Author : Batul Mamman Category : Read Hausa Novels
gama bikin.
Dad dinta ne zai tafi Japan shine zata je yi masa sallama sai wata lahadin zata dawo. Ransa a bace
yace Izzy ba haka muka yi dake ba. I need you here, bama ni da lafiya. Izzy tace kayi hakuri baby
amma Dad zaiyi wata biyu kaga ya kamata naje muyi sallama. Idan yace bai amince bama yasan sai
taje ko tasa mamanta ta kira shi a waya. Abin mamakin ma tsakaninsa da Allah rashin dawowar tata
bai wani dameshi ba. Shi da baya iya nisa da ita...yace to su Khalifa kinsan zasuyi missing school da
yawa ko. Eh zasu taho da Tala ranar lahadin amma da Nana zan tafi Abujan. Bye baby, love you. Dip
ta ajiye wayar, rike tasa wayar yayi a hannu yana mamakin Izzatu. Ko sau daya bata yi masa sannu ba
duk da muryarsa data canja ko bai fada ba za'a gane bashi da lafiya. Har tunani yake yi wai dama haka
take masa ko yanzu ne dai saboda bikin da suke yi.
Zuhra na saukowa aka kawo wuta. Tsabar murna yasa tayi ihu har sai da Hamza yaji. Da sauri ya fito
yaga abinda ya sameta sai yaga tana ta juyi a falo tana kiran nepa, nepa.... baki ya rike yana kallon
ikon Allah, sai kace wata karamar yarinya sai tsalle take yi. Riga da skirt ta saka na yadi mai laushi.
Dinkin ya kamata tsam ta daura dankwalinta. Duk da ba wata kwalliya tayi sosai ba amma tayi masa
kyau. Gabadaya surar jikinta ta fito sai tuna masa daren jiya take. Sannu da aiki yar kauye ya fada
yana tsaye a bakin koma.
Da farko tsoro taji har zata gudu sai kuma ta tsaya ta fara neman wuyan hijab dinta ta saka. Jira yayi
ta saka din sannan ya karasa gabanta ya kama kasan hijabin. Hannunta tasa tana neman kwacewa ya
janyota gabadaya jikinsa. A take ta fara rawar jiki tana cewa kayi hakuri na dena tsallen. Sosai ya
rungumeta yana kallon fuskarta ya cire mata hijab din cikin nutsuwa sannan ya saketa. Kirjinta ta fara
kokarin rufewa yace ke jiki ba jiki ba kiyi ta wani rufewa. Haushi taji ta dan tura baki sai ta fara juyi a
gabansa tace a hakan? Wallahi ina da jiki, kaga fa...dariyar da yake mata yana cewa juya na gani da
kyau yan mata yasa ta bar abinda take yi ta soma kokarin kwatar hijab dinta. Hannunsa ya daga sama
tace to na bar maka bari na dauko wani. Baifi taku biyu tayi ba ya jawota jikinsa. Hannuwansa na
gaban kirjinta ya dan rage tsaho daidai da kunnenta...ki hakura da hijab din kinga akwai zafi. Kuma
naga ashe kina da jikin da zan kalla. Yana magana taji yasa hannunsa a kafadarta yana mayar mata da
hannuwan breziyarta da suka fito. Daga daren jiya zuwa yau Hamza yasa Zuhra tsananin jin kunya.
Yadda ya rufe mata jiki gabadaya ta baya yasa ta kasa motsi. Zuciyarta ce kawai take bugawa da sauri.
Tana wannan yanayin har ya saketa bata sani ba. Ganinsa kawai tayi a gabanta yana murmushin da
yanzu take yawan gani tare dashi. Hada ido suka yi ta kawar da kanta, a hankali tace duk kasa ni jin
kunya. Sai ka rinka wayon taba min jiki. Kuma dai kasan babu kyau. Ya daga gira kina matar tawa. Tace
to ba sakina zaka yi ba. Tana fada ta wuce kitchen ta barshi a tsaye. Maganar Zuhra tasa ya shiga
damuwa sosai.
Dambun shinkafa ta hada mai rai da lafiya. Ta rinka yawo tsakanin falo da kitchen har abincin ya
dahu. Daya da yan mintuna ta gama ta mikawa maigadi. Shi kam yana jindadin sauyin da ake samu na
girki a gidan nan. Gashi harda ruwan sanyi tunda an kawo wuta. Na Hamza ma ta hada masa komai a
tray ta shiga falonsa ta ajiye sai dai baya ciki. Yunwa take ji sosai domin yau tayi dauriya. Nata tayi
niyar zuwa ta diba a kitchen sai taga wata kofa ta bude ashe da toilet a wurin. Tashi tayi zata gudu
yace dawo ki zauna fita zanyi, da alama alwala yayi. Zan canja kaya naje office zaman gidan ya isheni.
Ba komai ke damunsa ba sai maganar Zuhra ta saki. Ya rasa gane yana son zancen sakin nan yanzu ko
kuwa. Da 'yar damuwa a fuskarta tace amma baka da lafiya, ka hakura mana. Yana jindadin yadda
take kulawa dashi yace bazan dade ba in sha Allah. A gaban tray din ya tsuguna Me kika dafa mana
ne...yar kazama ta iya girki. Tray din ta dauka tunda ni kazama ce ka nemi wani a waje. Yi hakuri ki
kawo kinji, ai kinfi kowa tsafta a gidan nan. Bubbude flask din yayi yaga dambun shinkafa tayi da
farfesun kaza. A take yawunsa ya tsinke. Wai me yake damunka ne Hamza da kaga abincin sai ka rude
kamar wani mayunwaci. Kinsan abincin da Hajiya tafi so kenan dambu ko wane iri ne. Zuhra tace da
gaske? tare da dauke flask din da ta zuba masa nasa. Bari naje na juye sauran ina ga zai kai cin
mutum uku idan aka hada. Tana magana tana neman fita daga falon. Hamza yace ke dawo bangane
me kike nufi ba? Ya daga kawo min abinci ko tasting banyi ba kin dauke. Buga kafa tayi irin ya ma zai
ki ganewa...yanzu fa kace min Hajiya na son dambu. Zan hada da sauran sai ka kai mata. Bari nayi
sauri ko taliya na dafa mana tunda kaima fita zaka yi.
Tashi yayi da sauri ya kamo wuyan rigarta ta baya ya dawo da ita...haba yar kauye daga magana sai ki
dauke abincin. Ya dan yi mata kalar tausayi, nima ina son ci don Allah ki ajiye. Zuhra ta dan harare shi
to Hajiyan fa? Flask din ya soma ja itama tana ja. Da taga yafi karfinta sai tace to bari na zuba maka
kadan sai ka kai mata sauran. Kaga duk duniya ga namiji bashi da abinda yakai mahaifiyarsa daraja.
Kafin na tafi in sha Allah idan kana so kullum duk abinda take ci ka fada min sai na dafa mata.
Ummana tace idan nayi aure na taya mijina neman aljanna ta hanyar kyautatawa iyayensa da sauran
ayyukan kirki. Kaga yanzu kafin ka sake ni ko dan yaya sai nayi abinda tace ko? Sai kuma ta rufe baki
da hannu daya...ka ganni ko? Umma cewa tayi ba fada maka zanyi ba sai dai ka gani a aikace. Don
Allah kada kace na fada. A shagwabe take masa maganar wadda tayi matukar tasiri a ransa. Har wani
dan dukan bakinta take yi ita a dole tayi laifi. Allah kadai Yasan farincikin da Hamza yaji a wannan
lokacin. Yau shine da matar da take nuna damuwa akan mahaifiyarsa fiye dashi. A wannan lokacin
gani yake Zuhra tafi masa kowace mace. Bai yarda sonta yake ba amma a shirye yake ya kyautata
mata iya karfinsa...a hankali take samun masauki mai daraja a zuciyarsa. Ido ya zuba mata kawai yana
kallonta. Ita kuwa kuwa tana kare maganarta tayi gaba da flask din ba tare da ya tareta ba.
A dan plate ta zuba daidai yadda zaici ta hada sauran wuri daya. Takaici ma take bata sani da wuri ba
ai da tayu mai yawa. Naman da ta soya ta diba ta zuba a kai saboda farfesun tayi shi da yaji tunda
Hamza na mura.
Tunda Zuhra ta fita yake ta kai kawo....ya tsani ta tayar da maganar sakin. Shigowarta tasa ya sami
wuri ya zauna ta mika masa plate din. Jan hannunta yayi ya zaunar da ita a gabansa. Nasan kin fini jin
yunwa ki ci ni ga nawa abincin ya nuna mata farfesun....cikinta har wani kullewa yake ta yi murmushi
da gaske ka bar min. Hamza yace eh...plate din ta janyo gabanta ta soma ci da sauri. Ya kama
hannunta lesson two yar kauye, ki dena cin abinci da sauri kuma banda katuwar loma. Ta danji kunya
sai tace to yaya zanyi? Dan madaidaici ya diba a spoon din ya nuna mata. Tace dama Babana yace
kada nayi loma a gabanka...Allah Yasa na iya denawa dai. Amma meye kake cewa lesson one da two?
Kallonta yake ya rasa me yake ji game da ita so nake ki zama yar gayu kafin lokacin rabuwarmu, yadda
zan dena kiranki yar kauye. Washe baki tayi da gaske don Allah? To ai da ka fada min da wuri yadda
zan kiyaye duk abinda ka gyara min. Rabin abincin taci ta ture plate din ni na koshi. Hamza yace don
nace ki rage loma? Yamutsa fuska tayi a'a cikina ne ya kulle tea zan sake sha. Sannu yayi mata sannan
yaja plate din ya ci sauran tare da shan farfesun. Kamar kullum yau ma abincin Zuhra yayi dadi. A
zuciyarta kuwa dadi taji ta bashi dambun saboda tana ganin irin kallon da yake yiwa abincin tunda ta
soma ci.
Yana gamawa ta hada masa wanda zai kaiwa Hajiya a wata yar jaka ta bashi. Yace to daga can zai biya
office. Har ya isa gidansu ko na sakan daya bai dena tunanin Zuhran Baban yara ba.
AL'ADUN WASU í ½í·¿49
Batul Mamman(Mrs)í ½í²–
Da yake weekend ne a falo ya tarar da mutan gidan suna kallon wani shiri da akeyi a Sunna TV.
Kannensa suka gaishe shi ys amsa da sakin fuska. Sannan ya gaishe da iyayensa. Mama tace Yaya yau
ina office din? Zama ya fara yi sannan yace mura ke damuna amma tayi sauki. Yanzu ma can zan
wuce, aiko ni aka yi wurin Hajiya. Hajiya tace ni kuma? Jakar hannunsa ya tura mata gabanta gashi inji
Zuhra. Hajiya dai kunyar bude jakar tayi Mama tace kaga Yaya miko min nagani.
Kowa a falon zuba ido yayi yaga abinda ke jakar sai ga Mama ta fito da food flask mai kyau. Tana
budewa dambun shinkafa ne ke kamshi mai dadi. Muryarta a shake kamar tayi kuka tace Adabiyya,
Nura, Hamida ku shiga ciki. Ba musu suka tashi suka barsu su uku a falon. Mama ta turawa Hajiya
flask. Kinga abinda ke ciki kice wani abu. Murmushi Hajiya tayi nagani Mama amma me zance? Ga
mamakinsa duka su biyun hawaye sukeyi. Hankalin Hamza yayi matukar tashi ya fara basu hakuri.
Mama tace Yaya ko kasan tunda kayi aure abincin gidanka bai taba shigowa gidan nan ba sai yau.
Kasan gidan iyayenka babu yunwa amma a tamu al'adar lokaci zuwa lokaci mace takan yi girki na
marmari ko da da sallah ne ta aika gidan surukanta. Irin haka yana sa iyayen miji su so matar
musamman idan tana da tarbiyya. Shima mijin indai yasan kimar iyayensa dole matar ta sake samun
wuri a zuciyarsa. Hannuwansa ta kama gam ta rike...Yaya yanzu kayi aure, nasan zaka ga kamar muna
kin Izzatu amma ko kai shaida ne akan bambancinsu da Zuhra. Kwalla ce ta cika masa ido shima ya
basu labarin yadda akayi ya kawo dambun. Hajiya dai kasa rike kukanta tayi ta tashi ta bar falon. Ashe
tana da rabon ganin Hamza ya auri macen da zata saka shi a hanya..Allah Yayi mata albarka. Ko ba'a
fada ba tasan shima ba karamin dadi yaji ba.
Tana tafiya Mama ta share hawayenta. Yaya ka rike Zuhra amana Alhaji bai maka zaben tumun dare
ba. Idan ka cutar da 'yar mutane saboda dalilin da ya jawo aurenku Allah zai kamaka da hakkinta.
Tana gama magana tace jirani ina zuwa. Kafin ta dawo Hamida tazo tace Yaya gobe bayan laasar zamu
zo ni da Adabiyya muyi weekend. Yace to Allah Ya kaimu.....shikenan zasu zo su takura masa idan
yana tare da Zuhra. Shima weekend din yake jira yini biyu a gida ba fita.
Mama dakinta ta tafi ta dauko dubu sababbin dari dari ta bawa Hamza ya kaiwa Zuhra tukwici. Tunda
yake bai taba tunanin irin haka na faranta zuciyar iyaye ba sai yau. A hankali yace God bless the day I
met you Fatima. Allah Yayi miki albarka. Ko flask din bai jira ba ya fita ya tafi office. Duk aikin baya
masa dadi so yake yaji muryar Zuhra tana masa shirmenta ko shagwaba. Har mamakin kansa yake, ga
babban abin kunya bashi da numbar wayarta ma. A lokacin ya tuna wayar tata tana da matsala,
bayan sun gama cinikin filayensa da wani dillali ya tashi. Beirut road ya wuce ya siyo wata sabuwar
waya kirar Samsung mai kyau. Nasa tukwicin kenan na abinda Zuhra tayi masa yau. Daga nan ya biya
wani shago yayi yar siyayya ya tafi gidansa.
Yana ajiye mota ko gida bai shiga ba ya fita masallaci saboda a hanya yaji kira. Can ya zauna har aka yi
sallar Isha sannan ya dawo ya shigo da kayan da ya siyo. Duhun da ya gani ya tuna masa bai nemi
wani maigyaran injin ba gashi har dare yayi. Zuhra ce ta fado masa ita da ko wayar kirki bata da ita.
Nemanta ya shiga yi daki daki baiji motsinta ba. Abin ya bashi mamaki ko bacci take yi ne? Yana hawa
sama tana fitowa daga dakinsa da fitila a hannu daya, daya hannun kuma tsintsiya ce da abin kwasar
shara. Har ajiyar zuciya yayi, ita ta fara magana tace sannu da zuwa. Murmushi yake yauwa yar kauye.
Me kike yi da tsintsiya a duhun nan? Tsoro na rinka ji ni kadai sai kawai na fara shara da wankin
bandaki. Amma dai ban bata maka rai ba da na shiga dakinka ko? Naga yanzu kana min kirki shine
nace bari nima na gyara maka daki. Bai amsa mata ba sai da yazo gabanta...baki yi laifi ba yar kauye,
nagode. Ki je kasa akwai kaya a falo ki kai kitchen dinki bari nayi wanka.
Bai shiga dakin ba sai da ta saukq kasa. Dadi yaji sosai har da turaren wuta ta saka. Ta gyara gadon
tayi shara. Toilet din ma ta wanke shi tas har boxers dinsa da vests da suke cikin wani abin zuba kayan
wanki duk ta wanke amma bata shanya ba saboda wurin shanyar yayi mata tsaho. Sau uku take niyar
wankewa sai ta fasa wai kada yace bata da kunya. Sai daga baya ne ta daure zuciyarta ta wanke su
harda kawar da fitilar gefe ita bata kalla ba bare ace mata 'yar iska.....
Ba jimawa ya sauko yace mata tayi girkin dare ne tace a'a amma zata dora yanzu. ki dafa mana
indomie kawai akwai a cikin kayan da nazo dasu. Cikin 'yan mintuna ta gama ta kawo. A plates daban
ta zuba musu. Maigadi kuwa dama ana magariba ta dafa masa taliya. Hamza na kallonta har ta zauna
zata fara ci ya dauko nasa plate din ya dawo gabanta, tasa ya juye a cikin natan sannan ya soma ci
batare da yace mata komai ba. Ido ta zuba masa ta kasa ci saboda tana gudun tsokanarsa. Ya dago kai
suka hada ido....lesson three, yana da kyau mata da miji suci abinci tare. Yana kara musu shakuwa da
son juna. Kyakkyawan murmushi tayi...Allah, to amma ba da kai ya kamata naci ba kada mu shaku
gashi zamu rab....hannunsa yasa ya rufe mata baki ta daga ido tana kallonsa. Ki dena zancen
rabuwarmu akwai sauran lokaci. Just eat. Babu abinda yaki jini yanzu kamar tayi zancen rabuwarsu,
idan lokacin yayi sai asan abinyi amma for now so yake yayi enjoying moments dinsu tare.
Sai da Zuhra ta gyara kitchen sannan tace masa sai da safe Allah Ya kara sauki. Lokacin aiki yake da
laptop a gabansa. Suma yan nepa kamar sunsan injinsu ya lalace suke kim basu wuta sosai.
Wanka ta dauki lokaci tayi don so take duk abinda ya koya mata ta rinka yi. Zafin yau da sauki akan na
jiya shiyasa ta dan shafa mai kadan sannan ta shiga barnar bodyspray. Har humrarta da bata taba
shafawa ba ta dauko kwalba daya mai kamshi ta rinka bin duk gabobinta tana shafawa. Rigar baccin
da ta dauko yar karama mai siririn hannu har tafi ta jiya kankanta da rashin kauri. Wani dadi take ji
ashe haka tsafta ke da dadi...gadonta ta haye ta ajiye fitilar a bedside drawer tayi kwanciyarta. Zafi
baisa ta rufa ba amma ba bacci ma take ji ba. Tunani take ko me Hamza yake yi yanzu.......
Kusan rabin awa kenan da yayi wanka ya gama shirin kwanciya sai dai ko alama babu bacci a
idanunsa. Zuhra yake son gani amma yana kokarin hana zuciyarsa sabawa da son kasancewa tare da
ita. Sakon kudin da Mama ta bashi ya tuna yana wallet dinsa ga wayar da ya siyo mata duk bai bata
ba. Murmushi yayi ya tashi don ya sami dalilin zuwa dakinta.
AL'ADUN WASU í ½í·¿50
Batul Mamman(Mrs)í ½í²–
Zuhra na kwance tana 'yan tunane tunane taji ana bude kofar dakinta. Tasan babu kowa a gidan sai
Hamza shiyasa tayi saurin kashe fitilar gefen gadon. Ba komai ne a ranta ba sai yar rigar jikinta. Wayar
Hamza ce ta hasketa da sauri ta fara jan bargo ta rufe jikinta. Shima saurin yayi da ya lura da abinda
take yi...me kike saurin boyewa ne haka 'yar kauye? Babu komai ta bashi amsa. Dan kashe wayar
kada chajinka ya kare kaga babu wuta. Kashewar yayi amma ya zauna a kan gadon gefen bangarenta
na dama. Kamshin turarensa maidadi ne yake tashi a wurin.
Shiru baiyi magana ba Zuhra tace ko akwai abinda kake bukata ne? Sake gyara zama yayi sannan yace
yanzu ke haka ake jinya? Kinfi kowa sanin bani da lafiya yau amma saboda kirki yayi miki yawa kika
barni na kwana ni kadai. Yanzu idan wani abu ya same ni cikin dare fa. Zuhra ta dan muskuta gefe
saboda ya danyi kusa da ita. Kayi hakuri amma ai mata da mijin gaske ne suke kwana daki daya.
Hamza yace ni kuma gani kwarto ko??? Zuhra ta kwashe da dariya harda hawaye da kyar ta iya tsayar
da dariyar tace kasan mun taba zuwa biki Ajingi a gidan da 'yan