Aladun Wasu Hausa Book Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Read Hausa Novels

Chapter   14 / 40

39K to 42K   out of 117.5K words

fada a ranta. Dauka tayi
gabadaya hudun ta shigar dasu kitchen din. Kallon mamakin da yayi mata yasa ta tuna maganarsu
dasu Anas da suka ce mata maza basa son mata masu karfi. Sai kuma ta tunawa kanta ai Hamza ba
mijin da zasu so juna bane.

Kwalin gas cooker dinta ya farke ya sake fita. Bai dade ba ya shigo dauke da karamar cylinder. Daga
can gefe ya ajiyeta sannan ya hada mata gas din. Ya koma kan fridge din shima dan madaidaici ya
jona mata. Ita dai tana gefe tana binsa da ido. Sai da ya gama tsaf yace ga kayan miya nan da nama
sai ki saka a fridge kada su lalace. Daga yau ki rinka dafa iya abincin da zaki ci. Idan akwai abinda babu
a cikin kayanki sai ki fada a siyo. Tsananin farinciki da taji yasa ta washe baki da gaske kake don
Allah....daure fuska yayi, na taba wasa dake ne? Nagode, nagode, nagode ta rinka fada tana bude
ledojin. Ji tayi yace kuma ki kula kada ki bata wurin nan kinga tun asali ba kitchen bane. Ya nuna mata
sink shi kadai zan iya sawa idan kin tafi sai a cire amma bazan miki wani kitchen kabinet ba. Duk da
haka ma nagode ta fada cike da murna. Yau zata dafa abinci son ranta taci ta koshi. Hango kanta take
da kwano ba ma plate ba shake da abinci.

Wannan irin farinciki da take yi yasa shi jindadi. Ko ba komai yana ganin ya tsira daga laifin tauye
mata hakki a ganinsa. Zuhra tana susar kai tace uhmmm....yes ya amsa don yasan akwai abinda take
son fada. Dama...dama... gajiya yayi da inda indarta yace dama me? Uhmm nace shi gas din ya zan
rinka kunnawa? Au dama baki iya kunnawa ba aka kawo ki dashi. Turo masa baki tayi to mu a gida ba
da itace muke yi ba ko risho. Ganin ya daga hannu tasan a bakinta zai sauke shi tayi saurin ja da baya.
Nufi na fa ban saba dashi ba amma cikin kayana akwai risho din sai na fito dashi. Hannu ya daga yana
nunata, ki fito da me? Wallahi kada kuskura ki kunna min risho a wurin nan in ba so kike ki sake min
sabon fenti ba. Kinji ko! Gyada kai ta rinka yi kamar kadangaruwa da taji ya fara daga murya. Sai
kuma yace matso ki gani..kunnawa yayi sannan ya gwada ragewa da kashewa duk tana gani. Idan kin
kasa ki kira Tala ta nuna miki don naga alama kin fita kauyanci. Ni ba yar kauye bace ta fada tana kara
turo bakin nan nata. Biyota Hamza yayi zaiyi maganin rashin kunya ta juya da gudu. A bakin kofa suka
ga Izzatu tana dariya. Ai tunda naji kana daga murya nasan kun fara fada shine nazo kallo. Ta kalli
Zuhra bai dake ba ko...babu wanda ya bata amsa ta cigaba da dariyarta ta kama hannun Hamza suka
fita.

Tuwo Zuhra tayi niyar yi Izzatu tace kada tayi girki an riga anyi abincin dare da ita. Har ranta bata ji
dadi ba amma haka ta daure taci abincin.

Inuwa sakatare yana ta hada wasu files zai kaiwa Hamza saboda meeting din da zasu yi sai gashi ya
fito daga office dinsa rike da waya da makullin mota. Inuwa yace ranka ya dade fita zaka yi ne? Akwai
meeting fa biyu da rabi. Ba jimawa zanyi ba Inuwa in sha Allah. Zanje banki ne tun friday kaga yau
alhamis banji alert ba na kudin da ka ciro. Inuwa yace to Allah Ya kiyaye adawo lafiya. Amma ranka ya
dade yaushe Oscar yace zai dawo ne muna bukatar sa hannunsa a wasu takardu. Hamza yace nima
duk na damu ko jikin mahaifiyar tasa ne sai dai ban same shi a waya ba. Bari nayi sauri na dawo sai
muyi maganar dai. Koda ya fita jikin Inuwa sakatare yayi sanyi....Allah Yasa abinda zuciyarsa take kitsa
masa ba gaskiya bane.

Manyan architects yau da kanka a office dina. Manaja ke magana yana tashi tsaye suka gaisa da
Hamza. Kowa fuskarsa dauke da murmushi suka tambayi juna iyali. Manaja yace sai kuma naji kayi
aure ba labari. Kai Hamza ya dan sosa yana tunanin yadda zance ke yawo a gari..kayi hakuri abin ne
yazo a gaggauce. Babu komai Allah Ya sanya alkhairi. Yanzu dai how can I help you? Tashi Hamza yayi
kada ka damu shigowa nayi mu gaisa na riga na sanar dasu a costumer care alert ne bana ji tun last

friday. Kuma har a atm da na cire kudi still banji ba. Manaja yayi dariya ai dole ka damu ku masu
harka da manyan kudi. Suna magana text ya shigowa Hamza. Yayi murmushi dadina da bankin nan
saurin gyara abu. Gashi har alerts din sun shigo. Yanayin fuskarsa ne ya soma canjawa a take. Manaja
ya naga alert na an cire ten million har sau biyu a ranar friday din? Manaja ma dena murmushi yayi ai
sau biyun ne Architect. Ka turo sakatare dinka sannan ga mamakina ka turo wani Mr..Mr....mtsw na
manta sunan amma dai na kira nayi confirming a wurinka kafin a sakar masa kudin.
Jiri ne ya soma dibar Hamza daga tsaye yayi saurin dafa tebur din manaja ya zauna. Da kyar ya iya
cewa Mr Oscar? Eh shi kuwa manajan ya amsa. Ka tuna na kira na tambayeka kace eh kaine ka turo
shi. Tabbas manaja ya kira amma a lokacin Izzatu ke faman daga murya tana masifa sai ya saki Zuhra
baiji abinda manajan yace ba ya amsa masa. Wato shiyasa Oscar yace mamansa ba lafiya ya tafi
garinsu gashi an kusa sati babu mai samunsa a waya. Allahumma ajirni fi musibati wa akhlufni
khairan minha. [25/09 3:56 pm] Inna��: AL'ADUN WASU 🗿38

Batul Mamman(Mrs)💖





A rikice manaja ya fara tambayar Hamza ko sunyi kuskure ne. Numfashin Hamza da kyar yake fita ya
dago idanunsa da suka yi nauyi lokaci guda yace babu abinda kayi manaja. Matsalar daga bangarena
ne. Sau biyu yana yunkurin tashi amma kafafunsa sun kasa daukarsa. Manajan sai bashi baki yake
yana rokonsa ya zauna har zuciyarsa ta daidaita amma sam yaki zama. Ko da ya shiga mota rasa wurin
zuwa yayi. Gidansa zai tafi ko office zai koma. Yafi rabin awa a motar kafin ya tayar ya dauki hanya.
Lokacin da ya shiga gidan babu kowa sai Kande mai aikinsu. Da fara'arta ta tare shi tana masa sannu
da zuwa. Jikinsa duk a sanyaye yake yace ina mutan gidan ne naji shiru. Nura yana daki su Adabiyya
kuma sun tafi makatanta. Hajiya da Mama kuma sunje unguwa. To din ma da kyar ya iya fada sai ya
tashi ya tafi dakin Hajiya. Babu abinda yake a lokacin kamar yaga mahaifiyasa. Yaji dadi a bude ta
barshi kamar tasan zai zo. Gadonta ya nufa ya kwanta abinda ya dade baiyi ba. Yana rufe ido sai wasu
zafafan hawaye suka sauko masa. Ji yake kamar komai nashi ya tsaya cak. Cheque din da Mr Oscar ya
dauka hade da sauran da suke office dinsa idan an hada miliyan arbain kenan zai hada ya bawa su Mr
Peter ya kawo karshen contract dinsu. A dalilin hada wannan kudin gabadaya maaikatansa suka
amince da karban rabin albashinsu a wannan watan don kawai su tseratar da kamfanin. Yanzu gashi
miliyan goma ta tafi a kudin bai san ta ina zai samu su ba. Ginin gidansa yaci kudi ba na wasa ba. Idan
kuma ya tattara kudaden account dinsa tare da sayar da filayensa zai iya biyan kudin to amma rike
iyalinsa zai zama da matsala domin kuwa akalla kafin kudin ayyukan da yake su fito zai dan dauki
lokaci. Yana wannan tunanin bacci ya dauke shi.

Hajiya ta kira Mama ko sun taho daukarta daga tata unguwar Mama tace tun dazu nake kiranki ban
samu ba. Gamu a garejin makanike ban je inda zani ba. Amma na fasa ana gamawa zamu biyo. Hajiya
tace babu komai bari na bi adaidaita sahu kaina ke ciwo. To ki kira Nura mana yazo ya dauke ki. Hajiya
tace babu komai shima yau da mura ya tashi. Sai kun dawo ni zan wuce gida. Tana gama wayar suka
yi sallama da kawarta da taje dubawa ta fita ta hau adaidaita sahu.
Gabanta yayi mummunan faduwa ganin mutum a kwance a kan gadonta. Alhaji yana Kumo kuma ko
shine da wuya ya kwanta a dakinta. Nura kuma sai da ta leka dakinsa ta dubashi sannan ta taho nata.
Babu inda baya rawa a jikinta ta ja kafa ta je gefen gadon inda zata ga fuskar mai baccin. Sai da ta dan
ja baya saboda wanda bata taba tsammani ba ta gani. A tsorace tace Yaya....shima kansa ke masifar
ciwo ya bude idanunsa da kyar. Hawaye ne bushe a fuskarshi Hajiya ta matsa ta taba shi. Bakinta har
rawa yake saboda tsoron abinda zai ce tace Yaya me ya faru? Tashi yayi ya gyara rigarsa da ta yamutse
sannan ya mayar da hularsa. Yana dan murmushi yace Hajiya babu komai. Zuwa nayi mu gaisa duk
bakwa gidan. Bari na koma office sai anjima. Hannunsa ta rike. Itama hawayen take yi....haba Yaya
duk duniya idan akwai wanda zaka boyewa damuwarka kasan banda ni ko. Bar ganin ban fiye shiga
harkarka ba duk yanayin da ka shiga nakan gane na farinciki ne ko akasinsa. Dawowa yayi yasa mata
kuka kamar karamin yaro. Kai bakace Hamza bane dan shekara talatin da takwas mijin Izzatu da
Zuhra. Akan kujera ta zauna tana rike da hannunsa ya zauna a gabanta. Kansa ta dora akan cinyarta
yayi kukansa mai isarsa. Rabonsa da yi mata irin kukan nan tun ranar da zai tafi Canada. Duk ranar da
yayi irinsa to ba karamar damuwa yake ciki ba. Babu wanda yasan yana yi sai ita mahaifiyarsa. Cike
da tausayawa irin ta uwa ta rinka shafa kansa har yayi shiru. Ko da ya dago kansa murmushi ne a
fuskarsa yace Hajiya na dade banyi miki kuka ba ko. Yau ma sha'awarsa nayi shine na taso daga office.
Bari na koma ana jirana meeting karfe biyu da rabi. Lokacin biyu saura kwata. Tunaninsa bai wuce
yadda ya mori kudinsa ba lokacin da yake dasu shi kadai. Sai da matsala ta tashi zaizo ya tayarwa da
mahaifiyarsa rai. Ya santa bata da magana sosai, ba lallai ko Alhaji ta fadawa amma zata shiga
damuwa. Hajiya tace tunda baka son fada min damuwarka zan tayaka addua kamar kullum. Allah Ya
kawo sauki cikin dukkan al'amuranka. Ka yawaita ambaton Allah hakan yana yaye damuwa da bacin
rai, sannan kayi kokarin sauke hakkin wadanda ke kanka Allah Yayi maka albarka. Wani hawayen ne ya
sauko masa yayi saurin gogewa. Amin Hajiya nagode. Tana kallo ya fita ta shiga toilet tayi alwala.
Tasan da kansa zaizo ya fada mata matsalar amma abinda yafi dacewa yanzu tayi zata masa. Addua ta
dukufa yi masa sannan ta saka dukkan kannensa da iyalansu.

Waya yayiwa Inuwa meeting sai gobe baya jindadin jikinsa. Tunani ne fal a zuciyarsa. Sai yanzu yake
tunawa cewa Allah SWT Ya na jarabtar bayinsa ta hanyoyi da dama. A irin rayuwar sakaci da addini da
yayi ai dole watarana ya fuskanci irin wannan. Sai yanzu ya sake nadamar abubuwan da yayi a baya
da wanda yake kanyi yanzu wato sake da hakkokin matarsa don a zahiri suna damunsa. Sonta kawai
baya yi. Zaiyi kokarin kyautata alakarsa da Mahaliccinsa da sauran mutane. Itama Zuhra zaiyi kokari ya
sake da ita zuwa lokacin da zai saketa. Tunda basa son juna rabuwar ce zata fi. ta yadda bazai cigaba
da daukan hakkinta ba. Zai bari sai komai ya lafa masa a wurin aiki sai ya sanar da Alhaji zai saketa
saboda gudun kada Allah Ya kamashi. A lokaci daya duk sai ya zama abin tausayi.
[25/09 3:56 pm] Inna��: AL'ADUN WASU 🗿39

Batul Mamman(Mrs)💖




Karo na biyar kenan da Zuhra ke dandana ruwan miyarta. Yawunta duk ya tsinke saboda yadda
kamshin daddawa ke tashi. Nana na biye da ita a kitchen din har ta gama. Tuwon shinkafa tayi
malmala biyar yadda zai isheta taci da rana, da daddare sannan ta sami na dumame da safe. Plate ta
dauko mai dan fadi da zurfi ta saka malmalar da tafi kowacce girma da miyar kukarta duk a hade.
Manshanu kadan ta zuba ta goya Nana a bayanta ba zani ta dauki plate din da hannu biyu ta tafi falo.
Tana tafiya tana cewa Nana rike wuyana sosai fa. Ita kuwa Nana sai murna take tace toh.
Sai da ta shimfida tabarma kusa ta dinning table sannan ta zauna cin tuwo. Loma take kaiwa kamar
za'a kwace. Tana ci tana bawa Nana a baki. Sun kusa cin rabi Izzatu ta sauko...idanunta kan Zuhra tana
bawa yarta tuwo a baki. Har da nan gudunta tayi saurin zuwa inda suke ta dauke Nana tana ta warin
kuka da daddawa. Zuhra ya zaki bata abincinki ke da aka ce ki dafa naki ke kadai? Ni ban saba bata
abinci da hannu ba kuma bama tuwo sosai saboda yayi mata nauyi. Bata nuna jin haushi ba tace kiyi
hakuri ban sani ba. Ganin Izzatu tayi hanyar kitchen yasa Nana ihu tana cewa Mummy sauketa,
sauketa abinci. Izzatu tace naji yunwa kike ji bari na wanke miki baki na zuba miki couscous. Bata
ankara ba Nana ta galla mata cizo a kafada. Ba shiri ta sauketa tana sosa wurin. Ita kuwa da gudu ta
koma gaban kwanon Zuhra. Hannu biyu tasa tana ci bata jira Zuhra ta bata ba. Sake komawa Izzatu
tayi zata dauketa sai taji muryar Hamza yana sallama.

Yana shigowa Zuhra ta kai wata shirgegiyar loma bakinta. Ido suka hada ai kuwa ta kware saboda
kunya. Ji yayi nauyin zuciyarsa ya ragu saboda yadda yaga tana cin tuwon cike da nishadi. Izzatu tace
sweety kaga rigimar Nana wai sai taci abincin Zuhra. To ki kyaleta mana ya fada tare da wucewa
sama. Ita kanta Zuhra tayi mamakin amsarsa. Bayansa Izzatu tabi tana masa sannu da zuwa.

Zuhra ji tayi jikinta yayi sanyi saboda yanayin da taga Hamza. Da gani yana cikin damuwa Allah Yasa
ba wani laifin tayi masa ba. Plate din tuwo kuwa sai da suka sude shi tas ita da yarta Nana sannan aka
tashi aka wanke hannu.

Bayan yayi wanka Izzatu ke tambayarsa ya aiki. A hankali yake magana yace Alhamdulillah. Tana
zaune akan kujera tana masa kallon tuhuma tace Hamza ko ka fara sonta ne? Bangane ba shima a
zaunen yake don baya jin zai iya cin abinci. Banda damuwar da yake ciki hannun Zuhra yake hangowa
miya na binsa ta gefe tana kai lomar tuwo. Yarinyar ta fiye kazanta. Izzatu ta dan sha kunu Zuhra nake
nufi. Lokacin da ka shigo ita ka fara kallo kuma ka danyi murmushi. Izzatu kenan,yanzu baki bani
komai nasa a baki ba kike tuhumata. To idan naso ta laifi ne? Matata ce fa. Sosai ta daure fuska bana
so, Hamza bana son irin wannan wasan. Nan da wata shida zata koma gidan iyayenta mu cigaba da
zamanmu yadda muka saba. Daga nan sai kuma ta soma murmushi baka ga yadda take cin abinci ba
dazu. Baka ce dan bakin nan tana zai dauki abinda take tura masa ba. Idan ka fita yau pizza zaka siyo

mana Baby a matsayin dinner. Ko sau daya bata damu da rashin walwalarsa ba. Hmmm kina bani
mamaki Izzy...me kuma nayi Babyna? Murmushi take masa tana kashe ido. Fada mata ma bata lokaci
ne don karshenta ta fadi abinda zai kara bata masa rai. Babu komai bari na dan kwanta kaina na ciwo.
Tashi tayi to bari na kawo maka magani. Amma kafin nan ga wannan....ta dauko cards har kala hudu
na biki. Ni duk matsalar Zuhra yasa na manta next week za'a fara bikin Mardiya cousin dina ta
kaduna. Yar Uncle Jibril kanin Dad dinmu. Wai matar da miji ya fadawa yana ciwon kai kenan. Ga naka
na daurin aure, ni a son raina ranar saturday na tafi kadunan saboda muna da shirye shirye a
gabanmu. Kasan dani suka dogara tunda na zauna a Canada suna son ayi abin da tsari sosai. Kije Allah
Ya kiyaye hanya ya fada a takaice....bargo yaja ya rufa har kansa. Bashi da kwarin yi mata fada ko fada
mata abinda ya kamata. Sai da ta gama yi masa lissafin kudin da take bukata sannan ta dauko masa
magani da ruwa.

Sai la'asar ya tashi jikinsa ya danyi kwari sannan kan ya dena ciwo. Masallacin kusa da gidansa yaje
yayi sallah ya dawo yaci abinci. Yana gama cin abincin ya dauki key din mota....Izzy ni zan fita ki
fadawa yarinyar nan kada tayi abincin dare zan taho muku da pizza din in sha Allah. Duk maganar a
sanyaye yake yinta, wani salihanci yake ji tunda Oscar ya dibga masa sata. Tace harda Zuhra kuma? Ba
kayi mata siyayyar kayan abinci ba. Yace nasan nayi amma as long as tana gidan nan zanyi kokarin
sauke nauyinta. Tabe baki Izzatu tayi to shikenan sai ka dawo. Har bakin mota ta rakashi ya tafi
gidansu. Nan ya zauna suka sha hira da kannensa kamar bashi ba. Hajiya taji dadin ganin ya sake ba
kamar dazu ba.
[25/09 3:56 pm] Inna��: AL'ADUN WASU 🗿41

Batul Mamman(Mrs)💖





Washegari meeting din gaggawa ya kira da dukkan maaikatansa. A nan yake sanar dasu abinda Mr
Oscar yayi. Inuwa sakatare yace shi yayi mamaki da ya ganshi a banki amma tunda manaja yace da
yardar Hamza aka saki kudin shiyasa bai tayar da zancen ba. Maaikatan suka tambayi Hamza garin
yaya haka ta faru yace matsalace ta taso daga gida a lokacin. Yana kujerar tsakaya a conference room
din yadda kowa zai iya ganinshi a katon zagayayyen table dinsu yace kada ku damu in sha Allah bazan
bari kwazonku ya tashi a banza ba. Sauran cheques din ya nuna musu Allah Yasa na

14 / 40