Author : Batul Mamman Category : Read Hausa Novels
dalilin da zata shigo masa daki babu sallama ba. Ita kuwa Zuhra bargo taja ta suturta
jikinta saboda rigarta ba mai kauri bace. Cikin masifa Izzatu tace Hamza me zan gani haka? Karuwa
har cikin gidan aure, har kan matrimonial bed(gadon aure)din mu. Daurw fuska yayi shima yana
fadan...Izzy a wane dalili zaki shigo min daki babu sallama.
Heyyyy! aa'a! maza har abada bakwa rabo da abin mamaki. Na kamaka da karuwar kace zaka min
wa'azin sallama. To ban karba ba sai ka kama wata hanyar borin kunyar ba wannan ba.
Kallonta ta mayar ga Zuhra ta daka mata tsawa ke kuma tsohuwar 'yar bariki wallahi ni da kike gani
bani da mutumci akan mijina. Sai kinyi nadamar hada jiki dashi. Zaki sakko daga kan gadon nan ko sai
nazo na babballaki?
A gigice Zuhra tayi yunkurin sauka daga gadon tana lullube da bargo hakan ya jawo ta bige gwiwarta
da gefen gadon, tana tashi ta soma dingisa kafa. Hamza yayi saurin tareta, Cutie koma kiyi zamanki let
me handle this issue. Ya nuna kofa Izzy wuce muje dakinki we need to talk.
Ko sauraronsa bata yi ba ta taho gaban gadon ta kwaye bargon da Zuhra ke ta rufe jikinta dashi.
Idonta cike da hawaye tace Hamza buduwar ka samo shiyasa naga har wani jan kafa take yi. Zuhra ta
rasa inda zata saka kanta saboda wannan tozarci da Izzatu tayi mata. Bayan Hamza taje ta tsaya
saboda tasan ko kadan bai kamata Izzatu ta ganta da wannan shigar ba. Gadon Izzatu ta rinka dubawa
Hamza yana mata fada ko daga kai bata yi ba. Ka barni na duba shaidar cin amanar da kayi min da
wannan 'yar isakar da take son nuna min ita budurwa ce. Hamza yace Izzy idan baki nutsu kin fita
daga dakin nan ba wallahi zaki ga baccin rai.
Jajayen idanunta ta dago tana kallonsa, bacin rai har ya wuce wannan munafukar karuwar da ka
dauko daga bakin titi. Hannu ta kai zata janyo Zuhra dake zubar da hawaye a bayan Hamza ya rike
hannun tare da zagba mata mari. Shima nasa idon bacin rai yasa sunyi ja yace kada ki sake kira min
mata karuwa wallahi.
Izzatu ta dafe kunci ni ka mara Hamza??? To na fada din karuwa matsiyaci....wani wawan marin ya
bata wanda yafi na farko. I am warning you Izzy ki kiyaye bakinki. Zuhra matata ce ba karuwa ba.
Magana Izzatu taso yi sai dai kalmarsa ta karshe tasa ta hadiye maganar tare da kukan da take yi.
Kunnenta ta dan buga sannan tace me kace Hamza, Zuhra matarka ce? Wannan karuwar ce Zuhra? Ta
fada tana nuna ta.
Hamza yace idan ba ita ba ina da wata matar ne bayan ke? Haka kawai kin shigo kina ta bala'i kamar
wata mahaukaciya. Ki fice daga dakin nan kafin na saba miki.
Sai a lokacin Izzatu ta karewa Zuhra kallo. Ko da wasa bata ganeta ba da farko saboda ba haka tasan
Zuhra ba. Jikinta a sanyaye tayi zaman 'yan bori akan gadon. Ta dago kai a hankali tana kallon Zuhra
dake labe a bayan Hamza. Tsakanina da kai Hamza bazan taba yafe maka ba. Ni Izzatu Sunusi zaka
yiwa irin wannan cin fuskar? Ka kasheni kuma bazan yafe maka ba. Har gara ace sophisticated
prostitute( hadaddiyar karuwa) ka dauko sai nasan cewa gazawa nayi shiyasa ka nemi wadda ta fini
amma ZUHRA, HAMZA KWANA DA ZUHRA yana nufin mummunan kaskanci gareni a matsayin mace.
Maganar Izzy ta batawa Hamza rai sosai yace kinga for the last time ki fita daga dakin nan. Kina iya
daukan tarayyata da Zuhra duk abinda yazo ranki amma ki sani matata ce ta sunnah wadda all thanks
to your stupidity na aureta, kuma nake alfahari da auren. Now GET OUT.
Cikin sanyin jiki Izzatu ta tashi jiri na dibarta ta kalli Zuhra da gabanta ke faduwa. Nayi miki alkawarin
barin gidan nan kamar yadda nayi sanadin shigowarki cikinsa. Sai kinyi dana sanin cin amanata kika
kawo kanka ga mijina. Nasan ba laifinsa bane Hamza baya iya dadewa babu mace shine kika yi amfani
da wannan kika bashi kanki. Bakiyi nasara ba Zuhra sai kin koma inda kika fito domin ni ban daukeki a
matsayin mace ba ma.
Hannun Izzatu Hamza ya kama zai fitar da ita ta doke hannun, kada kayi tunanin zan sake bari ka
tabani bayan ka taba waccan kazantar. Fita tayi daga dakin babu ko digon hawaye a idonta. Bakin
cikin da take ji yafi karfin kuka.
Hamza ya juyo ga Zuhra ya rungumeta, sai a lokacin ta soma kuka da sauti. Bayanta yake shafawa kiyi
hakuri Cutie. Duk laifina ne da sakaci har ya janyo haka. In sha Allah Izzatu sai ta koyi mutuntaki a
matsayin matata. I love you so much. Rabon Zuhra da ganin wulakanci tun ranar da aka mata April
fool. Tayi kusan minti goma tana kuka Hamza na aikin rarrashi. Daga baya ta sake shi ta nemi zaninta
ta daura. Hannunta ya riko Cutie ina zaki kuma. Muryarta a dashe tace dakina. Zama yayi ya dorata a
cinyarsa. Ki zauna anan kema kinsan bazan iya barinki ki fita a haka ba. Tashi nayi miki
wanka....murmushi tayi ta dora kanta a kafadarsa ni bazan yarda kayi min wanka ba. Shima murmushi
yayi zaki zo da kanki ne kuma lokacin nima yanga zanyi miki. Rungumeta yayi a jikinsa yana ji tana
ajiyar zuciya. A hankali ta tashi bari naje nayi wanka. Ya dan ja hancinta please Cutie na kada kisa
komai a ranki kinji ko. Komai zai daidaita in sha Allah zanyiwa Izzy magana. Murmushin yake kawai
Zuhra tayi ta fita.
Tana zuwa falo Hamza ya tashi shima wankan yake shirin yi ya jiyo ihunta da salati. A guje ya fito ya
ganta a tsaye jiki na bari. Ya Hamza kaga jini.....jini ne digo digo a falon har bakin kofa. Da hanzari suka
bi jinin har kofar dakin Izzatu. A kulle Hamza yaji kofar ya soma bugawa yana kiranta amma shiru. Duk
ya rude ga Zuhra tana kuka. Sai da ya gaji da bugun ga kofar da karfin tsiya ya tuna yana da spare key.
Daukowa yaje yayi ya bude kofar dakin nata. Kwance suka tarar da ita a sume ga jini yana bin kafarta. [10/14, 9:16 PM] +234 703 570 0909: AL'ADUN WASU í ½í·¿65
Batul Mamman(Mrs)í ½í²–
Gabadayansu ba karamin tashin hankali suka shiga ba. Da sauri Hamza ya koma dakinsa ya dauko
wata doguwar riga ya sakata gaba a baya ya dauko Izzatu. Zuhra ma hijab ta burma ta bi bayanshi da
gudu da wani mayafi da ta gani a dakin Izzatun domin a suturta mata jiki. A kasa suka tarar da Tala da
Nana zata hada mata tea. Idanunta ne suka bi Hamza dauke da Izzatu ga jini a jikinta. Zuhra tace mata
ta kula da gidan da yara zasu je asibiti.
Gudu Hamza ya rinka yi cikin dan lokaci suka isa asibitin. Maaikatan asibitin suka yi masa jagora zuwa
emergency inda aka bukaci su tsaya a waje shi da Zuhra. Haka suka rinka kai kawo a wurin sai gashi
an turo Izzatu akan gado an wuce dakin operation da ita. Hamza ya tambayi wani cikin likitocin
menene ya sameta. Likitan yace bari mu fito zamu yi maka bayani. Ku dai kuci gaba da addu'a.
Sun kusa awa biyu a corridor din babu wanda yake iya yiwa wani magana. Kowa da abinda yake
sakawa da warwarewa a zuciyarsa. Zuhra ce tayi karfin halin cewa Hamza ko zai yi waya gida ya sanar
dasu Hajiya, jikinsa duk a sanyaye yace ya barota a gida. Itama Zuhra tace bata dauko tata wayar ba.
Suna magana likitan ya fito yace Hamza ya biyoshi office. Ga mamakin Zuhra sai taji ya kamo
hannunta suka tafi tare.
Ko zama basu yi ba Hamza yace don Allah ka fada min halin da take ciki. Likitan yace to ka zauna
mana, Zuhra ya zaunar tare da rike mata hannu gam. Likita yace kaine mijinta ko? Hamza ya gyada
kai. Ya cigaba da cewa to sai dai kuyi hakuri bamu iya saving din abinda ke cikinta ba.
Bangane ba doctor? Kana nufin tana da ciki ne.
Kwarai kuwa don har ya kusa wata biyu. To matsalar da aka samu shine mahaifar bata da kwari kwata
kwata. Don ita da abinda ke cikin tare suka fara fitowa.
A gigice Hamza yace fitowa kamar yaya?
Ina nufin bari tayi wanda har mahaifarta ta fara fitowa saboda rashin kwarinta. Shiyasa muka ga dole
muyi mata virginal hysterectomy saboda ceto rayuwarta.
Kokari Hamza yake kada ya rasa nutsuwarsa yace kayi min bayani a yaren da zan gane. A wane hali
Izzatu take?
Likita yace yanzu tana bacci saboda anyi mata allurar anasiziya. In sha Allah nan da kamar awa daya
zata farfado. Abinda nake nufi da hysterectomy shine mun cire mata mahaifa saboda ba karamin
lalacewa tayi ba.
Wata muguwar faduwar gaba Hamza yaji wanda hakan yasa shima ya zauna. Zuhra ta sake kankame
hannunsa saboda firgici. Yace doctor kana nufin yanzu bazata sake haihuwa ba.
Haka nake nufi amma don Allah kayi hakuri bamu fara sanar da kai ba kafin mu aiwatar da nufinmu.
Yanayin da take ciki ne baya bukatar bata lokaci. Idan ta tashi ita tafi cancanta da ta fadi maganin da
tasha ya illata mahaifar haka. Bazamu iya yanke komai ba sai munji daga gareta. Tashi likitan yayi ya
barsu a office din bayan ya gama yi musu bayani.
Yana fita Zuhra ta rungume Hamza tana kuka. Kayi hakuri Ya Hamza duk laifina ne. Ganina ne ya bata
mata rai har hakan ta faru. Da hannunsa ya share mata hawaye...ki dena fadin haka Cutie kaddara ce
da bata wuce kowa. Amma shima a kasan zuciyarsa gani yake kamar laifinsa ne tunda Izzatu ta fada
masa ranar zata dawo, sai abin ya zama kamar cin fuska ma.
Sabon dakin da aka kai Izzatu suka je. A nan ya bar Zuhra yace zaije gida ya fada musu tunda baizo da
waya ba.
******
Daga Hajiya har Mama babu wanda labarin yayi masa dadi. Duk sun tausayawa Izzatu. Mama tace
watan cikin nawa? Ni ban san dashi ba Hamza ya bata amsa. Sai a lokacin ta kula da rigarsa tace ya
gyara ta. Kunu da kayan tea suka hada ya daukesu ita da Hajiya da Adabiyya ya kaisu asibitin sannan
ya dauko Zuhra suka tafi gida. Har lokacin Izzatu bata farfado ba.
Saboda yanayin da suka fita maigadi da Tala suna ganinsu suka fara tambayar ya mai jiki. Zuhra ce
take iya basu amsa tana cewa da sauki. Wanka duk suka yi sannan Zuhra ta sauko ta hada masa
abinci. Da kyar ta samu yasha tea yace zai koma asibitin. Damuwa ce tayi masa yawa yana tambayar
kansa ta ina zai samo kudin asibitin Izzatu? Bashi da sauran kadarar da zai sayar sai wani fili da ya siya
a Kumo wanda yanzu kafin a samu mai siya ma aikine guda. Shi ko irin budewa yara account dinnan
bai taba tunanin yi ba saboda basu hango rana irin wannan da zasu fuskanci matsin rayuwa ba.
Zuhra na kallon yadda ya zurfafa a tunani ta dan dafa kafadarsa. Ya Hamza kaine fa kake cewa
kaddara ce abinda ya faru. Don Allah kayi hakuri. Idan ka bari damuwa tayi maka yawa waye zai
rarrasheta idan ta farfado? Murya a sanyaye yace babbar damuwata yanzu inda zan samo kudin
asibitin Izzy. Kinsan halin da nake ciki bansan inda zan samo kudin ba indai ba kudin kamfani zan
dauka ba. Zuhra tace idan ka dauka aikinku zai sami rauni. Kuma kace har kun kusa kammala daya. Ta
mike tsaye ina zuwa....
Bata dade ba ta dawo da wata karamar leda mai kyau a hannunta. A tafin hannun Hamza ta ajiye
ledar yace koma meye ki rike kayanki zansan yadda nayi na sami kudin. Ko bashi ne sai na nema.
Idonta fal hawaye tace yanzu ka gwammace ka nemi bashi akan ka karbi abinda kake da iko dashi?
Wannan abin da na baka kai ka siya fa? Idan ka karba ai ba yana nuna gazawarka a matsayin namiji
bane. Jarabawace Allah Ya dora maka.
A hankali ya bude ledar ya ciro wata yar roba mai murfi. Sarka ce da dankunne da zobe na gwal a ciki.
Saurin rufewa yayi ya dora mata a cinyarta. Cutie ki dauke kayanki bazan sayar miki da sarkarki
ba....abinda ya kasa fada shine ko pant bai siya mata ba a lefenta. Komai Alhaji ne yayi. Hannuwanta
biyu tasa ta rike kumatunsa tana kallon fuskarsa mai dauke da tsantsar rashin kwanciyar hankali.
Tunda nake ban taba saka gwal ba a rayuwata don an sayar da wanan bazanji komai ba. Duk irin
wadannan abubuwan dama ai saboda rana irin yau ake tanadin su. Ni a abinda su Baba suka koya
min wannan shine aure. Taimakon juna a lokacin bukata batare da mun fita waje mun tonawa kanmu
asiri ba. Su Alhaji ne baka son sanarwa halin da kake ciki to ni din da na sani ka bani damar
taimakonka mana. Sarkar da hannunta ya hada ya rike sosai sai kawai taga hawaye ya fito daga
idonsa. Lallai rayuwa bata da tabbas, babu wani yanayi da bawa zai tsinci kansa yace wannan yanayin
zai tabbata a ciki har ranar busa kaho. Yau kana da arziki gobe waninka ne. Wa zai taba tunanin
akwai ranar da Architect Hamza Nasir Hamza zai karbi taimako a hannun Fatima Bashir? Yarinyar da
ko certificate din shaidar tayi secondary school bata dashi,ga kazanta ga rashin wayewa. Ikon Allah
kenan, kada ka taba raina bawa domin baka san abinda Allah yayi masa na arziki ba. Arziki kuwa ko da
ba na kudi bane. Hawayen da Hamza yake yi ya karyar mata da zuciya ta soma kuka. Haka suka
rungume juna na tsawon lokaci. Daga baya Hamza yace ta tashi su koma asibiti tace a'a yaje kasuwa
ba'a rasa masu bude shago ranar lahadi ya sayar. Ita kuma zata kara yin saka zuwa la'asar ko bai dawo
ba zata yi girki ta tafi asibitin da kanta. Sai da ya kwashe kusan minti biyar yana kissing dinta sannan
ya fita. Bai san da yaya zai gode mata ba. Tunda ya shiga mota har ya isa kasuwar ALHAMDULILLAH
yake ta nanatawa saboda godiya ga Allah da Ya azurta shi da mace tagari a lokacin da rayuwarsa take
tsaka da rushewa.
A dalilin mugun tashin da dollar tayi wanda muke ta addu'a Allah Ya yafe mana Ya kawo mana
sassauci sai da Hamza ya sami dubu dari uku da tamanin da hudu a matsayin kudin sarka, dankunne
da zobe. A haka ma don mutanen sun kula kamar a matse yake da ya sayar.
A hanyarsa ta tsallaka titi ya koma motarsa yaga wata tsohuwa tukuf itama ta rasa yadda zatayi ta
tsallaka. Da a lokacin da yake Hamzansa ne mijin Izzatu ita kadai baya jin zai iya yadda hannunsa ya
taba matar. Amma yanzu ya koyi darasin zaman duniya. Hannun matar ya riko tana tafiya da kyar har
ya tsallakar da ita titi. Godiya ta rinka yi masa tare da addua. Harda dan kukanta tace ba don kai ba
sai nayi kusan minti shabiyar ina kokarin tsallaka titin nan. Magani na karbowa dana yana fama da
lalurar asma. Ta dauki wata leda da magani ta nuna masa. Hamza ya tausaya mata yace baki da wasu
yaran ko jikoki da zasu je miki? Tayi murmushi, shi kadai ne dani. Bayan shekaru shabakwai sai yanzu
matarsa take da tsohon ciki. Idan abin ya tashi ita take zuwa amma yanzu bazata iya doguwar tafiya
ba. Yana ganin kansa a wani yanayi ga wadanda suka fishi. Kudin aljihunsa ya shafa ya sa hannu ya
kirga dubu goma ya bawa matar. Hannu na rawa ta karba tana ta kuka...Allah Ya albarkaci rayuwarka
data iyalinka, Allah Ya rabaka da masifun zamani, Allah Ya baka arziki na halali daga inda baka taba
tsammani ba. Yaro nagode, nagode. Hamza na tsaye har ta shiga adaidaita sahu sannan shima ya tafi
zuciyarsa kamar an cire masa wani nauyi. Hakika sadaka maganin masifa ce kuma waraka daga bacin
rai.
Asibitin ya koma ya tarar Izzatu ta farfado. Raliya ya kira a waya ya sanar da ita halin da Izzatu ke ciki.
Cikin kidima tace gobe zata taho in sha Allah. Tana ajiye wayar ta kira kanwarta Larai ta fada mata
asibitin da suke.
Tsananin bacin rai da kishi yasa Izzatu kuka tunda ta farfado. Yanayin da taga Zuhra da Hamzanta shi
kadai yake mata yawo a ka tunda ta bude ido. Su Mama kuwa sai tausayinta suke yi a nasu tunanin
bakincikin bari da cire mata mahaifa da akayi take yi. Cike da tausayi Hamza yake mata sannu amma
ko kallonsa taki yi. Su Mama sai suka dauke kai kamar basu kula da abinda suke yi ba. Adabiyya tace
Yaya ina Anti Zuhra? Yace zata taho girki yasa bamu fito tare ba.
Basu dade ba kuwa sai gata da kwandon abinci. Bata tashi daga kan sakarta ba sai da tayi mai yawa ta
yadda abin da ya rage mata saura kadan. Itama ko kallo bata ishe Izzatu ba duk da halin ciwon da take
ciki. Sauran 'yan uwan Hamza suma duk sun zo. Zuhra ma ta kira Baba ta fada masa Izzatu na asibiti
yace zasu zo washegari tare da Umma.
Anti Larai kanwar Raliya tazo tare suka karasa yinin sai dai ta baro maigidanta babu lafiya saboda
haka bazata iya kwana a asibitin ba. Dole aka yanke shawarar Adabiyya da Zuhra su kwana da Izzatu.
Ranta inyayi dubu ya baci amma ko tashi bazata iya yi ba shiyasa dole ta hakura. Shabiyu saura na
dare su Zuhra suka fita suka bashi wuri ya dan zauna wurinta. Sai lallabata yake tana kuka ita bazata
zauna da wadda tayi sanadiyar zubar mata da