Author : Batul Mamman Category : Read Hausa Novels
ruwan
zafin sannan kamar jiya yayi mata wanka. Sai da ya shiryata sannan ya shiga wankan shima. Kafin ya
fito tayi baccin wahala. Gyara mata kwanciya yayi ya rumgumeta cike da tausayawa. A haka suka yi
bacci tana kwance a jikinsa.
Yau dai bata ji kunyar tashi da asuba ba har Hamza na tsokanarta. Da wuri ta kammala ayyukanta na
gida saboda jiki yayi kwari ta dena tafiya da kyar. Da tayi zancen zuwa asibiti Hamza yace bazashi ba
office zai tafi. Itama baiyi mata izinin taje ba. Ganin ya dauki zafi yasa bata matsa masa ba. Bata
damuwa da bin kwaf akan matsalarsa da Izzatu. Tare ta gansu tasan idan fushin ya kare zasu daidaita.
Kullum Tala ke kai abincin asibitin.
Cikin 'yan kwanakin nan Zuhra da Hamza sun kara shakuwa sosai. Soyayya yake nuna mata tamkar
wata 'yar yarinya haka yake lallabata. Itama dai ta fara sakewa dashi amma har yanzu tana jin
kunyarsa. Ko kayan bacci tasa sai yayi da gaske yake cire mata hijab. Ana tashi daga office gida yake
tahowa su sha soyayyarsu. Ana haka Hajiya ta kirashi tana masa fadan kwana biyu bata ganinsa a
asibiti meye dalili. Dama yasan ba son Izzatu suke yi ba, idan ya fadi abinda tayi kuma kara wutar abin
zaiyi sai kawai ya bata hakuri yace ayyuka ne suka saka shi a gaba.
Kwanan Izzatu tara a asibitin sannan aka sallameta. Duk irin nasiha tagari Raliya tayi kokarin yi mata
domin ta samu ta rike igiyar aurenta dake lilo a iska. Itama ta danyi karatun ta nutsu saboda bata taba
tsammanin zai iya shareta haka ko waya babu ba. Tun safe akayi sallamar ta kira shi a waya yana can
jikin Zuhra bai bi ta kai ba. Sai daga baya yaga missed call ya kira tace an sallameta ne tun safe.
Hamza yace to sai ki tari adaidaita sahu ki taho gida ni motata jiya da kyar ta kawoni gida. Anjima
kadan makanike zai zo ya dauka. Kamar ya kwada mata guduma haka taji maganar tasa. Adaidaita
sahu kuma??? Ita ba don kada tayi karya ba sai ta iya cewa bata taba shigarsa ba. Motoci uku ne a
gidansu kuma duk inda zata indai ba aiki ne yayi masa yawa ba Hamza da kansa yake kaita. Gashi ko
zancen motarta da ta bari a Kaduna baya yi. A sanyaye tace Baby ko daga gidanku kasa azo a daukeni
mana. Saboda yadda ta bashi haushi ko amsa bai bata ba ya ajiye wayar.
Zuhra na falo tana biyewa yara suna shirmensu Hamza ya fada mata an sallami Izzatu tayi abinci da
ita. Tace Mamanta fa? Gidan kanwarta zata wuce, kisa Tala ta gyara mata daki kafin ta karaso. Yana
gama magana ya shige falonsa. Sakonsa ta fadawa Tala sannan tabi bayansa dama ta riga tayi girkinta
kuma zai isa indai cikin Izzatu ne ita kadai.
Kwance ta same shi akan doguwar kujera ya dafe kansa da hannu daya idonsa a rufe. A hankali ta
rinka tafiya har tazo gabansa ta durkusa. Gashinta ta janyo daga cikin dankwali ta matso kusa dashi
sosai sannan ta zira masa gashin a kunne tana wasa dashi. Da sauri ya bude ido ya dagota ta fado
jikinsa. Kinci bashi Cutie ya fada yana karkade kunnensa. Tayi dariya kai dai kaji tsoro kawai zaka
wayance. Hancinsa ya goga a jikin nata yana murmushi...Cutie I love you so much. Ganinki yana sa na
manta damuwata. Mayar masa da murmushin tayi tace I love you too. Amma yanzu ka tashi muyi
magana kaji. Ba haka yaso ba a yadda ta kwanta a jikinsa so yayi su zauna a haka. Yace idan na tashi
kin min alkawarin zan sami duk abinda nake so. A kunyace tayi hada bakinta da nasa tace harma da
kari.
Zama ya gyara ya dorata akan cinyarsa. Ina jinki Cutie. Har wani dan gyaran murya tayi sannan tace Ya
Hamza nasan bani da wani iko akan duk matsalarka da mamansu Khalifa. To amma abinda yake
faruwa yanzu yana iya shafarsu. Idan har iyaye na fushi da juna yara su kan gane idan sun fara wayo.
Jiya Khalifa cewa yayi yanzu baka zuwa wurin Mummy dinsu saboda tayi maka laifi. Nayi kokarin yi
masa wayo nace kana zuwa. Daga baya yazo yace yanzu nice mamansu ko, ita kuma zata koma Abuja
su dena ganinta. Bansan ya akayi yake irin wannan tunanin ba amma ya kamata ka nuna masa ba
haka bane. Yanzu yaro ne bazai kawo komai ba, amma nan gaba idan ya kara wayo zai ga kamar baka
sonta ne. Daga nan ko kai ko ita zai goyi bayan daya ya bar dayan wanda hakan bai dace ba.
Hamza kallonta kawai yake yi har ta gama bayaninta. Fuskarsa dauke da murmushin jindadi, shi kam
yaga ranar biyayya ga iyaye. Iska ta busa masa a ido da taga baya kiftawa. Ya shafa fuskarta, Zuhra ke
dabance a mata. Lokacin da ya dace kiyi farinciki hankalin miji ya dawo gareki gabadaya sai kike
tunanin kyautatawa wadda tayi sanadiyar jefaki cikin kunci.
Zuhra tayi saurin dora yatsanta a bakinsa...Ya Hamza ni bana cikin kunci. Na aureka ba don ina so ba
amma yanzu bana fatan ganin ranar da zamu rabu. Yayi murmushi Allah Cutie? Kice karatun da na
koya miki yayi aiki kenan. Kunya taji ta sunkuyar da kai, ni ba haka nake nufi ba. Yayi murmushi ni
haka nake nufi. In Sha Allah zanyi kokarin gyarawa kuma. Sai dai sai kinyi min hakuri da kunnenki kika
ji abinda tayi. Zuhra tace babu komai indai zaka gyara itama zatayi da yardar Allah. Hamza ya jinjina
kai, Cutie fada min gaskiya ke bakya jin haushin duk abinda tayu miki? Zuhra tace tabdi, ya za'ayi naji
haushi ta hadani da mijin da babu kamarsa. Tana fadar haka ta tashi ta gudu tana masa dariya.
******
Mai adaidaita sahu ga gaji da ihun da Izzatu take yi ko yaya suka shiga gargada. Dama da ganinsa ko
ba'a buge yake ba to yana dan tabawa ya kallota ta mudubi idanunta wuri wuri. Ke Hajiya ya zaki
rinka min ihu kamar yau kika fara shiga adaidaita? Izzatu ta kankame karfen gefen da take tana mai
nadamar kin bin mamanta a wanda ta tafi...ban taba shiga ba wannan ne shigata ta farko. Dan
matashin yayi dariya yace shegiyar karya kice daga turai jirginki ya sauka kawai. Kallon yadda yake
kurdawa tsakanin motoci take yi baki na rawa tace wallahi ba karya nake yi ba a Canada na girma.
Dreban ya kwashe da dariya yace bari na dan shillaki kiji kamar a jirgin Canadan kike.
Ai bata kara samun nutsuwa ba sai da ya tsaya a bakin gate din gidanta. Gudu yake yi da ita sosai har
wani abokinsa na tambayarsa ina zuwa haka da suka tsaya a danja yace yau Canada ya nufa. Izzatu
taga tashin hankali duk jikinta ya bugu. Kafarta kamar bazata dauketa ba da suka tsaya a kofar gida.
Maigadi ne ya kwaso mata kayanta ta shiga ciki tana jan kafa. Tana shiga falon idonta ya dire akan
Zuhra zaune a kan ledar cin abinci ta dora Nana a cinyarta ga Junior da Khalifa duk sun zagaye tray
suna cin abinci. Zuhra ta dago kanta a dan tsorace tace mata sannu da zuwa. Ko bi ta kanta bata yi ba
tace where are your table manners kids? Yaushe kuka fara cin abinci a kasa kuma a tray? Khalifa yace
zumunci yake karawa. Izzatu ta dakawa Tala tsawa, daukesu ki zubawa kowa plate dinsa su koma
dinning table. Tala ta ruga kitchen a ranta tana cewa shikenan mun shiga uku.
Sai a lokacin Izzatu ta karewa abincin kallo tace meye wannan kuke ci a wulakance. Zuhra taji babu
dadi. Farar shinkafa ta dafa sannan tayi miyar alaiyahu. Jajjagen attaru da albasa tayi sai tumatir
kadan ta soya da manja ta zuba alaiyahu wanda ya tsane ruwansa sannan ta dafa kwai ta sakawa
kowa. Tala na zuwa da plate din Hamza ya fito yace ta mayar ko kallon Izzatu baiyi ba ya koma falonsa
rai a bace. Zamansa kenan wayarsa tayi kara ya dauka.
Mutumin yace shine sakataren ministan tsara birane. An turowa Hamza sakon email ana bukatar ya
karanta ya turo reply kafin gobe.
AL'ADUN WASU í ½í·¿
7⃣0⃣
Batul Mamman(Mrs)í ½í²–
Daga asibitin gidan 'yan uwansa mata suka wuce. Dukkaninsu sunyi farincikin ganin Zuhra kowacce
tana janta a jiki. Daga nan suka je gidan Anti Faiza wadda ta rasa inda zata sa kanta don murnar ganin
Zuhra da Hamza tare. Dabarun kula da miji ta sake karanta mata da kyau sannan na karshe suka je
gidan Ibrahim. A nan suka ci abincin dare sannan suka taho bayan Hamza da Ibrahim sun dawo daga
sallar isha.
Kafin suje gida su Khalifa duk sunyi bacci sai Hamza da Zuhra ke ta hira. Kayan da suka biya suka siyo
Zuhra ta iya dauka yaran kuwa Hamza ne ya dauko su. Dama sauri take su iso gida gabadaya bata
jindadin jikinta tun yamma daurewa kawai take yi tana tafiya.
A dakinsu ya kwantar dasu Zuhra ta fadawa Tala taje ta kwana dasu sannan ta hau sama. Tana tafiya
Hamza na binta da ido, jan kafa kawai takeyi tana tafiya da kyar. Tun yamma ya kula da yadda
tafiyarta ta canja amma idan taga mutane sai ta daure ta rinka tafiya daidai tana bata rai. Girgiza kai
yayi saboda yasan meye matsalarta.
A dakinta ya sameta tana daura tawul zata yi wanka yace ta jira shi yana zuwa. Turo baki tayi ...Ya
Hamza don Allah kada kace zaka yi min wanka yau ni bama ni da lafiya. Yace to Allah Ya sauwake,
maganin ciwon naki zan baki. Idonta har ya fara kwalla tace kasan me ya sameni ne? Cike da
tausayawa yace na sani Cutie, bari ki gani ina zuwa.
Toilet dinta ya shiga ya tara ruwa mai zafi sosai a katuwar roba ya sirka shi kadan sannan ya fito ya
cire rigarsa ya bar singlet yace muje. Duk ta gama tsorata ta fara ja da baya. Bai tsaya sauraronta ba
ya dagata tanata dukansa. Tawul din kawai ya zare ya sakata a cikin ruwan zafin. Ihun da tayi yana
tsammanin har maigadi sai yaji domin ba wutar inji bace bare ya rage sautin karar.
Zuhra kuka take yi sosai tana kokarin tashi Hamza ya tsaya daga bayanta ya danna kafadunta. Ya
Hamza akwai zafi sosai.
Na sani kiyi hakuri, son jiki irin naki yasa baki shiga ruwan zafin tun da safe ba. Yayi 'yar dariya... Yau
duk mai hankali kin gama tona min asiri a wurinsa da wannan tafiyar taki.
Sharkaf haka fuskarta ta jike da hawaye tace na shiga ruwan zafin da asuba.
Hannuwanta ya rike da take neman tashi tsaye yace nasan kin shiga ruwan da kika gama sirkawa ba.
Wannan idan kika haihu da kaina zan miki wankan jego don kada ki cuce ni.
Muryarta har ta soma dashewa tace cuta har ta wuce gasa ni da kake yi. Ta kai masa cizo a kirji ya
kauce yana dariya. Zumbura baki tayi kuma na dena sonka.
Yana dariya yace babu komai Cutie son da nake miki ya ishemu ai.
Bata kula ba ya sake kara ruwan zafin saboda na robar ya fara hucewa. Kuka kala kala Hamza ya gani.
Da kyar take magana don bakin ya mutu. A hankali tace to ka dawo ta gabana na rungumeka naji
dadi.
Yadda tayi ya bashi tausayi amma yasan abinda yayi mata zaisa taji dadin jikinta. Zagayowa yayi ta
rungumeshi tana kuka yana shafa bayanta. Bai kyaleta ba sai da tayi kusan minti talatin a cikin ruwan

matashin yayi