Aladun Wasu Hausa Book Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Read Hausa Novels

Chapter   25 / 40

72K to 75K   out of 117.5K words

ta rike hannunta na dama tana kuka sosai. Saurin matsowa yayi kusa da

ita Cutie me ya same ki? Kara matsawa tayi baya tana kuka tace kada ka matso Ya Hamza ni tawa ta
kare. Bai fahimci inda zancen nata ya dosa ba yace taki ta kare kamar yaya? Ki dena kukan kiyi min
bayani.

Murya a shake tace abinci naci a wurin nan, ta nuna kujerar...sai bacci ya daukeni amma na tabbatar
ban wanke hannu ba. Ina farkawa yanzu naga alamun an lashe hannun amma dai da saura kadan.
Hannun damanta ta daga ta nuna masa. Yayi murmushi zai fada mata shi ya goge mata da tissue ta
cigaba da magana. Ashe ni kuma a haka zan tafi Ya Hamza, Allah ma Ya sa mutuwa a dalilin annoba
ana sakata cikin shahada. Ta sake barkewa da kuka, bera ya lashe min hannu Ya Hamza, ya saka min
zazzabin lassa. Yadda Zuhra take kuka da gaske ya bashi dariya sosai. Yace banda sharrinki Cutie kin
taba ganin bera a gidan nan. Tace shi bera ina ne baya shiga. A yadda naji a rediyo mutum ba wani
dadewa yake ba idan ya kamu da ita.

Dariya Hamza yake son yi amma ya gimtse. Zuhra bata da dama ya fada a ransa. Hannu ya mika mata
zo kinji Cutie dina, babu wani bera ki kwantar da hankalinki. Can karshen dakin ta koma kada ka
tabani ka kwasa kaima. Ka barni kawai anan har lokacina ya cika. Kodayake naji ance gwamnati na
bayar da magani ka sanar dasu akwai mara lafiya a nan sai suzo su daukeni. Ta sunkuyar da kai, nasan
ma dakyar zan kai labari. Shi dai Hamza dramar Zuhra nishadi ma ta saka shi ya zauna akan kujerar da
ta tashi tace tashi kada ka dauka anan na kwanta. Yana kallo tasa hannun hagunta ta dan tattaba
wuyanta. Kaga har na fara jin zazzabin kuwa. Yace Allah ko Dr Zuhra yana murmushi. Sake taban
wuyan tayi tace inajin ba zazzabin bane amma shima nasan yana kusa.

Hamza ya taso ya taho wurin da take tsaye ni zan zauna dake ko wane irin ciwo kike dashi kinji.
Hannu ta daga masa alamun kada ya matso fuska duk hawaye tace Allah Sarki Ya Hamza shiyasa nake
SON ka wallahi saboda kana da kirki da tausayi. Cak Hamza ya tsaya maganarta ta sauka a zuciyarsa. A
hankali ya daga kai ya kalleta. Da gaske kina sona Cutie? Kunya taji har ta soma girgiza kai sai ta dena
ta dago tana kallonsa. Ya Hamza idan mutum zai mutu ai babu zancen kunya da karya ko? Gara ma na
fadi gaskiya na sami lada. Hamza yace wannan gaskiya ne. Zuhra harda gyaran murya tace nasan
munyi daku zaka sakeni bayan wata shida to Allah Ya gani wallahi ni bansan ya akayi ba sai naji ina
sonka. Ba a matsayin Yayana ba fa. Dadi Hamza yake ji sosai sai ya dan basar to a matsayin me?
Sunkuyar da kanta tayi tana magana a hankali. Wallahi Ya Hamza irin na soyayya nake maka jiya har
mafarki nayi ka kaini asibiti zan haihu. Amma kada kace min mara kunya wallahi ina zaman zamana
tunanin yake zuwa. Kuma in fada maka wata gaskiyar ma duk sallah a sujjada sai nayi addua'a idan da
alkhairi Allah Yasa kada ka sake ni. Tamkar ya zuba ruwa a kasa yasha haka Hamza yake ji a wannan
lokacin. Ashe ba shi kadai yake sonta ba suka yi shiru da zasu kwari kawunansu. Ya dan bata rai dazu
kika ce bakya sona kuma har kin tsayar da mijin aure. Tace wallahi karya nake, irin abin nan ne na
mata zan maka ashe ma bani da rabon dadewa a gidan aure.

Ko kanta ta kasa dagawa saboda yadda take jin kunya gashi zata mutu ko soyayyar basu fara ba. Takun
Hamza taji ya matso gabanta yasa hannu ya bude bargon da ta rufe kanta dashi. Kuka take tana
rokonsa zai kamu da zazzabin lassa. Hamza yayi mata kyakkyawan murmushi sannan ya dauketa
tamkar ya dauki karamar yarinya. Da wata bakuwar murya mai dadi yace Cutie ni na goge miki
hannun da tissue, ta ware masa idanunta da yake son kallo tace da gaske? Ya gyada kai. A take kunya

mai tsanani ta lullube Zuhra. Hamza yayi murmushi yace bari na karasa lada na nayi miki wanka, sai
na fara koya miki lesson din soyayya. Irin soyayyar da zata sa mafarkinki na jiya ya tabbata nan da
wata tara. Kanta ta tura a kirjinsa don kunya ta kankameshi. Zuciyarsa cike take da son Zuhra yace
kinsan wani abu? Girgiza kai tayi batare da ta dago ba...I love you too Cutie. Nima bansan yadda akayi
ba sai kawai naji ina matukar sonki. Dadi ne ya mamaye zuciyarta wai ita Hamza mijin Izzatu yake
furtawa so. Tafiya taji ya fara yi da ita hanyar toilet ta soma kokarin zillewa.
[10/14, 9:14 PM] +234 703 570 0909: AL'ADUN WASU 🗿63

Batul Mamman(Mrs)💖





A kofa toilet ya ajiyeta ya fara juyata a gabansa yana karewa kayan jikinta kallo. Kokarin rufe jikinta ta
soma yi yace wai ni ta ina kika saka rigar nan? Duk na duba na rasa maballi ko zip. Ajiyar zuciya tayi
mai karfi tana murna da bai gani ba. A tsorace take da Ya Hamza. Janyota yayi jikinsa ya zagayeta da
hannuwansa. Daga gefen kafadarta ta dama taji ya kama zip din wanda yake boye a jikin riga ya soma
sauke mata shi kasa. Duk yadda tayi ta gudu abu ya gagara. Jiki na rawa tace Ya Hamza don Allah
banda wanka. Yace kin manta sunnah ne? A'a amma akwai wasu dayawa. Idan nayi wankan da kaina
duk abinda kake so zanyi maka. Wani murmushi yayi mata wanda shi kadai yasan ma'anarsa yace to
amaryata. Zan jiraki a daki. Sai da ya manna mata kiss a goshi sannan ya tafi.

Sai yanzu take jin tsoron Ya Hamza kuma. Wanka zatayi kawai tayi kwanciyarta. Ta dade tana kalkale
jiki ta fito aka bata lokaci a gaban mudubi ana ta shafe shafe. Turaruka ta saka masu kamshi sosai da
daukar hankali sannan ta daura zani ta tayar da sallar isha da bata yi ba. Tana idarwa ta cire hijab ta
fara neman rigar da zata saka. Daga ita sai daurin kirji Hamza ya turo kofar.

Cikinta har kullewa yaso yi don kaduwar da tayi. Yana lura da yadda ta kidime ya matso daf da ita.
Zuhra idanu kamar su fado kasa don tsoro tace dama riga zan saka na fito. Yace Cutie ba na hanaki
daurin kirji ba. Da sauri tace yanzu zan kwance nasa kayan bacci. Don Allah ka tafi zan zo. Bai kulata
ba sai ma hugging dinta da yayi yana murmushi. Kamshi kike yi maidadi Cutie. Ita dai kasa magana
tayi jin yadda yake shafa kanta. A hankali ya saketa ya bude inda kayan baccinta suke. Wata riga ya
dauko ruwan madara wadda da alama sabuwa ce ya warwareta. Bazata wuce mata gwiwa ba amma
tamkar net haka take tasha ado sosai. Tana kallo ya karasa gaban mirror ya fesheta da turaruka
sannan ya ajiye a kan gado. Wani irin kallo yake bin Zuhra dashi yace saka hijab muyi sallah.

Idan baka kalli bakinta ba bazaka ji yadda tace nayi sallah ba can a kasan makoshi. Yace wannan nafila
ce da zamuyi kafin mu kwanta. Abin sallah ya shimfida a gaban nata ya jasu sallah raka'a biyu. Bayan
sun idar ya dade yana musu addua sannan yayi mata alama da hannu. Dan matsawa tayi kusa dashi
ya dora hannunsa a kanta ya karanto addu'a kamar yadda yazo a sunnah.

Rigar da ya ajiye ya dauko sannan ya kama hannunta ya kashe fitila suka tafi dakinsa. Kamar wani
sabon mutum haka take ganinsa. Sonsa ne yake karuwa a zuciyarta amma ta kasa sakin jiki. Sai da ya
kaita har bakin gado sannan ya kama hijab din ya cire mata. Duk abinda yake yi idanunsa a kanta yana
yi mata murmushi. Rigar hannunsa ya saka mata sannan a hankali ya zare zanin ta kasa. Bin jikinta
yiya da kallo ita kuwa kamar walkiya don sauri ta haye gado ta kudundune jikinta. Dariya yake yi yana
kallonta ke da kika ce zaki min duk abinda nake so, ai ban fara ba ma. Zuhra ta turo baki cikin
shagwaba Ya Hamza haka ake soyayyar,ka sa sai kunyarka nake ji. Sai da ya kashe fitila ya zauna kusa
da ita yace wannan sunansa sharar fage yanzu za'a fara karatun sosai. Tana ji ya kwantar da ita rub da
ciki, tashi take sonyi domin bata san abinda zaiyi mata ba. Ga mamakinta hannuwansa yasa a bayanta
ya fara yi mata tausa tun daga kafada har karshen bayanta. Nasan kin gaji sosai just relax ki huta. Yau
karatun bazaiyi nisa ba naga duk kin tsorata. A hankali ta saki jikinta tana dan murmushi. Bata taba
kawowa a ranta rana irin wannan zata taba zuwa tsakaninsu ba. Ya kusa minti goma yana yi mata
tausa yaji tayi shiru. Cutie, ya kira sunanta a hankali. Itama a hankalin tace Ya Hamza. Gyara mata
kwanciya yayi ya dora kansa a kirjinta tare da kankameta a jikinsa. Tace Ya Hamza kunyarka nake ji
sosai. Hannuwansu ya hada wuri daya yace zan rage miki ita a hankali ne Cutie. Yanzu bacci nake so
kiyi saboda kin yini kina aiki. Kansa ta shafa a hankali tace a haka zanyi baccin da kanka a kirjina
kamar wani baby? Dagowa yayi duk da duhun dakin ya saita fuskarsa da tata. Cutie na fada miki miji
tamkar baby ake son matarsa ta rinka bashi kulawa. Gyada kanta tayi tace to sai da safe. Yace babu
goodnight kiss? Rufe ido tayi ita kam yau Ya Hamza ya hanata sakewa. Idonta a rufe taji lips dinsa
akan nata. A hankali yasa ta saki jikinta har suka dade a haka. Daga baya ya kwantar da ita a jikinsa a
kunnenta yace love you Cutie, yanzu da nasan wace ce ke bana fata Allah Ya kawo abinda zai raba mu
. Kanta na kirjinsa tace love you too Ya Hamza tana mai jindadin abinda ya fada .

A haka bacci maidadi ya daukesu. Hamza yana tunanin ranar da zai mayar da ita cikakkiyar amarya. A
hankali yake so ta gama sakin jiki dashi sannan su gina soyayyarsu cikin aminci.

Ita ta fara tashi da asuba Hamza na rike da ita kamar zai mayar da ita ciki. Murmushi tayi cike da
farincikin Allah Ya amsa adduarta Ya daidaita tsakaninta da mijinta. Kwantawa ta sakeyi kusa dashi ta
kama gashinta ta soma zirawa a cikin kunnensa. Sau biyu yana kawo hannu idonsa a rufe sai tayi
saurin matsawa. A na ukun janyota yayi ta fado jikinsa. Ya dan bude idanu, Cutie tsokana ko? Dariya
tayi ka tashi asuba tayi. Ya sake rufe ido ba fa haka ake tashin miji daga bacci ba. Ina koya miki karatu
kin kasa....bakinta ta hada da nasa tayi kissing yaji wani abu na masa yawo a jiki. Kafin ya ankara ta
tashi ta fice daga dakin da gudu. Shi kam ya dace da mata ya fada a ransa sannan ya tafi yayi alwala.

Yana dawowa daga masallaci suka hadu da ita tana saukowa zata kitchen. Kada ma ki karasa saukowa
ya fada yana hawa benen. Ta dan bata fuska Ya Hamza ina da aiki da yawa fa. Ya kwaikwayi muryarta
Cutie baki da aikin da ya wuce nawa, ni kuma bacci nake so mu koma. Daukarta yayi tana dariya ya

koma da ita. Tala dake makale a bakin bene basu ganta ba tace Allah Yasa Hajiya Izzatu sai badi zata
dawo gidan nan.

*****
Karfe takwas na safe jirgin su Izzatu ya sauka a filin jirgi na Mal Aminu Kano. Ta kira wayar Hamza yafi
sau ashirin bai sani ba. Wayar tana falonsa tun dare yasa ta a chaji. Ranta a bace domin tayi zaton zai
zo tararta a airport din. Gajiya tayi ta nemi taxi ta daukota har gida.

Koda maigadi ya bude mata kofa sai da jinin nasa ya dan haura. Shikenan zasu dena jindadi yadda
suka saba. Tala ma tsoro ne ya bayyana a fuskarta da suka hada ido da ita. Ta wayance tana
tambayarta lafiya ta dawo da sassafe? Izzatu tace Babyna bai fada miki kiyi min girki ba zan dawo yau
da safe? Anyway ki kai min jakata daki tana bakin kofa. Tana magana tana hawa sama. Tala tace yau
mun shiga uku.....
Dakinta ta fara zuwa tayi wanka aka sha turare da kwalliya sannan tasa wata doguwar riga iya gwiwa.
Surprising din Hamza zata yi. Tasan kila makara yayi shiyasa baije daukanta a airport ba.
[10/14, 9:15 PM] +234 703 570 0909: AL'ADUN WASU 🗿64

Batul Mamman(Mrs)💖





Tunda Hamza ya kai Zuhra daki akan gado ya ajiyeta ya soma bubbuga hannu, wai yarinyar nan haka
kike da nauyi dama. Zuhra ta turo baki ni bani da nauyi. Yadda bakinta yayi ya bashi sha'awa ya zauna
kusa da ita yasa dan yatsansa yana shafa bakin. Ina son dan bakin nan naki na rashin kunya Cutie mai
nauyin buhun shinkafa biyu. Zuhra ta hade fuska kamar zata yi kuka ta sauke kafafunta daga kan
gadon. Ni dakina zan tafi, dama dauko ni kayi don ka tsokaneni. Kuma yau da daurin kirji zan wuni a
gidan nan. Yayi murmushi Allah Ya baki sa'a da yin daurin kirjin nan. Idan suka koma suka kwanta
kamar na wata tsohuwa aure zan kara yi. Zuhra tace suwaye zasu kwanta? Abinda kike daurewa da
zani mana ko na nuna miki su? Sunkunyar da kanta tayi tana murmushi don ta gane abinda yake nufi.
Shima murmushi yayi ya tashi ya cire rigarsa saboda tun asuba yasa ake kashe inji yanzu. Garin sai
yayi zafi kamar za'ayi ruwa dama wasu garuruwan na kusa da Kano sun fara samun ruwa. Tana ji tana
gani ya kwance mata zanin da ta daura akan 'yar rigar jikinta tare da cire mata mayafi. Yace to mu
kwanta da gaske bacci nake ji. Jiyan nan....sai yayi shiru yana gyara kwanciya a kusa da ita.

Ya Hamza me ya faru jiyan?

Babu komai Cutie kawai dai ki shirya yau ba irin jiya bane.

Danyi min bayani meye bambancin jiya da kuma yau da kace na shirya.

Bai bata amsa ba sai kallo da yake binta dashi. Zuhra tayi masa kyau sosai ga rigar jikinta.....

Kula tayi da abinda yake kallo taji kunya. Rufe jikinta tayi tana cewa Ya Hamza zan dena zuwa dakinka
indai haka zaka rinka kallo na. Yace to na dena amma dan cire bargon kinga ai babu laifi idan na kalli
matata. Dariya tayi ta sake kankame jikinta. Tashi yayi ya koma can inda kafafunta suke ya daga
bargon ya turo kansa. Dariya Zuhra takeyi tana cewa yayi hakuri.

Bakiga komai ba yarinya ya fada lokacin da ya fito da kansa a daidai kirjinta da yake dukan uku uku.
Runtse idonta tayi saboda yadda take jin kunyarsa. Gabadaya ya danneta sannan ya zubawa fuskarta
idanu. A hankali ya fara kissing ko'ina a fuskar har ya kai bakinta. Jira kawai take yayi mata abinda ta
fara sabawa dashi sai taji ya tsaya tana jin saukar numfashinsa a fuskarta. Cutie kice kin yafe min duk
abinda nayi miki a baya. Ido a rufe tace Ya Hamza na yafe nima ka yafe min. Ya sake matso da
fuskarsa, kin yafe har da na kusa cutar kaina nace zanyiwa Inuwa tayinki? Hakan ya bata dariya ta
bude ido a hankali. Har shi na yafe Ya Hamza.

Ya lumshe ido to tabbatar min da hakan.

Bata san a inda ta sami kwarin gwiwar daga hannuwanta ta sauko da fuskarsa sosai ta hada bakinta
da nasa. Shiru bata kara komai akan hakan ba yace naga alama karatun nan bai gama shiga kanki ba.
Kinga yadda ake yi.....daga nan ya fara nuna mata sabon salon da bata san akwai shi ba.

******
Da wata irin tafiyar jan hankali Izzatu ta shigo falon Hamza. Da tayi niyar kiran sunansa sai ta fasa
kada ta bata surprise dinta. A hankali ta bude kofar dakin ko bacci yake yi kada ya tashi sai ta kwanta
a kusa dashi. Labulen ta daga ta dan tura kai......tamkar wadda taga wani mugun dodo haka tayi
saurin sakin labulen ta koma da baya a hankali. Dakinta ta tafi kai tsaye ta wuce bandaki ta wanke
fuskarta da sabulu. Ta fito ta tsaya a gaban mudubi tana mayar da numfashi a wahale. Lallai Izzatu,
yau da abinda kika gani gaske ne kila sai kin shiga coma. Shine abinda ta fada a zuciyarta sannan ta
sake sabuwar kwalliya ta fita. Tasan ba wani abu bane dama ance abinda kafi so ko kafi tsana wani
lokacin sai kaga yana maka gizo. In ba haka ba me zaisa taga hannuwan mace sun rungume mijinta
Hamza suna kissing juna irin haka.

*******

Zuhra ke kokawa da Hamza ya dage sai ta cire rigarta tasha iska. Kamar tayi kuka tace Ya Hamza,
bama Yaya ba, Baba Hamza kayi hakuri mana. Yace ni gaskiya Inna Fatima bazan hakura ba. A haka
kike son nan da wata taran na kaiki asibiti haihuwa. Yana jan rigarta itama tana ja suna ta dariya.

*****
Sake komawa dakin nasa Izzatu tayi sai dai wannan karon tun daga falon take jin dariyar Hamza da
wata mace. Zuciyarta ce tayi wani mugun bugu kamar zata ballo kirjinta. A fusace ta banka kofar
dakin ta ga wace karuwar Hamza ya kawo gidansa.

Karar kofar ya mayar da hankalin Hamza da Zuhra kofar dakin. Izzatu ce ta shigo tamkar wata zakanya
idanunta sun kankance babu abinda ake gani sai tsantsan bacin rai.

Shima Hamzan a fusace ya tashi da ya ganta. Shaf ya manta tace yau zata dawo amma duk da haka
hakan bai zama

25 / 40