Aladun Wasu Hausa Book Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Read Hausa Novels

Chapter   28 / 40

81K to 84K   out of 117.5K words


murmushi tace da dadi....Hamza ya dauke plate din to kinci rabonki. Rokonsa ta fara yi taga yaki kawo
mata, wuri ya samu ya zauna yana ci. Ta zauna ta soma kukan karya sai ya kawo mata. Tare suka
karasa ci suna hira. Suna gamawa ya kulle gidan yace to sai bacci.

A kofar dakinta tace masa zata je tayi wanka. Yace ke da kika gaji, muje ki dauko kayanki a dakina zaki
kwana. Duk abinda zata bukata shi ya dauko mata sannan suka tafi dakinsa.

Kai tsaye ta shige toilet zata yi wanka. Ta gama tara ruwa mai zafi saboda hannuwant da kafada duk
sunyi tsami tana son gasa su taji an bude kofar. Wani irin ihu ta saka ganin Hamza a tsaye daga shi sai
dogon wando. Da sauri yaje ya toshe mata baki da nasa. A haka ya karasa cire mata riga. Kuka take
masa kamar wadda zai yanka yayi murmushi kin fiye tsoro Cutie. Ni taimakonki nazo yi kike min kuka.

Hannunta ya kama tana ta harararsa ya sakata a cikin bahon sannan ya dauko karami tawul ya saka a
ruwan zafin ya danna mata a kafada. Wani ihun tayi ta mike zata gudu ya riketa sosai. Kinga idan baki
zauna ba matseki zanyi. Ki cigaba da hararata sai idanunki sun fado.

Kunya taji ta dena harararsa. Kamar mai rada tace Ya Hamza ka dan rufe ido mana.

Ki dena magana ba'a son surutu a toilet. Daga nan duk kauce kaucenta haka ya gasa mata jiki sosai
sannan yayi mata wanka. A katon tawul ya nadota ido duk sunyi ja saboda kuka. Da kansa ya shiryata
sannan ya dauko wata katuwar shirt dinsa ya saka mata. A bakin gado ya zaunar da ita shima yaje yayi
wankan ya fito. Har ya gama shiryawa Zuhra na tura baki. Cak ya dauketa suka kwanta ta janye jikinta
can gefe.
Haka kawai kayi min wanka kamar wata yarinya karama. Ni bazan sake wanka a dakinka ba.

Yana ji tana mita yayi dariya...zo na baki hakuri kinji my cute baby.

Matsawa tayi gefe yasa hannu ya janyota ta fado jikinsa. Fuskarta yake shafawa da hannunsa daya
yace duk abinda nayi miki kiyi hakuri harda wanda zanyi miki ma.

Tace wanne kuma.....bai barta ta karasa maganar ba ya katseta ta hanyar kissing dinta da nuna mata
soyayya irin wadda ya jima yana fatan zuwan ranar da zai nuna mata.
[10/14, 9:19 PM] +234 703 570 0909: AL'ADUN WASU 🗿68

Batul Mamman(Mrs)💖

Babu irin yadda Hamza baiyi ba domin ya tashi Zuhra da asuba taki tashi. Ganin yana neman rasa
sallah yasa ya rabu da ita yaje yayi wanka ya tafi masallaci. Niyarsa idan ya dawo sai ya sake tashinta.

Tana jin sautin rufe kofar ta yaye bargon jikinta ta tashi jiki babu kwari. Abinda Ya Hamza yayi mata ne
yasa ta tashi da wata irin kunyarsa, da wane ido zata sake kallonsa ma. Shiyasa tayi shiru tamkar bata
jinsa lokacin da yake ta kokarin tashinta.

Dama ita bata iya jin ciwo ba ta rinka raki da koke koke kenan to yau an sami maidalili. Da kyar ta iya
zama cikin ruwan zafi sannan daga baya tayi wanka ta fito. Don kokari harda dan fesa turare tunda an
zama 'yan gayu sannan tayi sallah. Zama ta cigaba tana azkar bayan ta idar taji har taji alamun
antaba kofa.

Jiki na rawa ta tashi ta jefar da hijab dinta ta haye gado. Har kanta ta rufe ta koma ta kwanta ko
numfashin kirki bata yi.

Dariya ta bawa Hamza da ya kula tabbas tayi sallah bayan fitarsa. A gefenta ya zauna yana mata
magana a hankali.
Cutie bazaki tashi mu gaisa ba?

Shiru tayi babu amsa sai alamun tana kuka da yaji.

Da kyar ya iya budeta ya kwantar da ita a jikinsa. Yace dama matsalar irinku kenan wadanda suke
tashi babu wa babu kani. Kunfi kowa iya shagwaba. Yanzu duk kukan da kika yi jiya bai isheki ba shine
zaki tashi da wani sabon.

Tashi tayi suka hada ido tayi saurin juyar da kanta, to ba kai bane ina ta......

Yace na fa baki hakuri tunda wuri kuma me ya rage? Hmmm ko baki gane lesson din bane da kyau. Ya
fada yana kashe mata ido.

Murguda baki tayi ni bance ka koya min irin wannan ba.

Eyye, Cutie ashe baki dena tsiwa ba. Lallai ya kamata a maimaita karatun ko zaki fi dauka. Irin wannan
juya baki kamar idan na fara kissing kada na saki.

Ido ta rufe ta kwanta a jikinsa...ai nasan Ya Hamza yana da kirki bazai kara sani kuka ba ko. Don Allah
kayi hakuri na dena yi maka tsiwa.

A hankali yace gaskiya banyi miki alkawari ba. Ke ko irin addu'ar da maza ke yiwa matansu da safe irin
haka baki bari nayi miki ba sai korafi. Tashi zaune kiji wannan kwanciyar da kike yi a jikina sake kashe
min jiki kike yi.

Yadda yake magana yasa da saurinta ta tashi harda matsawa gefe. Hamza ya rinka
dariya...matsoraciya kawai. Sannan ya kama hannunta...nagode miki Allah Yayi miki albarka Ya bamu
zuri'a dayyiba. In sha Allah Zuhra zan rike ki amana kuma zan so ki fisabilillah. Idan har nayi miki wani
abu ba daidai ba ina so ki rinka fada ba ki barshi a ranki ba muzo muna samun rashin fahimtar juna.
Naso ace kinyi wanka a gabana dazu domin nasani ko akwai gyara duk da nasan matar tawa tana da
ilimi. Amma kamar yadda naji wata malama Ummi Aisha tana fada yana da kyau duk miji ya san ko
matarsa ta iya tsarki.

Zuhra dai kunya duk ta isheta ta sunkuyar da kanta kasa. Hamza yace ina jinki fada min yadda kika yi
ko muje nayi miki da kaina. Sanin ba karamin aikinsa bane yin hakan yasa ta soma yi masa bayani a
hankali kamar wadda aka kamawa baki. Ya gamsu sosai da amsar da ta bashi yace to yanzu me ya
rage?

Zuhra tace naje kitchen nayi girki ko don asibiti...tana magana ta tashi da sauri saboda su Junior da ta
tuna.. .Ya Hamza su Khalifa yau bazasu school ba? Tashi ka kaisu gashi har bakwai da kwata.

Murmushi yayi...kinsa miji a daki kina masa dadin baki ba dole ki manta da yaranki ba. Ta tura baki ta
fara jan hannunsa, don Allah ka tashi kada su makara yau. Yace to laifin waye? Ko kadan bai damu ba
harda kishingida akan pillow Zuhra tana ta kokarin tayar dashi.

Gajiya tayi ta hakura bari naje kasa nasan Tala tayi musu wanka. Don Allah ka taso kaji Ya Hamzana.
Har wani fari take masa da ido duk don ya tashi. Sai da ya bari taje kofa sannan ya kirata. Da sauri ta
dawo amma hankalinta yana kan yaran da tasan tun waccan alhamis din bayan dawowarsu daga
Kaduna suka fara jarabawa.

A gabansa ta dan durkusa tana jiran taji dalilin kiran. Bakinsa ya nuna mata...yau bamu gaisa ba. Idan
kina so na tashi kizo mu gaisa. Kuma ki dena tafiya da sauri sauri kafin kizo kina min raki anjima.

Kallonsa kawai take yi yadda yayi kwanciyarsa kamar bai damu da zuwan nasu makaranta ba. Bakinsa
ya sake nuna mata tace jiya fa kaji min ciwo har ya kumbura ko ka manta? Dariya yayi ....you are not
serious, duk abinda kika yi da bakin nan jiya sai yanzu zaki tuna da ciwo. Ko dai kiyi abinda nake so ko
yaranki su zauna a gida yau.

Da sauri ta fada jikinsa saboda tana hangowa su Khalifa makara sannan ta hada bakinta da nasa. A
hankali Hamza ya rinka janta har ta saki jiki. Da kyar ta iya tuna masa su Khalifa...yace don't worry sun
gama exams jiya so bazasu school ba sai ranar friday da zasuyi class party. Ta dan daki kirjinsa amma
shine....bata sami damar karasa maganar ba ya katseta da wani salon soyayyar tasa.

****
Sai shadaya saura ta samu Hamza ya kyaleta ta fito. Wanka ta sake yi ta saka wani lace dinta mara
nauyi. Dinkin yayi mata kyau riga da zani tayi kwalliya sai kamshi take yi. Dakinsa ta fara shiga ta same
shi zaune akan gado da laptop bashi da niyyar tashi. Ya dago mata hannu alamun ta je wurinsa...Cutie
kinyi kyau. Har nan nake jin kamshink mai dadi. Murmushi tayi a kunyace tace ina daga nan Ya
Hamza. Ni yanzu ko hannunka tsoron tabawa nake yi. Yana daga zaune ya rinka dariyar maganarta. Ka
fada min me zaka ci ni yunwa nake ji. Kansa ya kada irin ya zama abin tausayi tunda taki zuwa. Zaki
kawo kanki ne yarinya. Yanzu dai ki hada min tea kuma idan akwai sauran tuwon jiya ki dumama min.

Bata jima ba ta kawo tea din falonsa da tuwon suka ci sannan tace zata dora abincin rana. Rabin cin
abincin duk Hamza ke tsokanarta tana ta sunkuyar da kai. Can tace ni har kunya nake ji ba'a kai
abincin safe ba asibiti kuma duk laifinka ne. Ya dauke kai su Mama sun aika shiyasa kika ga ban damu
ba. Abincin ranan ma kiyi wake da shinkafa amma da manja shi nake sha'awa yau. Zuhra tace to
abincin asibitin fa. Ya dan sha kunu, suma shi zasu ci ko akwai matsala ne? Zuhra tace babu, sannan
ta kwashe kwanukan ta sauka kasa. Amma a zuciyarta tana tunanin yadda mara lafiya zata ci wake da
shinkafa da mai duk da Izzatun ta fara cin abinci.

Kafin azahar ta gama komai na abincinta ta hada salad da kunun aya yasha kankara. Su Junior duniya
sabuwa sunji dadin abinci sai karawa suke yi. Bayan sun gama ta shiryasu saboda Hamza yace tare
dasu zasu je asibitin.

Sai da yayi sallah ya gama nuko nukonsa sannan ya fito suka tafi. Duk motsin Zuhra akan idonsa jin
kansa yake kamar sabon shiga a aure saboda irin son da yake yi mata. Makarantun da suka bada aikin
saka suka fara zuwa ya kai musu duk suka biya suna yaba kyan aikin da saurin da akayi aka gama. Sai
gashi ya tashi da dubu dari uku da arba'in da hudu kudin da duka makarantun suka biya. A mota ya
rinka yiwa Zuhra addua yasa su Nana suce Amin. Bakinta kamar gonar auduga don farinciki saboda
yadda taga Hamza yayi murna. Har cewa yayi washegari zai karbo mata form ta cike zai bude mata
account. Dubu dari biyu da hamsin zai saka mata a cikin kudin sauran suyi amfani dashi a gida. Tun a
wurin tace bata yarda ba yace to abar magabar sai sun koma gida.

*****

Duk magiyar da Raliya tayiwa Izzatu sam taki yarda taci abincin da aka kawo daga gidansu Hamza da
kuma na gidan Anti Larai tace tana jiran Hamza tasan duk tsiya bazai barta da yunwa ba. Anti Larai dai
ko kulata bata yi ba dama ba shiri take yi da Izzatu ba. Tun su Hajiya na asibitin ake cewa taci taki cin
komai har suka tafi. Raliya tace ke yanzu banda baki da kunya yaushe zaki jira Hamza mutumin da
kika batawa rai. Kina kallo yau tun safe bai zo ba shi da yana kai yara makaranta yake tahowa. Izzatu
dai ta kafe bazata ci abincin ba dole Raliya ta kyaleta.
Sai wurin karfe uku suka iso asibitin. Su Khalifa ne suka fara shiga dakin da gudu Hamza da Zuhra na
bayansu. Shi ya dauko kwandon abincin ma sannan suka shiga dakin yana rike da hannunta yana
tsokanarta tana dariya.

Kiris ya rage Izzatu ta hadiyi zuciya sai dai ta hakura. Tunda yazo tasan baya iya dogon fushi da ita.
Wannan 'yar banzar yarinyar kuwa sai tayi maganinta.

Zuhra da Hamza suka gaisa da Raliya sannan Zuhra tayiwa Izzatu ya jiki. Kamar tayi magana da dutse
haka ta shareta. Khalifa yace Mummy baki ji Maama tana yi miki ya jiki ba? Izzatu ta dan matse banji
ba Khalifana. Junior ya dora hannuwansa biyu a baki yace Daddy kaji Mummy tayi karya ko? To mai
karya dai dan wuta. Mu duka a dakinnan munji sai ke kadai. Hmmm, Maama fadawa Mummy idan
jirgin aljannah yazo a nan zamu barta. Hamza ya kwashe da dariyar mugunta yace haka ne Junior
Allah Ya shiryi masu karya. Yara suka ce amin. Ran Izzatu ya gama baci tace zuwa kayi ku wulakantani
kai da matarka? Shine zaku saka 'ya'yana ma su tsaneni ko. Zuhra ce tayi karfin halin bata hakuri, shi
kuwa Hamza dariya ya sake yi ya cigaba da wasa da yaransa.

Raliya ta bude abincin zata zubawa Izzatu. Tana daga kan gado amma idanunta na ga abinda
mamanta ke yi. Kamar tayi kuka tace Mum me nake gani kamar wake da shinkafa. Raliya tace shine
kinji kamshin kayan salad ko? Tana bude man Izzatu ta sa ihu, Mum manja ne fa. Raliya tace to sai me
kike yamutsa fuska kamar kinga abin kyama.

A raunane Izzatu ta kalli Hamza,Baby wane irin abinci ne wannan kuka kawo min? Yace irin abincin da
muke ci ni da iyalina. Sai nanatawa take yi a ranta wake da shinkafa. Basu taba yi ba tunda suka yi
aure. Kamar tayi kuka tace ko dai ka sami karayar arziki ne, shi kadai ne dalilin da zaisa a fara cin irin
wannan a gidanka. Junior ya dubi abincin da Raliya ta gama hadawa yayi kyau yace Mum ki bani inci,
Maama ta iya girki.
Izzatu tace haba ko da naji,ashe Zuhra ce ta dafa. Kaga irin abinda nake fada maka ko. Yarinyar nan
bazata ta taba wayewa ba. Kamar kai Baby aci wake da shinkafa a gidanka sai kace wani talaka. Jikin
Zuhra duk yayi sanyi.

Hamza yace Cutie ga key ku tafi mota da yaran ina zuwa. Tana fita ya zauna a gaban Izzatu ya
warware mata halin da yake ciki da irin gudummawar da ta bayar wurin fadawarsa wanda yasa ta

mugun mamaki. Ya mike tsaye...saboda haka Izzy ki kiyayeni domin ko banyi aure ba ina gab da
sakinki wallahi saboda kin jefani cikin tashin hankali sannan dayake kinfi amara son biki kika tsallake
kika barni. Izzatu tace don ka sami matsala sai kayi min sharri? A take ya tuna mata duk abubuwan da
tayi wadanda sukayi sanadiyarsa fadawa wannan halin. Baki bude haka ya fita ya bar Izzatu da Raliya
don ma bai fada musu yadda Zuhra ta taimaka masa ba. [10/14, 9:20 PM] +234 703 570 0909: AL'ADUN WASU 🗿69

Batul Mamman(Mrs)💖






Daga asibitin gidan 'yan uwansa mata suka wuce. Dukkaninsu sunyi farincikin ganin Zuhra kowacce
tana janta a jiki. Daga nan suka je gidan Anti Faiza wadda ta rasa inda zata sa kanta don murnar ganin
Zuhra da Hamza tare. Dabarun kula da miji ta sake karanta mata da kyau sannan na karshe suka je
gidan Ibrahim. A nan suka ci abincin dare sannan suka taho bayan Hamza da Ibrahim sun dawo daga
sallar isha.
Kafin suje gida su Khalifa duk sunyi bacci sai Hamza da Zuhra ke ta hira. Kayan da suka biya suka siyo
Zuhra ta iya dauka yaran kuwa Hamza ne ya dauko su. Dama sauri take su iso gida gabadaya bata
jindadin jikinta tun yamma daurewa kawai take yi tana tafiya.

A dakinsu ya kwantar dasu Zuhra ta fadawa Tala taje ta kwana dasu sannan ta hau sama. Tana tafiya
Hamza na binta da ido, jan kafa kawai takeyi tana tafiya da kyar. Tun yamma ya kula da yadda
tafiyarta ta canja amma idan taga mutane sai ta daure ta rinka tafiya daidai tana bata rai. Girgiza kai
yayi saboda yasan meye matsalarta.

A dakinta ya sameta tana daura tawul zata yi wanka yace ta jira shi yana zuwa. Turo baki tayi ...Ya
Hamza don Allah kada kace zaka yi min wanka yau ni bama ni da lafiya. Yace to Allah Ya sauwake,
maganin ciwon naki zan baki. Idonta har ya fara kwalla tace kasan me ya sameni ne? Cike da
tausayawa yace na sani Cutie, bari ki gani ina zuwa.

Toilet dinta ya shiga ya tara ruwa mai zafi sosai a katuwar roba ya sirka shi kadan sannan ya fito ya
cire rigarsa ya bar singlet yace muje. Duk ta gama tsorata ta fara ja da baya. Bai tsaya sauraronta ba
ya dagata tanata dukansa. Tawul din kawai ya zare ya sakata a cikin ruwan zafin. Ihun da tayi yana
tsammanin har maigadi sai yaji domin ba wutar inji bace bare ya rage sautin karar.

Zuhra kuka take yi sosai tana kokarin tashi Hamza ya tsaya daga bayanta ya danna kafadunta. Ya
Hamza akwai zafi sosai.

Na sani kiyi hakuri, son jiki irin naki yasa baki shiga ruwan zafin tun da safe ba. Yayi 'yar dariya... Yau
duk mai hankali kin gama tona min asiri a wurinsa da wannan tafiyar taki.

Sharkaf haka fuskarta ta jike da hawaye tace na shiga ruwan zafin da asuba.

Hannuwanta ya rike da take neman tashi tsaye yace nasan kin shiga ruwan da kika gama sirkawa ba.
Wannan idan kika haihu da kaina zan miki wankan jego don kada ki cuce ni.

Muryarta har ta soma dashewa tace cuta har ta wuce gasa ni da kake yi. Ta kai masa cizo a kirji ya
kauce yana dariya. Zumbura baki tayi kuma na dena sonka.

Yana dariya yace babu komai Cutie son da nake miki ya ishemu ai.

Bata kula ba ya sake kara ruwan zafin saboda na robar ya fara hucewa. Kuka kala kala Hamza ya gani.
Da kyar take magana don bakin ya mutu. A hankali tace to ka dawo ta gabana na rungumeka naji
dadi.

Yadda tayi ya bashi tausayi amma yasan abinda yayi mata zaisa taji dadin jikinta. Zagayowa yayi ta
rungumeshi tana kuka yana shafa bayanta. Bai kyaleta ba sai da tayi kusan minti talatin a cikin

28 / 40