kawaici da zan iya ci gaba da yi,

domun cutata hakan zai yi. Duk wata kunya dole na shureta gefe, ina kukan fitar hayyaci,
muryarta ma sai katsewa ta ke yi.
In nah, D'ana na ke so in karb'o zuchiyata ba za ta samu nutsuwa ba. A bani in shayar da
Jaririna, d'uminshi kawai na ke son ji. Wallahi Innah shima ya fi buk'atata..
Kukane yaimun illar da dole na yi shiru, sai kuka da na ke ta rintimawa. Innah da Anty Jamila da
za ta mun wankan jego su kai shiru, Anty Jamila ce ta ce.
"Sadiya ki yi hak'uri, dukkanmu iyayene mu san irin zafi da rad'ad'in da ki ke ji. Amma ki yi shiru,
bari Safwan d'in ya dawo, ni da kaina zan karb'o miki Jaririn in kawo miki. Na rok'eki kar ki je
b'arayin da Badiyya ta ke, dan kin ga Safwan shi ya ba ta Jaririn da hannun shi. zai fi kyau ace
shi ya karb'o miki Jaririnki." K'uta Innah kawai ta yi ta ce. "Shige ai miki wanka Sadiya, ki bar komai a hannuna, bazan zuba ido Safwan ya salwantar miki
da hakkinki ba."
Ban d'akin na wuce ina sharar hawaye, ga nonuwana sun yi mugun nauyi, sun ciccika da
mama, har zuba su ke yi. Take nonon su ka sakarmun da wani mugun zazzab'i mai zafin
gaske."

Safwan
Jiki a sab'ule ya shigo gidan, matan gidan kowa ya yi jigum jigum a cikin tausayin Sadiya, tare
da ganin rashin kyautawar Safwan da ita kanta Badiyya. Anty Jamila ta ce.
"Yauwa Safwan kai na ke ta zurga zurgar jira, mu je mu yi magana.
Ledar hannun shi ya mik'a ma Anty Zulai ya ce.
"Anty Zulai ga naman k'auri na me jego, itama Badiyya a d'ebar mata, tunda shayarwa za ta
shiga." Hannu Anty Zulai ta mik'a ya saka mata ledar. Ya bi Anty Jamila har falonta.
"Safwan ya yanke hukunci mai tsaurin gaske ita kanta Sadiya ta shiga wani mawuyacin hali na
jin zafi da rad'ad'i, barin fad'ama gaskiya. Babu wata uwa da za ta yadda a kwace mata Jariri
bisa wani dalili mara tushe da kan gado, ko da kuwa wannan uwar a cikin hauka tuburan take.
Yanxu haka Sadiya ta na can kwance a cikin mashassara mai zafi, mamanta sun yi tauri, a ban
d'aki sai da na d'an matse mata su ta d'an samu sassauci, ga kuka da ta ke ta faman yi. Innah
ta yi mugun fishin da za ta iya yin mummunan furuci a kan ka. Ita kanta Badiyya ba za ta iya
rik'e Jaririn a wajanta a na cikin wannan turku_ turkar ba. Abune ko da ya yuwu kamar yanda ka
ke fata. Toh zukata da yawa za su kasance a jagule kuma a cikin rik'o tare da ajjiye miki a
zuchiya mara warkewa sai dai ruruwa. Safwan ka mayar ma da Sadiya Jaririnta." Murmushi
abun ma ya ba shi. Sororo Anty Jamila ta bishi da idanu, da ma fa kowa ya san Safwan da
kafiya akan duk abunda ya sa a gaba, musamman in ya san cewar ba addininshi ya tab'a ba"
"Anty Jamila kenan ni fa mamakin wannan lsmarin na ke yi. Jaririnnan fa D'a na ne, kuma ina
da damar da zan iya kyautar da shi ga duk wanda nai niyya. Kuma Sadiya ta ba ni mamaki da
ta kasa yi mun biyayya bisa abinda na yanke duk girmanshi, balle ma Jaririnnan nawa ne.
Badiyya kuma matatace, tsawon shekaru goma sha uku mu na tare Allah bai ba ta Haihuwa ba,
dan na bata D'a jinina ban yi zaton zai zama damuwa ba.
Anty barin fayyace miki wani sirri. Likitoci sun tabbatar mun Badiyya ba za ta tab'a haihuwa ba,
ita kanta ba ta san da hakan ba, shi tasa nai mata wannan kyautar, kuma ni ba na son Jaririn
ma yasan ba Badiyya bace ta haifeshi ba, duniya da lahira na ba Badiyya Jaririnnan ita na ke so
ta zamo uwarshi. Sadiya hak'uri za ta yi Allah zai ba ta wani, ga Haidar ma.

Ajjiyar zuchiya Anty Jamila ta sauke ta lura Safwan ba zai sauka a kan bakan shi ba, mik'ewa
ma ya yi ficewar shi a d'akin. D'akin Badiyya ya shiga.
Tana zaune a takure a bakin gado, Jaririnta na shan nono. Dubanta ya yi cikin tausayawa,
Jaririn ya fi dacewa da'ita sosai. Idanu Badiyya ta zuba mishi ta na shirin yin kuka. Da sauri ya
k'araso gareta. Waje ya samu kusanta ya zauna."
"Badiyya ki toshe kunnuwanki da duk abunda za ki ji, idanuwanki ma ki runtse su, na tabbatar
babu mai iya kwace jaririnnan a hannunki. Ni kuma kyauta na ba ki shi, na rad'a mishi suna
Adam sunan mahaifin Sadiya, domun in nuna mata godiyata a bisa jariri da ta ba ni." Kuka
Badiyya ta fashe da shi. "Wallahi Safwan so da k'aunar Adam ta shige ni, wallahi bazan iya rayuwa ba tare da Adam ba,
ko ni na haifeshi ban yi zaton zan so shi kamar haka ba. Ka ba Sadiya hak'uri kar ta yi mun
mummunar fassara. Adam zai samu kulawa da soyayyar da ko a wajan ta ba zai sa mu ba. Zan
gina shi bisa tartibiyar tarbiyyar da za ta yi alfahari da hakan bazan iya ba ta yaron ba."
Hawayenta Safwan ya ke ta sharewa.
"Badiyya ba na son kukannan na ki sam ki dena. Kin ga yanda yaron da ke kan ki ku ka yi mun
kyau kuwa, kamar in mayar da ku ciki." Shafa fuskar yaron su kai ta yi, shi kuwa ya sha nono ya
k'oshi baccin shi ya ke yi bawan Allah."
Mik'ewa Safwan ya yi.
"Toh bari in lek'a mai jego da jiki, ba ta jin dad'i zazzabi da ciwon nono ya kamata, ki goya Adam
sai ki je ki gaisheta." Murya a sark'e Badiyya ta ce.
"Nauyi da kunyar Sadiya ba zai barni in iya had'a idanu da'ita ba. Sannan na dai ga su Anty
Zulai sun fita da gado da katifar ta, da kuma kayanta na sawa da sib d'in tata."
Ji ya yi kanshi ya mugun sara mishi, da hanzari ya fice a d'akin, kai tsaye zuwa d'akin Innah."
Ta na zaune a k'asa ta mimmik'e k'afafunta ta na shan fura. Ba ta ko kalle shi ba. Ko
sallamarshi ba dan ta san muhimmancin sallama ba, da bazata iya amsawa ba.
Waje ya samu a nutse ya zauna."




Mrs Bukhari ce
MRS BUKHARI
77/78

"Innah ki yi hak'uri dan Allah a bisa fishi da ni da ki ke yi, ba ku gane manufata na yin wannan
abun bane, wallahi na yi tunanin za ki yi farin ciki a bisa wannan abun sai na ci karo da sab'anin
hakan...
"Dakata Safwan, ka ga maganar nan? Toh ba na son sa ke jinta a kunnuwana, zab'i d'aya zan
baka a cikin umarnin da zan baka biyu, wallahi ka ji na rantse dole ka d'auki d'aya.
Ko ka dawo ma da Sadiya Jaririnta, ko ka sake ta domun ba sonta ka ke yi ba, bazan zura ido
ka salwantar mata da hakkinta ba, amfani da ita kawai ka ke so ka yi na lura."
Tashin hankali da firgicin da ya ke ciki yafi gaban k'awatance, kai ya sake sunnewa, ya na jiyo
k'wak'walwarshi na kad'a mishi k'ararrawar da ta ke shirin salwantar da nutsuwarshi, da

kuzarinshi, ya na son Sadiya so irin wanda ba ya yi ma Badiyya sam, shi manufar alkhairice ta
sa ya ba Badiyya jariri, bai jin zai iya kyautar zobe, kamar yanda ya ke jin in duniya zata taru a
kan shi bazai iya sakin Sadiya ba. Cikin dashasshiyar murya ya ce ma Innah."
"Ki yi hak'uri dai Innah, babu kyau kyautar zobe, ba dai_dai bane in yi ma Badiyya ta lek'o ta
koma ba. Kuma wallahi ina son Sadiya, ni bazan iya rabuwa da'ita ba." Ya na kaiwa nan ya fice
a d'akin, kan shi sai sarawa ya ke yi, idanuwanshi sun zama jawur da su, Anty Zulai ce ta zo
wucewa da kwanon gashasshen nama, wanda aka bad'eshi da farin kwalli. Duban Safwan ta yi,
tare da girgiza kai, har ta gota shi sai kuma ta juyo.
"Safwan ka kuwa shiga wajan Sadiya ka ga yanayin jikin nata kuwa? Jikin sai tsanani ya ke yi
fa. Mamanta ya kumbura yayi him, ruwan da ya ke fitowa ma ya sauya kala, daga fari zuwa
ja_ja. " cikin rud'ewa ya juyo da mugun zafin naman da bai san ya na da shi ba.
"Ina ta ke Anty Zulai, bansan inda ta ke ba ai."
"Ka biyoni wajanta zani." Bin bayanta ya yi, har zuwa cikin d'akin."

Sadiya
Ina kwance sai cije baki na ke yi, ji na ke tamkar mutuwata ce ta riske ni, a cikin azaba na ke
sosai, kirjina kamar zai tsinke dan nauyi, mamana sun yi sutu sutu, sai digar wani ruwa mai kala
su ke yi. Ba ko riga a jikina, sai tsumma da na d'aura a tudun cikina da bai gama sauka ba.
Amma ganin Safwan tsaye a tsakiyar d'akin ya sa a take na had'iye duk wani rad'ad'i da na ke ji.
Kwanciya na yi tare da juya mishi baya. Har ga Allah ba na son ganin Safwan sam_sam, sanin
shi ma ina nadama.
Anty Zulai ta ajjiye kwanon gashsshen naman a gefen gadona."
"Sadiya, sannu, na ga jikin sai tsananta ya ke yi, bari kirawa Yaya Jamila ta zo ta ga ni." Ficewa
ta yi a d'akin, hakan ya ba ma Safwan damar zama a bakin gadon da na ke, ya d'aura
hannunshi a gefen wuyana, kau ya ji zafin jikina. Wuff na mik'e zaune, ina huci kamar wacce ta
ci gudu. Wani rad'ad'ine ya shige ni sosai, sakamakon na fama Mamana." Kar ka sake k'azamin hannunka ya sa ke tab'a jikina. Ka fita a d'akinnan wallahi bana son
ganinka, zan iya zaginka na rantse da Allah." Cike da mamaki ya zuba mun idanuwanshi kawai,
mamakina k'arara a shinfid'e a fuskarshi."
"Sadiya ni ki ke fad'ama maganganu son ranki, akan wani dalili na ki can na sakarci?" Idanu na
ware cike da tsiwar da bansan na iya ba.
Kaine sakarai amma ba dai ni ba. Kuskure na tabka ashe na zab'an tumin dare, ka bani mamaki
da ka iya aure na dan kawai in haifama yara ka kwace ka dinga ba bagidajiyar matarka, ka sani
sai Allah ya saka mun.
Kuka na raushe da shi, na d'aura da cewa.
Allah Sarki Aliyu, kaine ka nuna mun son da babu wanda zai iya min irinshi, kai ka soni da
zuchiya guda, ka sadaukar da farin cikinka domun ka kasance da ni...
"Sadiya baki da hankali ko, a gabana ki ke kiran sunan mataccen tsohon mijinki ko?
Jikin Safwan har rawa ya ke yi, cikin tsawa ya mun wannan maganar idanunshi na kawo ruwa."
Eh na fad'a, Aliyu sabo ne fil a zuchiyata, shi ya soma sanina mace, shiyasa ya fi ko wanne
namiji sanin mutuna da darajata, na yi imani da shine bazai mun haka ba....
Tas na ji saukar mari a kuncina, wanda ya makanta mun ganina na wucin gadi, na ji mugun
zafin marin. Kuka na saka tare da zama a kan gado jagwab, na fama mamana, nan su ka shiga

sabon zugi, amma na ji dad'i na motso ma da Safwan kishi, na tabbatar ya na cikin
cunkushewar zuchiya.
Da wata murya mai rawa ya ce mun.
"Bansan baki da kunya ba sai yau ai, Jariri kuma na kyautar da shi ki yi duk abunda za ki yi.
D'anane ni ke da iko akan kan shi. Ki kula da irin furucin da zai dinga fitowa a bakin ki dan
bazan d'auki rashin kunya ba." Innah ce ta shigo d'akin, ina ganinta na ce."
Ni ka mara Safwan, ga mari ga tsinka jaka?" Innah tai saurin matsowa in da na ke, fuskata ta
d'ago, shatin hannun Safwan ta ga ni kwance a kuncina. A zafafe ta d'ago ta zabga mishi mari,
hawayene ya gangaro a idanun da ya ke kuncin da Innah ta mare shi. Wani abu ya had'iye k'ut,
ya na jin zuchiyar shi na tafasa. Cikin rawar murya da jiki ya ce." "Ta taso mu je Asibiti."
"Ba zata taso ba, ka je abunka. Ko mutuwa Sadiya za ta yi ina ruwanka? Dubi jikinta yanda yai
zafi, ga mamanta na ciwo, ga gyanbon da zuchiyarta ta samu sanadin zaluncinka, amma a
hakan ka d'aga hannu ka doketa, sabida zalunci da son kai na maza." Dubana ya yi idanunshi
tamkar garwashi, ya kad'a kai. Wani zazzab'ine na kishi ke saukar mishi. "Sadiya saka hijabi mu je asibiti kinji?"
Ban yi mata musu ba, dan jikina har rawa ya ke yi tsabar azabar da mamana su ke yi mun.
Hijabi na saka kawai, ta rik'e hannuna mu ka fita.
Yana biye da mu har Asibiti. Rannan na shi a mugun b'ace.
Gado aka ba ni, sauran abun da ya kamata a yi Safwan duk ya yi shi.
Ya na gefe na a zaune ya na mun sannu, wata nose na matse mun ruwan mamana, ni bana ma
cikin haiyacina sam.
Tuni Safwan ya dena fishi da ni ya shiga yi mun sannu cikin tausayawa. Sannun Innah kawai na
ke amsawa.
Magunguna aka ba ni da allurai, da yamma a ka sallame ni.
Mu na zuwa gida na tarad Goggo Hansatu ta zo. Duk hankalin Safwan ya bi ya tashi ainun.
"Sadiya ni na zo banga jaririn ma da ki ka haifa ba, ciwon nonon nan ya sa na sha'afa."
Cikin juyayin me zan ce ma Goggo Hansatu na ke, ina ganin kamar za mu daidaita da Safwan
ya mai do mun da d'ana. Dabara ta fad'o mun na ce mata."
"Sabida maman nawa ya gurb'ace ga ciwo kuma, shine Badiyya ta taimaka mun da shayar da
Jaririn, mu je ki ganshi ya na wajanta." Duk wannan maganganun da na ke yi cikin dariyar yak'e
nake yi.
Idanu Goggo Hansatu ta zuba mun kawai ta yi murmushi.
"Sadiya ta yaro kyau ta ke yi ba ta k'arko. Ni uwarki ce, bazaki tab'a ninkeni bai_bai ba. Ki sanar
da ni kawai me ke faruwa?"

Safwan
"Innah ki dena maganar saki dan Allah ni fa ina son matata gaskiya."
"Sai in tsine maka wallahi akan Sadiya. Ka rubuta mata takaddarta yanzu kafin ka bar
d'akinnan, ka je can ka zauna da matarka Badiyya wacce ta nifi daraja, da k'arfin fad'a ka ji. In
ka yi wata magana anan falon Allah ya isa nonona da ka sha, ka rubuta mata takaddarta."
Safwan gigicewa ya yi sai ambaton Allah kawai ya ke yi, yanason yai ma Innah magana, amma
ta riga da ta d'aure shi da jijiyoyin jikinshi, ta kafa mai dokar da ko hauka ya ke yi bai isa ya

tsallake ba."
_"Ni Safwan na saki matata Sadiya saki d'aya."_
Abunda ya rubuta a takaddar kenan mai kunshe da rubutu rabin layi. Sai sa hannu daga k'asa."
A gaban Innah ya ajjiye takaddar ya fita fuuuu, Turakar shi ya shige ya kulle k'ofar shi. Yana
tunanin fuskar Sadiya, tare da auna sonta a sikelilin zuchiyarshi, tana da babban keji mai girma
a rayuwarshi. Ta ya zai ko yi rayuwa kuma ba tare da Sadiya ba, sannan ya zai yi da nauyin
sonta. Cikin dakiyar zuchiya ya busar da iskar bakin shi, tare da zama a bakin gadonshi." "Itama ba sona ta ke yi ba. Tunda da Aure na a kanta ta na beken mijinta na da matacce ma."
K'ut ya had'ye wani curi mai zafi daga mak'ogorinshi zuwa cikin shi. Gani ya ke yi abun kamar
almara, wai shine ya saki Sadiya yau, da hannunshi ya rubuta takaddar sakin nata"
kwanciya ya yi a kan gado tare da lumshe idanunshi. Zazzab'ine ya saukar mishi bai mugun
zafi, take ya soma jin d'ari. Bargo ya jawo ya lullub'a, hak'oranshi sai kakkarwa su ke yi."

Sadiya
Da hawaye shab'e_shab'e a kumatuka na kamar wata k'aramar yarinya, na ba Goggo Hansatu
labarin abunda ke faruwa."
"Hmmm Sadiya rayuwarki cike da ke da k'addarori masu girma da tayar da hankali. Amma
shawarata a gareki shine in za ki iya zaman hak'uri da Safwan toh, in kuma ba zaki iya ba, sai ki
sanar da shi ya sauwak'e miki.
Amma gaskiya abunda ya aikata zalunci ne, kuma zan fad'a miki gaskiya ba sonki ya ke yi ba.
Bazan so in ganki a cikin damuwa ba, kuma bazan saki a cikin damuwa da kaina ba. Amma ki
san meye matsayinki taka mai_mai a wajan Safwan mata, ko Baby Mama? Domun duk wanda
zai kalli wannan lamarin dole kan shi ya d'aure sosai." Ni dai kuka kawai na ke yi, kuma na fi
gamsuwa da Baby mama Safwan ya d'auke ni, ba sona ya ke yi ba tun farko."
Innah ce tai sallama tare da shigowa hannunta rik'e da takaddar da ganinta ya fad'armun da
gaba, jiki a mace ta ce."
"Hansatu, ke da Sadiya ku yi hak'uri da abunda na zo muku da shi, a nawa ganin hakan shine
maslaha. Wannan takaddar sakin Sadiya ce, da na tursasa Safwan ya sake ta, bisa sharad'in in
bai sake ta ba, saina tsine mishi. Ga takadda ya rubuta. Hansatu inaso Sadiya tai nisa sosai, ta
yanda Safwan ba zai ganta ba sai nan da wasu shekaru, inaso ya san mahimmancin Sadiya a
rayuwarshine, inaso ya san amfaninta, ya kuma reni sonta, yayi begenta, har da damuwar
rashinta kusa da shi."
Sadiya ki yi hak'uri inason in kwatar miki 'yancinki ne a wajan Safwan."


Mrs Bukhari ce
MRS BUKHARI
79/80




KATSINA/JIBIYA:

(Asalin Jibia ya samo asaline tun lokacin yaƙin cin nasara da Sarakunan Katsinq su ka yi, inda
su ka yi hijirar maraɗi da Katsina kan yanki da addini, musamman bayan jihadin Usman Bin
Fodiyo)
Gari ne mai cuɗanyar ƙabulu,

30 / 33