Aladun Wasu Hausa Book Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Read Hausa Novels

Chapter   11 / 40

30K to 33K   out of 117.5K words

da ba sa yi kama daga shaye~shey zuwa
Kungiyar asiri tun lokacin abin bai gama bazuwa ba,
babu kuma babu kalar yaren da babu a cikin su,
akwai iyamurai, akwai yarabawa da hausawa da
sauransu, kasancewar .Federal collage ce, tun da
aka kai ni daya daga cikin ‘yan Group din nan Jonh
ya sanya mini ido, sati guda da kai ni' ya shigo
dakina yayi mini fyade, ina ihu da kururuwa ya toshe
mini bakina, daga karshe suka tsorata ni da idan na
gayawa wani sai sun kashe ni, har suka bani misali
da yaran da ya mutu ranar da aka kawo ni wanda
cikinsa ne kawai ya kumbura ya
dinga aman jini, sai suka ce sune suka yi masa
haka, saboda yace sai ya tona musu asiri, ina ji ina
gani na kasa fadawa kowa, tun daga wannan
lokacin kullum dare sai john ya yi mini wannan abin
da ya saba mini, har aka shekara guda, tun yana
mini bana so har na fara yadda da shi ta dadin rai,
domin na riga na saba, a wannan lokacin suka bar
makarantar bayan ya riga yagama lalata ni, amman
kasancewar akwai irin su da suka maye gurbinsu

wato ‘yan aji Biyar ya sanya wasu suka ci gaba da
mu’amala da ni, tun daga wannan lokacin ya
kasance idan ban yi wannan harka ba bana jin dadi,
duk yanda zan yi na dai na na yi amman na kasa
Karima, don Allah ki yi hakuri ki yafe mini.”
“Na yi shuru cikin jinjina halin maganarsa,a qasan
raina tausayin sa ne ya cika ni, amman a fili na
kasa cewa komai, sai na tashi zaune na dube shi
cikin Bacin rai nace masa, Murtala ina son ka
amman bazan iya zama da kai da wannan halin
naka ba, don haka gwara mu rabu, ga mamakina sai
na ga
[25/09 3:48 pm] Inna��: AL'ADUN WASU 29

Batul Mamman(Mrs)





Idan kaga dakin Zuhra baka ce na yar Mal Bashir kafinta bane. Tabbas duk dakunan gidan sunfi nata
kaya masu kyau da tsada. To amma itama nata iyayen sunyi kokari sosai. Gida ya cika da yan kawo
amarya. Izzatu ita kadai ce a daki dama ita ba mai rakice rakicen kawaye bace. Daga ita sai 'ya'yanta.
Duk da tasawa ranta bazata kula Zuhra ko tayi kishinta ba sai da tayi kuka da aka shigo ana guda.
Adabiyya da Hamida sunfi kowa rawar kafa Yaya yayi amarya. Hakuri da nasiha aka sake yi mata
sannan suka tafi. Hajara da wasu yan uwanta ne karshen tafiya bayan sun sake gyara mata daki. Tashi
tayi ta cire mayafin jikinta saboda su hudu ne kawai a dakin. Hajara tayi saurin mayar mata.
"Abinda ake son amarya da jan aji. Kin wani cire mayafi, idan wasu suka sake shigowa fa."

Sake cire mayafin tayi "ke kyaleni nasha iska. Da zafin gari zanji ko na rabuwa dasu Umma." Tana
magana idanunta suka cika da hawaye.

Hajara ta ja hannunta suka koma kan gadon. Sake gyara mata dauri tayi aka fesa turare."to mu zamu
tafi amarya. Kada ki tashi nasan ango na hanya. Kuma ki dena kukan su Umma haka. Irin haka sai
yaga kamar auren dole aka yi muku.

A zuciyarta Zuhra tace meye maraba. A zahiri kuwa godiya tayi musu suka tafi. Sai da taji dakin tsit ta
tashi tana leka ko ina. Wurin yayi kyau sosai ga kamshin turaren wutar da kanwar Umma ta hada
mata. A hankali ta bude kofar toilet ta shiga. Wani murmushu tayi. Irin wannan bandaki kamar a
gidan shugaban kasa. Ta mika hannu sink taga ruwa ya fito tun kafin ta kunna famfon. Zabura tayi da
gudu zata fita don a zatonta famfon ya lalace ne , kada ace ita ta lalata. Ko da ta juyo sai taga ruwan
ya dauke. Gabanta na dukan uku uku ta sake komawa tana mika hannu saman zata kunna sai taga bai
sake fitowa ba. Har tayi ajiyar zuciya ta sake saka hannu a wurin fitar ruwa sai gashi ya sake fitowa.
Fita kawai tayi ta rufe toilet din. Allah Yasa tayi sallar Isha. Dama nafila take son yi, sai ta hakura.

Tun tana jira ko angon nata zai shigo har ta fitar da rai. Dama bata sa a ka ba. Wuri ta samu a tsakiyar
gadon tayi kwanciyarta ko kaya bata chanja ba. Bata dade ba bacci mai nauyi yayi gaba da ita.

Hamza bai shigo gidan ba sai shadaya da rabi na dare. Tun kayan jikinsa na daurin aure bai dawo gida
ba. Babbar rigarsa da hula duk a hannu ya shigo dasu ya hadu da Tala tana ta gyara gidan. Ita kam
dole a yaba mata wurin tsafta. A gajiye yake sosai, tayi masa sannu da zuwa ya amsa ya haye sama.

Sai da yaji ba dadi da ya kalli kofar dake hagun dakinsa. Wai matarsa ce a ciki. Ko alamar zuwa baiyi
ba. Kofar dakin Izzatu ya taba yaji bata rufe ba. Muryarta a shake alamar taci kuka yaji tace
"Waye?"
Shiga yayi ta taso da sauri ta rungume shi tana kuka. Bai hanata ba sai da tayi shiru don kanta.
"Ina su Nana?" Ya tambaya lokacin da yake cire takalmansa.

"Suna sabon dakinsu. Tala zata rinka duba min su." Yadda take maganar kasan har yanzu tana bakin
cikin canza musu daki da aka yi.

Kiss Hamza yayi mata a kumatu." Goodnight Izzy. Kije ki kwanta" Ya juya zai fita. Kansa ke ciwo kamar
ya tsage. Yau baici wani abin kirki ba tun safe. Yana son tambayar Izzatu amma yasan idan bata da
nutsuwa girki ma baya gabanta.

Saurin biyoshi tayi. Ta rike masa hannu" Don't tell me wurin Zuhra zaka kwana".

Hannun nata ya saki." No, dakina zani. Na gaji kema ki kwanta haka"

Kallon tuhuma take masa." Are you sure?". Kai ya gyada mata. Baya son magana saboda yadda kansa
ke sarawa "Ko nazo mu kwana? Ina fargabar ranar da zaka kwana dakin yarinyar nan. Zan iya mutuwa
saboda kishi." Ganin baya son magana yasa ta kyale shi. Tasan bazai fadi magana ba yaki cikawa.

Bayan ya tafi itama sake gyara jikinta tayi tabi bayansa. Da ya tambayeta abinci tace babu amma bari
tayi sauri ta dafa masa wani abin. Jallop din taliya tayi masa. Kafin ta gama yayi wanka. Abinci yaci ya
dan zauna ya fada masa. Suka kwanta shi da Izzatunsa. Ba wata hira tsakaninsu domin kuwa akwai
abinda ke damunsa.
[25/09 3:52 pm] Inna��: AL'ADUN WASU 31

Batul Mamman(Mrs)





Sai karfe uku da rabi Tala ta kwankwasa mata kofa. Ko da ta bude abinci ne a plate an rufe da wani sai
ruwa roba daya mai sanyi da cup. Godiya tayi mata ta karba. Gara a rinka kawo mata don ita bata jin
zata iya jurar zama tare da mutanen da basa kaunarta su ci abinci.

Dama tuni ta soma jin yunwa. Tana budewa taliya ce da miya sai coleslaw a gefe. Kare masa kallo tayi
tana mamaki. Abin kuma harda rowar abinci? Abincin dan kukut a plate kamar zaa bawa Khalifa. Tas
ta cinye ta sha ruwa rabin robar. In ba haka tayi ba tasan bazata koshi ba.

Hamza tun bayan azahar suka fita da wani abokinsa. Gidansu Zuhra suka je yi musu ban gajiya. Su
Umma sunji dadi sosai. Har ta cire kunyarta ta tambayeshi ya Zuhra ta kwana. Murmushi yayi sannan
yace mata lafiya kalau. Tana gaishe su. Da zasu tafi Baba ya bawa Hamza wayar Zuhra. A jakar Hajara
ta manta ta daren jiya. Juya wayar ya rinka yi, banda tsufa ta dade da fita yayi.

Da daddare ma har daki aka biyota da abincin. Macaroni ce da vegetable soup. Sai dai Zuhra ta tsani
macaroni. Duk yunwar da take ji dole ta hakura. Gudun kada aga kwadayinta ma ko naman dake cikin
miyar bata ci ba ta dauki tray din ta sauka kasa dashi. Tana tafiya Hamza da Izzatu dake zaune a
dinning table na binta da ido. Bata ko tanka musu ba ta wuce ta ajiye abincin a kitchen. Ta fito kenan
Tala ta biyota da sauri. "Naga baki ci abincin ba"

Dan murmushi tayi "na koshi ne".

Tana wucewa idonta ya kai kan nasu abincin. Shinkafa suke ci, wato ita suka hada da macaroni.
Hamza na lura da irin kallon da take musu har ta wuce.

Wurin karfe goma da rabi Zuhra tana zaune tunani duk ya isheta gashi ta manta wayarta a gida. Ga
uwa uba yunwa. Turo kofar taji anyi tayi saurin tashi zaune ta saka hijab. Daga ita sai daurin kirji
saboda zafi ya dameta.

Kafin ta rufe jikinta ya kula da daurin kirjin. Ba karamin tsanar sa yayi ba. Bai tsaya jan zance da ita ba
yace..
" kina jindadin cin abincin ke kadai ko zaki rinka ci tare damu?"

Tasan har ransa ba so yake taci dasu din ba." Zanci ni kadai"

"Fine, sai ki rinka fada da wuri idan bazaki ci ba saboda a dena wasting. An kawo miki kin mayar
batare da kin taba ba".

Idan kika yi shiru zaki kwari kanki shine abinda zuciyarta ke raya mata. Ta dan rage murya "bana cin
macaroni ne"

"Macaroni kuma? Mtsw ke bana son karya."

Turo baki tayi "ni ba karya nake ba. Abinda aka kawo min kenan."

Dafa kansa yayi yadda yake idan yana cikin damuwa." Me yasa bakiyi magana ba. Anyway nasan
shinkafar bata kare ba idan kina so kije ki ci."

Tana kallo ya karaso cikin dakin ya kunna wani abu. Da yake tana setin AC din tuni ta fara jin iska.
Yana gani tayi murmushi. Sannan tace.
"Don Allah ina ka kunna? Jiya zafi ya isheni na zata da sankarau zan tashi da safe"

Ta kusa sashi dariya sai ya gimtse. Idan ya sakar mata fuska zata yi tunanin ta sami karbuwa ne.
Remote din AC din ya nuna mata sannan ya miko mata wayarta da chaja a cikin leda. Murna tayi sosai
tayi masa godiya.

Sai da ya kama hannun kofar ta sake magana tana sosa keya.
"uhmmm"

Ya tsaya yana kallonta
"yes" ganin taki magana.

"Dama, dama famfon bandakin ne naga kamar sun lalace."

"Kin lalata su dai" ya fada yana shiga ciki. Ya duba duka komai lafiya kalau. Ya fito "wai ni abokin
wasanki ne? Babu famfon da ya lalace"

Bata ce komai ba tayi saurin shiga. Hannu ta tara a famfon sink da baho duk ruwa ya fito da kansa. Sai
da ya tsorata ta duk da ta gani jiya. " ka gani ko, yau tun sallar asuba da shaya nake yin alwala."

Wannan karon murmushi yayi. Sannan yayi mata bayanin yadda kan famfon yake. Tun kafin ya fita ta
rinka bi tana tara hannu ruwa na zuba. Dariya take yi don abin ya burgeta. Yace to kada ki karar mana
da ruwan gidan. Kunya taji tayi saurin cire hannunta ta fito. Shi kuwa tuni ya fice ya tafi nasa dakin.
[25/09 3:52 pm] Inna��: AL'ADUN WASU 30

Batul Mamman(Mrs)




Zuhra anji dadin bacci saboda gajiyar da ta tara ta biki. Ba ita ta farka ba sai bayan tara. A firgice ta
tashi ganin hasken rana a dakinta. Ko sallar asuba batayi ba. Sai da ta shiga bandakin ta tuna da
matsalarsa ta jiya. Gashi ta makara sallah. Banda bahon wanka daga gefe wata yar matakala ce mai
karamin bene da yayi kasa akwai shower a wurin. Kunnawa tayi ruwa ya watso mata saboda yayi
karfi. Da kyar ta iya rage karfin ruwan. Cire kayanta tayi ta koma tayi wanka tare da alwala.
Tun kafin ta gama shiryawa cikinta ya soma kukan yunwa. Nan fa ake yinta. Zuhra bata jurar yunwa
gashi tunda aka kawota ko motsi bataji a kofar dakin ba. Haka ta gama duk abinda zata yi ta sami wuri
ta zauna. Tunanin iyayenta ne ya zo mata ta soma kuka.

Izzatu da Tala sun gama hada komai na breakfast suka jera akan dinning table. Sama ta hau ta kira
Hamza. Sanye yake da jallabiya light brown sai kamshi yake. Yayi kyau sosai sai dai fuskarsa da ta
zama maabociyar damuwa yan watannin nan. Yaransa duk suka yi masa kiss a goshi kamar yadda
suma iyayen suka saba yi musu. Sannan suka zauna Izzatu tayi serving dinsu. Lomar farko da zai kai
bakinsa ta tuna masa da Zuhra da ke daki tun jiya ko lekata baiyi ba. Tsaki tayi ya tura kujerarsa ya
tashi.
"Baby what is wrong?" Izzatu ta tambaye shi itama tana mikewa tsaye.

Sama ya kalla ya sake yin tsaki "zan kira yarinyar nan tazo taci abinci ne."

A take Izzatu ta hade rai. "Ka bari Tala ta mika mata mana. Ai ba sai kaje dakinta ba."

"Hakkinta ne na ciyar da ita" yana fadin haka ya hau saman.

Ya kusa minti biyu kafin ya murda kofar ya shiga. Akwai kamshi dai saboda dakin amarya ne sai dai
zafi sosai duk da tagar a bude take. Ko meyasa bata kunna AC ba oho.

A tsaye take tana jera kayanta a wardrobe har ta kusa gamawa taji an taba kofar. Cikinta sai da ya
bada sauti saboda tsoro. Ko da ya shigo duk rashin kunyar da taso yi masa sai ta fasa saboda yadda ya
cika mata ido. Bata taba kare masa kallo ba sai yau. Da ace zaman lafiya suke yi da ta fada masa
yadda yayi kyau. Shima ita yake kallo. Riga da skirt tasa na atampa fuskar nan tasha farar hoda. Kana
ganinta ita daban fuskar ma daban. Ga hannun breziya ya fito ta kowane gefen hannun rigarta. Ya dan
tabe baki....kai kuma irin taka jarabawar kenan Hamza.
"Ke baki iya gaisuwa bane?"

Saurin durkusawa tayi tare da jin kunya.
"Ina kwana, an tashi lafiya"?

Bai amsa ba ya juya"ki sauko muyi breakfast".

Kafin ya kai kofa ta biyo bayan shi. Yunwa take ji sosai. Ace yau har shadaya saura bata ci abinci ba. Ita
kanta tasan tayi abinda zaa jinjina mata.

A baya ta rinka binsa har suka sauko. Izzatu ta kai karshe wurin bacin rai, sai kawai ta danne. Kujera ta
samu kusa da yaran ta zauna tare da yin sallama. Khalifa ne kawai ya amsa. Ya kalli Mamansa.
"Mummy wannan ma mai aiki ce?"

Hamza ya ce masa yayi shiru kawai yaci abinci. Zuhra tana sane bata ji ya gyara masa yace ita ba mai
aiki bace ko da bai kirata matarsa ba.

Izzatu ko daga kai batayi ba bare ta bashi amsa. Itama Zuhra taki kallonta. Yadda take jin haushin
Izzatu ko kallo bata isheta ba. A dalilinta tazo gidan nan da bata da wata kima a idon mazauna cikinsa.
Muryar Hamza ce ta katse mata tunani.
"Wai ba kya gaishe da mutane ne?"

Ta dago fuska suka hada ido. "Na gaisheka a daki"

Da kansa yayi mata alamar bata gaishe da Izzatu ba. Amma lallai ya rainata da yawa. Su basu ce
'ya'yansu su gaisheta ba sai ita zata gaishe da matarsa. Kamar bazata yi ba sai kuma tace "ina kwana"

Maimakon ta amsa sai kawai ta tashi ta koma dakinta. Hamza ya bi bayanta. Yaran ma suka gama
suka tashi. Suna tafiya Zuhra ta janyo flask ta bubbude sannan ta debi abinda zata ci ta hada tea. Sai
da taci ta koshi sannan ta tashi daga dinning area din ta koma wurin yaran inda suke zaune suna
kallo. Tambayarsu sunayensu tayi suka bata amsa. Junior yace "ke kuma ya sunanki?".

Murmushi tayi "sunana Zuhra". Khalifa yace "nice name, will you be my friend?"

Ido ta dan zaro "tohhh kun iya turanci tun yanzu..." da haka suka rinka hira da ita tana jansu da wasa.
Hatta Nana mai kyuya ta yarda da Zuhra.

Hamza ya dauko laptop zai fara aiki sai kuma ya rufe. "Izzy kirawo yarinyar nan, I need to talk to both
of you"

Wani irin kallo tayi masa. " sweety nice zani dakin Zuhra? Allah Ya kiyaye. Kuma ai bai kamata ta shigo
mana bedroom ba. As far as am concerned ni ban dauketa matarka ba."

"Gashi kuma na biya sadaki" yadda yayi maganar tasan har yanzu yana ganin laifinta a matsayin
wadda ta jawo masa auren.

Tana fitowa ta jiyo muryar Junior yana cewa Zuhra ta yi masa tatsuniya. Daga saman ta leka ta kirawo
Khalifa. Shi ta fadawa ya rako Zuhra dakin daddysu yana jiranta.

Rike da hannun Khalifa suka shiga dakin. Wata irin niima taji. Ita nata dakin sai zafi. Falo ne a farko
sannan kofar dakin daga ciki. Wurin ya tsaru sosai ta tsaya tana kallo. Izzatu tace da Khalifa yaje
wurinsu Junior.

Babu wadda ta kula yar uwarta har Hamza ya fito. Kusa da Izzatu ya zauna. Ita Zuhra kasa ta zauna
kan kafet saboda gudun kada ace tayi laifi. Gyara zamansa yayi fuskarsa ta nuna alamun ba wasa.
Sannan ya soma magana

"Kamar yadda kuka sani dukkaninku matana ne duk da cewa circumstances behind auren kowacce is
different......

Zuhra anzo wurin...gabadaya jumlar karshe bata fahimta ba.

.....bana son tashin hankali a gidan nan. Izzy kece babba ina so kija girmanki. Ke kuma ya juya ga
Zuhra ki bata girmanta. Tun farko na gargadeki akan auren nan kika ki ji. So duk abinda kika gani sai
kiyi hakuri. Sannan a yanzu baki da kitchen don sai an gyara miki daki a kasa. For now idan Izzy tayi
girki zata baki. Saboda haka babu zancen rabon kwana sai an gama kitchen din." Ya kallesu duk su
biyu. "Ko akwai mai magana?"
Izzatu tana ta kumbure kumbure tace " ka fada mata ta fita harkar yarana".

Bai ce mata komai ba yace da Zuhra tana iya tafiya. Tunda ya soma magana bata

11 / 40