Author : Batul Mamman Category : Read Hausa Novels
kaima tashi ka tafi wurin matarka. Da gudu ya fice
yana dariya.
****
Rasa dakin da zai shiga da ita yayi ya ja hannunta zuwa dakin Nura. Yana rufe kofar ya juyo yana
kallonta. Sai da ya juyata a gabansa yace Cutie babu inda yake miki ciwo? Dariya take yi tace Ya
Hamzana babu.
Ya rungumeta sosai yana suna ajiyar zuciya. Ya dago kai yana shafa bakinta...I miss you Cutie. Kiyi
hakuri don Allah ban kula dake yadda ya kamata ba. Duk abinda ya faru laifina ne. Yakamata ace naga
tafiyarku kafin na koma ciki.
Hawaye fal idonta tace duk ya wuce. Zai sake magana ta rufe masa baki da nata. Sun jima a haka
sannan yace Cutie duk kin canja kin kara kyau.
Hannunsa ta kama ta zira a karkashin rigarta. Ya ware ido sosai yana kallonta...tauri fa nake ji Cutie.
Sai kuma taji kunya ta sunkuyar da kanta kasa tana murmushi. Ya sa hannuwansa biyu ya dago kan
nata....are you pregnant? Maimakon ta bashi amsa sai kawai ta rungumeshi. A hankali tace wata
hudu kenan. Sakinta yayi ya durkusa a gabanta yana shafa cikin cike da kulawa...baby your daddy is
back. Yayi kissing cikin sannan ya tashi ya kura mata ido. I love you so much Fatima.
Tace nima haka..
Hamza yace ban karba ba.
Tayi dariya I love you Ya Hamza.
Wani kallo yake binta dashi ya kama hannunta muje ki dauko mayafinki mu tafi gida.
Tace har girki nayi maka kuma su Hajiya basu ce na tafi ba.
Kinga na baki minti goma ki dauko abinda zaki dauko mu tafi idan ba haka ba kuma na maimaita irin
abin dazu a gabansu. Fita tayi cikin farinciki ta dauko dan kwandon da ta saka flask din abincin.
Dakinsu Adabiyya ta shiga daukar mayafi su Jidda suka fara tsokanarta. Mariya tace kinga wuce ki tafi
Mama tace sun yafe sallamar wai wadda kuka yi dazu ta wadatar. Zuhra taji kunya sosai ta fita suka
rakata har bakin mota suna ta shakiyanci. Ganin Hamza ya hade fuska yasa suka koma ciki. Shi kuma
ya tada mota sai gida.
AL'ADUN WASU í ½í·¿77
Batul Mamman(Mrs)í ½í²–
Da kuka Izzatu ta fito daga motar Nura. Maigadi ya biyota yana tambayar ko lafiya. Bata bashi amsa
ba sai kallon banza. Murya a sama tana kuka ta shige ciki. Nura dai tsaki yayi ya ja motarsa.
Tala ma da yaran duka babu wanda ta kula ta wuce ta tafi dakinta. Wai ita Hamza zaiyiwa saki har
biyu? Lallai dan Adam ba'a ci masa laya. Irin soyayyar da suka yi tun kafin suyi aure ta zauna tana
tunawa. Bakincikinta ya karu ne saboda a ganinta ba karamin kaskanci bane ace an saketa saboda
wata Zuhra. Yarinyar da bata jin ko brush din kirki ta iya lokacin da Hamza ya aureta. Rasa mafita tayi
ta dauki waya ta kira Raliya. Babu abinda ta ragewa mahaifiyar tata na dangane da abinda tayiwa
Zuhra zuwa halin da take ciki yanzu.
Raliya ma kukan ta soma yi tace Izzatu kinga abinda nake ta ji miki tsoro sai da ya faru. Ban ga ranar
bin al'adun wasu don ka burge wasu tsiraran mutane ba.
Kwalin tissue din da ta kusa kararwa daga shigarta daki ta kuma janyo wata ta goge hawaye....Mum
ya zaki ce ina bin al'adun wasu. Duk abinda muke yi da ai tare dashi mukeyi. 'Yan wadanda nayi da
baya so sosai kadan ne. Kuma naga shima dan zaman da yayi a Canada ya isa ace ya waye da
dabi'unsu. Ace mu kullum 'yan Nigeria babu wani canji a rayuwarmu. Ni a ganina kawai gajiya yayi
dani amma babu wasu al'adun wasu da nake yi.
Ta yaro kyau take Raliya ta fada tana tuna irin sakacin da ya samo asali daga wurin Alh Sunusi a fannin
tarbiyar 'ya'yansu. Shine ya dage sai su barsu su sake bayan sun bar kasarsu. Tun Raliya bata jindadin
yadda 'ya'yansu ke sajewa da na turawa ta fannin dabi'a har ta fara so musamman idan suka zo gida
Nigeria suka shiga cikin 'yan uwa. Dan turancin da sukeyi da 'yar fitsara shi yake burge mutanenmu.
Sai kaga kowa na kokarin kyautata musu tamkar anga 'ya'yan wani shugaban kasa. Kuma irin haka
dama halinmu ne musamman Hausawa. Da 'yan uwanmu sun tafi kasar waje mun rinka shela kenan
sai kowa ya sani. Idan suka zo ganin gida kuwa ba'a magana. Kowa jiki na rawa yana tasa bajintar.
Raliya tayi ajiyar zuciya....yanzu duk bazaki gane abinda nake nufi ba kila sai nan gaba. Amma ina so ki
sani namiji duk inda yake indai akwai sauran mutumci a tare dashi to yana son a kyautatawa
iyayensa. Sai kika yi rashin sa'a gidan Alh Nasiru tsarin rayuwarki bai burgesu ba. A zatonki sonki ne
basa yi shiyasa kuka yi ta samun sabani da Hamza da farko har sonki ya rufe masa ido ya koma yana
biye miki. To kada ki manta dama tun da fari ga irin tarbiyar da ya tashi da ita yake hakuri da irin taki
tunda ke kinki canjawa don ki faranta masa. Sai Allah Ya kawo wadda zata yi masa yadda yake so kafin
yace yana so. Ai wallahi dole ra'ayinsa ya juya can. Gashi ke kuma sai shirmenki ya karu ninki akan na
baya.
Izzatu dai kuka take tana sauraron mahaifiyarta. Raliya tace kina jina kuwa? A hankali tace eh.
Duk abinda kika yi masa kinga ai ya hakura musamman cire mahaifa. Amma yau da yarinyar nan ta
mutu wallahi banda saki uku nasan sai yasa an kulleki. Kinyi sake tauraronki ya dishe a zuciyarsa.
Abinda Larai take ta korafin zai iya faruwa kenan duk muka banzatar da ita. Yanzu ki bari zan kira
Ustaz dan gidan Kawu mai zare na tambayeshi game da dalilin cewa sai kinyi idda a gidan. Kafin nan
don Allah Izzatu ki kama kanki kinji ko. Zan kiraki idan munyi magana.
Yau daya a rayuwarta da take ganin ta rasa abu mai matukar mahimmanci ta nutsu ta saurari
mahaifiyarta. Idan har akwai yadda zatayi ta sake mallakar Hamza to zata yi. Abu daya ne bata yarda
dashi ba saboda tashin turai da tayi shine bin malaman tsibbu da bokaye. Kyankyaminsu take ji kuma
gata da tsoron zuwa irin wuraren nan. Ta taba kawa da ta kaita wai a basu maganin mallaka. Tunda
taji ana zancen tayi masa lemo da jinin al'adarta na ranar karshe a wata bata koma ba. Bokan na fada
tana amai ma.
****
Babu wata hira tsakanin Hamza da Zuhra a motar sai kallon juna da murmushi. Karshe ma hannunta
ya hada da giyar motar ya rike. Dukkaninsu farincikin da suke ciki bazai misaltu ba.
Maigadi na bude gate da ya hangota kamar yayi tsalle don murna. Tabbas yasan inda take a bakin
Tala amma dole yayi kewarta. Abinci da kyautawar da take musu ai bazasu manta ba.
Hatta jakar hannunta mika hannu yayi zai karba Hamza ya karbe yana dariya...Mal Talle anya kayi
farincikin ganina ranar da na dawo kuwa. Irin wannan murna haka?
Zuhra tayi murmushi kawai ta shige ta barsu. Maigadi yace Yallabai ka rike matarka da kyau. Wallahi
tana da kirki sosai.
Hamza yace nagode. Ga wannan gobe kaje gida kayi sati biyu....Kudi ne maigadi ya karba da murna.
Lallai an sami canji. A da Hamza don kansa baya barinsu zuwa ganin gida sai sunyi ta roko amma
yanzu ya san hakkin mutane sosai.
A cikin gidan ma tamkar an kawo wutar nepa bayan shekara daya haka suka yi ta murna. Tala ta
kwashi 'yan kayan da Zuhra ta sami daukowa ta kai sama. Su Khalifa kuwa suka dane jikinta. Nana
sarkin rigima tace Maama goyani..
Zuhra na durkusawa Hamza ya shigo yace ke rufa min asiri. Nana zo na goyaki kinji. Maama da kayana
a jikinta.
Nana ta sa kuka ita bayan Maama. Tun yana lallabata har ya soma fada. Zuhra ta dage zaya iya goyata
yace sam bai yarda ba.
Izzatu ce taji kukan ya isheta ta fito. Ganin Hamza yasa zata koma sai kuma ta kula da Zuhra. Ba
karamin kyau tayi ba idan aka hadata da Zuhran da ta sani da farko. Kamar ta sauko tayi mata
magana taji dalilin da yasa ta boya ta jawo mata saki. Sai ta tuna da shawarar da Raliya ta bata ta
koma dakinta tare da bugo kofa da karfi.
Da kyar Hamza ya lallaba Nana ta yadda ya goyata. Amma ta dage sai ya saka zani. Zuhra dasu Junior
suna ta yi musu dariya yace bazai saka ba. Zuhra ya kalla yace zaki san ni kika yiwa dariya idan na
kamaki. Tana jin haka ta haye sama tasan zata sha aiki. Sai dai ga mamakinta dakin fes ta same shi.
Komai a gyare, hatta zanin gado Hamza ya dauko sabo Tala ta shimfida a kan gadon.
Tare dasu Junior ta tafi dakin suna ta bata labarin abubuwan da sukayi lokacin da bata nan. Hamza ya
shigo da Nana a hannu tun yana saka baki a hirar har ransa ya soma baci. Yau da yake son kasancewa
da Zuhra bayan lokacin da suka dauka basa tare shine ta biyewa yara hira. Gajiya yayi ya fita dakinsa
ya bude jakar kayan tsarabar da bai sami damar budewa ba tunda ya dawo. Kayayakin da ya siyowa
yaran ya debo harda wasu riguna da ya siyowa Tala da maigadi. Bawa kowa nasa yayi sannan ya basu
nasu Tala. Harda kashedi idan kun kai musu kuje ku nunawa Mummy.
Yara an sami abinda ake so suka fita suna ta murna. Suna tafiya ya rufe kofar harda murda mukulli.
Zuhra ta dawo kusa dashi ta tsaya yana ta kallonta musamman dan cikinta da ya tasa kadan.
Hannuwanta ta sakala a wuyansa ta rungumeshi. Yace da kinsan abinda kike so kenan kika biyewa
yara kina hira kawai don ki ja min aji....ya kama hannuwan nata ya cire...nima yanzu zan ja nawa sai ki
bisu kuyi hira ni bacci nake ji.
Zuhra tayi dariya ta sake rungumarsa. Haba Ya Hamza kaga suma nayi kewarsu ne shiyasa. Dan zo kaji
irin yadda nayi kewarka duk tafi ta kowa.
Matsawa ya kara yi naki din. An fada miki mata ne kadai suka iya yanga. Sai nan da sati daya zamu
fara kwana a daki daya ma. Kinga tafiyata.
Yana tafiya Zuhra ta sake binshi ta rungumeshi ta baya tana masa dariya....idan ka fita abinda na
kawo maka na murnar dawowarka zan fasa baka....yadda take magana tana jan kowane harafi yasa
shi saurin juyowa suna kallon juna. Kafin ya daga hannu ya tabata an soma kiran sallar magriba.
Ya cije lebe Zuhra ta kwashe da dariya. Ai kaga yanzu sai kayi yanga da hujja. Ni bari naje nayi alwala
sai bayan sati idan mun hadu.
Hannunta ya rike suna bin kiran sallar har aka gama suka yi addua sannan yace yau idan kika shigo
hannuna Cutie...hmmmm sai na dawo dai. Love you.
Itama tace masa Love you too sannan ya fara shiga toilet dinta yayi alwala ya fito ya tafi masallaci.
Da Zuhra ta idar da sallah kasa ta sauka wurinsu Tala. Abincin da tayiwa Hamza bashi da yawan da
zasu ci duka gidan shiyasa ta dora jallof din taliya. Ba jimawa ta gama ta zubawa kowa. Tala sai
kallonta take tana murmushi. Ba karamin kewa ta barsu dashi ba. Bare da ta kula kamar Zuhran ciki
gareta shikenan komai sai tace kawo na karasa. Haka suka gama girkin ta koma dakinta tayi sallar
Isha.
Bayan Ishar Hamza ya dawo. Yau fa anga Cutie bashi da wurin zama sai inda take. Hijab din da tayi
sallah ya samu tana ninkewa ya karba ya karasa mata sannan yace ta zauna zasu yi magana.
Zancen abinda Izzatu tayi yayi mata sannan yace nasan kina sane da hukuncin da Alhaji ya yanke na
cewa na saketa ko?
Sunkuyar da kai Zuhra tayi bata ce komai ba sai hawaye dake barazanar saukowa daga idonta. Sauran
abubuwan da Izzatu tayi mata duk da bata ji dadi ba amma tana iya danne bacin ranta ta hakura.
Wannan karon kuwa idan har tace ta hakura babu komai ita kanta tasan dole a jerata sahun farko a
makaryata. Babu macen da zata fuskanci abu makamancin wannan tace ta hakura lokaci daya.
Duk tunanin da Zuhra take yi Hamza na kallonta. Abu ne mai wuya ace Zuhra ta yafewa Izzatu....sake
matsowa yayi jikinta sosai yace..babu wanda zai iya kwatanta halin da kika shiga sai wanda ya tsinci
kansa a ciki. Abinda Izzy tayi miki ba abu bane da zamu iya mantawa da wuri. Sai dai ina rokonki
alfarma yadda kike kokarin kiyaye dukkan abinda kika san ya sabawa shari'a ko zaman aure don Allah
Cutie kada ki fara shi saboda bacin rai, kinji.
Bata iya magana ba sai kai da ta gyada a hankali. Hawayen da take boyewa suka fara sintiri a fuskarta
lokacin da yace mata a gidan Izzatu zata yi Idda. Ga kishi ga bakincinkin abinda ya faru. Hamza bai
hanata kuka ba sai ma rungumarta da yayi. A hankali ya sake magana saboda yasan ranta a bace
yake... Cutie nasan abinda zan fada yanzu zai kara bata miki rai sai dai ina son kada kiyi hukunci da
son zuciya. Kiyi tunani a matsayinki na musulma wadda take fatan itama idan tayi kuskure a yafe
mata. Rikon da tayi masa ya tabbatar masa tana jinsa.... Alhaji yasa na mayar da Izzy bayan fitarta
dazu saboda haka a matsayin matata take har yanzu duk da bata san hakan ba. Na fada miki ne
saboda kada kiga wani dalili yasa naje inda take tana da hakki a kaina har yanzu. Zan bari sai tayi
tunanin ta gama idda sannan na sanar da ita. Hakan muna fata ya zama sanadiyar nutsuwarta. Batun
girki kuma zata dafa iya na cikinta banda su Nana.
Zancen Hamza har zuci ya daki Zuhra sai dai kuma tana da tabbacin son zuciya bazai taba zama
alkhairi gareta ba. Shi Izzatu tayi sai gashi ita da take raina kanta da kanta ta mallaki zuciyar mutum
kamar Hamza. Dago fuska tayi suka hada ido tayi saurin rufe nata....Ya Hamza in sha Allahu bazan
taba shiga tsakaninka da matarka ba. Tare na ganku kuma nasan duk matsalolin nan saboda ni suke
faruwa. Idan a da ban fahimceta ba yanzu nasan ya mace take ji idan taga mijinta da wata. Allah Yasa
a samu abinda ake nema...ta mike tsaye tana jan hannunsa.... ka tashi muje muci abinci sai ayi wanka
a kwanta.
Dawo da ita yayi kan cinyarsa...dan fada min ya mace take ji idan taga mijinta da wata.
Zuhra tace tabdi ai rai ne yake baci sosai. Nifa ranar da ta dawo da kyar nayi bacci.
Hamza yayi dariya yace kina ta tunanin ko muna can muna....
Bakinsa ta toshe da hannunta ta tashi tana jin kunya. Kafin ya tashi ta fice daga dakin.
****
Abin duniya ya ishi Izzatu sai juyi take akan gado ga wata uwar yunwa na cinta. Bata son fita ta hadu
da Zuhra ko Hamza. Da wane ido zasu kalli juna? Kila Zuhra ta rinka mata dariya ma saboda yanzu an
saketa. Tana wannan tunanin Raliya ta kirata. Da sauri ta dauki wayar tana son jin jawabin Ustaz.
Raliya tace to ki saurare ni da kyau Izzatu. Idan kika bari wannan damar ta wuceki babu ruwana.
Ustaz yace ba karamin kokari suka yi ba suka ce kiyi idda a gidan. Mutanenmu da yawa basu san cewa
yana da kyau idan anyi saki daya ko biyu mace tayi idda a gidanta ba. Hakan zai sa a wannan lokacin
tayi kokarin jan hankalin mijinta har ta mantar dashi dalilin sakin ya yafe mata ya dawo da ita . Sai ayi
saki daya ace na baki minti biyar ki kwashe kayanki.
Izzatu tace to Mum hakan dole ne ko mutum nada zabi?
Raliya tace mace na da zabi amma zaman shi yafi. Kinfi kowa sanin Hamza saboda shekarun da kuka
yi tare. Kinsan me kike yi ki janyo hankalinsa. Sai ki dage da ladabi da biyayya. Girki ma ko bazaici ba
kiyi maidadi kiyi masa tayi. Banda saurin fushi kuma babu ruwanki da Zuhra. Idan kika yi ganganci da
sauran igiyar nan zaki yi kuka da idanunki don yanzu 'yan mata ma neman miji suke ido rufe bare
bazawara mara mahaifa.
Haba mana Mum ya zaki fadi haka? Izzatu ta fada kamar tayi kuka.
Ya bazan fada ba Izzatu. Ai mahaifar nan da kika cire wallahi ko yau ko gobe sai kin cije yatsa. Naga
har yau baki fara damuwa bane. Allah Ya kyauta .
Izzatu tace Amin ta tashi da kwarin gwiwa. Wanka tayi ta bata lokaci wurin gyara jikinta sosai tayi
kwalliya. Wata rigar bacci ta saka shara shara ta feshe jikinta da turare ta fito ta sauka kasa.
Tala har bari tayi saboda shigar da Izzatu tayi. Tayi saurin rufe ido tana tunanin yaushe Hajiyarsu zata
dena irin wannan abubuwan. Ita bata taba ganinta da riga irin wannan ba duk da ta saba yawo a
gidan da kayan bacci amma masu mutumci ne.
Hayaniyar su Khalifa ta jiyo a falon Hamza tayi murmushi tasan yana ciki. Canja tafiya tayi ta shiga
falon.
Zuhra da Hamza ke cin tuwon da tayi masa da Nana wadda idonta idon tuwo. Junior da Khalifa suna
ta wasa da bindigar roba. Kamshin turarenta ne ya fara sanar dasu ta iso.
Junior ya kalleta baki bude yace Mummy yau kuma baki saka kaya ba kika fito daga daki?
Khalifa yace kai ta saka amma irin rigar da Malam yace idan mace ta saka ta fita za'a sakata a wuta
ne. Mummy wallahi babu kyau yawo a haka.
Zuhra dai kawar da kanta tayi gefe don