Aladun Wasu Hausa Book Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Read Hausa Novels

Chapter   3 / 40

6K to 9K   out of 117.5K words

Kaltume duk ta rude ta tambayi abinda ke faruwa. A
madadin amsa sai mari da duka da Alh Sabiu ya rinka kai mata. Sahura na kuka tace muguwa saboda
baki haihu ba shine zaka kashe min nawa 'ya'yan. Tunda kika fita nake neman Ihsan banganta ba. Sai
dazu kawai naji kukanta a dakinki. Ba yadda banyi ba na kasa budewa, tun tana kuka har muka ji
shiru. Ta cigaba da kuka ina jin ma ta mutu Alhaji. Shi kuwa sai dukan Kaltume yake har sai da aka
bude dakin. A kwance suka tarar da Ihsan yar wata takwas. Sahura tace ai kawai ta mutu ko ta suma.
Alhaji Sabiu ya cire babbar rigarsa yana ta dukan Kaltume. Babu mai hanashi har Allah Ya kawo Alh
Nasiru. Yayi ta rokon abokinsa amma sam yaki dena dukanta. Alh Nasiru ganin babu yadda zaiyi ya ja
hannunta. Sahura tace shikenan Alhaji dama tunda yake kare mata kwartonta ne. Ji yadda yake rike
mata hannu a gabanka. Alh Sabiu yace ko Sahura, to ke Kaltume na sakeki saki uku in kin gama idda ki
auri kwarton naki. Kai kuma Nasiru bani ba kai. Da haka abokan suka rabo. Ashe mukulli Sahura ta
sata na Kaltume ta durawa yarta maganin bacci ta kaita dakin.

Halima taji tausayin Kaltume sosai barin ma da aka rinka yadawa a gari abokin mijinta ne kwartonta.
Gashi ya gujeta bayan aurenta ya mutu. shi kanshi sai da abin ya shafi kasuwancinsa. Sai da ta kai ko
makaranta ta dena zuwa. Har yan uwanta wasu suna kyamarta. A wannan halin ne Halima ta bawa
mijinta shawarar ya auri Kaltume domin ta tsira da mutumcinta. Da kyar Kaltume da Alh Nasiru suka

yarda. Bayan anyi auren saboda Halima ta lura Kaltume na son 'ya'ya ta dauki Hamza da Mariya ta
kayansu ta mayar dakin Kaltume. Wannan abu ya kara musu zaman lafiya sosai. Kaltume har kullum
bata yiwa Halima kallon kishiya sai yar uwa. Haka suka zauna lafiya Halima ta haifi Jidda. Daga nan
Kaltume ita ta sami ciki ta haifi Nura da Adabiyya. Sannan Halima ta haifi auta Hamida. Gidansu abin
sha'awa saboda kan 'ya'yan a hade yake. Daga baya asirin Sahura ya tuno Alh Sabiu yaji tana bawa
yarta labari. Har gida yazo bawa Kaltume hakuri domin ya gane bai kyauta ba. A yanzu ma dai komai
ya sukurkuce musu shi da Sahura don yaran babu wani mai abin kirki gasu har su shadaya.

Tun daga farkon layin gidansa yake hango motoci. Hankalin Hamza ya sake tashi sosai. Innalillahi wa
inna ilaihi rajiun kawai yake fada. Shikenan Junior ya rasu.........jikinsa duk a mace yayi parking din
motarsa daga can baya ya fito. Sai kawai ya kasa karasawa gidan. Kifa kansa yayi a saman motar. A
wannan yanayin Ibrahim ya iso. Yana neman gurin parking don layin ya cika ya hango yayansa a tsaye
ya kifa kai. Ibrahim ya fito da sauri da matarsa Ummahani da yaransu uku.
Hannu yasa ya taba Hamza a kafada. Hakan yasa ya juyo da sauri. Muryarsa a raunane yace ashe
kuma kunji. Ummahani tana gaishe shi yace mata shiga ciki Umma ai dukkanmu mukayi rashin.
Ibrahim yace rashi kuma Yaya? Nifa tun jiya Izzatu tace muzo da yara yau. Nayi tunanin irin partyn da
kuka saba ne na kawo su don kada ace ina raba zumunci. Amma wallahi barnar kudin naka tayi yawa.
Hamza yace ina maganar party Ibrahim. Junior ne ya rasu. Baka ga mutane da yawa ba. Ummahani
na kokarin bude gate Junior ya bude tare da wasu yaran. Sun sha sababbin kaya. Hamza ya kura masa
ido sannan ya dubi Ibrahim. Ibrahim yace kai wa ya fada maka ya rasu? Hamza a rikice yace Izzatu tayi
waya Office tace a fada min ya karye a hannu. To ina zuwa naga motoci nayi tunanin ya rasu ne.
Ibrahim yayi tsaki cike da bacin rai yace Allah Ya kyauta ni na tafi. Zuciyarsa na kuna yaja motarsa yayi
gaba. Ace babban mutum kamar Yaya dan shekara talatin da bakwai ya bari mace na karanta masa
yadda zasuyi rayuwa. Kodayake ba laifinta bane. Tare suke yin komai. Daga nan Ibrahim gidansu ya
tafi.

A hankali Hamza ya tura karamar kofar gate din ya shiga. Kawai sai ji yayi mutanen wurin sun ce
SURPRISE!!! farfajiyar gidan ya gani ya sha kwalliya an jera kujeru da tebura. Ga fitilu suna ta haskawa
an kunna inji. Kida aka kunna yana tashi a hankali. Bai gama tantance abinda ke faruwa ba Izzatu taja
hannunsa suka shige cikin gida. Muje ciki ka canja kaya. Suna shiga daki ta rungume shi. ....HAPPY
ANNIVERSARY MY BABY. [25/09 3:14 pm] Inna��: AL'ADUN WASU 🗿8


Batul Mamman(Mrs)💖

Hamza ya yiwa Izzatu kallon rashin fahimta. Izzy me yake faruwa ne? Kince Junior ya karye but it
seems lafiyarsa kalau. Fari tayi masa da ido irin yadda tasan yana kara dauke masa hankali, sai a
lokacin ya kula da kayan jikinta. Wani irin yadi ne mai matukar santsi aka yi mata doguwar riga wadda
ta dameta daga sama har gwiwa sannan ta bude sosai. Ga wani abu kalar takalminta da sarka anyi
mata dauri. Tamkar wata amarya ta fito. Jikinta mai kyau ne ba kace ta haifi 'ya'ya uku ba. Tana lura
da yadda yake binta da kallo tayi murmushi. Dama nayi ne kawai don ka dawo gida akan lokaci. Na
gama komai na shirya mana anniversary dinmu na shekara goma. Ya shafi gefen fuskarta amma Izzy
ba kya ganin abin ya danyi yawa. Ki ce dana ya karye kinsan zan tsorata. Kiss tayi masa a kumatu to yi
hakuri daddyn Junior. Kaga ana jiranmu a waje.

Tare suka fito rike da hannun juna. Sunyi matukar kyau sosai ga yaransu suma sun sha ado. Babban
shekararsa biyar suna kiransa Khalifa mai sunan Alhaji Nasiru. Sai Junior mai shekara uku sunan
baban Izzatu gareshi Sunusi sai kuma Nana(Halima) mai neman shekara ta biyu. Sunan Mama yaso
saka mata sai dai Maman taki saboda Ibrahim da Mariya duk sunyi mata takwarori.

Hajara tana ta binsu da ido duk inda suka yi ana ta gaisawa da daukar hotuna. Ga masu rabon abinci
suna ta yi su ma. Tace kai Anti Faiza ina ma Zuhra tazo muci son ran mu. Ji kaji kamar su suke
kiwonsu. muma dai Allah Ya bamu kudin nan muji dadin rayuwa mu rinka party duk shekara. Mariya
tace ba amin ba kanwata. Anti Faiza da Hajara suka juya suna kallonta. Hajara tace kinji min mata da
bakinciki. Faiza ta kai mata duka to shashasha baki san mutum ba zakiyi rashin kunya, yi hakuri
baiwar Allah. Ko ba'a fada ba daga shigar Mariya an san tana da kudi. Murmushi Mariya tayi ba komai
ke dai kiyi adduar arziki mai albarka ba na party ba. Daga nan ta tashi ta hada kan 'ya'yanta sukayi
waje.

Haka aka cigaba da taro har wurin karfe takwas na dare. Nura ne suna shirin tafiya dasu Adabiyya
yazo ya fadawa Hamza sakon Mama kan cewa tana son ganinsa a yau. Sai bayan fitarsu ya duba
agogonsa. Subhanallah ya fada da karfi tare da mikewa. Izzatu tace yaya akayi? Ya nuna mata lokaci.
Kinga har lokacin isha yayi bamuyi magriba ba. Ta dan tura baki idan an watse ba sai muyi ba. Bana
son a fara shiga ciki ne azo a bata min toilets. Hamza yace ni dai bani key please. Ta dan daure fuska
Allah bazan bayar ba. Kana shiga mutane zasu fara bin bayanka. Ya girgiza kai yana murmushi Izzy
baki da dama. Wani famfo ya zagaya a bayan gidan yayi alwala sannan ya fita masallaci. Duk
lalacewar lamarinsa bai tashi da tarbiyar sakaci da sallah da gangan ba.

Ana gyaran wurin jamaa sun watse sauran kadan Hamza ya fito zuwa gidansu. Izzatu ta bashi manyan
kuloli cike da abinci, nama da snacks. Ga katon din juice da na ruwa ya kaiwa su Hajiya.

Kula daya ya dauko maigadi ya biyoshi da sauran. Da sallama ya shiga babban falon. Mama da Hajiya
ne a wurin sai Jidda da ta biyo su Nura tana jiran mijinta. Duk suka amsa sallamarsa sannan Mama
tace maraba da Mungo Park. Turus Hamza yayi ya kasa furta gaisuwar da yake shirin yi musu. Hajiya
tace Jidda tashi mu shiga ciki uwa da danta zasu gana. Dama zamanta a wurin ta kara tunzura mama
da bayanin abinda ya faru a wurin partyn. Hamza yayi murmshi da wuya kaga fuskarsa a hade sai dai
idan yana cikin tashin hankali. Mama nasan nayi laifi ko baki fada ba. Amma wallahi nima bani da

masaniyar wannan party din. Surprising dina tayi nima. Mama tace ai naga alama. Zaka ce iyayenta
basu da labari ne? Ka hado kuloli ka kawo wa mayunwatan iyayenka abinci ko. To duk ka kwashe
abinka bama so. Yace Mama ita da kanta ta bani na taho dashi. Tace kaga ni ba wannan ke gabana ba
kaji ko. Yanzu don Allah Yaya yaushe zaka san ka girma? Wace irin rayuwa ce kuka daukarwa kanku kai
da iyalinka. Kanka aka fara zuwa kasar waje karatu ne da zaka dauko al'adun da ba naka ba kayi ado
da su. Sau nawa muna yi maka fada ni da Hajiya akan birthday partyn da kuke wa yaranku duk
shekara amma ka share. Irinsu valentine dinnan ma duk kuna yi ko? Shiru Hamza yayi don yau kam ya
san ya batawa Mama rai. Tace ba tambayarka nake ba. Yace munayi. Ta cigaba da fada....duk wani
dan iskan day da yahudu da nasara ke girmamawa kaima ka girmama. Ka iya kashe kudi mai tsoka ka
shiryawa yara party kawai don suji dadi. Irin sadakar nan ta abinci ko kudi kuwa sai karshen
ramadan. Baka tunanin halin kuncin rayuwa da mutane ke ciki yanzu.
Alhamdulillah muna da rufin asiri ci, da sha da sutura babu wanda Alhaji baya saukewa amma ai
ihsani yana da dadi ko. Ko kasan duk wata sai Ibrahim ya kawo buhun shinkafa gidannan sannan ya
bamu dubu biyar biyar ni da Hajiya. Ya san ba kudin ko abincin muka rasa ba. Amma yana neman
albarkar iyaye. Mariya da Jidda suma suna nasu kokarin da dan abinda sukeyi. Duk cikinsu kafi kowa
morar Alhaji kuma ka fisu kudi amma daga kai sai iyalinka. Kawaici kawai mahaifinka yake maka irin
na bafillatani amma ko kadan baya jindadi. Shin ka taba zama ka tambayeshi a halin da kamfaninsa
yake ciki? Ko ka tambayi Hajiya me take bukata ko da ba na kudi bane? Hamza ya girgiza kai a hankali.
Mama bata san cewa tana fadan ma hawaye take yi ba. Tace to girma ya kama babanku. Ibrahim
lecturer ne amma daga wurin aikinsa yana zuwa kamfanin taya shi aiki. Nura yanzu yake ajin karshe a
jamia amma tun yana level one yake zuwa. Hamza yayi mamaki wai Nura har ya kai level four yanzu
sai dai bai nuna ba kada fadan ya karu. Ita kuwa Mama cigaba tayi da fadanta. Yan uwanku na Kumo
makusanta. Ina nufin yan uwan Hajiya da na Alhaji kasan halin da suke ciki? Ko kasan a rage
maaikatan banki harda kanin Hajiya. Hamza ya dago kai wanne? Tace Nafiu. Gashi yana da mata biyu
da 'ya'ya goma sha uku. Watansa kusan bakwai ba aiki. Akan Nafiu Hajiya ta soma kukan rashin
taimakon da kake yi. Maganganun sun ratsa Hamza sosai. Ji yayi kamar wanda aka tasa daga bacci.
Mama tace ni dai lahirarka nake duba maka Yaya. Rayuwarka nema take ta sauka daga turbar addini.
Har yau ban manta yadda Izzatu tasha maganin hana haihuwa ba wai sai ta gama karatu. Allah ne ma
Yaso kuna da rabon haihuwar daga baya. Ka tashi ka je ka bawa Hajiya hakuri ka tafi dare yayi. Hamza
yayi godiya sosai tare da sake bata hakuri. Har ya kai bakin kofa tace Yaya....naam ya amsa. Nasan
saura baifi sati biyu ba birthday din Nana. Kwana hudu kafin ranar ka dawo dasu nan. Wallahi ka sake
celebrating birthday a gidanka zaka ga fushina sosai.. Allah Yayi muku albarka
[25/09 3:14 pm] Inna��: AL'ADUN WASU 🗿10

Batul Mamman(Mrs)💖





Zuhra ta shigo layin gidan Anti Faiza sai ta hango mai tsamiyar biri yana turawa a baro. Tsallakawa tayi
bangaren da yake zata siyo. Dama tana ta tunani yar tsarabar da zata kaiwa su Abba.

Hamza da Izzatu suna mota suna hira tana fada masa Inuwa sakatare ya kira yaji ya jikin Junior fa.
Dariya sukayi yace kin mayar dani makaryaci dai. Khalifa ne ya hauro daga baya ya dawo gaba ya
zauna kusa da Izzatu. Ta juya ta harari maiaikinta. Ke Tala garin yaya kika bari ya taso har ya dawo
nan. Oya Khalifa koma wurin zamanka. Ko kulata baiyi ba yace daddy ka kawo na tayaka driving.
Hamza yace not today Khalifa kaga anyi ruwa jiya titin babu kyau. Kuma akwai mutane a nan. Khalifa
yace ko sau daya ka bari na dana. Izzatu ta kama shi zata mayar bayan mota yasa ihu tare ta riko
wuyan Hamza. Iyakar karfinsa yasa yana jan babansa. Garin ya cire hannun Khalifan ya dan dauke ido
daga kan hanya.

Tana tura ledar tsamiyar birin a jaka taga mota ta yo kanta. Hantar cikinta ta kada ta rasa ina zata yi
ma. Gabadaya ta rude kafafunta sun kasa daukarta. Da kyar Hamza ya iya tsayar da motar bayan ya
shigar da ita cikin wani ruwa da ya kwanta a gefen titi. Har fuska ruwan ya watso wa Zuhra sannan ta
zame ta fadi a zaune cikin ruwan.

Karshen bacin rai kam taji shi a lokacin. Musamman da ta hango mai tukin da yaro suke kicikici da
sitiyarin motar. Da sauri Hamza ya tura Khalifa wanda yake ta kuka cinyar Izzatu ya sauke glass din
motar yana duban Zuhra. Leko da kansa yayi zai bata hakuri sai dai akayi rashin sa'a kwalliyar fuskarta
ta bashi dariya. Izzatu da Tala ma da suke cikin motar sai da suka yi saboda yadda lebenta ke daukar
ido. Ita kuwa Zuhra haushi ya kara kamata. Hamza ya dan daure amma fuskarsa dauke da murmushi
yace don Allah kiyi hakuri kinji. Yaro ne ya rike sitiyarin Allah Ya kiyaye ban tabaki ba dai ko? Zuhra ta
tsuke baki ban sani ba...don tsabar wulakanci kayi min wanka da kwatami sannan ka wani kame a
mota kana tambayar ko ka tabani. Hamza ya dan sha kunu jin abinda ta fada yace to naji kiyi hakuri
don Allah. Ya zaro kudi a aljihunsa ya mika mata dubu biyar. Gashi ki sayi sabulu. Ganin ya tayar da
motar ta kama hannun gefen inda yake zaune ta soma masifa. Amma kai baka da mutumci
wallahi...tana kallonsa tana kallon kudin. Kudinka me zasu min. Malam ka fito ka duba ko naji ciwo ka
kaini asibiti. Izzatu ta dan leko kiyi hakuri kinji, kinga yaron da ya jawo, ta dungure Khalifa. Maganar
Zuhra ta bawa Hamza haushi yace idan bazaki karbi kudin ba sauri nakeyi. Kin samu na tsaya zaki
rinka yi kin rashin kunya. Zuhra tace anyi din, nace anyi din kuma Allah Ya isa abinda kayi min. Ka wani
makale a mota kai mai kudi ko. Yadda take magana ya sake bawa Izzatu dariya. Haka kawai yarinyar ta
burgeta. Hamza kuwa harararta yayi sannan cikin fushi ya fito daga motar. Tun kafin ya karaso tsoro
ya cika mata zuciya. A gabanta ya tsaya ta daga kai ta kare masa kallo. Tabdijam...da kyar in kanta zai
kai kafadarsa ma. Ta hadiyi yawu da kyar. Mutumin duk da bashi da kiba amma dai baya sahun masu
rama, gashi da tsaho. Idanunta suka kawo ruwa don kallon da yake mata ba na wasa bane. Idan ya
dake ta kuwa ya daki banza. Ya dan rage sautin muryarsa ke kinga nayi kama da sa'anki ne? Ta girgiza
kai. Yace to ina baki hakuri sai ki rinka yimin rashin kunya. Izzatu ta dan bude kofa tace babyna ka
taho mu tafi kawai. Zuhra ta zaro ido ta kara kallonsa....baby kuma? Katon gardi da kai a kiraka baby.
Lallai an cuci kalmar nan al'quran. Ran Hamza ya sake baci ya daga hannu zai mareta. Tace kana
tabani zanyi suman karya a wurin nan sai mazan can sun taru. Kuma in fada musu abinda kayi min.
Daga kai yayi ya kalli kofar kantin da ta nuna yayi murmushi yace bismillah. Zuhra ta dan ja da baya da
gaske nake fa...shima ya kara matsawa gabanta ai ban hanaki ba. Ta tabbatar dai ba wasa yake ba
kawai sai tace Allah Ya isa da karfi ta kwasa da gudu.

Binta yayi da ido sannan yayi tsaki. Idan ya sake ganin yarinyar nan sai jikinta ya gaya mata. Shi zata
yiwa Allah Ya isa har sau biyu. Yayi kwafa ya shiga mota. Izzatu sai dariya take. Yarinyar kamar wata
clown. Ita fa gani take tayi kwalliya karshe ko? Hamza yayi tsaki yanzu duk abinda ta fada min bai
dameki ba Izzy sai ki rinka dariya. Tace ai abin naku ne da ban dariya. tayar da motar yayi don idanun
Izzatu suna ga yarinyar da ke gudu ba maganar da yake ba. Tana kallo har Zuhra ta fada gidan Faiza.... [25/09 3:14 pm] Inna��: AL'ADUN WASU 🗿9


Batul Mamman(Mrs)💖




Tunani ne duk ya ishi Hamza har ya isa gida. Tabbas ko makaho yasan kasarmu tana cikin matsi a
wannan yanayin da muke ciki. Sai fatan Allah Ya kawo mana sauki. Amma a haka duk shekara basa
rasa dalilin yin taro a gidansu. Duk da hakan ba ra'ayinsa bane tun farko amma ya goyi bayan Izzatu
akan duk abinda take yi. Dole ne kuma ya nuna mata kuskuren rayuwar da suka daukarwa kansu ko
don inganta tarbiyar 'ya'yansu. Kila mutane suna ta zaginsa bai taba tunanin haka ba sai yau. A haka
ya isa gida zuciyarsa duk ba dadi. Izzatu ta gama gyaran dakin yana ta kamshi ita kanta ta yi kyau sosai
tace ya shiga yayi wanka.

Inuwa Sakatare ya karanta

3 / 40