Aladun Wasu Hausa Book Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Read Hausa Novels

Chapter   32 / 40

93K to 96K   out of 117.5K words

sujjadar godiya ga Allah SWT.
Tayi kusan minti biyu tana hamdala da takbir. Ko da ta dago kanta wasu zafafan hawaye ne suka sauko
daga idanun Hamza. Kullum Zuhra daban yake ganinta.

A tsorace ta tashi yana daga zaune ta rungumeshi a kirjinta. Murya a raunane tace Ya Hamza me yasa
ka hawaye?

Muryarsa a can kasa yace Cutie ina sonki. Ina sonki. Ina sonki. Kuma nagode miki for being who you
are.

Sake kankameshi tayi tace nima ina sonka Ya Hamza. Uhmm sai dai dan turancin nan na karshe kace
who you are ko.. Toh, I am Fatima Bashir.

Mai Hamza zaiyi in ba dariya ba. Zuhra tayi kicin kicin da fuska ita tayi fushi. Hamza ya rike habarta
haba my darling Zuhra? Kada kiyi fushi dani. In sha Allah idan komai ya daidaita na wannan course
din da za'a turani zamu fara English lessons dake. Dole na ware lokaci na koya miki da kaina.

Zuhra ta turo baki ni bazan koya ba kuma ka tashi ka koma dakinka ni munyi fada. Cakulculi Hamza ya
rinka yi mata har ta soma dariya sannan ya fita zuciyarsa fari kal.

Washegari da safe ya sami cikakken bayani game da zuwansa Abuja. Da yake abin na gwamnatin
tarayya ne kuma da izininsu kwana biyu aka ce zasu yi a tantance su. Babu wani zancen masauki
alamun kowa yayi ta kansa kenan. Harda dariyar mugunta ya fadawa Izzatu basu da masauki saboda
haka bazai tafi da ita ba. Kila yaje gidan abokinsa ya kwana. Itama dariyar tayi tace ta riga ta sanar da
iyayenta batun zuwansu har an gyara musu wurin kwana a gidansu. Baiji dadin wannan karambanin
ba shiyasa yace mata baza shi ba. Ko minti ashirin basuyi da maganar ba Alh Sunusi mahaifin Izzatu ya
kirashi da kansa yace lallai yazo gidan anyi masa masauki ko da shi kadai ne. To ta yaya zaije gidan shi
kadai dole ya tafi da Izzatu. A haka suka rabu yayi shirin tafiya office.

Da rana da ya dawo a kitchen yaji motsin Zuhra. Yana shiga ya tarar da ita tana rabon abinci a cikin
irin abin take away dinnan. Jallop din shinkafa tayi sai kwai da ta dafa ta yanka shi bibbiyu take
sakawa a abincin. Hamza ya dan dauki lokaci yana kallonta bata kula ba saboda ta juyawa kofa baya.
A hankali yaje ya rufe mata ido tayi murmushi tace Ya Hamza ka dawo?

Cikin wasa ya bata rai, ya akayi kika gane nine?

Tace da kamshin turarenka mana.

Jera abincin yaga tana yi a wasu manyan robobi yace abincin meye wannan Cutie?

Ta dan kalle shi tayi murmushi...ni banso ka dawo ka tarar ban gama ba. Abincin sadaka ne zan bawa
maigadi yace akwai makarantar allo a nan baya. Nayi da niyyar Allah Ya baka sa'a kuma Yasa kayi
karatun ka gama lafiya. Tana kaiwa nan idonta ya ciko da kwalla, tunanin rabuwarsu da Hamza na
wata biyu ke damunta. Shi kuwa kasa magana yayi kamar kodayaushe idan tayi wani abin da yafi
karfin tunaninsa. Har abincin sadaka take yi wanda yasan akan yi lokaci lokaci a gidan iyayensa. A take

yayi wa kansa alkawari indai ya sami sarari da yardar Allah Hajji zai kai Zuhransa. A duniya dai shine
kawai abinda zaiyi mata na karshen jindadi a matsayinta na musulma. Amma a nan kanta ya dafa ya
rinka saka mata albarka. Sonta kuwa kullum karuwa yake a zuciyarsa saboda kyawun halayenta.

Kwanaki biyu a tsakani su shirya tafiya Abuja. Izzatu sai rawar kafa take kamar farin shiga a zuwa
Abuja. A motar Hamza suka tafi da aka gyaro. Zuhra tasha kukanta a daki Hamza na rarrashi sannan ta
fito ta rakasu.

Kwanansu uku suka dawo aka fara shirye shiryen tafiyar Hamza zuwa kasar South Korea. Kwanaki uku
suka rage ya tafi idan kaga Zuhra duk tayi wani iri. Har rama ta danyi saboda zulumin tafiyar Ya
Hamza. Dambun nama ta roki Umma tayi mata saboda ita idan tayi duk sai rabi ya kone. Ai kuwa
Umma tayi mai dadi musamman da tasan na tafiyar Hamza ne. Da aka kawo yayi ta murna.

Izzatu ma a nata bangaren cake tayi masa kanana mai dadi ta jera a wata roba sannan ta liketa
saboda kada ya bushe. Itama Hamza yayi mata godiya.

Da asuba ana saura kwana biyu ya tafi kuma ranar Zuhra zata fita girki. Tunda ta idar da sallah take
masa kuka. Duk abinda zaiyi mata tayi shiru yayi amma minti kadan sai ta cigaba. Ya zuba mata ido
kawai yana kallonta.

Cutie wai kukan nan na meye? Ba fa yau zan tafi ba.

Ta dago jajayen idanunta...to meye maraba Ya Hamza daga yau kai da ka sake kwana...sai tayi shiru
kanta a kasa

Ya share mata hawaye kina tunanin zanyi wata biyu bamy hada shimfida ba ko? Gashi ke kuma kina
son kwanciya a jikin mijinki.

Rufe ido tayi a kunyace...ni ba haka nake nufi ba.

Hamza yayi dariya yace ai ba sai kin fada ba na sani. Addua kawai nake bukata daga gareki. Kinga jiya
munfi awa daya ina nuna miki yadda ake whatsap saboda haka zamuyi ta hira kullum kinji ko. Idan
kika yi kwalliya kullum ki turo min hotonki na gani.

Ta gyada kai wani hawayen na taruwa a idonta...Ya Hamza yau kada kaje ko'ina har sai lokacin da zan
fita girki. Don Allah ka zauna dani.

Hannunta ya kama ya tasheta daga kan gadon. Muje har breakfast tare yau zamuyi.

Manne jikin juna suka sauko saboda asabar ce su Khalifa basu da makaranta. Sai karfe goma zasu je
islamiyyar safe.

Kayan kwabin fanke Zuhra ta debo ta fara kwabawa. Hamza taji ya tsaya a bayanta ya zira hannu a
robar da take kwabin yana wasa da hannunta sannan yana bin wuyanta yana kissing. Gabadaya aikin
gagararta yayi cikin kankanuwar murya tace Ya Hamza don Allah ka bari na gama. Koma can gefen ka
tsaya.

Yi yayi kamar yayi fushi yace ba ke kika ce kada na barki ba yau. Ni babu inda zani ya fada yana sake
rumgumarta ta baya. Muryar Junior ce tasa ya saketa ba shiri da ya shigo kitchen din yana murza ido.

Maama fanken zaki yi min don Allah?

Zuhra tayi murmushi tace kaga har na gama kwabawa sai mu dan jira ya tashi ko.

Rungumeta yayi daidai kafarta yace Maama kinfi sona akan Daddy shiyasa kike dafa abinda nake so..
nima idan na girma ke zan fara siyawa mota da jirgi kafin Mummy da Daddy.

Hamza ya bude baki
yana kallonsa. Lallai yaran zamani kun iya sa ido. Kai yanzu har kasan so? Ya fada yana daga Junior
sama suna dariya.


***********

Wannan shafin naki ne Maman twins. Gaisuwarki ta riskeni ina fata nima tawa ta iso gareki. Godiya
mai tarin yawa tare da fatan alkhairi. Allah Ya albarkaci zuria.💖


AL'ADUN WASU 🗿73

Batul Mamman(Mrs)💖






Jirginsu Hamza shabiyu da rabi na dare zai tashi shiyasa ya yanke shawarar barin gidan karfe goma
domin ya sami damar zuwa gidan iyayensa yayi musu sallama.

Sai da ya dawo daga masallaci bayan sallar isha sannan yaci abinci kadan yaje yayi wanka. Gidan duk
yayi wani iri saboda kowa na tunanin tafiyar Hamza. Ya shirya cikin kananan kaya yayi kyau sannan ya
dauki rigar sanyi a hannu saboda banda sanyin jirgi ya bincika ana sanyi sosai a South Korea. Ya gama
shirinsa tsaf suka sake wata sallamar da Izzatu sannan ya fito zaije dakin Zuhra. Gabansa Izzatu tayi
saurin tarewa ta daure fuska....Baby ina zaka je kuma?
Shima tasa fuskar a daure saboda bata masa lokaci da yake ganin zata yi yace zanje sallama da Zuhra
mana.

Yana soma tafiya ta rike masa hannu....bafa zan yarda ba. Yau girkina ne saboda haka bai kamata kace
zaka wata sallama da Zuhra ba. Ba tare zamu airport din ba? Sai kuyi sallamar a can.

Dan rufe idonsa yayi sannan ya bude a hankali....Izzy kada kisa mu rabu da bacin ran juna. Zanyi
tafiyar wata biyu har zancen wani girki zai taso? Kije ki fito min da jakar kayana, idan bazaki iya ba ki
jirani a kasa ina fitowa zamu tafi.

Bai kara saurararta ba ya tafi dakin Zuhra. Zaune ya ganta akan kujera tana sharar hawaye. Ta gama
shiryawa ta saka wani katon hijab tana jira Hamza ya fito su tafi. Tana ganin ya shigo tayi saurin goge
hawayenta ta mike tsaye...Ya Hamza har ka fito?

Murmushi yake yi yana kallonta. Na fito Cutie, wato baki dena kukan ba ko?

Kamar yace yi wani kukan ta soma wani sabo. Ya dauki lokaci yana bata hakuri da rarrashi duk ta
hanyar da yasan zai dauke mata hankali. Da kyar tayi shiru tana fada masa irin yadda zata yi kewarsa
idan ya tafi. Wayarsa ya dauko yana daukarta hoto tana ta rufe fuska wai bata yi kyau ba.

Yace gara na dauki fuskar a haka nasan cewa idan na tafi kullum zaki tuna dani kamar yadda zan tuna
dake.

Jin haka yasa ta dauke shi itama sannan suka yi wani tare. Suna cikin haka suka ji wani mahaukacin
bugun kofa. Yasan aikin Izzatu ne dama yana sane ya kulle kofar dakin don ba karamin aikinta bane ta
bude su. Sai da ya sake yiwa Zuhra kyakkyawar sallama sannan suka fito tare fuskokinsu dauke da
murmushin da ya kona ran Izzatu.

A gida aka bar yaran wurin Tala saboda dare ne. Kowa yana fadar me Daddy zai siyo masa na tsaraba.
Suna zuwa gaban mota Izzatu tayi saurin shiga gaba. Dama Zuhra bata yi tunanin shiga ba saboda
tasan ba ita ke da girki ba. Kafin su je gidansu Hamza taga kayan takaici kala kala. Hannun Izzatu a
cinyar Hamza yana tuki. Ko ta sakala hannun a wuyansa ta wani kwanta a jikinsa. Yayi mata magana
har ya gaji. Baya son abinda zai batawa Zuhra rai. Da suka je gidan Izzatu ta zauna kwam sai Hamza ya
bude mata kofa. Hakan ya bashi damar tsayawa bawa Zuhra da ta fito hakuri. Don bata son ya tafi da
baccin rai shiyasa ta nuna masa babu komai. Izzatu ta gaji da jiransa ta bude ta fito suka shiga ciki.

Duk kannen Hamza sun zo yi masa sallama. Mota uku suka yi zuwa airport wasu a tasa wasu a ta
Ibrahim da Nura.

Sai da zai shiga ciki Izzatu ta soma kuka duk ana jinta ta rungume shi tana cewa zatayi missing dinsa.
Tamkar ya tona kasa ya rufe kansa saboda kunyar kannensa dake wurin. Ibrahim barin wurin yayi
saboda bacin rai. Sai da Hamzan yayi mata tsawa sannan ta kyale shi tana kallon yanayin Zuhra
wadda ranta ya gama baci. Abinda yake gudu dai sai da ya faru sun rabo da Cutie dinsa ranta babu
dadi. Key din motarsa ya bawa Izzatu yace su tafi gida ita da Zuhra don yasan ta kware a tuki.
Bayan ya shige ciki motocin su Nura da Ibrahim ne suka fara yin gaba sannan Zuhra da Izzatu suka tafi
wurin motar Hamza. Da Izzatu ta bude ta shiga sai tayi saurin danna central lock ta rufe Zuhra a waje.
A take hankalin Zuhra ya soma tashi ga dare ta fara buga glass tana yiwa Izzatu alama da ta bude
mata. Glass din ta sauke kadan tace....naga babu abinda baki iya ba shiyasa kullum Hamza yake
yabonki to wannan yabon ya kaiki gida. Daga nan ta fige mota tayi gaba ta bar Zuhra a tsaye.
Wayarta ma Hamza ya jona mata chaji tana cikin motar. Zuciyarta ke wani irin bugu saboda tsananin
bacin rai. A rayuwarta bazata taba mantawa da Izzatu da ire-iren wulakancin da take mata ba. Kukan
ma ta kasa ita daga airport din ma bata san hanyar da zata bi taje gida ba gashi tasan ko ba'a fada ba
shabiyun dare ta kusa. Wani irin tsoro ne ya ziyarci zuciyarta ta fara addu'o'i. Jiki a sanyaye ta fara
tafiya hanyar da tasan zata kaita bakin gate ta fita. Motoci kadan ne suke wuceta tana tafiya a gefen
titi. Ga irin yanayin da muke ciki na raunin tsaro babu wanda ya tsaya yayi yunkurin taimaka mata.
Itama ko an tsaya bazata shiga ba saboda tsoro.

Shabiyu saura minti uku Izzatu ta shiga gida. Maigadi ya tareta yana mata sannu da zuwa. Cike da
nishadi ta shige ciki saboda ta gama tsara abinda zata fadawa Hamza idan Zuhra ta kai kararta.
Rantsewa zata yi motar Ibrahim ta ga ta shiga shiyasa ta taho. Dama shima Ibrahim din ta tsane shi
saboda tun farkon aurenta ta kula baya sonta. Kai tsaye dakinta ta wuce ta tafi ta kwanta hankali
kwance.
Shiru Tala bata ga shigowar Zuhra ba tana son bata canjin kudin kulu da ta aiketa saboda bayan asuba
take son tafiya garinsu zata je tayi sati biyu kamar yadda Hamza ya bada umarnin ta je. Gajiya tayi da
jira ta fita waje maigadi har ya kwanta ta buga masa kofa ya fito ta tambayeshi ko yaga shigar Zuhra
ciki. Yace shima yayi mamaki amma Izzatu ita kadai ta dawo.

Har Tala ta juya zata koma ciki sai dai hankalinta bai kwanta ba. Da yake da waya ta fito sai ta gwada
kiran Zuhra. Karar wayar suka ji daga cikin mota saboda a gefen motar suke a tsaye. Nan da nan Tala
da maigadi suka shiga tashin hankali. Tace bari naje na tambayi Maman Khalifa ko ba a gida zata
kwana ba.

Maigadi yace ashe baki da tunani ban sani ba? Tare ya kamata su dawo amma basu dawo ba kuma
duk munsan ba da ita maigida zaiyi tafiya ba. Ni a tawa shawarar ki kira wani a gidansu Yallabai kiji ko
a can zata kwana tunda ya fada min da bakinsa can zai fara zuwa kafin yaje iyafot din.

Da yake a rude take a take tace bata da numbar kowa. Har ta soma kuka tana tunanin ko wani mugun
abin ne ya sami Zuhra. Daga baya ta tuna jiya da safe Hamida ta kira wayarta saboda bata sami ta
Zuhra ba. Sai da suka rinka bin nambobin da aka kira a wayar wajen shida gashi babu kudi sosai
sannan suka yi sa'ar samun ta Hamida.

****
Hamida da Adabiyya suna ta hira basu ji wayar da wuri ba. Tala har ta hakura sun kira wasu nambobin
biyu sai ga kiran Hamida ya shigo. Ita duk ta tsorata ganin daga gidan Yaya aka kira da wannan daren.
A tunaninta ko babu lafiya Zuhra ta kirata da numbar Tala. Jiki na rawa Tala ta dauka tace kiyi hakuri
na kiraki a tsohon daren nan. Dama tambayarki zanyi ko a nan gidanku Maama zata kwana ko gidan
iyayenta?
Hamida tace bangane ba Tala. Kina nufin Anti Zuhra bata dawo gida ba? To ina Anti Izzatu?

Tala tace tana dakinta munga ita kadai ta shigo kuma ga wayar Maaman a motar Yallabai an jona ta
da wani abu. Sautin kukan Hamida Tala ta jiyo tasan lallai ba lafiya ba.

Ko ajiye wayar bata yi ba ta tafi dakin Mama ta tarar bata nan. Dama tasan Hajiya na falon Alhaji tun
da suka dawo daga airport a nan suka gansu suna hira. Falon ta nufa da gudu tana yiwa Adabiyya
bayanin abinda Tala tace. Sallama tayi ko amsawa basu jira anyi ba suka daga labulen suka shiga
falon. Alhaji ne da matansa suke ta hira yau basu kwanta da wuri ba.

Hajiya ta daka musu tsawa tana son jin dalilinsu na shigowa a haka. Cikin kuka Hamida ta fada musu
wayar da suka yi da Tala. Babu wanda hankalinsa bai tashi ba a wannan lokacin. Alh Nasiru ya dauki
waya ya kira Ibrahim ya sanar dashi sannan ya tafi dakin Nura ya taso shi. Ko hula babu a kan Alhaji
suka fita da Nura. Airport din zasu fara dubawa kafin suje gidan iyayenta.

*****
Hadari ne yake hadowa garin yayi duhu sosai sai fitilun cikin airport na gefen titi. Iska da kura sai kada
Zuhra suke tana tafiya idonta sharkaf da hawaye. Banda Izzatu hatta Hamzan haushinsa take ji. Don
me bai tabbatar da ta tafi ba ya shige ciki. Kullum Umma na fada mata maza basa son macen da tafi
kawo kara amma wannan karon suna yin waya da Hamza idan har ta isa gidanta lafiya kenan zata
fada masa. Dole ayi mata iyaka da Izzatu idan ba haka ba kuma lallai zasu daku. Ko a unguwarsu babu
mai takalar Zuhra dambe don da gaske karfi gareta.
Ajiyar zuciya tayi da ta ga ta kusa isa bakin gate sai dai tun kafin ta isa ta fara jin ana daka mata tsawa.
Nan take ta gigice ganin sojoji sunfi biyar a kanta da bindigogi.

*****
Sanarwar karshe akeyi cewa jirgi zai tashi kowa yasa seat belt kuma a kashe waya. Ran Hamza a bace
ya kira Zuhra yafi sau ashirin bata dauka. Izzatu kuma da suka sake sallama tace Zuhran na dakinta. Ya
tabbatar idan yace ta kai mata tata wayar kuma bazata kai ba. Dole ya hakura ya kashe wayar. Sauran
mutum hudu da zasu tafi tare duk ta Abuja suka tashi da kyar ya sami alfarmar tashi ta Kano saboda
iyalinsa. Yayi yunkurin kashe wayar sai ga text ya shigo. Da sauri ya bude ya zata Zuhra ce. (Sir idan kana da lokaci gobe ka kirani.
Mr. Oscar)

Rasa abin yi yayi ba don yana cikin jirgi ba ai yanzu zai kirashi yaji abinda zai fada masa. Addu'ar abin
hawa da ta tafiya Hamza yayi ya kashe wayarsa zuciyarsa tana tunanin me ya sami Cutie dinsa.

****
Kneel down sojojin suka saka Zuhra

32 / 40