Author : Batul Mamman Category : Read Hausa Novels
daga kan nata. Babu inda baya rawa a jikinta don tsoro...shi
kuwa wani irin yanayi na daban ya tsinci kansa. Kukan gaske yaga tana yi sai ya soma dariya har sai da
tayi mamaki. Yayi ajiyar zuciya, kin iya tsokana amma kina tsoron hukunci ko. Shiru tayi yau babu
rashin kunya su kadai a gida. Duk laifinki ne baki taba yimin tayin abinci ba, baki damu da inda mijinki
yake samun abinda zaici ba. Kunnenta yaji da kyau kuwa? Miji fa yace. Bata iya kallonsa ba tace kai
kace na rinka dafa na iya cikina. Kuma itama kafin ta tafi tace kada nayi girki da kai. Hannunta ya
kama suka tashi muje na hukunta ki. Sake yin alamar kuka tayi yace kinga ni na dena yarda da kukan
naki na karya.
Plates din ya dauka yace babu ruwa ne ko juice. Akwai ta amsa da mamakin me zaiyi. Ki dauko ki
hado da wani spoon din. Falonsa ya shige da abincin. Sai a lokacin tayi ajiyar zuciya....wai amma ta
tsorata. A tray ta dora jug cike da zobo mai sanyi da cup da kuma spoon din da yace ta dauko.
Samunsa tayi a falonsa yana zaune a kasa yana cin abincin. Murmushin da tayi yayi masa kyau yace
na dena satar abincin a bayan idonki. Gabansa ya nuna mata zauna muci.
Dawa??? Ta kwalalo idanu tana kallonsa. Tashi yayi ya zaunar da ita. Punishment dinki kenan na
tsokanata kici abinci tare dani. Idan baki ci ba kuma nayi bakinki zan dalle. Don Allah kayi....hannu ya
daga mata. Kada ki bata bakinki ki bani hakuri. Daga yau har Izzy ta dawo zaki rinka yin abinci dani.
Tace to amma ni bazanci da kai ba. Harara ya sakar mata. Don ma kin samu Hamza zaici abinci plate
daya dake...kuma wallahi bana son kazanta. Idan zakiyi na dare zan zo inspection naga yadda kike
girkin don nasan halinki.
Ba yadda ta iya dole ta zauna suka ci. Sai dai bata iya sakin jiki ba don da ta diba zaice lomarta tayi
girma ko kuma tayi kadan. Haka yayi ta mata har suka gama ta kwashe komai ya wanke. Zobon kuwa
bayan ya shanye cewa yayi ta hada masa wani...zobo ma yana cikin abinba Izzy bata masa. Shima na
masu karamin karfi ne.
Da daddare tuwon semovita yace tayi da duk miyar da ta ga dama. Su Hamza an sami sake Izzy bata
nan. Miyar kuka ta kada taji wake da nama. Bai iya boye mata santinsa ba. Sai da ta gyara kitchen din
tsaf ta tafi dakinta.
Wurin shadaya da rabi tana kallo aka dauke wuta. wayarta tayi saurin janyowa daga jikin chaja sai
taga ashe bata yi chajin ba. Chajar bata shiga jikin socket din da kyau ba, ga wayar dama bata rikon
chaji yanzu. A take ta fara jin tsoro ga zafi. Da bin bango ta janyo bargo daga gadonta da pillow tayi
shimfida a gefen kofa. Bata son duhu ko kadan shiyasa take kwana da fitila a kunne ko ta kunna torch
light din wayarta.
Hamza na fesa bodyspray ya fito daga wanka aka dauke wuta. Wurin minti biyar baiji maigadi ya tayar
da inji ba sai ya sauka. Maigadi yayi yayi injin yaki karbar wuta kuma akwai mai a ciki. Dama irin
babban nan ne da yake daukar har AC da fridge. Sunyi iya kokarinsu abu yaci tura Hamza ya kira
mutumin dake masa gyara yace ko zaizo da safe. Mutumin yace yana kauyensu yaje karbar kudin
auren kanwarsa amma jibi zai dawo. Hakan baiyiwa Hamza dadi ba ya yanke shawarar neman wani
washegari domin zafin gari sai ya hana mutum bacci. Dakinsa ya koma sai ya tuna da Zuhra yace bari
ya doba ko tayi bacci.
Tsoro yasa Zuhra ta dukunkune kanta cikin bargo duk zafin da akeyi. A hankali ya bude kofar dakin
gudun kada ya tasheta idan baccin take yi.
Dishi dishi take ganin inuwar mutum da yayi hanyar gadonta. A ranta tace shikenan barawo ya fado
dakinta. Tashi tayi da sauri zata gudu ko da bin bango ne taje dakin Hamza taji anyi saurin rungumota
ta baya. Sandarewa tayi a wurin don tsoro kamar ta saki futsari, gumi ya rinka tsatstsafo mata. Hamza
bai ankara ba yaji ta kai masa naushi a ciki ta soma ihu...Wayyo Allah barawo. Duk da zafin cikin
bakinta ya samu ya toshe da hannunsa ai kuwa ta gantsara masa cizo iya karfinta. [17:23, 26/09/2016] +234 813 652 9082: AL'ADUN WASU í ½í·¿46
Batul Mamman(Mrs)í ½í²–
Ba shiri ya saketa, yana yarfe hannu. sake bude baki tayi zata yi ihu a hankali yace ke nine....ajiyar
zuciya tayi da karfi sannan tace da tsoratani kazo yi kake min sanda a daki? Kaima baka da fitila ne?
Dukan da tayi masa ya kulle masa ciki gashi ta dame shi da surutu. Da waya na shigo karama bansan
inda kika jefar min da ita ba. Yayi kokarin dukawa ya lalubi wayar yaji zafi a cikin....auchhhh. Zuhra tayi
saurin matsawa kusa dashi menene ta tambaya a tsorace. A duhun ya harareta naushi na fa kikayi a
ciki ga cizo sai kace wata yar dambe. Duk hanyar mugunta kin sani. A wahale take jin muryarsa na fita
ta mika hannu tana sannu taji ta taba cikinsa....kamar wadda aka tsikara tayi saurin janye hannun
tana cewa yi hakuri. Shima hakan yaji amma bai so ta dauke hannunta ba. Dakin yayi shiru na dan
lokaci...Hamza ya kasa gane dalilin da yasa ko yaya jikinsa ya taba na Zuhra sai abin yayi affecting
dinsa sosai. Dan gyaran murya yayi bazaki tayani neman wayar ba? Kamar jira take ta durkusa tana
rarrafe tana shafa hannu a kasa. Abu taji ta taba tayi saurin janyowa ashe hannun Hamza ne shima
yana duddubawa. Da yake da karfinta taja shi kuma baiyi tunanin hakan zai faru ba sai ya fada kanta.
Bakon yanayi duka suka tsinci kansu a ciki. Kunya kamar Zuhra ta nutse a wurin, kamshi ne mai dadi
yake fita daga jikin Hamza.
Yana fadawa ya gane daurin kirji ne a jikinta...a hankali ya soma yi mata magana. Nifa bana son
daurin kirji don Allah ki dena. Wai ita yake hadawa da Allah....saurin dawowa tayi hayyacinta ta fara
kokarin ture shi. Yana ji ya sakar mata nauyinsa yana mata dariya.....wai kema kina son jin dumin
mijinki shine kika janyoni. To saboda ina tausayinki bazan miki fada ba mu kwana a haka. Wayyo
Allah, karshen kunya Zuhra ta gama ji. Har wata in'inar karfi da yaji ta fara. Al'Quran....Al'Quran
ba...ba haka bane. Ko kadan bashi da niyar tashi don ya soma jindadin tsokanarta yace to yaya ne?
Abinda kika ga munayi da Izzy kike so nayi miki? Wani karfi ne yazowa Zuhra ta dage ta ture shi. Tana
ji yana dariya ita kuwa sauran kadan ta soma kuka. Bata dade da matsawa ba yaga wayar ya dauka ya
kunna tare da soma haska dakin.
Can bakin kofa ya ganta ta takure harda jan bargonta ta rufe jiki. Koda ya matso harda dan
hawayenta. Kusa da ita ya koma me kuma nayi miki kike min kuka? Sai da ta dan matsa sannan tace
ba kaine kace wai...wai...wai....kwafa tayi ta kasa karasa maganar. Dariya shagwabarta ke bashi, dazu
fa aljani kika kirani banyi kuka ba sai kece mai arhar hawaye zaki min kuka daga wasa. Kin kallonsa
tayi saboda kunyar ganinsa babu riga. Yace kinga fito daga bargon nan kisa rigar bacci bana son
daurin kirji. Tana kumbura baki tace ni a haka zan kwana. Mikewa yayi to ya rage naki...wai ma kinyu
wanka kuwa kafin ki kwanta. Tsami nake ji a dakin nan....dama zuciya na kusa ta fara kuka wallahi
bana tsami. Yace to kinyi wankan..tsakaninki da Allah. Rufa tayi har ka sannan tace banyi ba. Rufe
bakinta ke da wuya ya janye bargon gaba daya tana kuka ko kulata baiyi ba. Lokaci daya ya yankewa
kansa shawarar abinda zaiyi ya taimaka mata kafin su rabu.
Kan gadonta ya jefa bargon sannan ya shiga toilet dinta. Babu komai sai sabulun wanka da omon
wanki da wanke toilet. Ficewa yayi ya barta a duhun baiyi magana ba. Ga tsoro tana ji ita kadai amma
bata son binsa.
Bayan kamar minti biyar ya dawo da wata fitila mai haske wadda tafi karamar wayar tasa. Shima a
babbar bashi da chaji sosai. Wani abu ta gani a hannunsa kamar toothpaste tace ina da makilin fa.
Wannan ba makilin bane yar kauye zo nan. Baya ta dan matsa tace yi hakuri. Fitilar ya ajiye a kan
dressing mirror dinta sannan ya jawota ya zaunar da ita kamar ranar da yayi mata kwalliya. Duk ta
tsargu da daurin kirjinta, shi kuwa ya saka kayan bacci marasa nauyi yanzu. Yana zaunar da ita ya
kama hannunta duk da yadda yaji ya daga. Allah Sarki Zuhra sai hawaye...ashe dazu bata ga komai a
kunyar da Hamza yake shirin bata ba. Kokarin sauke hannunta tayi ya sha kunu zan matseki idan baki
tsaya ba. Kuma kinga mu kadai ne a gidan babu mai taimakonki. To me zaka yi min? Yace sa ido ki
gani bana son surutu kuma ki hadiye kukan nan. A hankali take hawaye tana gani ya bude abinda ta
zata makilin ne ya zuba a wani abu kamar cokali mai dan fadi ya soma shafa mata a hammata. Ji tayi
kamar cakulkuli ta soma dariya....girgiza kai yayi kina da matsala, daga kuka sai dariya. Bata dena
dariyar ba har ya gama yace ta bar hannunta a bude. Dayan hannun ya daga ya shafa a nan ma.
Wurin minti biyu yana dube dubi a dakin har yaga inda ta ajiye turaruka da body spray din lefenta.
Tace wai a haka zan zauna ne? Sai da ya dauko wurin kala biyar sannan ya dawo ya dauki yar robar da
tisssue a hannunsa ya kwashe duka gashin. Zuhra ta wage baki ....lahhhh kaga gashin ya cire. Hamza
murmushi kawai yayi..yar kauye bata san shaving cream ba. Fes ya share mata sannan ya mika mata
shaving stick har uku. Shiga toilet kiyi shaving sannan kiyi wanka ina jiranki a nan. Ya Salam yau
Hamza so yake ta tona rami ta boye kanta don kunya.
Kasa shiru tayi tace can kasa wai yau kunya kake son sani ji? Bata san yaji ba yace yes idan baki wuce
ba zanzo nayi miki da kaina. Fitilar ta dauka da sauri ta shige harda murda key. Murmushi Hamza yayi
ya dan matsa kofar toilet din...kada ki fito sai kinyi wanka sau uku. Ki tabbatar jikinki ya fita sosai don
zan duba. Idan baki fita ba na iya yiwa kazamai irinki wanka. Kuma kiyi brush sosai. QTo an hada
Zuhra da aiki, sai da tayi amfani da duka shaving sticks din wurin gyara jikinta sannan ta shiga dirzar
jiki. Allah Ya kiyaye ta bari yayi mata wanka. Sau biyar ma tayi harda goge kafa da abin kaushi duk da
kafar tata bata da matsala. Brush da toothpaste kuwa sun san Hamza na dakin don sun sha aiki.
Katon tawul tasa ta goge jikinta sai taji wani dadi da iska na shigarta. A hankali tace na gama. Yana
kwance akan gadon nata yace to fito mana. Lallai ma a hakan? Rigar bacci yake duba mata amma sai
yace to meye ya rage da zaki boye min. Shiru yaji bata fito ba ya dan kwankwasa, bude ga riga ki saka.
Dan kadan ta bude kofar ta zura hannu. Wata rigar bacci ce mai kyau amma cotton mara nauyi ta
wuce gwiwarta ma da karamin hannu. Yace ki goge jikinki sosai kafin ki saka. Dama ta goge ta saka ta
yafa tawul din ta fito. A kan stool din yake zaune yace tunda yau akwai zafi sosai ba sai kin shafa mai
ba. Har gabanta ya karasa ya cire mata tawul din sannan ya fesa mata body spray kala uku. Don Allah
baki ji dadin jikinki ba yanzu ya tambayeta yana murmushi. Kanta a kasa tace naji...yace good, lesson
one duk dare sai kinyi wanka kafin ki kwanta kinji ko. A hankali tace to. Wayarsa ya kunna yace to sai
da safe ya fita ya bar mata fitilar.
Gado ta haye tayi addu'o'in kwanciya sai dai baccin yaki zuwa. Duk abinda Hamza yayi mata tun
shigowarsa ta rinka tunawa tana murmushi......
[17:24, 26/09/2016] +234 813 652 9082: AL'ADUN WASU í ½í·¿47
Batul Mamman(Mrs)í ½í²–
Zuhra na idar da sallar asuba ta sauka zuwa kitchen. A zafin nan da rashin wuta tana tsoron kada
naman cikin fridge din ya lalace. Fito dashi tayi tana wankewa Hamza ya dawo daga masallaci ya
sameta. To acici me kike yi a kitchen da asubar fari. Muryarsa taji kamar hancinsa a toshe yake.
Amma yau gabadaya kunyarsa take ji da ladabin musamman ta gaisheshi. Sannan tace nama zan
tafasa na soya kada ya lalace saboda babu wuta. Ta sunkuyar da kanta, ya jiki naji kamar yau murar
tafi ta jiya. Hamza yace eh amma da sauki. Yaji dadin yadda har ta fuskanci bashi da lafiya ta nuna
damuwarta. Kallonta yake yadda take aiki ga hijab dan madaidaici a jikinta, hakan bai hanashi tuno
surarta da ya gani ba daren jiya duk da duhun dakin. Ji tayi kamar ana kallonta ta dan juya suka hada
ido. Murmushi kawai yayi mata ya tafi.
Flask ta dauko sabo na tea ta wanke sannan ta tafasa ruwan zafi da lipton, citta da kaninfari. Ta soya
kwai guda uku da albasa yar kadan saboda bata sani ba ko Hamza na son kwai da albasa. A karamin
plate ta zuba ta rufe shi da wani irinsa sannan ta dora mug na shan tea da teaspoon a tray. Bread
daya ta bawa maigadi ya siyo musu jiya gashi bata da dankali ko doya. Duka bread din ta dora masa
da kayan tea. Kasa shiga falon nasa tayi tana tunanin ko tayi masa karambani ne.
Sai da ta gaji da tsayuwa sannan tayi sallama ta shiga. A kwance ta ganshi kan doguwar kujera ya
zurfafa a tunani. Ba komai ke damunsa ba kamar harkar office ga mura tayi masa kamu sosai.
Sallamarta ce ta tashe shi ya zauna. Batayi magana ba ta ajiye masa tray din a gabansa sannan ta
koma ta dauko flask din. Kallon kayan yakeyi har ta dawo...ta ajiye flask din tana dan sosa kai tace
uhmm dama nasa citta da kaninfari a ruwan. Idan baka so sai na tafasa wani. Dago kansa yayi jikinsa
duk babu kwari sosai yace me yasa kika dafa da cittar? Naga kana mura ne zai bude maka kirji. To
nagode da kulawarki, taimaka ki hada min amma kada kisa sugar. Tausayi ya bata sosai bata yi masa
musu ba ta hada masa sannan ta fita ta koma kitchen.
Kazar dama daya ce tayi mata saura ta wanketa sosai ta hada da kayan kamshi da jajjagen kayan miya
tayi farfesu. Yana kan wuta ta wanke shinkafa ta baza a tray sannan ta shiga yanka su cabbage, albasa,
attaruhu, karas da koren wake. Harda grating din tafarnuwa kadan. Duk bayan ta gama ta sake
komawa falon ko ya gama cin abincin. Ya gama amma fa bread din da rage bazata iya raba musu ita
da maigadi ba saboda dama ba wani babba bane. Duk yadda take jin yunwa da ta kwashe kayan kwai
biyu ta soya ta hadawa maigadi tea da bread din. Tace idan ya gama zai kai mata nikan shinkafa. Talle
maigadi yanzu duk gidan babu wanda yake ganin girmansa kamar Zuhra yace to Hajiya nagode.
Kitchen ta koma ta kashe farfesun sannan ta fara soya sauran naman. Tana yi ta hada tea ta zauna a
kan kujera tana sha don bazata iya cin kwai zalla ba.
Bayan yaci abinci yasha magani jikinsa yayi dan kwari. Shiru babu motsin Zuhra sai yaji babu dadi.
Sama yazo hawa yaji alamun har yanzu tana kitchen. Tea ya hangota tana sha shi kadai. Shiga yayi
yana kallonta tea kadai kike sha ba bread? A'a na cinye bread din ne. Yadda tayi magabar yasa bai
yarda ba ya duba dustbin dinta ina ledar. A zuciyarta tace kaji mutum da bin kwaf. Shiru tayi ba amsa
yace bakya jina ne? Na bawa maigadi....kin me? Dama bashi da yawa kika bani, kuma sauran kika
bawa maigadi to ke me zaki ci. Baki da Indomie ne? Murmushi kawai tayi ai yanzu zan dora abincin
rana bana jin yunwa ma. Mamakinta yake...yanzu kamar Zuhra tasan ta hakura da abinda take so
domin wani. Ji yayi ta sami wani gurbi a zuciyarsa. Hannunta ya kama suka koma falo...meyasa baki
fada min ba kika yi shiru zaki kwari kanki. Wasa ta soma yi da yatsunta taki kallonsa..ai naga baka da
lafiya kuma zan iya jira. Lallai yau ya koyi darasi a wurin Zuhra...shi bai taba bata kudin siyan wani abu
ba yasan da kudinta ta sayi bread din kuma ta bashi. Kallon da yake mata yasa duk ta kasa sakewa .
Shi kuwa hannu yasa yana shafa gefen fuskarta har sai da tsigar jikinta ta tashi. Nagode kinji, Allah Ya
baki lada, kin nuna damuwa da rashin lafiyata sannan kin iya hakura da abinci don wani yaji dadi.
Amma daga yau ki rinka fadamin duk abinda kike bukata, tace to cike da kunya sannan ya saketa ta
koma aikinta zuciyarta na bugawa da sauri. Sauran naman ta kwashe ta bawa maigadi nikan shinkafar
sannan taje tayi wanka. Har ta dauko foundation sai ta tuna da kwalliyar da ya gyara mata ranar da
suka fita. Irin yadda yayi mata haka tayi aka dauki deodorant da body spray aka fesa. Sannan kayanta
ma suka sha turare mai kamshi.
AL'ADUN WASU í ½í·¿48
Batul Mamman(Mrs)í ½í²–
Hamza na falonsa ya gama waya da assistant director akan wasu ayyuka. Duk yayi musu bayanin
yadda yake so ayi aikin da alkawarin idan yaji sauki anjima zai shiga office. Bayan ya gama Izzatu ya
kira. Hira kadan suka yi ya gaisa da su Khalifa tace masa tana son wucewa Abuja idan an