Author : Batul Mamman Category : Read Hausa Novels
da
mukayi jiya akwai shawarar da nake son baka amma don Allah idan hakan laifi ne kayi hakuri. Ina jinki
yace cikin muryar bacci. Ta tashi zaune, kayi hakuri bansan ka soma bacci ba. Bude ido yayi yana
kallonta, babu komai ina jinki. Komai nata kishiyar na Izzatu ne.
A nutse ta soma magana kamar ba ita ba. "Nasan duk wadanda suka san abinda ke faruwa da kai sun
baka shawara kila ma irin wadda zan baka ko wadda tafi ta. Lokacin da tsautsayi ya ritsa da Baba a
wurin aikinsu mun sha wahala. Sanda yake da duka hannuwansa munfi wadata da rufin asiri. Da aka
yanke hannun yana jinya a gida ga kudin magani da sauran abubuwa na yau da gobe ya kasance an
koro ni daga makaranta. Ba don Malam babansu Hajara ba abinci ma sai ya gagare mu wata rana duk
da a haka Baba ya fishi rufin asiri. Wata rana Umma tace naje makota na sanar dasu zata fara wainar
flawa. Ranar baka ga kukan da nayi ba." Hawayen ta soma Hamza ya sa yatsansa ya share mata. Ta
cigaba da magana "bakincikina mun talauce har abin ya kaimu ga sayar da wainar flawa. Ina kuka na
sanar da Umma bazani ba, ta soma fada nace so take kawayena suyi min dariya. Sai ta zaunar dani ta
dena fada tace min. Zuhra aure ba abin wasa bane. Aljannar mace kuma tana karkashin kafar mijinta.
Ma'ana samun aljannarta na tattare da yardar mijinta. Lokacin da babanki yake da lafiya ya wadata
mu Alhamdulillah. Yanzu kuma lalura ta same shi 'yan uwa da abokan arziki duk sunyi mana kokari
amma dole mu yiwa kanmu. Idan miji ya shiga matsala mace ana so tayi iya kokarinta da yin abinda
bai sabawa shari'ah ba wurin kyautata rayuwarsu. Idan har bata da hali kuma sai ta taya shi da addua
dare da rana har Allah Ya kawo musu sauki. Kada ki taba daukar maganar masu cewa idan mace ta
taimaki mijinta wata rana zai saka mata da tsiya. Dama don Allah kika yi saboda haka ki nemi lada a
wurinSa. Tun daga ranar na koyi tattali da adana abu saboda na ragewa Baba kashe kudi. Idan ya siyo
min turare ko sabulu na rinka janjaninsa har kazanta ta dan kamani. Amma dai yanzu na dena ko "
tayi maganar da murmushi sannan ta dago kanta suka hada ido da Hamza." Kasan me yasa na baka
labarin nan?" Yace "sai kin fada". Zuhra ta gyara zama." Ni a shawarar da zan baka Ya Hamza kafin
komai ya daidaita ka rage kashe kudi. Misali tunda nazo gidannan tun karfe shida na yamma ake
kunna inji har tara na safe. Wani lokacin da rana ma sai an kunna duk yadda abubuwa suke tsada
yanzu. Kuma na kula ranar alhamis a waje kake siyo abinci. Gashi yawancin safiya kullum za'a soyawa
su Khalifa kwai kowa bibbiyu. Suci rabi su bar rabi ya shiga shara." Ta dan daga hannu " ba cewa nayi
a takurasu ba amma a rage irin wannan. A koya musu yau su sami yadda suke so gobe su hakura
saboda halin rayuwa. Injin ma a barshi sai kamar tara ko goma na dare a kunna. Da duk abubuwan da
kasan basu da mahimmanci sai a barsu."
Tunda Zuhra ta fara magana Hamza yake kallonta. Kallo irin na tsabar soyayya da mutuntawa. Yarinya
ce Zuhra sosai a kanshi da Izzatu amma duk yadda suke ganin shirmenta ta san abinda take yi.
Matsalar gabansa bata dame shi ba kamar yadda yake son gina soyayyarsa a zuciyar amaryarsa.
Zuhra duk ta tsargu da kallon da yake mata tace Ya Hamza na shiga abinda bai kamata ba ko? Nasan
duk aikin Maman Khalifa ne. Dama kawai nayi ne don nima na sami ladan da mata ke samu a gidan
aure. Kaga bansan lokacin da zan sake aure ba idan muka rabu. Tayi masa murmushinta mai
kyau...shiyasa nake son samun lada a iya zaman da zamuyi.
Kasa magana yayi sai mamakinta kawai. Dan taba shi tayi saboda yadda ya kasa dena kallonta. Ba tare
da ya dauke idonsa daga kanta ba ya dorata kan cinyarsa tare da rungumeta sosai a jikinsa. Sannan
yace nagode sosai Fatima, Allah Yayi miki albarka. Abinda na fada miki jiya babu wanda ya sani sai ke
sai mutane kadan a office dinmu saboda haka ki rike min sirrina. Kuma na baki dama ki fada min duk
abinda kika ga ya dace na gyara ni Hamza nayi miki alqawari zan gyara. So yake yace mata yana sonta
amma baya son tsorata ta don yasan tana tsoron halin Izzy. A hankali zai bi da ita har sai yasa taji irin
yadda yake ji game da ita a tasa zuciyar.
Ba jimawa ta fito daga dakin ta sauka kasa. Adabiyya da Hamida ta gani sun share ko'ina sun dafa tea.
Abinda za'a ci ne basu sani ba. Kunyarsu ta kamata ta soma 'yan kame kame. Yau makara nayi wallahi.
Kuyi hakuri....da yake su Jidda sun kawo mata dankali tace rbari a soya dankali. Hamida tace gaskiya
Anti dankali akwai bata lokaci kawai muci indomie. Tace to Adabiyya ta dafa musu harda ita, zata
soyawa Ya Hamza shi kadai. [10/12, 7:34 PM] Salma: AL'ADUN WASU 55
Batul Mamman(Mrs)
Zuhra na hada kayan wanki a dakinta Hamza ya shigo yace su shirya yaji jiya suna zancen zuwa salon
ita da su Adabiyya. Taji dadin hakan sosai dama a dalilin bata son auren taki yarda a saka mata relaxer
a kanta wai kada ya rinka hanata zuwa tunda yace kuntata mata zai yi a gidansa. Dubu ashirin ya bata
ita da su Hamida kowa yayi abinda yake so. Zuhra ta bude baki, wannan kudin yayi yawa har ka manta
zancen da muka yi dazu? Ban manta ba baki nayi ki rike a hannunki koda bukata zata zo miki. Tayi ta
masa godiya duk da a ganinta kudin sunyi yawa. Shabiyu saura suka fita tare ya sauke su yace zai je
unguwa idan sun kusa gamawa su kira shi. Zuhra tace ai babu nisa sosai muna tafe muna hira ma sai
mu koma. Su Adabiyya dake bayan motar yacewa su fita su jirata a ciki. Suna tafe suna waige da yiwa
yayan nasu dariya har suka shige. Ya mayar da hankalinsa gareta. Akwai abinda kike so na taho miki
dashi ne? Ta girgiza kai Allah Yasa kaje lafiya ka dawo lafiya. Allah Ya bada abinda ake nema. Ya nuna
mata jindadinsa da adduarta yace nagode sai na dawo. Da ta fito wata mata ta gani ga baby a
hannunta ga jaka da zanin goyo duk kayan sun mata yawa. Da sauri ta karasa ta tare mata jakar da ke
shirin faduwa. Matar tayi murmushi kai amma nagode miki. Sai da na zo nan hannun jakar ya tsinke
ga Muhsina ta min kuka. Zuhra ta karbi yarinyar matar ta hade bakin jakarta da zanin goyon suka
shiga tare. Har su Adabiyya sun kama mata layi da yake weekend ne wurin ya cika. Wuri daya Zuhra
da matar suka zauna tana ta yiwa yarinyar wasa ita kuma tana dariya. Matar tace ni sunana Sa'adatu
ke fa? Zuhra ta fada mata sunanta tace ina son baby dinnan. Sa'adatu tayi dariya ai naga alama kema
tana sonki don kyuya take yiwa mutane amma gashi tana miki dariya. Suna hira matar tace ita har
lalle zata yi. Hamida ta taso daga inda Adabiyya ke tayata tsifa Anti don Allah kema kiyi lallen wallahi
Yaya yana so. Duk sallah baya fashin bamu kudin lalle ko Adabiyya. Adabiyya tace ce eh.
A wani daki ake yin lallen Zuhra tabi bayan Sa'adatu ta shiga. Ai kuwa mutum daya suka tarar ana
tsara mata ado sosai. Sa'adatu tace ni dai kada kiga ina ta kallonki wallahi kamar na taba ganinki a
wani gida. Zuhra tace kila mun hadu, a wace unguwa ne? Sa'adatu ta soma bata labarin wasu da suka
tare a unguwarsu ana walima aka yiwa wata April fool. Wallahi sai kuke dan yimin kama da yarinyar
duk da ba kare mata kallo nayi ba. Murmushi Zuhra tayi sannan tace nice yarinyar. Sa'adatu ta bude
baki don Allah da gaske? Ana ta rade radin mijin matar ya auri yarinyar. Don Allah ke ce? Zuhra tayi
ajiyar zuciya. Nice, har an kusa wata biyu da auren. Sa'adatu tace lallai Zuhra rayuwarki ishara ce ga
wawayen mata. Duk yawancin matan unguwar nan da Izzatun nan ta gayyata walimar tarewarsu sai
da suka zageta ranar da abin ya faru. Yadda kika san kanwata aka yiwa wulakancin nan, har maigidana
na bawa labarin abinda ya faru. Mai lallen ce ta fita karo leda Sa'adatu ta matso kusa da Zuhra. Ko
baki fada ba nasan aurenku da mijin Izzatu bazai zama na jindadi kamar na kowa ba duba da irin
abinda ya faru da farko. Amma zan baki shawara ki rike mijinki sosai yadda har abada idan Izzatu ko
mai hali irin nata tayi niyyar daukan al'adun wasu zata sake tunani. Kinga yau muka fara haduwa
amma haka kawai naji ina sonki da alkhairi. Zuhra dai sai murmushi take yi. Auren da yake da lokacin
karewa wane rike miji zata yi?... Sa'adatu tace kina son mijin naki? Kanta ta sunkuyar kasa kawai tana
murmushi. Ai an gama wannan murmushin naki ya isheni amsa. To kalleni da kyau bari na koya miki
karatun saye zuciyar mijin matar da bata san inda ke mata ciwo ba. Ina ma da Ummu Sudais muka zo
wurin nan. Don baki ga yadda tafi kowa jin haushi ba ranar. Kada kiga kamar cin fuska amma ko ba'a
fada ba wayewarki da ta Izzatu ba daya ba. A irin haka tayi miki wayo har hakan ta faru. Abu na farko
da nake so dake shine daga yau mijinki ya ga kin canza masa gabadaya. Canji irin wanda zaisa ko fita
yayi yana tunanin Zuhra a gida. Ki rike TSAFTA sosai domin ita ce abu na farko da kowane miji yake
nema daga matarsa. Duk kyaunki da iya kwalliya idan baki da tsafta ko jiki na wari miji bazai so
kusantarki ba. A hankali kuma zaki fice masa a rai ya fara neman wata. Na biyu ki iya KWALLIYA irin ta
zamani amma fa ba mai yawa da za'a kasa ganeki ba saboda tsabar fuska tasha fenti. Na uku
SHAGWABA,Zuhra ba sai na bata lokaci ba a nan. Duk mijin da zaki mayar da kanki yarinya a gabansa
dole ya soki. TATTALI DA ADANI yana da kyau ga dukkan matar aure. Babu namijin da zai so ya auri
matar da take da almubazzaranci. GIRMAMA IYAYE da son 'yan uwan miji shima yana karawa mace
daraja a idon mijinta. IYA ABINCI wannan kowa yasan shine jigon dorewar zaman lafiya a gidan aure.
KULAWA, maza nason mace ta kula dasu tamkar yara kamar yadda muma muke son hakan. Ki rage
kunya domin ba'a son don kinyi aure ki ajiyeta gabadaya, ki nunawa mijinki so da kauna ta sigar da zai
manta da yadda ya auroki ya rike ki da zuciya daya. Ke kike aurensa saboda haka kinsan bukatunsa,
idan baki sani ba kisa ido sosai ki nemi soyayyar mijinki da gaskiya. Abu na karshe kuma mafi
mahimmanci shine ki rike ALLAH SWT DA MANZONSA SAW, idan kika yi haka to in sha Allahu komai
zai zo miki da sauki. Mu 'yan unguwar nan duk 'yan bayanki ne wallahi. Abinda duk ya shige miki
duhu zan baki numberta sai mu rinka zumunci.
Zuhra tsaf ta nade shawarwarin Sa'adatu tayi mata godiya sosai. A ranta ta kudurce in Allah Ya yarda
zata yi iya kokarinta taga cewa Hamza bai saketa ba domin tsakani da Allah tasan tana sonsa. Karshe
ma sai kafin a fara lallen tace ita gyaran jiki zata fara yi tunda suna yi. Bayan an gama aka yi mata lalle
da retouching. Idan kaga Zuhra sai ka zata ba ita bace jiki sai sheki yake don ma na rana daya tayi.
Hamza sai waya yake Adabiyya na dauka tace ba'a gama ba har sai da ransa ya baci yace wane irin
abu suke yi a wurin. Sai karfe biyar Zuhra ta kira shi lokacin ya dade da komawa gida. Yaso yi mata
mita sai dai tana zuwa gaban motar ta daga masa hannuwanta tana dariya.. Ya Hamza lallena yayi
kyau? Fasa fadan yayi saboda yayi kyau din. Baki da ja aka yi mata tamkar wata amarya. Hamza na
son mace tayi lalle amma Izzatu tace kauyanci ne shiyasa bata sake yi ba tun na aure.
Wai ya labarin Izzatu a Kaduna???
[10/12, 7:34 PM] Salma: AL'ADUN WASU 56
Batul Mamman(Mrs)
Izzatu na tsaye akan Tala ta gama hada kayan su Khalifa suna ta shiri washegari zasu koma Kano. Tuno
babban dalilin da zai kaita Abuja tayi tace kinga Tala ki hada harda kayan Nana ku tafi tare. Ga
wannan wayar zan rinka kiranki akai-akai kina sanar dani abinda ke faruwa a gidan. Nasan babyna
bazai kula wannan yarinyar ba amma dai ki sa ido kafin na dawo. Ki rinka yi masa girki saboda nasan
ya wahala a siyan abinci kwanakin da bana nan. Tala tace to Maman Khalifa. Izzatu tace ba to ba aiki
zaki min. Idan kika ga zata shige masa ki hanata ni na baki wannan damar sannan ki kular min da yara
bana son suna cin kazantar da take kira abinci. Sosai ta karantawa Tala dukkan abinda take so tayi
mata idan ta koma. Daga nan suka shirya aka tafi kai amarya. Sai da suka kaita akayi sallar magariba
suka shirya aka tafi dinner wadda ango ya shirya.
Ko wanka Zuhra bata yi ba da suka koma gida sai da tayi sauce din hanta wanda yaji albasa da kayan
lambu sannan ta dafa farar shinkafa. Harkar girki duk aikin Anti Faiza ne shiyasa take son yi mata
siyayya mai kyau idan zata je gidanta. Hamida da Adabiyya sun tayata suka hada komai sannan aka
fara layin wanka. Zuhra kayanta ta dauka ta fita ta tafi dakin Hamza. Yana falonsa yana aiki shiyasa ta
shiga kai tsaye.
Bata dade da shiga toilet din ba ta fito zuciyarta babu dadi. Tasan yau da kyar zata sami bacci tunda
abin yazo. Matsanancin ciwon mara yake saka mata. Dama kwana biyu kenan tana jin alama. Dakinta
ta koma ta dauko pad sannan ta dawo ta shiga wanka. Lallenta ya kara yin fes dashi. Harda humra ta
dauko a dakinta tabi duk jikinta ta shafa musamman cinyoyinta. Sannan ta fesa turaren jiki kala daban
daban. Dogon skirt ta saka baki mara fadi don ya kama mata jiki sannan tasa wata jar top itama ta
kamata sannan hannunta dan iya kafada kawai ya rufe. Sake fesa turare tayi sannan tabi gashin nan
da yasha gyara tayi styling dinsa. Ta taje shi baya ta zubo da wani ya rufe mata rabin fuska. Juyi ta
rinka yi gaban madubi tana yiwa kanta dariyar yadda zata je gaban Hamza a haka. Kwalliyarta ta dan
gyara wadda tayi alkawarin mayar da hankali ta kara koya sannan ta fito daga dakin.
Kamar abin kirki har ta fara saukowa ta koma daki neman mayafi. Ai da kunya taje gaban Ya Hamza a
haka. Tana shiga dakin su Adabiyya suka fara yaba kyan da tayi. Karfafa zuciyarta tayi ta bi bayansu
suka sauka.
Sai da ta dan tsaya a kofar falon tana tunanin da tadda zata shiga a haka. Daga baya dai ta tuna yanzu
dama ce ta samu da zata yi kokarin samun soyayyar Hamza idan ba haka ba nan da 'yan watanni
sunanta bazawara. Muryarta a can kasa tayi sallama sannan ta shiga ciki. Hamza na zaune a kan wata
kujera irin mai juyawar nan a gaban wani table daga karshen falon yana aiki a computer. Bayansa take
iya gani shima ba tare da ya juyo ba yace ni yau munyi fada Cutie. Duk sai shareni kike yi tunda muka
dawo sai yanzu zaki zo. A hankali take tafiya tana gwada yadda taga mata masu ji da gayu suna tafiya.
Ta hadu dasu kala kala a salon yau. Cikin nutsuwa ta karasa kusa da shi kamshinta mai dadi ya sanar
masa da isowarta. A daidai bayan kujerar ta tsaya tace Ya Hamza bazaka juyo kaga kwalliyata ba?
Murmushi yayi amma yaki juyowa. Ni lessons din da na koya miki bamu zo kan jan aji ba amma har
kin koya. To nima nawa zanyi miki bazan juyo ba. Turo baki tayi ta soma shagwaba....Allah sai ka gani.
Ji yayi tasa iya karfinta tana kokarin juyo kujerar. Ko da ta juyo dashi da kyar sai taga ya runtse ido.
Duk kiyi ki gama bazan kalleki ba yau. Murmushi tayi sannan ta matso da fuskarta kusa da tashi har
yana jin numfashinta. Ya Hamza don Allah ka bude idonka ka gani. Irin kwalliyar da zanyi ce idan na
sake aure. Bukatarta ta biya domin tana rufe baki ya bude idanunsa suka sauka a kanta. Ya tsani ta
rinka zancen idan sun rabu balle kuma idan tana cewa ga abinda zata a gidan sabon mijinta. Mikewa
tayi ta soma juya jikinta a gabansa. So da kaunar Zuhra ke kara karfi a zuciyarsa. Kallonta yake kamar
ba ita ya aura ba saboda yadda tayi masa kyau. Da ya kula tana jindadin kallon nasa amsa take jira sai
ya dan tabe baki....to,kin so kiyi kyau amma dai da saura. Muryarta kamar zata yi kuka tace da saura
fa kace? Hamza yayi murmushi eh mana. Da akan wannan 'yar kwalliyar kika zo zaki dameni.
Ba karamin mamaki yayi ba da yaga ta soma hawaye da gaske tana buga kafa. Baka ga yadda na dade
ina yin kwalliyar nan ba shine zaka ce banyi kyau ba. Hankalinsa ya tashi ganin tana kuka yace wasa fa
nake miki. Hannunta ya ja ya zaunar da ita a kan cinyarsa a kujerar yace haba Cutie ke kin fiye rigima.
Meye abin kuka don na dan tsokaneki.