Author : Batul Mamman Category : Read Hausa Novels
daga kai ba. Yayi
tsammanin zata nuna bacin rai amma sai yaga tayi shiru. Kanta a kasa ta fita daga dakin ta koma nata.
Tana rufe kofar ta suma kuka duk yadda taso daurewa ta kasa....ba son Hamza take ba amma babu
macen da zata so a nuna mata ita ba komai bace a gaban kishiya.
[25/09 3:52 pm] Inna: AL'ADUN WASU í ½í·¿32
Batul Mamman(Mrs)í ½í²–
Haka rayuwa ta kasancewa Zuhra a gidan Hamza. Kullum safe, rana da dare duk zaa kawo mata
abincin marowata kamar yadda take kiransa. A kullum zata yi waya da iyayenta. Idan bata kira ba zasu
kira ta. Idan aka tambayeta Hamza tace yana nan kalau. Bata taba tunanin fadin komai ba domin Anti
Faiza tace zaman gidan miji yana bukatar sirri. Ko Hajara ta hanata ta sanarwa komai na dangane da
gidan aurenta. Hamza dai yasan ana bata abinci saboda haka bai taba damuwa da sanin yawansa ba.
Idan ta fito sauka da kwanunkan abinci suka hadu da Izzatu zata gaisheta a ciki ciki. Itama da kyar
take amsawa. Don Hamza yayi mata fadan baya son gaba ne da ko kallon Zuhra bazata yi ba. Shi kuwa
matsalar kamfaninsa tasa shi a gaba, bashi da lokacin gidansa sosai.
Ranar alhamis da safe Tala ta kawo mata abinci kamar kullum. Tea ne a dan karamin cup irin mai
saucer dinnan wanda kurba biyar zuwa shida zai kare. A plate din kuma sliced bread ne guda uku.
Wani irin kallo Zuhra ta yiwa abincin. Ta dauki bread daya taji shi a bushe da tauri. Murmushin yake
tayi... Tala yau kuma bushasshen brodi kike kawo min. Tala ta dawo ta dan durkusa gabanta amarya ai
wannan tos ne. Tala zata yi sa'ar Izzatu ko ta girmeta da kadan. To...to me? Zuhra ta fada tana
yamutsa fuska. Tala tace tos. A tosta ake sakawa sai kiga ya fito ta sama kamar an jeho shi. Har dan
bota na shafa miki don kiji dadinsa. Zuhra ta gyada kai, naga alama. To nagode.
Bayan fitar Tala tayi ta juya bread din a hannunta. Tunda tazo gidan breakfast dinta na farko ne kawai
ta taba koshi. Kullum sai dai rage hanya, gashi bata taba ganin alamar za'a fara aikin nata kitchen din
ba. Ba yadda ta iya a dole ta fara cin bread din. Kana ganin fuskarta kamar mai shan madaci. Ko rabi
bata ci ba ta shanye tea din. Ta sake kai bread din bakinta Hamza yayi sallama ya shigo batare da ya
jira ta amsa ba. Zaune take da tray a gabanta kanta babu dankwali. Doguwar riga ce a jikinta ta wani
material. Dinkin dai yayi kyau sai dai wadda tasa kayan ce sai a hankali. Sunkuyar da kanta tayi kasa
tace ina kwana?
Bai amsa ba yana daura agogo a hanunsa ya dubi plate din gabanta. Ashe ma zaki iya ci. Dama naga
toasted bread aka yi nayi tunanin baki saba ci ba a baki wani abincin. Zuhra tayi sauri ta tofar da na
bakinta akan tray din. Wallahi bana iya ci, hakan ma dauriya ce kawai.
Hamza ji yayi kamar ya amayar da abinda yaci. Wannan wace irin kazanta ce ta gama jika bread a
bakinta ta dawo dashi. Fuskarsa na kallon gefe yace naga saura biyu da rabi ki cinye. Tashi tsaye tayi
tana karkade hannuwanta...wallahi dama uku ne. Dan murmushi yayi...haka Izzatu take bata son ayi
abinci da yawa, a cewarta zasu yi kiba suyi loosing shape. Farkon aurensu har rama ya rinka yi. Daga
baya sai yake siyan biskit da cake a ajiye a office. Kyalesu zaiyi, kila idan Zuhra ta dan horo zata nemi
komawa gidan iyayenta. Sai ya saketa cikin sauki. Ba tare da ya kalleta ba yace zansa a kawo miki wani
abincin. Da ya juya zai tafi yaji tace adawo lafiya, Allah Ya kiyaye, Ya bada sa'a, Ya tsare kuma Ya kare
dukkan sharri. Adduar tayi masa dadi yace Amin a hankali. Wannan adduar kullum Umma sai tayiwa
Baba idan zai fita wurin sana'arsa.
Tunda ya fita bata ga alamun abinci ba sai uku saura aka kawo na rana. Cikin kankanin lokaci ta tayar
da abincin. Ta fito daga toilet kenan Tala ta shigo tace amarya kinyi baki. Shikenan anzo
wurin.....kullum addua take yi kada tayi baki saboda bata san me zata basu ba, yau gashi wasu sun zo.
Tunani ta soma yi lokaci guda idea ta zo mata. Kanta ta rike da hannu biyu ta rufe ido. Tala kaina ciwo
yake min sosai kamar zai tsage. Tala tayi saurin karasawa ta riketa har bakin gadonta. Sannu amarya
ko na karbo miki magani wurin Anti Izzatu? A'a Zuhra tayi saurin dakatar da ita. Nima ina da shi. Kice
su hawo nan bazan iya saukowa ba. Tala duk tausayin Zuhra ya kamata tace ba komai amarya. Kafin
ta fita Zuhra tace ki dan taimaka musu da ruwan sha don Allah.
Tana fita Zuhra ta gyara kwanciya. Bata san ko su waye ba amma dai tasan gidan amare ana son a
bawa baki dan abin kusa da baka. Ita kuma bata da komai, idan za'a bata ma karba zata yi.
Ba jimawa yan uwansu na Ajingi suka shigo. Kirikiri Zuhra taki tashi tana ta langabewa ita mara lafiya.
Da muguwar rawa gwamma kin tashi. Anti Faiza ce ta rako su. Suna ta mata tsiya ko har an fara
laulayi ne na kwana biyar. Ita dai sai murmushi take yi a dole taji kunya. Tala ta kawo musu ruwa
harda lemo a jug da kofona. Basu dade ba suka ce gobe zasu koma Ajingi. Tayi musu godiya ta rakasu
har kofar daki. Sai da suka sauka kasa Anti Faiza ta dawo da sauri take tambayarta yaya zaman nata.
Kuka Zuhra tasa mata ta sanar da ita ko abincin kirki ba'a bata. Anti Faiza tace kiyi hakuri gobe za'a
kawo gararki. Akwai kudi ne a wurinki? Zuhra ta share hawayenta tace eh Baba ya bani. Duka ta debo
ta bata Anti Faiza ta dauki dubu goma a ciki ta bata sauran. Zanje kasuwa gobe kafin azo kawo garar
zan zo in sha Allah. Ta dafa kafadarta...ki kara hakuri kuma kada ki bari Izzatu ta san ba kya jindadin
zaman. Daga ita har mijin nata so suke kiyi abinda zai sakeki. Kuma In sha Allah kinzo kenan, yadda
iyayensa suka yi miki kokari kema ki dage nemawar kanki wurin zama a zuciyarsa. Zuhra ta tura baki
ni me zanyi dashi Anti? Ai kawai idan ya gaji ya sakeni. Anti Faiza toshe mata baki tayi. To banza na
sake jin zancen saki sai na fasa miki baki. Biskit ta dauko guda biyu a jakarta ta bawa Zuhra sannan ta
sauka kasa suka tafi.
Fitarsu ke da wuya Izzatu ta shigo tare da Tala. Zuhra tana kwance akan kujera ta gansu. Tashi tayi
zaune tace lafiya cike da tsiwa. Fuskar Izzatu a daure tace ke kika ce Tala ta bawa bakinki ruwa da
juice a jug dina? Zuhra ta kalli Tala tayi tsuru tsuru. Kiyi hakuri na zata mijinmu ne ya saya shiyasa
nace ta taimaka ta kawo. Izzatu ta soma fada rai a bace...mijinmu fa kika ce? Yanzu Zuhra don baki da
kunya sai ki hada baki da inlaws dina ki auri mijina kawai don kinga ina sakar miki fuska. To Tala mai
aikina ce ni kadai kuma kada ki sake taba min kaya. Ignorant fool yadda kika zo haka zaki fita ki bar
min gida. Zuhra tayi yar dariya ko na kwana daya ne Izzatu kin taba zama da kishiya a tarihin
rayuwarki. Izzatu ta tsaya tana kallon Zuhra..dama bata da kunya? Kwafa tayi sannan ta fita tare da
buga kofar da karfi. Tala ta dauki tray din Zuhra na bata hakuri tace babu komai. Ita sai mamakin
wannan aure na ubangidanta take da yadda suke wulakanta amaryar. Zuhra tayi murmushi ko ba
komai yau ta dan gasawa Izzatu magana taji dadi.
Daren ranar ba'ayi girki ba ana jiran Hamza ya kawo abinci daga tantalizers. Da yake bai fito office da
wuri ba abincinsu ya kare sai snacks ya siyo. Yana wanka Izzatu ta rabawa kowa banda Zuhra. Shima
burger yaci ya kwanta a zatonsa an aikawa Zuhra nata. Tala tana son tambayar na amarya tana tsoro
don ba karamin fada Izzatu tayi mata ba.
Har shadaya da rabi babu abinci babu dalilinsa. Dole Zuhra ta karasa sauran biskit din da Anti Faiza ta
bata ta shiga toilet ta sha ruwa sannan ta kwanta ciki na kukan yunwa.
[25/09 3:52 pm] Inna: AL'ADUN WASU í ½í·¿34
Batul Mamman(Mrs)í ½í²–
Kafin Hamza ya dawo daga raka su Mama mota tayi saurin shigowa ta hayewarta sama tana murza
hannunta wanda ya matse mata harda hawayenta. Tala tana kwashe trays din da aka yi amfani dasu
Izzatu ta tsaya mata a ka. Nace Tala ko kin gaji da aikin ne? Ido ta zaro a'a Hajiya wani abin ne ya faru?
harara Izzatu ta jefa mata. Jiya banyi miki magana akan yiwa bakin yarinyar nan amfani da kayana
bane? Tala tace Allah Sarki ai naga harda maman Alhaji shiyasa na dauko musu. Kiyi hakuri. Izzatu
tace ba mamansa bace kishiyarta ce. Kuma na karshe kenan da zaki taba min kaya da sunan karrama
bakinta. Wallahi ranar zaki koma kauyenku. Daga nan ta juya ta koma kan kujera ta zauna tana huci.
Yadda Mama da su Mariya suka ki amsa gaisuwarta ke damunta. Kwafa tayi inma suna rawar kafa ne
sun koma bayan amarya zata bar gidan ne da wuri. Su basu san wasa bane ko abubuwan nishadi da
har zasu ji haushin abinda tayiwa Zuhra asa mijinta aurenta. Tana ta karkada kafa tana mita a ranta
Hamza ya shigo yayi hanyar sama. Da bibbiyu yake tsallake steps din. Murmushin mugunta tayi Allah
Yasa daga nan ya saketa kowa ya huta.
Zuhra na tsaye gefen kujera tana hawayen yadda hannunta ke zafi tace kuma Allah Ya isa na....dawa
kike taji Hamza ya fada yana shigowa dakin. Duk da ta tsorata cike da tsiwa fuska duk hawaye da
majina harda murguda baki tace da wanda ya tsargu. Baki Hamza ya saki lallai yarinyar nan bata da
kunya. Shi saboda yadda yaki jinin raini shiyasa baya shiga sabgar autarsu Hamida. Itama tsiwa ce da
ita....
Ke, dani kike? Share shi tayi ta cigaba da matsa hannu. Tsawa ya daka mata ke ba kya jina ne. Nace ni
kike yiwa Allah Ya isa? Waige ta soma yi hagu da dama ita a dole bata san da wa yake ba. Ransa ya
kara baci yayi kanta. Da gudu ta kara shigewa cikin dakin sai da ta kai jikin bango. Kafa yasa ya buga
kofar da karfi daidai da bugawar zuciyarta. Sai rarraba idanu take. Wani irin kallo yake mata kafin ya
sake cewa wai kina ji ina tambayarki kin kasa bani amsa saboda ki nuna min ban isa ba. Tsoro kam ta
gama ji amma ta rantse bazata yi shiru ba tace au dama dani kake? Maganar ta sake sosa masa rai ya
biyota har inda take tsaye jikinta ya soma rawa. Tana cigaba da hawaye tace to ai ke naji kace ni kuma
da aka haifeni Baba saniya da rago ya yanka ya rada min suna Fatima. Dayake sunan Innarsa ne da
kuma Ummana shine ake kirana Zuhra. Ta turo baki sai ka zabi daya a ciki ka dena ce min ke kamar
wata...yan lips din nata ya kama da yatsunsa biyu. Taji zafi ta fara kokarin cire hannun nasa. Idan kika
ki tsayawa tsinkesu zanyi sai naga na tsiwar . Idanunta duk sun firfito sai hawaye sharrr.
Sai lokacin ya kare mata kallo. Ba wani tsahon kirki gareta kuma tana da jiki madaidaici. Kalar fatarta
bata da haske sosai amma kuma ba baka zaa kirata ba. Akwaita da idanuwa masu kyau ga hancinta da
baki duk yan madaidaita. Banda rashin iya kwalliya da itama zata shiga jerin matan da basu da muni.
Hijabin jikinta ya kalla duk yasha hawaye da majina. Sai lokacin yaji kyankyami ya sakar mata lebe. Ta
karkace baki ta sake cewa Allah zai saka min. Kan gadon ta haye zata zagaye shi ta gudu. Yasa hannu
ya fizgota ta saki kara. Da karfi ya manna ta da bango ta runtse idanunta tana jira ya sake kama leben.
Dalli taji masu zafi guda uku ta sake cewa Allah Ya....wani ya kara mata da yafi sauran zafi. Nan da nan
ta soma kuka mai sauti. Irin kukan da idan ta fara a gida har makota sai sun leko an bata hakuri take
denawa.
Hamza huci kawai yake don bacin rai. Me zaisa Alhaji ya hadashi aure da wannan mara kunyar
yarinyar. Gashi ta kafeshi da idanu kamar wani sa'anta. Yi min shiru ya fada da karfi. Tsaf ta hadiye
kukanta. Ina so kisan cewa ba'a min rashin kunya. Sannan kika kara cewa Allah Ya isa sai na dirje miki
baki. Kina jina? A hankali ta gyada kanta domin taji zafi a bakin da ya dalle. Good ya fada, me yasa
baki fada min za'a kawo gara ba? Kuma a ina kika sami abinda zaki bawa bakin? A hankali tace Anti
Faiza ce ta kawo. Ga gidan yunwa ko, shine abinda za'a bawa baki ma sai kin roka don ki jawo min
magana ace bana kula dake. Hannu tasa ta rufe bakinta sannan tace nima bansan zasu zo ba sai jiya.
Kuma ban ganka ba bare na fada maka. Ni duk abinda kuke yi min banji haushi ba sai....sai me ya
tambaya da yaga ta kasa karasa maganar. Ba komai ta sunkuyar da kai. Zare mata ido yayi bazaki fada
ba sai na kara dalle bakin. To ba kaine jiya kace zaka aiko min da abinci ba amma naji shiru. Da
daddare ma kuka barni na kwana da yunwa. Wani iri yaji a jikinsa...kika kwana da yunwa??? Nufinki
ba'a kawo miki abinci ba. Zaka ce baka sani bane.....auuuu, tayi saurin rufe kanta da hijab kada ya
sake mata wani abin. Ga mamakinta shiru taji tana dago kai har ya bude kofa sai ya juyo. Da sauri ta
sake rufe bakinta. Key din kitchen din ya jefo mata gashi nan zansa a hada miki gas cooker. Bai kula ba
yayi tafiyarsa. Key kuwa a goshinta ya sameta ta soma tsalle tana ihu. Allah Ya isa ta fada a hankali.
Kasa ya sauka ya sami Izzatu tana kallo. Tana ganinsa ta taso Baby....hannuwanta ya ture da take
shirin taba shi. A wane dalili ne jiya baki bawa yarinyar nan abinci ba? Wani irin kallo ta masa Why do
you care? Saboda matata ce hakkinta ne na ciyar da ita. Matarka fa kace Hamza? Har Zuhra takai
matsayin da zata hada kai dani. Wallahi sai ka saketa a yau....wayarsa ce ta soma ringing. Yana
dubawa yaga manajan bankin da ya tura Inuwa ne ya karbo kudi a cigaba da aikin ginin da suke yi.
Izzatu sai fada take yana daga mata hannu tayi shiru taki.
Mr Oscar ya gama tsorata tunda manajan yace bari ya kira Alh Hamza ya tabbatar ko shi ya aiko shi.
Ya gama hango kansa a matsayin korarre daga aiki kila ma a rufe shi. Bayan sun gaisa manaja yace
Alhaji dama na kira ne domin confirming ko kai kayi authorizing cheque na 10 million. Gefe Hamza ya
dan matsa amma Izzatu har nan ta biyo ita wallahi ko ita ko Zuhra. Daidai sanda manaja yace ka turo
Mr Oscar Hamza baiji ba amma tunda yasan ya turo Inuwa sakatare sai yace eh ya ajiye wayar. Ya juyo
ransa ya gama baci Izzatu ki shiga hankalinki dani wallahi. For God's sake ya kike so nayi da rayuwata
ne. Daga ke har yarinyar da kika yi sanadiyar zuwanta gidan nan bakwa gabana. Duk kin birkita min
lissafi lokaci guda. Da kamfanin zanji ko masifarki? Come on get out of my way ya tureta ya fice don
ya kusa makara masallaci.
Mamaki ya kama Mr Oscar lokacin da manaja ya bada order a bashi kudin. A tsorace ya karba jiki na
rawa yana ta tunanin kada ace ya dawo dasu. A daidai bakin gate suka hadu da Inuwa sakatare. Cikin
Mr Oscar ya murda sosai ji yake kamar ya saki zawo don firgici. Inuwa yace Oscar kaima ashe kana
banking a nan. Nima sauri nake kada su tashi kasan yau Friday Oga ya aiko ni. Kai kawai Oscar ya
gyada yayi gaba yana kankame jakar kudin.
Inuwa bai kawo komai ba ya shiga bankin. Shima wurin manaja aka kaishi saboda yawan kudin.
Manaja yace kuma kaga yanzu wani maaikacin kamfaninku ya karbi the same amout na 10 million.
Hala babban project ne a gabanku. Inuwa sakatare yace Oscar ma kudin kamfani ya karba? Manaja
yace eh har da Oganku nayi confirming. Inuwa yayi mamaki dai amma sai ya karbi kudin ya tafi. A iya
saninsa shi kadai Oga yake aika banki. [25/09 3:56 pm] Inna: AL'ADUN WASU í ½í·¿33
Batul Mamman(Mrs)í ½í²–
Washegari Jumaa tun bakwai da rabi Hamza ya fita zuwa site din da suke wani gini. Dama a daren
Izzatu ta kai masa karar Zuhra wai tayi mata rashin kunya. Da safe ta sake tuna masa yace idan ya
dawo zaiyi maganin abin. Yau bakin shayi da bread aka kaiwa Zuhra a matsayin breakfast. Bata nuna
damuwa ko kadan a fuskarta ba da Tala ta kai mata. Tasan Izzatu na neman suyi fada ne ita kuwa
bazata biye mata ba. Bayan ta gama sha ta dauki kofin ta sauka kasa.
Junior ne ya tareta a kofar kitchen din...Zuhra meyasa kika dena cin abinci tare damu? Shafa kansa
tayi babu komai nafi son zama a daki ne. Hannunta ya rike to nima zan rinka zama a dakinki. Khalifa
ya taho da sauri ayi hirar dashi suka hada ido da Izzatu. Ba shiri ya koma dakinsu don yasan ma'anar
wannan kallon. Tsawa ta dakawa Junior tace ya bar wurin. Ya buga kafa a kasa ni Mummy ki kyale ni
Zuhra is my