Aladun Wasu Hausa Book Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Read Hausa Novels

Chapter   19 / 40

54K to 57K   out of 117.5K words

mata suka kwana kwarto ya fado
mana. Nishadi yake kawai saboda yasa ta farinciki yace bai taba ki ba ko. Zuhra tace ina fa ai lokacin
ni ban girma ba sosai amma har fitsari sai da nayi a wurin don tsoro. Kowa ya gudu ya barni ina ta
salati. Sosai Hamza yake dariya. Amma an kamashi kafin ya gudu. Yaci duka sosai har hakorinsa daya
ya cire. Hamza ya dan kwanto jikinsa akan gadon, to yanzu kin girma dai ko? Da dan murmshinta
tace sosai ma. Kudin da Mama ta bashi ya mika mata a cikin duhun tayi godiya sannan yace nima
akwai kyautar da zan baki amma sai an kawo wuta. Yau manatawa nayi da batun inji but hopefully da
safe maigyaran zai zo.

Allah Ya kaimu Zuhra tace, amma kaje ka kwanta kaga gobe zaka je aiki. Maimakon ya tashi sai taga ya
gyara zama sosai don yanzu irin yadda bayanta ke jingine da pillow shima haka yayi. Kara matsawa
tayi shima ya matso. Haka suka yi har ta kai karshen gadon. Ta dan turo baki wai sai ka rinka wayon
tabani kuma kasan dai babu kyau. Yayi dan murmushi tare da shafa fuskarta. Miji ai ba sai yayi wayon
taba matarsa ba, abinda kike boyewa nake son gani. Pillow tasa ta kare jikinta...ka rufa min asiri rigata
yar karama ce. Hamza yace to na rufa, dan matso na tambayeki. Ba musu ta matso kadan domin a
karshen gadon take. Wai baki san sunana bane? Ban taba ji kin fada ba. Sai dai kice yi kaza, ko kayi
kaza. Alamar tana jan bargo yaji yasa hannu ya danne. Baki amsa min tambayata ba. Naga alama so
kike na kwana a nan. Bari ki gani...kwanciyarsa yayi tare da dora kansa a cinyarta. Idanunta kamar su
fito waje tace don Allah ka tashi. Gyara kwanciyarsa yayi naki din. Idan kina so na tashi ki bani amsa.
Baki san sunana bane? Dadin kwanciyar yaji ga kamshi mai sanyaya rai da jikinta ke fitarwa. Ita kanta
kawai fada take da tace ya tashin, duk da taji kunya amma hakan yayi mata dadi. Duk iya kokarinta na
ta janye jikinta ta kasa, gashi rigar jikinta ta danyi sama. Rabin kansa a cinyarta yake babu riga a
wurin. Shi kanshi Hamza bazai iya tantance yadda yake jin Zuhra a wannan lokacin ba. Gajiya tayi da
yunkurin tashi tace nima baka fadan sunana sai dai kace ke ko yar kauye. Yace to yi hakuri kafin nayi
bacci zan sama miki wani sunan. Ina amsata? Cike da shagwaba tace to ba sunayen naka bane masu
yawa. Hmmmm lissafa min su ya fada yana lumshe idanu. To nasan sunanka na gaskiya sunan babban
sahabin Annabi SAW ne kuma Kawunsa. Ta dan sunkuyu da kanta har yana jin dumin numfashinta a

fuskarsa in fada bazaka ce nayi rashin kunya ba? Fadi....tace HAM-ZA. Yadda taja sunan yayi masa
dadi har wani abu yaji tun daga kansa har kafarsa. Na biyu kuma a gida su Hamida na kiranka Yaya, su
Khalifa suce Daddy, maigadi da Tala suce yallabai. Ita kuma Maman su Khalifa tace su Honey,
Sweetheart....har wani kwafar muryar Izzatu take yi idan ta kasheta tana kiran Hamza. Abin dariya ya
bashi yace kin iya gulma yarinyar nan, to su kenan kika sani? Zuhra tace ina fa...harda wani Babyna,
shima a wata irin murya ta fada kamar rada. To idan kai baby ne jariran gaske kuma me za'a kira su.
Da gaskenta take magana Hamza yace lallai da sauranki. Lesson four...maza suna son matansu su
rinka kiransu da sunaye masu dadi kamar yadda suma matan suke so. Kuma idan miji ko mata ya kira
dayan baby ai saboda a aure ana son mutum ya rike abokin rayuwarsa tamkar jariri. Kinga a aure ana
son mace ta girmama mijinta kamar wanta sannan a bangaren soyayya da kulawa ta rike shi kamar
baby dinta. Ta bashi abinci a baki, ta yanke masa farce, saka masa turare, cire masa kaya da saka
masa, tayi masa wanka da shafa mai ko suyi tare......mun shiga uku !!! Zuhra ta katse shi harda dora
hannu a ka. Ni kasa ni jin kunya ma, don Allah a bar zancen haka. yanzu harda wanka kuma duk
girmansa. Ni dai gaskiya a'a wannan karatun ban dauka ba. Hamza yace amma kinsan ko a hadith
daga Nana Aisha RA ta kasance suna wanka tare da Annabi SAW. Zuhra tace haka ne an fada a
islamiyya...amma da kunya.
Hamza yace indai kina son zamanku ya dore da miji dole ki rinka yi masa irin wannan da abinda yafi
haka domin nuna kulawarki gareshi. Shiru tayi tana tunanin duk abubuwan da ya fada mata. A hankali
tace Ya Hamza.....har ransa yaji dadin sunan....in sha Allah duk abinda ka koya min idan na sake aure
zan gwada. Daga yau ka zama yayana saboda kana min kirki sosai .....tayi 'yar dariya wai, don Allah Ya
Hamza hangoni ina yiwa kato wanka. Rufe idona zanyi don bazan iya kallonsa ba. Nagode da yadda
kake bani shawarwari. Ko yau muka rabu bazan dena yi maka addua da fatan alkhairi ba.
Ba ma jinta yake ba sosai. Ya hangotan tana yiwa katon wanka kuma ko kadan hoton da zuciyarsa ta
nuna masa bai masa kyau ba. Ransa ne ma yayi matukar baci ya tashi ba shiri zai koma dakinsa.
Meyasa zata kawo zancen wani suna tare? Ita kuwa bata kawo komai ba a ranta tace Ya Hamza sai da
safe. Juyowar da yayi aka kawo wuta ta haske dakin gaba daya. Idanunsa a kan Zuhra suka sauka da
yar rigarta. Numfashinsa sai da ya canja saboda yadda ya ganta a cikin rigar. Tayi masa kyau sosai.
Maimakon ya fita makunnin fitilar dakin ya nema ya kashe tare da kunna AC. Zuhra duk kunya ta
isheta ta shige cikin bargo harda rufa har kanta. Ji tayi ya dawo ya kwanta sannan ya janyota jikinsa ya
rungumeta kamar wani zai kwace ta, rabin jikinta duk a nasa jikin yake. Sai kokarin gudu take ya kara
matse ta. A kunnenta ya rada mata
" Good night Cutie, kuma ki dena yi min shure shure haka". Dena motsin tayi amma ta kasa sakewa.
Wai yau ita Hamza ya rungume a jikinsa haka. Basu sake magana ba kowa da tunanin dake ransa har
suka yi bacci makale da juna kamar ba Hamza da Zuhra ba.


[10/12, 7:34 PM] Salma: AL'ADUN WASU 51

Batul Mamman(Mrs)

Kiran farko na assalatu Hamza ya bude idonsa. Murmushi ne ya bayyana a kyakykyawar fuskarsa
saboda jin har yanzu Zuhra na jikinsa. Hannunta ya zagaye cikinsa, ga kanta a wurin wuyansa. Yana jin
lips dinta a wuyan nasa. Sake matseta yayi zuciyarsa na fada masa yayi a hankali kada ya fada
soyayyar da zata iya zame masa rigima nan gaba. A hankali ya rinka shafa kanta yana kiranta da sabon
sunan da ya rada mata. Cutie ki tashi asuba tayi. Sake makalewa tayi a jikinsa batare da tasan halin da
hakan ke sake jefashi ba. Cikin dabara ya fara janye jikinsa sai itama ta bude ido. Ji yayi ta tashi da
sauri Ya Hamza ba dai a haka muka kwana ba. Mikewa yayi ni bana son gulma kin gama makale min a
jiki kamar babu pillow a kan gadon zaki wani wayance yanzu. Kunyarsa sosai take ji ta koma cikin
bargo ta dukunkune kanta. Gudun kada ya makara sallah yasa yayi murmushi kawai ya fita. Sai da taji
ya rufe mata kofa ta tashi ta shiga toilet. Har addua tayi bayan ta idar da sallah,kada yayi mata kallon
mara kamun kai.

Tana idarwa dakinta ta gyara da toilet sannan ta sauka ta share falon tayi mopping. Falon ne da girma
shiyasa taga gara tayi aikin da wuri. Tun dare ya fada mata bread kawai zaici da safe da tea, wani
maidadi ya siyo a Grand square. Ruwan zafi ta dafa ta juye a flask ta hada da kayan tea ta kai dinning
table ta ajiye. Ta sallami maigadi ma sannan ta koma daki ta tsefe kitson kanta ta kama gashin da
ribbon. Wanka ta shiga ta bata lokaci a bandaki don yanzu an dena jika jika. Ta zauna gaban mudubi
ta shafa mai sannan ta rinka feshe jikinta da turaruka. Ta kula Hamza na son kamshi sosai, yau so take
ta burge shi yasan tana daukar karatun da yake mata. Wani dogon wando tight baki ta saka ta hada
da riga pink wadda ta kusa gwiwarta mai hannu three quarter. Rigar da dan matseta daga sama
sannan ta yi fadi kadan daga kasa. Da Hajara suka je kasuwa aka siyo kayan da kudin sakarta. Hoda
tasa da kwalli sai dan janbaki kadan pink wanda tayi lining lips dinta da liner pink amma mai dan
duhu. Har wani tsalle tayi da tafi ganin tayi kyau. Ta fesa turare a kayanta sannan ta dauko karamin
pink da bakin mayafi ta daura irin yadda dai 'yan gayu suke yi. Kasa ta sauka har lokacin Hamza bai
sauko ba gashi har takwas da rabi. Tana son zuwa ta duba ko bacci ya koma bayan ya dawo daga
masallaci amma tana jin kunyar kayan jikinta.

Wayarta da ta dan sami chaji ta duba taga text din Hajara tana sanar da ita zata zo wurin shabiyu ta
kira wayar tun jiya taji a kashe. Wayyo dadi, Zuhra sai murna. Kada Hamza yace wannan karon bata
fada masa zata yi bakuwa ba ta yanke shawarar zuwa dakinsa.

A darare tayi sallama ta shiga falon sai taji ya amsa daga cikin daki. Kanta tsaye ta shiga ciki ta ganshi
daure da tawul yana tsaye a gaban wardrobe dinsa yana neman kayan sawa. Kafin ya juyo ta runtse
idonta tana cewa yayi hakuri. Dariya yaso yi sai dai shigarta ta matukar daukan hankalinsa. Ji yake
kamar ya dauketa yayi hugging. Zata fita yace tsaya a nan ina zuwa. Kayan ya saka sannan ya taho
gabanta da coat a hannunsa da necktie. Kamshin turarensa ya sanar da ita isowarsa. Cikin murya mai
jan hankali yace bude idonki Cutie. A hankali ta budesu ta ganshi tsaye da shirt dinsa duk maballan a
bude. Yace jiya na fada miki ana taimakawa miji yasa kaya ko? Kai ta gyada kawai tana kallon kasa. To
balle min buttons dinnan naga ko kin koyi karatun. Ta dan zaro ido tana kallonsa. Come on Cutie ina
da meeting kada na makara. Hannu na rawa ta soma ballewa daga kasa. Shi dariya take bashi ga tsoro

ga baki. Har tazo na karshen wuyansa jikinta sai bari yake. Bayan ta balle ya bata tie din saura
wannan. A sanyaye tace ban iya daurawa ba. Gwada mata yayi sannan ya ware ya bata ta daura
masa. Kallon da yake mata yasa hannunta ya kasa tsayawa sosai. Nasa hannun ya saka ya taimaka
mata har suka daura tare. Yau duk ta kasa kallon shi ya dago kanta da hannunsa sai kawai ta rufe ido
tace Ya Hamza kunyarka nake ji ka barni na fita. Zagayeta yayi da hannuwansa sannan ya matso da
ita gabansa. Cutie kinyi kyau. Ta danyi murmushi da gaske? Yace da wasa. Kafa ta buga a kasa cike da
shagwaba tace haba Ya Hamza mana kace nayi kyau don Allah. Hancinta yaja sannan yace kinyi sosai
shiyasa na saka miki Cutie. Muje muyi breakfast kada na makara. Dan tsayawa tayi yau ban gaisheka
ba, sai ta durkusa ina kwana ya jiki? Tayar da ita yayi tsaye kinga irin wannan gaisuwar bata dacewa
da miji da mata. Kinga yadda ake yi ko don gaba. Duka hannuwansa yasa a kafadunta yayi kissing din
lips dinta lightly. A take taji wani abu yana yi mata yawo a ciki. Shi kuwa jan hannunta yayi suka sauka
don yasan ko rabin minti suka kara a wurin abinda zai mata sai ya fi wannan.

Yau cin abinci nasu babu wata hira ake yi domin dukkansu tunani suke. Hamza sai tambayar kansa
yake ko dai ya fara son Zuhra ne? Itama Zuhra tambayar da take yiwa kanta shin zata iya rabuwa da Ya
Hamza. Suna gamawa ya tashi tace anjima Hajara zata zo kanwar Anti Faiza. Yace nima kinga na
manta su Adabiyya zasu zo kwana. To da safen nan kuma naga text din Jidda ita da Mariya da matar
Ibrahim kanina zasu zo. Inajin duk da yaransu zasu zo anya zaki iya da baki da yawa haka? Ga
mamakinsa murna take yi sosai, zan iya mana in sha Allah. Gara na dora girki da wuri saboda yara ma.
A dawo lafiya....bata saurare shi ba shige kitchen tana tunanin abinda zata dafawa bakin nata. A
hadith na shabiyar a Arba'una Hadith Manzon Allah SAW yace duk wanda yayi imani da Allah da
ranar karshe to ya karrama bakonsa. Kuma tarbiyar Ummanta da Baba kenan. Ita yanzu me zata dafa
ta burgesu kuma kowa yaci ya koshi?

Hamza ya gaji da tsayuwar mamakin irin wannan murna da Zuhra keyi ya dauki jakarsa ya fita. Izzatu
bata taba son 'yan uwansa su zo gidansa ba. Idan sunzo ma zasha ruwa ne da juice su koma gida.
Zuhra daban take.... Sai da ya shiga mota ya tuna da sabuwar wayarta ya dawo ya dauko har lokacin
tana kitchen. A tsaye ya ganta ta rike haba ita a dole tunani take. Tana ganinsa tace yauwa Ya Hamza
dan bani shawarar abinda zan dafa mana. Yace naki din, nida kika tafi kika barni daga cewa zaki yi
baki. Ta marairaice masa to yi hakuri kaji Ya Hamzaaaaa. Murmushi yayi Cutie kina abinda kike so.
Tayi murmushi tana kallonsa. Shima yayi mata kyau. Zo ga wannan I hope you like it. Da dan
murmushi tace ina fa dan gane turanci kalma me tsauri ce dai bana fahimta. Amma dan fassara min
abinda kace yanzu turancinka ba irin na malamin English dinmu bane. Fassarawar yayi yana dariya ya
mika mata wayar. Gashi nan na saka miki wani sim din sai ki saka na daya wayar tunda mai sim biyu
ce. Bade baki kawai tayi tana kallonsa. Sai kuma hawaye Ya Hamza wannan tawa ce? Ya gyda kai, tace
Allah Ya saka maka da alkhairi Ya baka ladan faranta min. Allah Ya kareka daga dukkan sharri. Nagode
sosai. Wayar dubu ashirin Zuhra kewa kuka da wannan addua, Izzatu kuwa dubu dari ya bata da zata
yi tafiya amma kirikiri ta nuna ta raina. Matsowa yayi gabanta ya goge mata hawayen da hannunsa
sannan yace nagode da adduarki. Su kuma bakin kiyi musu danwake idan kin iya, a iya sanina dasu
Mariya duk mayun danwake ne. Yana gama magana ya fita tabi bayansa. Sai da motarsa ta fita daga
cikin gidan ta dena daga masa hannu.
[10/12, 7:34 PM] Salma: AL'ADUN WASU 52

Batul Mamman(Mrs)

Zuhra aiki ya kankama. So take ta gama abincin kafin su iso yadda ba zasu zauna da yunwa ba.
Katuwar roba ta samu ta dora danwake sai da tayi tukunya uku tana yi tana juyewa a wata roba mai
dan girma. A kalla mutum goma sha biyu zasu ci su koshi sosai. A ranta tace idan bai isa ba sai ta kara.
Bata san adadin yaransu ba ga maigadi. Bayan ta gama ta dafa kwai guda goma, ta wanke tumatir,
albasa, koren tattasai da cucumber ta ajiye bazata yanka da wuri ba kada yayi tsami. Man da ta soya
yasha albasa sannan ta duba bata da juice da yawa. Zobo tayi wanda ta dafa da citta da kaninfari. Ta
tace ta saka sugar da lemon tsami sai ruwan cucumber da ta gurza ta tace. A leda ta kulla ta zuba a
fridge saboda jug bazai shiga ba. Tana sauke mai ne ya tsallo mata a wuya har wuri biyu. Wani uban
tsalle ta doka saboda zafin da taji ta soma karanta ALLAHUMMA AJIRNI MINANNAR saboda neman
tsari daga azabar Allah. Allah Ya kiyayemu, amin. Sanda ta gama komai shadaya da rabi ta gyara
kitchen sannan taje tayi wanka. Riga da zani ta saka tayi irin kwalliyar dazu mara yawa ta sauko kasa.

Sabuwar wayarta ta dauko sai dai ta kasa gane kan wayar. Tana ta tabe-tabenta taji sallamar Hajara.
Kamar kananan yara haka suka rungume juna suna tsalle. Can Hajara tace ke dena jijjiga ni kada ki
barar da danki ko 'ya. Zuhra ta zaro ido tana shafa cikin Hajara. Doke hannun tayi to yar duniya meye
na shafa min ciki. Kema ina tunanin akwai fa, ji yadda kika yi haske kika kara cikowa. Zuhra ta kama
hannunta zo ki zauna yau tattalinki zan taya Yaya Sahabi. Ah su Hajara daga aure sai ciki. Hajara tace
ke bana son iskancinki fa. Kema naki yana hanya idan babu in sha Allah. Ai burina mu shiga labour
room tare. Shakiyanci suka yi ta yiwa juna. Daga baya suka shiga kitchen da Zuhra tace kannen Hamza
zasu zo. Hajara ta bude taga danwake...anya Zuhra kina da kai kuwa? Yan uwan miji zasu zo ki rasa
abinda zaki basu sai danwake? Zuhra tace yayansu ne yace shi suka fi so. Plates suke hadawa da cups
suka ji sallama a falo. Dama Zuhra da hijab dinta a hannu saboda kada suzo da maza. Kuskuren da
mata da yawa keyi kenan. Yan uwan miji maza ko abokansa su zo sai mu fito babu lullubi ko hijab.
Muji tsoron Allah mu kare mutumcinmu. Mota biyu suka yo duk a gidan nasu suka hadu suka taho
tare. Zuhra fuskar nan dauke da fara'a sai kunyar su Mariya take yi. Suka gaisa da Nura yace zai tafi sai
bayan sallar Juma'a zai dawo. Bajewa suka yi da 'ya'yansu ana ta hira da Zuhra. Ta sake musu sosai
kada ma Adabiyya da Hamida suji labari. Ta tambayi yaran sunayensu suka fada mata. Karamin dan
da Ummahani ke goyo kuwa Zuhra ta goya shi saboda ya hana mamansa sakewa. Tun yana kuka har
yayi bacci. Da taimakon Hajara dasu Adabiyya ta hado musu abinci. Cikin tabarminta ta shimfida
manya biyu. Jidda tace ai ki hada mana a tray kawai

19 / 40