Author : Batul Mamman Category : Read Hausa Novels
tafi makota bara. Baki Zuhra ta turo tana rike ciki ni shiyasa bana so kice zakiyi girki Umma
musamman tuwo sai ki dade. Miyar nan tun kafin magariba kika dora gashi har an idar da isha.
Umma tace ni kuma kinga bana son danyen girkin nan naku. Sai ayi tuwo da miya cikin rabin awa.
Suna magana Baban Yara ya shigo. Zuhra tana matse ciki tana masa sannu da zuwa. So take yasa
Umma ta kada miyar haka. Dariya yayi musu ya shige ciki. Ga mara juriyar yunwa , ga mai dadewa a
girki.
A falo suka zauna suna ci. Da yake ba wuta Zuhra kasa jira tayi nata tuwon ya huce tasa mafici tana
fifitawa tana ci. Ta cika baki da tuwo tace Ummana kin iya girki sosai sai dadewa. Umma tace bazaki
yaba min ba sai kin hada da mita. Wannan mijinki sai yayi da gaske wurin noma. Baba yace to dai
kada ki takurawa babata. Ya fito da wata leda daga aljihunsa. Ya danne ta da dungulmin hannunsa
sannan ya bude da dayan ya dauko gasashshiyar kaza. Umma tace yau dadi zamu ci BabanZuhra. Yace
Ya'u ne ya siya shine ya debar min yace na kawowa Zuhra. Dadi ya kamata taje ta durkusa a gabansa.
Cinya ya dauko mata da fikafiki biyu. Ta karba da murna ta koma wurin zamanta.
Kamar ance ta daga kai ta hango hannuwan iyayenta a gefen kwano suna kokarin raba wuya su ci.
Duk zumudin da take a lokacin wani daci taji a wuyanta. Hawaye ya sauko mata tayi saurin gogewa.
Ta dan gutsiri naman kadan tace washhhh. Umma tace kin kone ko? Dama cin abinci kin kasa jira ya
huce. Zuhra tace hakori na ne yake min ciwo daga nasa naman a baki. Baba yayi mata sannu. Ta tashi
ta mayar da duka naman gashi ku cinye bakina zafi. Baba yace ki ajiye zuwa gobe mana. Idan ya lalace
ai sai nayi kuka Baba. Ta dauki tuwon bari na kai kitchen bazan iya ci ba. Ta fice tana fifita baki.
A bakin rariya ta tsuguna ta cinye tuwonta ta wanke baki. Umma tace ya naji shiru ko bakin ne. Tace
a'a almajiri na nema a waje. Wuraren shadayan dare su Umma sun kwanta Zuhra ta lallabo ta fito
falo. Tayi sa'a kuwa ledar naman tana nan kan dan tebur din da suka ajiye tare da jug din ruwa. Zuhra
ta bude ledar a hankali ta sami yan kasusuwan da basu cinye ba duk ta tsotse don naman yayi mata
dadi.
Baba ya taso Umma suka tsaya ta yar kofar jikin tagar dakinsu suna kallonta. Hawaye Umma take
sosai a hankali tace bar mana tayi muci. Baba yace muna tausayinta tana tausayinmu. Allah Ya
albarkaci rayuwarki Fatima. Suka koma suka kwanta.
Da safe Umma ta riga ta tashi. Ta fito suka gaisa ta dauko tsintsiya zata fara shara. Umma tace kamar
na bar ledar naman nan a falo. Zuhra ta dan tsorata sai tace ai da asuba na dauke saboda beraye.
Umma tayi murmushi kawai ta fita tsakar gida.
[25/09 3:14 pm] Inna: AL'ADUN WASU í ½í·¿5
Batul Mamman(Mrs)í ½í²–
Kafin karfe tara ta gama duk ayyukan da zata yi. Wanka tayi sannan tayi shirin islamiyya tunda asabar
ne ana yin ta safe. Ta gama shirinta tsaf ta yiwa iyayenta sallama ta tafi.
A darasi na uku Malama Rabia ta shigo. Ita kadai ce mace da ke koyarwa a islamiyar tana koya musu
Nahawu. Zuhra jira tayi sai da aka kammala darasin gaba daya sannan tace tana da tambaya. Yan ajin
har sun soma dariya sannin halinta. Wata tambayar idan tayi sai kaji kamar shirme. Ita kuwa sai ta
dake, sai an bata amsa tace nasan ku ma kun karu. Malama Rabia tace ina jinki Fatima. Zuhra tace
menene hukuncin macen da ke karin gashi ko bleaching a musulunci. Malama tayi dan murmushi ai
hukuncinsu a bayyane yake, babu kyau. Zuhra tace ai nima nasan babu kyau ina nufin akwai wata aya
ko hadisi da yayi nuni an hana ko kuwa fatawar malamai ce kawai. Malama Rabia tace to bari mu fara
da maganar karin gashi tunda shi tabbas akwai ingantattun hadisai a Sahihul Bukhari da Sahihul
Muslim da suka nuna anyi hani da yinsa.
Manzon Allah SAW yana cewa Allah SWT Ya tsinewa mai karawa wata gashi da wadda tace a kara
mata. Ki duba hadisi na 5934 a Bukhari da 2122 a Muslim.
A wani hadisin kuwa, Asma'u bint Abubakar(RA) tace wata mata tazo wurin Annabi SAW tace masa ta
aurar da yarta amma lalura tasa gashin kan yar ya zube. Shin zata iya saka mata gashi? Sai Annabi
SAW yayi kashedi ga mai karin gashi da wadda aka karawa. Bukhari 5479, Muslim 3962.
Malamai sun dauki karin gashi a matsayin yaudara sannan suka yi hani dashi. Akwai hadisin
Mu'awiyya RA wanda yace Annabi SAW yace karin gashi yaudara ce. Sahihul Bukhari 3229.
Ta koma ga sauran daliban gaba daya. Ku kanku a ma'aunin hankali kunsan cewa akwai ha'inci a karin
gashi. Banda asarar kudi da kuma warin da yake yi a kan mai sawa. Sannan duk mai karin gashi bata
taba rufe kanta gaba daya domin tayi ne don a gani. Asali ma a shekarun baya muna ganin mace da
karin gashi mun san ba musulma bace. Sai gashi a hankali mun dauki al'adu da dabiun wasu muna yi.
Allah Ya shirye mu baki daya.
Sai tambayarki ta biyu akan masu shafa mai su canja kalar fatarsu daga baka ta koma fara. Wasu
masu zalamar ma fararen ne suke kara kode fatarsu. To duk wannan yana cikin nau'in canja halitta
wanda Allah Ya hana. Shaykh Ibn Uthaymeen yayi bayanin canja kalar fata na dindindin kamar
bleaching a matsayin laifi kamar masu yin tatoo(zane da wuta ko abu mai kaifi a jiki) da kankare
hakori ayi wushirya. Irin wadannan laifukan Annabi SAW ya sanar damu tsinuwar Allah ta tabbata ga
masu yinsu. A bangaren lafiya kuwa munsan cewa babu wani nauin bleaching wanda bashi da illa ta
kusa ko ta nesa. Wanda munsan Allah Ya hana mu cutar da kawunanmu. Ga zubar da mutumci da
kimar mai yi a idon wadanda suke da hankali suke amfani dashi. Ga asarar kudi da sauran abubuwa
marasa kyau. Allah Shine mafi sani daga kurakuran da muke aikatawa. Allah Yasa duk abinda zamuyi
mu tsaya a iyakar da Yayi mana. Laifukanmu kuma Ya Yafe mana.
Gabadaya ajin suka ce Amin. Jikin yan matan duk yayi sanyi saboda ba'a rasa masu dan shafe shafe da
masu dora gashi ko da a jikin acuci ne irin na Hajara. Zuhra tayi godiya ga Malama Rabia sosai. Duk
bayanan da tayi kuwa ta rubuce su a yar takarda wanda zata nunawa Hajara shaida. Ta so ace Hajarar
na nan tayi tambayar.
Daga kofar daki 'yan matan biyu suka ce Mama mun tafi. Ba tare da ta dago kanta daga laptop din
gabanta ba tace Allah Ya kiyaye hanya ku gaishe su. Shiru taji ba amsa...tana dagowa taga sun tafi. A
ranta tace na rasa saurin me yaran nan suke yi haka.
Hajiya ta fito daga dakin Alhaji taji karar mota. Sauri tayi kada su tafi ta basu sako su siyo mata a
hanya idan suna dawowa. Kayan da ta gani a jikin Adabiyya ne yasa ta kara sauri tana kwala musu
kira. A tsorace Adabiyya mai shirin shiga mota ta juyo. Hamida tace shikenan mun gama yawo. Ko
kadan ba haka suka so ba. Hajiya na dakin Alhaji suka ki zuwa yi mata sallama. Ita kuma Mama daga
bakin kofa suka yi mata basu bari iyayen nasu sunga kayan jikinsu ba. Hajiya ta fito har wajen rai a
bace tace duk su shigo ciki.
Mama ta fito daga daki tace Hajiya lafiya? Kafin ta bata amsa yaran suka shigo. Ya Salam...Hamida?
Adabiyya? Meye hakan kuma? Hajiya tace kema basu ce miki zasu tafi ba ko. Nima karar mota naji na
fito da sauri ashe rabon idona ya gane min ne.
Hamida yar shekara ashirin da biyu jeans ne a jikinta da top wadda ko rabin cinya bata rufe mata ba.
Duk ta dameta sai tayi rolling da karamin mayafi. Adabiyya mai shekaru shatara kuwa skirt ne a jikinta
amma itama ya matse har shatin pant dinta ake gani. Shima don tafi yayarta jiki ne ta saka. Sai riga
matsatstsiya karama har da wata belt a samanta an kara tamketa. Da dan karamin mayafinta. Hajiya
ta kalli yayansu Nura. Kai mahaukacin ina ne da kana ganin sun fito a haka kake shirin jan mota. Ku
fada min gaskiya ina kuke shirin zuwa. A tare suka ce gidan Yaya.
[25/09 3:14 pm] Inna: AL'ADUN WASUí ½í·¿6
Batul Mamman (Mrs)í ½í²–
Mama tace ni na rasa gane me ake yi a gidan Yayan naku ne? Jiya kunje kun ce aiki zaku taya Izzatu
yau ma kun ce aikin zaku kara yi. Ko packing suke yi ne zasu tashi bamu sani ba, ta zauna akan kujera
kusa da Hajiya tace ni a iya lissafi na ma ai sai karshen August za'ayi birthday din Nana. Kuma ita ce
ta rage anyi na yayyenta. Hajiya ta tabe baki kina ma kokarin rikewa. Sun mayar da birthday tamkar
wata ibada. Duk shekara sai anyi sau uku a gidan. Allah Ya kyauta.
Mama ta ce Nura fada min gaskiya me ake yi. Indai birthday ne an saba yi mun kuma hakura mun
zuba ido. Tunda shima Hamzan bai ji maganar mu su dena ba ai matarsa bazata ji ba. Shiru yayi har
sai da Hajiya ta daka masa tsawa...baka ji ana tambayarka ne? Adabiyya ta soma kuka dama ita akwai
tsoro tace Hajiya party din wedding anniversary zasu yi na shekara goma da aure. Innalillahi wa inna
ilaihi rajiun shine abinda su Mama ke fada. Hajiya ta mike tsaya tana magana a hankali...lalacewar
Yayanku har ta kai nan? Allah Ya shirya. Daga nan dakin Alhaji ta koma ta cigaba da gyarawa.
Mama ta dubi yaran. Yanzu don Allah waye ya ce ku saka irin kayan nan? Yaushe ma kuka siya?
Adabiyya tace jiya da muka je ne Anti Izzatu tace kananan kaya zamu saka yau. Shine muka ce bamu
da masu kyau. Sai ta kaimu wani kanti ta siya mana. Mama tace eh lallai yarinyar nan bata nemawa
kanta zaman lafiya a gidan miji. Shirun da taga munayi don bama son zama iyaye masu sa ido a
lamarin gidan 'ya'yansu ne. Amma wallahi idan na bullo mata ta bayan gida sai ta gane karyar
rayuwar turai take yi. An gayyaci su Mariya? Hamida tace eh duk su biyun. Har Yaya Ibrahim ma an
gayyace shi da Anti Umma. Mama tace suma duk kananan kayan aka ce su saka? Hamida tace bamu
sani ba. Mu da kannenta tace mu saka dai jiya.
Mama tace duk su je su canja kaya tana zuwa. Nura yace harda ni Mama? Ta harare shi ban sani ba.
Dakin Alhaji ta shiga ta tarar da Hajiya a zaune a kan gado tana kuka. Mama tace haba Hajiya kukan
iyaye ga 'ya'yansu bai taba zama alkhairi ba. Hajiya ta share hawaye da gefen dankwali. To ya zanyi
Kaltume? Yaron nan ko kadan ban goyi bayan zuwansa Canada karatu ba amma Alhaji ya dage.
Karshe yaje ya hadu da mata itama tashin can. Mama tace shekara hudu fa kawai suka yi da babanta
yaje aiki. Hajiya tace to ai dai ta zauna ko. Gabadaya sun dauko wasu al'adu daban da namu.
Wadanda basu dace da addinmu ba. Kina kallo duk shekara sai sunyi party nasu da na yaransu. Sati
kusan uku da suka wuce ba ya kawo mana laces ba wai na Mother's day. Na Alhaji kuwa na Father's
day ai kinga bamu taba gaya masa dalilin bayarwa ba kila da zaginsa zaiyi ma. Duk wata rana da
turawa suke bawa mahimmanci Yaya da matarsa suna yi. Ko da ba kowanne muke gani ba amma
munsan anayi. Su a dole rayuwar turawa sukeyi. Mama tace kiyi hakuri yanzu zan kira shi a waya
yazo. Dole mu sake masa magana ko mu hadashi da Alhaji. Wannan karon sun wuce gona da iri tunda
suna son batawa yaranmu tarbiya. Hajiya tace Allah Ya shirya mana. Amma don baki ji yadda raina ke
baci ba idan su Khalifa na kirana Granny dinnan. Mama ta kwashe da dariya. Ai gara naki ma. Nida
ake kira Grams fa. Yau da bamuyi boko ba ai da mun sha kunya tunda sai kiyi musu magana ma amma
su amsa da turanci. A dole sai an bambanta su da 'ya'yan yan uwansu.
Sani masinja ya dauki wayar landline din office dinsu da aka kira. Muryar mace yaji tace matar Hamza
ce. Ji yayi tana kuka tace ya fada masa Junior ya fado daga kan kujera ya karye a hannu. Sani ya tashi
da sauri sai ya tuna meeting din da suke yi mai mahimmanci ne. Har ya koma ya zauna ta sake kira a
fada masa yanzu ya taho gida. Ta kira wayarsa a kashe. Dole Sani masinja ya shiga hall din da ake
meeting din.
Architect Hamza Nasir Hamza ya juyo a fusace yace meye haka Sani? Manyan baki gareshi turawa
masu son hadin gwiwa da kamfaninsa na zane da ginin gidaje da hotels da sauran manyan gine gine.
Sani masinja yace ranka ya dade uwargida ce ta bugo tace Jiniya ya fado daga kan kujera ya karye a
hannu. Hamza ya tashi da sauri....what? Ya dubi bakinsa yace da turanci kuyi hakuri dana ne ya karye
a hannu. Sun tausaya masa suka ce zasu dawo a karasa meeting din. Amma ya daure yasa hannu a
takardar shaidar amincewarsa da sharudansu. A gaggauce ya karanta ba tare da ya fahimci kalma ko
daya ba yasa hannu a duka biyun. Daya tasu dayar ta kamfaninsa. Sunji dadin amincewarsa sosai suka
tashi. Yana ta sauri a hanya wayar Mama ta shigo. Ya dauka a gigice a zatonsa Izzatu ce. tace Yaya
kana ina ne? Mama ke ce? ina hanyar zuwa gida. Tace to maza kazo ina son ganinka. Yace Mama
Izzatu bata kiraku bane? Junior ne ya karye a hannu. Yana hango wani dan sanda ya nufo motarsa
saboda yana amsa waya yana tuki da gudu yaja motar kafin a bada hannu har ya kusa karawa wani.
Mutane suka bishi da zagi da bakaken maganganu.
Mama ta dubi Hajiya tace bamu ga ta zama ba wai Junior ya karye a hannu. A tare suka fito daga
dakin suka kiran Nura yazo ya kaisu gidan Yaya. Hamida tace Mama me ya faru? Junior ne ya karye a
hannu. Yanzu yayanku yake fada min. Adabiyya tace ba gaske bane. Jiya ne Anti Izzatu tace bata san
da yadda zata sa Yaya ya baro office da wuri ba. Partyn surprise take son yi masa. Bai san komai game
dashi ba. Ana haka wata makociyarsu da aka bawa aikin meatpie ta shigo take cewa danta ne ya
karye kuma ya kwana da zazzabi shiyasa bata aiko ta karbi kayan yin meatpie din ba. tana fita ne
shine Anti tace ta sami idea din abinda zata fada masa. Hajiya ranta ya kara baci. Mama kuwa ashar
ta dannawa Izzatu saboda yadda zuciyarta ke mata zafi. Ta kalli su Hamida duk sun saka material ne
da mayafansu manya tace Nura ya kaisu amma ya fadawa Yaya tana son ganinsa komai dare.
Sai bayan fitar bakin sakataran Hamza yana hada takardu ya duba wadda ya saka hannu a kai. Jikinsa
ne ya fara rawa ya soma salati. Wani cikin yan office din yace menene. Inuwa Sakatare yace ai bana
jin oga ya karanta takardar nan da kyau. Ta nuna ya amince ya karbi kudin da suka bashi saboda haka
nan da wata shida duk ribar da aka samu tasu ce. Daga wani wata shidan kuma sai su rinka raba ribar
gida uku. Su kaso biyu shi kuma daya.
[25/09 3:14 pm] Inna: AL'ADUN WASU í ½í·¿7
Batul Mamman(Mrs)í ½í²–
Alhaji Nasiru Hamza dan kasuwa ne mazaunin Kano amma asalin iyayensa mutanen Kumo ne na garin
Gombe. Sana'ar siyar da shanu da tumaki ya fara wadda a hankali har ya fara fitar da fatar dabbobin
kasashen waje yana sayarwa. Shiyasa ma aka fi saninsa da Nasiru maifata. Halima wadda suke kira
Hajiya ya fara aure yar kanwar babansa. Sun fara zama a Kumo kafin kasuwancinsa ya bunkasa ya
dawo Kano. Lokacin ta haifi danta na fari Hamza suke kiransa da Yaya. Suna zamansu lafiya da mijinta.
Kuma suna yawan zuwa gida ganin iyayensu. Hamza na da shekara biyu ta haifi Ibrahim sai Mariya.
Alh Nasiru ba karamin soyayya yake nunawa yaransa ba. Yana da amini kuma abokin kasuwanci Alh
Sabiu. Kowa ya sansu tare hatta iyalinsu suna mutunta juna. Matan Alh Sabiu biyu. Kaltume ce
uwargida sai Sahura. Kaltume bata taba haihuwa ba a shekarun da sukayi da mijinta. Tana dai karatu
a lokacin. Ita kuwa Sahura 'ya'yanta shida. Da kamar gaske suke zaman lafiya. Sai daga baya Sahura ta
rinka daukar zigar yan uwa da kawaye ta fara yiwa Kaltume habaici da gorin haihuwa. Tun bata
kulawa har dai ta fadawa mijinsu akan ya yiwa Sahura magana sai cewa yayi ai ba matsayinsu daya
ba. Idan taji haushi ta haihu mana. Da kadan kadan suka juya mata baya. A lokacin tayi shawara ta
sanar da Halima halin da take ciki lokacin tana da ciki na hudu. Ita kuma sai ta fadawa mijinta. Ko
kadan Alh Nasiru baiji dadin faruwar hakan ba. Ya zaunar da abokinsa yayi masa nasiha. Sai dai duk a
banza. Wata rana Kaltume zata tafi makaranta ta shirya ta rufe dakinta sannan ta leka dakin Sahura
tace ta fita. Tana dawowa da yamma ta tarar da Alh Sabiu da Sahura har da wasu makota a kofar
dakinta. wasu samari ne suke kokarin balle kofar.