Gishirin Zaman Duniya Book 1 Mrs Bukhari

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   28 / 33

81K to 84K   out of 98.4K words


yi. Innah ta dinga jan Haidar da wasa, shi kuwa da ya ke mai d'an banzan surutune, sai ya sake
da'ita kamar sun saba sosai.
Bayan mun tafi b'angarenmu, a falon Badiyya mu ka ya da zango, kamar yanda ya ke a tsarin
Safwan, duk d'akin da ya ke, toh anan za'aci abinci ayi hira kafin a watse. Muna shiga Badiyya
ta soma murnar ganin Haidar, na ji dad'i yanda kowa ya amshi Haidar hannu Bibbiyu ba
kyama." Dama Kano ka ta fi Safwan shine ko Labari? Dariya kawai ya mun ya na kallona.

"Uhm ai d'aurin Auran Mama na je, an d'aura auran, shine na tawo da Haidar, ta yi mana k'ok'ari
ai." Kunya ce duk ta lullub'eni a wajan har na kasa cewa komai." Abinci mu ke ci, da ya ke miyar
ganye ce sai na ji dad'in abincin sosai, ina gamawa na rik'e hannun Haidar na ce.
Toh mu kam za mu ta fi, bacci na ke ji sosai."
Safwan ne ya mik'e.
"Mu je in ra ka ku."
Sallama mu ka yi da Badiyya, mu ka fice, Haidar na saman kafad'ar Safwan a kwance"
A kan gadona ya shinfid'eshi, har ya yi bacci abunshi, rumgune ni ya yi a jikinshi yace."
"Ya a ka yi ne uwar 'ya'yana, plz ki yi ma Haidar k'anwa mana." Dariya maganar ta shi ta ba ni,
kanshi na shafa na ce.
Lokacine kwanannan za ka ji kyakkyawan labarin da zai dadad'a rayuwarka, ya zama sanyin
idaniyarka."
Cikina ya shafo idanu a lumshe ya ce.
"Allah yasa Uwar 'ya'yana."
Ameen
Saman sib d'ina ya zarce ya d'anyi bincike a wajan, takaddun makarantata ya d'auka ya fice.
Da ido kawai na bi shi, kaya na tub'e, wanka na je na yo, na zura rigar bacci mai sauk'i. Ina
kwanciya sai bacci.
Asuba ta gari


mrs Bukhari ce

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. ‍♀️*




1, *MU GANI A ƘASA...*
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*‍❤️‍
_Miss Hajo_

Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya

0810 433 5144

Masu tura katin MTN

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* ‍❤️‍


Instagram links

https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Facbook group

https://facebook.com/groups/463653111781414/

Telegram links

https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk


*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google
za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
MRS BUKHARI
69-70




Washe gari ma, haka wunin ya k'are mun a daddafe na ke yin komai, dan laulayi na ke yi sosai.
Yau a d'aki na wuni a kwance, Innah da sauran matan gidan sun tafi Bauchi ana bikin Madina
d'iyar Anty Saliha, Badiyya ma ta tafi, ganin ba na jin dad'ine Innah ta ce in zauna a gida kawai.
Na dai ga ta fita ta na d'aga hannayen ta sama halamar ta na godiya ga Allah. Murmushi na yi
dan na fahimci Innah ta ga ne a wanne halin na ke.

Da daddare mu na zaune ni da Haidar, na gama amai kenan na shigo ina nishi, na jiyo dawowar
su Badiyya.
Innah ce ta soma shigowa ta same ni sai ni shi na ke yi, duk na galabaita.
" Sadiya, laulayin ne ya ke baki wahala haka? kai Allah ya raba lafiya.Allah na gode ma in da
rabo ashe zanga jinin Safwan."
Wuff Safwan ya shigo d'akin, Badiyya na biye da shi. Sai murmushi take yi.
"Innah na ji kamar kin ce laulayi ko?" Duk ya bi ya rud'e dan ji ya ke yi tamkar mafarki."
"Eh Safwan laulayi, juna biyu gareta, Allah ya amshi addu'o'inmu
Sujjada Safwan ya yi na godiya ga Allah, ya kusan minti goma a durkuse yana mai godiya ga
Allah. Innah sai sharce hawayenta ta ke yi. Safwan d'ima da hawaye ya d'ago a fuskar shi.
Sannu kawai ya shiga jera mun ya ma rasa ina zai sani. Innah tace.
"Me ki ke son ci Sadiya?" Cikin munfashi sama sama na ce mata.
Tuwo zanji."
"Toh shikenan, Badiyya sai ki je wajan Jamila ta zubo mata tuwo, aiki ai ya same ki, dan ko
tsinke Sadiya ta dena d'agawa a gidannan. Kai kuma dole Sadiya ta koma turakar ka kwata
kwata. Haidar ma tafiya da shi zanyi, jibi zan tafi b'oto da shi zan ta fi."
Sallama ta yi mana, ta ja hannun Haidar su ka wuce.
k'ank'ame ni Safwan ya yi, ya na jin d'umina da na yaron shi a jikina. Sai shafar bayana ya ke yi
kawai.
Badiyya ce ta yi sallama, Anty Jamila na biye da ita.
jikina na zame a hankali, ina jin kunyar wannan terere.
"Masha Allah sannu Sadiya, kai abun murna. An dad'e ba'a shiga murna irin ta yau ba a family,
su Saliha da su Bilki ma duk dai sun ce a yi miki sannu.
Ni dai kaina na k'asa kunya duk ta tufe ni.
Badiyya ta dure mun tuwon a gabana, har sai da Anty Jamila ta fita sannan na soma cin tuwon."
"Badiyya" Safwan ya kira sunanta da
"Na'am" Ta amsa"
"Za ki yi hak'uri zan kasance tare da Sadiya har zuwa wasu 'yan watanni kafin jikinta ya
warware. Ina ga hutu zan d'auka a wajan aiki ko na sati ne. Ki d'ebo mata kayanta a sib ki kai
mun turakata. Gashi da har na sama mata aiki a Babban asibiti na nan, kuma Dr Jibril har ya
d'auketa." Ina jin haka zumbur na gyara zama na nace."
Zan iya amma ai Safwan, wallahi ina son aikina" Shafar cikina ya yi
"Ni ma haka ina son Baby na, hak'uri za ki yi kawai."
Badiyya dai, mik'ewa ta yi abunta ta yi abunda Safwan ya umarce ta.
Tun daga wannan ranar na zama sha lele a gidan su Safwan, dan ina samun kulawa ta
musamman a wajan kowa da kowa. Innah ta na b'oto ita da Haidar. Sai rainon cikina na ke yi
cikin k'oshin lafiya, Badiyya ma na ga k'ok'arinta a kaina, dan har mamaki take bani, ko tsinke ta
hanani d'auka, hatta ruwan wanka in Safwan ya fita ita ke kai mun. Su Anty Saliha kuwa duk sai da su ka zazzo ganina, ni kunya ma duk ta isheni.
cikina na da wata uku
Fitowa na yi da 'yar jakata a hannu, Haidar kuma ya na makaranta. Badiyya na yi ma sallama.
B'angaren Innah na nufa.

Innah na fito zan je asibiti. Baki Innah ta washe ta ce.
"Masha Allah, ko Jamila ta rakaki ne, Sadiya.?" Kai na girfiza na ce.
A'a Innah, Anty Jamila akwai k'ok'ari, kullum sai ta aiko mun da tuwo, ban da su goba da yalo."
"Toh shikenan, ki d'an tattaka a k'afa tunda ba nisa, sabida tsinka jinin na da kyau a wajan mai
juna biyu. Da
Toh" na bi Innah"
Ahankali na ke tafiya har na isa asibiti, kati na yanka, sannan na ja layi, mata ana zazzaune,
masu tsohon ciki, da masu sabon ciki, sai hira su ke yi a tsakaninsu gwanin sha'awa. Zama na
ke da wuya, wata baiwar Allah ta k'araso a galabaice, da k'yar ta zauna, sai da na taimaka mata
ma. "wash wannan ciki ya na bani wuya, ko fa bacci bana yi, Allah dai ya ba mu ma su jin k'anmu"
wannan matar da ta zo yanzu ce ta yi magana, na ce
"Ameen, amma rainon ciki da rainon yaro bansan wanda ya fi wuya ba." Matar nan cikin cijewa
ta ce.
"Kai rainon Yaro ya fi wuya, shifa ciki dududu, wuyarshi ka haihu wata tara zuwa goma. Shi Yaro
kuma, sama da shekaru ashirin kana rainonshi da ceta shi, balle ni da Allah ya jarabceni da
'Ya'ya mata har bakwai. Maza uku, ga ciki kuma. Da idanu na bita ina jinjina ma Uwa, ba ya uwa
a duk duniya. Ji wuyar da ta ke sha amma ga cikin na goma sha d'aya a jikinta. Tabbb mu ma su na biyu kuma fa, ai ba ma tantance komai ba.
Tace
"Kinga baiwar Allah, duk ciki haka ya ke zuwa mun da laulayi, ga fitinar yara da hayaniyar su,
ga hawan jini ina fama da shi, Duk k'ok'arinka kuma Namiji akan k'ank'anin abu sai ya ce ka ga
za.
Da safe in ta ta shi kamar maukaciya haka na ke komawa, in sallami me gidan ya ta fi aiki,
Yaran in sallami 'yan makaranta suma su ta fi, yungu yungun muna tare a gida, wallahi har 'yan
makaranta su dawo ina aiki. Sai sun dawo ne na ke samu in sa d'uwawuna a k'asa, hayaniyarsu
ba za ta barni in d'anyi k'ailulaba, ga makaranta ina zuwa ta adults education dan yak'i da
jahilci, yanzu haka na kusa kammala sakandare, kuma zan fad'a tsangayar ilimin likitanci.
Rayuwar mace bata tafiya da kyau sai da ilimi, yawan yara bazai hana ka karatuba, ko dan ka
inganta tarbiyyar yaranka ai ka je makaranta kai ilimi. Mace uwar al'umma ce fa."
Mamakin wannan baiwar Allah duk ya bi ya cika ni, ga ta tsab da'ita kai ba ka ce ta hayayyafa
har goma ba, ga karatu ta na yi, abunda ya fi komai burgeni kenan nace mata.
Sunana Sadiya, kuma kina da ra'ayin in kin kammala karatun likitancinki, ki yi aiki akan abunda
ki ka karanta? Dariya ta yi, cikin hali irin na masu tsohon ciki tace.
"Sosai ma, ai amfanin karatun kenan, mata da yawa su na zaune basa neman ilimi, sai su fake
da aure ko yara. Kuma dukka basa hana ilimi ko aiki. Shi yasa mu mata mu ka zama koma
baya sosai, ko asibitocinmu ki ka shiga, sai ki ga maza sun fi yawa. Mazan da yawa suna
k'alubalantar ilimin mace, sai ki ga mace ta dage ta ci karatu dan ta yi ma k'asarta hidima,
amma daga k'arshe sai ta rasa mijin aure. Za ki ji wasu har d'an kira su ke yi mata da sunan
karuwa ko 'yar bariki, ga masu cewa 'Yan boko basa zaman aure ga raini, Wannan ma ya na
dak'ushe k'wazon mata kan neman ilmi." Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
"Abunda ke faruwa a Al'ummar mu kenan, matan da su ka yi zurfin karatu suna fuskantar
tsangwama da kyara. Gani su ke tamkar mace bazata tab'a fitowa da kwalin gama jami'a lafiya

ba face sai ta siyar da darajarta na d'iya mace. Da yawa yawan mazan dalilinsu na gudun 'Yan
bokon kenan. Iyaye ma wannan dalilin ke sa su hana Yaransu yin zurfin karatun sai ki ga an yi
ma yarinya aure da k'arancin shekaru a jikinta. Kuma hakan ba k'aramin cutarwa bane. Sai kin
je asibiti b'angaren 'Yan yoyyon fitsari. Nan zaki ga mata k'anana wanda wasu garin haihuwane
cutar ta kama su, wasu ta hanyar saduwa ne cutar ta kama su."
Baiwar Allah'n nan tace.
"Sadiya ni kaina, ina da shekaru goma aka aurad dani, na sha bak'ar wahalar rayuwar aure, dan
a lokacin ma bansan mai ke mun ciwo ba, dan ko jinin al'ada ban soma ba. Haihuwata ta fari, a
lokacin shekaruna sha uku, na haifi ni'ima, sai da na yi wata shida a b'angaren 'Yan yoyyon
fitsari. A lokacinma turawane likitocin da suke duba mu. Shekaruna Talatin da yin Aure. Babbar
yarinya ta, ta na jami'ar Bayare dake kano. Sauran kuma duk suna gabana. Sunana Safara'u
Maman Ummi."
Sunana da na ta mu ka jiyo ana kira, tare mu ka shiga d'akin awo da'ita. Tare mu ka gama
komai, mu na tafe mu na hira dan Maman Ummi akwaita da hira.
"Nan shine gidana Sadiya, wata me zuwa in mun had'u na biki in ga na ku gidan.
Toh Maman Ummi nagode sosai, a gaida yara."
Sallama mu ka yi da Maman ummi, na wuce gida.
Wasa wasa cikina na ta girma, kuma yanzu garau na ke ji na sosai. Xumunci ya k'ulle sosai a
tsakanina da Maman Ummi, dan da ta haihu ma har suna na je, turmin da ni da omo na kai
mata.
Ciiki na ya na da wata bakwai, Mama da Goggo Hansatu su ka kawo mun ziyara. Na ji dad'in
ganin Mama yanda ta sauya, ta yi kyau sosai.
Haka su ma sunyi farin cikin yanda su ka ga zaman mu da Badiyya. Yaro na aika zuwa gidan
Maman Ummi, kan ta zo su gaisa da su Mama.
Ai kuwa kafin ma ta zo, ta aiko yaranta da lafiyayyen tuwon masara miyar karkashi.
Shi su Mama su ka ci, sun yi farin cikin ganin k'awata Maman ummi.
Kwana d'aya tak su ka yi, shima kamar a kan k'aya su ke su ka ta fi.
Ciki na na wata takwas, Safwan ya sa yi komai da komai, siyayyar har da ta hauka abuka da ba
saban ba .
Ranar wani Lahadi kuwa da daddare nak'uda ta kama ni, Safwan da Badiyya ne su ka kaini
asibiti.
nak'uda na ke ta faman yi, kafin gari ya waye asibitin ya cika da jama'a. Har zuwa lokacin
nak'uda na ke yi. Sai wajajen bakwai saura na haifo kyakkyawan Yaro mai tsananin kama da
Safwan."


Mrs Bukhari ce

MRS BUKHARI
71-72

D'akin hutu a ka wuce da ni, tuni bacci ya d'ebe ni.

Safwan
Sai suntiri Safwan ya ke yi a k'ofar labour room. Wata nose ce ta fito hannunta rik'e da jariri
wanda ya sha seti mai ruwan madara."
"Ina ta ya ku murna. Sadiya Adam ta sauka lafiya, Allah ya azurtata da haihuwar D'a namiji.
Safwan jikinshi har rawa ya ke yi ya sa hannu ya amshi jaririnan. Rungumeshi ya yi a kirjinshi,
ya na jin so da k'aunar d'an na ratsa duk tsokokin jikinshi. Kunnen yaron ya kai bakin shi ya
shiga jero mai adduo'i tare da yi mishi hud'uba. Badiyya ya mik'a ma jaririn. Ta yi maza ta
amshe shi ta rungumeshi tsam. Su Anty Jamila duk su ka d'auki jaririn ana ta yi mishi adda'a. Zukatan su cike da ta ya Safwan
farin ciki, Kallon Anty Jamila ya yi ya ce.
"Anty wannan jaririn na mallaka ma Badiyya shi duniya da lahira, d'anta ne, kuma ko mutuwana
na yi ban amince a k'wace yaronnan da ga hannunta ba."
Kuka Badiyya ta fashe da shi tare da sake k'ank'ame jaririn a jikinta."
"Hak'i'ka bani da kalmar da zan iya maka godiya bisa ga wannan kyauta da ka yi mun, ina
godiya Allah ya ba ni lafiyar shayar da shi, kuma in sha Allah ba za a samu matsala ta b'angare
na ba." Anty Jamila ta ce.
"Amma fa wannan d'anyen hukunci ka yanke Safwan, Sadiyan ba za ta shayar da jaririn ba
ma?"
"Eh Anty kuma na wakilta ki yi ma Innah baya ni, ko da wasa wannan yaron ba na son yasan
cewar ba Badiyya ba ce ta Haifeshi ba. Ita za ta shayar da shi, Anty ku ta fi gida ke da Badiyya,
da jaririn, a samu gadali a bata ta sha, dan ta samu ruwan nonon da zai sha, Anty Zulai mu je
ciki mu ga jikin Sadiyan." Mamakine ya ishi kowa a wajan, Anty Jamila ta ja hannun Badiyya wacce ta k'ank'ame jariri
kamar za'a kwace mata, su ka bar cikin asibitin zuwa gida.
Su Anty Zulai kuma su ka bi bayan Safwan zungui zungui. a bakin gadon da Sadiya ta ke
kwance su ka tsaya. Anty Zulai cikin rashin hak'uri ta ce.
"Hukuncin da ka yanke babu abunda zai haifar sai d'a mara ido, ni na tab'a jin irin wannan
lamari Safwan, Anya ka na son Sadiya kuwa, ko dai yaran da za ta haifa maka kawai ka ke
dubawa, tai ta haifa ma yara ka na ba Badiyya su, ita ta na shayar da su, kai kasan me ye zafin
nak'uda kuwa? Tun wuri kafin Sadiya ta farka daga wannan baccin hawalar haihuwar gara ka yi
tunani akan wannan lamari, kar zaman lafiyan da ya ke gidanka ya lalace a sanadin abunda ka
aikata." Safwan ya dube ta, ya ce da ita."
"Anty Zulai ni a nawa ganin, yaronnan dai nawa ne, kuma ba wani gida na kai shi ba, Sadiya na
da damar ganin shi a ko da yaushe. Banyi tunanin wannan zai kawo rashin fahimta a tsakani
ba. Dukkansu matana ne, yaro kuma nawa ne." Cikin juyayi Anty Zulai ta ce."
"Tsakanin d'a da uwa sai Allah, bana ko shakkar zuchiyar Sadiya ba zata iya jure wannan horon
ba. Ta ya ma zaka raba ta da yaronta tun a tsunman haihuwarshi, ka dank'a shi ga kishiyarta,
kyauta ta halak malak, me yasa ba za ka bar mata wannan d'in ba in yaso in ta kuma haihuwa
sai ka ba ma ita Badiyyan, gaba na ke jiye maka me hakan zai haifar."

Sadiya
Ahankali na bud'e idanuna wanda su kai mun mugun nauyi, gefena na soma kallo dan sake
kallon jaririna

28 / 33