Aladun Wasu Hausa Book Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Read Hausa Novels

Chapter   1 / 40

1 to 3K   out of 117.5K words

[25/09 3:14 pm] Inna��: AL'ADUN WASU🗿1

Batul Mamman(Mrs)💖

Bismillahir Rahmanir Rahim







Mal Bashir dattijo mai kimamin shekaru hamsin da takwas na shigowa cikin layinsu yara suka fara
binsa suna oyoyo Baban yara. Da yake kullum haka suke masa shiyasa baya rabo da yar tsarabar da
zai kawo musu. Hannunsa daya yasa a aljihu wanda daga tsintsiyar hannun a yanke yake ba yatsu
sakamakon zarton da ya fada kai har ya tsinka masa jijiyoyin hannu. ya sha wahala sosai likitoci suka
ce hannun ya mutu dole a yanke shi. Duk da haka bai dena zuwa wurin sanaarsa ba ta kafinta. Da
dungulmin hannun ya bude aljihunsa ya saka mai lafiyan ya zaro carbin malam ya mikawa yaran. Suna
ta murna suka tafi su raba. Yayi gaba yana dan murmushin suka hada ido da wani matashi a layin. Da
sauri ya taba na kusa dashi kai don ubanka kashe ga Baban yara nan. Tare suka tashi suna karkade
jikinsu. Baban yara barka da yamma suka fada da ya karaso kusa dasu. Ya dan bata rai bazan amsa ba
Sani. Yanzu don Allah baza kuyiwa kanku fada ba da shaye shayen nan? Ya kalli katon ciki Anas so
kake ciwon babanka ya sake tashi saboda kai ko? Wanda aka kira Anas ya girgiza kai. Kayi hakuri in
Allah Ya yarda bazamu sake ba. Yayi murmushin takaici Allah Ya bada ikon denawa. Kuna ta batawa
kanku rayuwa a banza. Idan baku sani ba abinda mutum yayi da kuruciya yakan bishi har girma. Na
tabbatar babu wanda zai so nan gaba a bawa dansa labarin ya taba busa wiwi a tarihin rayuwarsa.
Sani ya dan yi murmushin jin abinda ya fada. Baban Yara ya ce au dariya na baka ko? Ya kama bakin
ya murde. Muna nan da ku idan baku dena ba wata rana kwata zaku shiga ku kwanta kuce gado ne.
Yayi gaba abinsa yana ta mitar halin da yara ke saka kansu a yanzu.

A kantin kofar gidansa ya tsaya suka gaisa Munkaila mai shago. Mal Bashir ya dauko naira dari ya
mika masa. Gashi nagode sosai. Munkaila ya karba na meye kuma wannan Baban Yara? Darin da ka
bawa Zuhra mana da safe. Ina shirin fita ta tambayeni kudi zata je karbo sakamakon jarabawarta.
Lokacin bani da chanji shiyasa nace ta karba a wurinka. Munkaila ya mika masa kudin, ai yau ko sau
daya banga fitowarta ba. Mal Bashir ya karba ya shiga gidansa da sallama.
Zuhra na yanka yakuwa taji muryar Babanta a soro. Hantar cikinta ce ta kada sosai ta tashi da gudu ta
shiga bandaki. Garin sauri ta zubar da yakuwar da take yankawa. Ummanta ta soma fada ke lafiyarki
kuwa. Mal Bashir ya karasa shigowa tsakar gidan. Ina ta sallama babu mai amsawa kamar babu kowa

a gidan. Atine Umman Zuhra ta ce yi hakuri Baban Zuhra. Wallahi bari tayi min nake fada banji
sallamar ba. Takalmansa ya cire ya zauna kan tabarmar dake shimfide a tsakar gidan. Fitsari ta bari ya
matseta shine take wannan gudun ko. Umma tace anya kuwa? Hira mukeyi fa kana yin sallama ta
tashi kamar wadda ta ga abin tsoro. Baban yara na jin haka yasha jinin jikinsa. Yace da Umma ta
karbo sakamakon jarabawarta kuwa?Umma tana kwashe yakuwarta ta ce bana jin amma ga wasu
takardu can akan taga wanda Hajara ta kawo mata dazu. Mal Bashir ya tashi ya dauko a sanyaye...ai
tunda ta gudu yasan bana ma bata kitsa abin arziki a makaranta ba.

Ai kuwa yana budewa yaga abin haushin da yasa rai da gani. Ta 48 tayi cikin su 52. Ransa ne ya sosu.
Ya rasa yadda zaiyi da yarinyar nan. A fusace ya tashi ya tafi kofar bandakin. Zuhra me kike yi ne ya
tambaya da daga murya. Daga ciki ta ce ehem ehem! Ya sake bugawa idan ba so kike na bude ki ba
gara ki fito tun wuri. Zuhra ta gwammace ta yini a bandaki da ta fito ta sha fadan Baba. Ta sake cewa
ehem..... ya ce bari na fita tunda mun koma wasan buya da ke. Sai da ta kara kusan minti biyar
sannan ta fito duk ta hada gumi. Ta dubi Ummanta, wai yau da Baba ya kamani bansan....saukar
rankwashi taji a tsakar kanta ta durkushe a kasa tare da rike kan ta soma kuka.
[25/09 3:14 pm] Inna��: AL'ADUN WASU🗿2


Batul Mamman(Mrs)💖





Baban Yara yace idan baki rufe min baki ba sai na kara miki. Da kuka Zuhra ta mike tsaye tana turo
baki ko saboda rankwashin nan ba dole na kasa kokari ba. Idan kana taba min mandula oblongata
dina haukacewa zanyi nan gaba kadan. Baban Yara yace kece mandular ai. Nan kika fi kauri dama. Kin
iya haddace 'yan kalmonin turanci kizo kina barazana dasu kamar wata wadda tasan abinda take yi.
Zuhra dai kuka ta cigaba da yi har sai da Umma tayi mata tsawa. Wallahi idan kika tara min makota
yau jikinki sai yayi tsami. Jin haka ta soma tsalle tana kara kukan. Baban Yara yace bari na dauko
wayar chaja na yi miki mai dalili. Ai kamar anyi ruwa an dauke haka ta hadiye kukan.

Takardun jarabawarta da aka hada da report card din ya soma dubawa. Wasu har zero ta ci.
Maths(lissafi) tace arbain da takwas, Arabic tace casa'in da hudu sai Hausa ta taci sabain da daya.
Dama sune darrusan da suke dan taimakawa bata daukar ta karshe gaba daya. Sai ko rubutu da ta iya
mai kyau idan ka gani zaka dauka na wata mai kokarin ne. Yana dubawa yana tsaki sai daga baya ya
kula da yadda take rubuta suna. Kansa ya rinka girgizawa kawai don takaici. Ko shi da iyakarsa aji
hudu a secondary ga shekaru sun mika amma yasan idan suka shiga aji shi da yar tasa sai yafi ta
kokari. Zo nan ya yi mata tsawa. A hankali ta ja kafa ta je ta tsugunna a can gefe. Yanzu kin tabbatar
duka takardun nan naki ne? Nawa ne Baba duba sunan da rubutun mana. Yace ai na duba. Wasu ki

rubuta Zuhra Bashir wasu kuma Fatima Bashir don tsabar rainawa malamai hankali. Yana cigaba da
dubawa yayi karo da wata. Takalminsa ya raruma ya kwada mata. Ya daga takardar yana nunawa
Umma. Kinga wulakancin yar nan wai Fatima Basiru. Ya nuna kansa nine BASIRUN??? yadda yayi yasa
ta soma dariya Umma tace Allah Zuhra zanci mutumcinki. Ana miki fada kina wa mutane dariya don
shakiyanci. Zuhra ta kara matsawa gefe tana sharar hawaye to ba haka naji su Kawu Sabiu da Innar
Ajingi suna kiranka ba. Baba ya cije lebe saboda takaici. Da kika ji sun fada ba sunan gida bane?. A
nan wa kika taba ji ya kirani Basiru? Tace to yi hakuri wallahi daga yau na dena. Ki ma kara ya fada
yana tattare takardun. Yana yi yana mita. Yarinya sau nawa ana miki repeating gashi kin kusa shekara
ashirin. Amma kanki kamar kifi, nasan duk ajin kece mamansu ko. A'a Baba ga Hajara, ka manta
ajinmu daya. Yace ina fa zan manta...an tara dakikai biyu a aji daya. Baku da aiki sai cin awara da
wainar flawa. Zuhra da baki baya shiru tace to ba kai kake bani kudin ba. Umma tace kaga ka dena
kula yarinyar nan sai jininka ya hau.

Takardun ya miko mata jeki ki ajiye min a dakina. Ni ina ta kokarin hada kudi na biya miki kudin WAEC
saboda kada a rufe amma naga kamar asara zanyi. Sau biyu kina qualifying din nan amma kin kasa
hada credit uku. Zuhra tasan yadda babanta ya damu tayi karatu amma duk yadda ta dage a cewarta
ko kadan bata ganewa. Zama tayi kusa dashi kaga Baba kawai ka kaini makarantar koyon sakar nan.
Har na tambayo matar tace a wata biyu zata koya min sau uku a sati zani. Kuma a dubu shida. Ai kaga
yafi sauki akan WAEC din. Ta nuna kanta ni da ka ganni bani da abinci a boko. Kan baya dauka yadda
kasan an zuba dusa a kwakwalwar haka nake. Shi din ma ya kusa dariya sai ya dan dake. Tashi ki bani
wuri ni. Ko damuwa ba kya yi yan ajinku zasu tafi makarantun gaba ke kina son koyon saka. Ta dan
tura baki to ya zanyi Baba. Suma fa duk harkar ta koma satar amsa. Idan sakar ma bazata yiwu ba
kawai kayi min aure ka huta. Shi da Umma a tare suka yo kanta suna mata fada. Da gudu ta tashi tayi
hanyar waje tana dariya tare da jan mayafin Umma a igiya.
[25/09 3:14 pm] Inna��: AL'ADUN WASU🗿3


Batul Mamman(Mrs)💖





Mal Bashir Ibrahim mutumin Ajingi ne ta jihar Kano. Su biyar ne maza a gidansu shine na biyu.
Mahaifinsu manomi ne kuma yana kiwon shanu da tumaki. Da farko sun fara karatu har ya kai aji
hudu a makarantar gaba da firamare sai babansu ya matsa akan basa samun lokacin taimaka masa a
gona. Shi a son ransa duk su hakura da karatun. Ko kadan Bashir baiji dadin hakan ba, sai da ya
hakura shi da wansa da mai bi masa suka koma gona. Sauran biyun suka cigaba. Akayi rashin saa
autanma ya dena zuwa don shi yafi son kiwo. Wanda ya karasa kuma kan nasa kamar na Zuhra. Ba
wani sakamakon kirki ya samu ba. A halin yanzu ma masinja ne a wani company. Mal Bashir ya dawo
birni shima aikin kafinta a nan ya hadu da Atine yar kwanar Diso ya aura.sun jima basu sami haihuwa

ba gashi yana da son 'ya'ya ,sai daga baya aka haifi Fatima wadda taci sunan mahaifiyar Mal Bashir
kuma sunan Atine shiyasa suke kiranta Zuhra.

Zuhra na fita gidansu Hajara ta nufa tana ta mita ta jawo mata fada a gida. Da sallama ta shiga sai dai
babu kowa a tsakar gidan. Daga dakinsu Hajara ta ji an amsa ta shiga. Kwalliya Hajara take yi anyi
wankan yamma tana shirin fita unguwa, mudubi ne a hannunta tana zana gira. Zuhra ta sakar mata
dundu a baya...shegiya kin hada min zafi a gida kin zauna kwalliya. Hajara na sosa bayanta suka ji
muryar mamanta. Ta shigo dakin haba Zuhra sau nawa za'a hanaki zagi ne? Zuhra ta sunkuyar da kai
tana hararar Hajara. Mama tace idan na sake ji Allah da yayanku Lawal zan hadaki. An kwana biyu ba
kiji bulala ba shiyasa kika dawo da yi mana zagi. Zuhra tace don Allah kiyi hakuri na dena daga yau In
sha Allah. Mama tace da kin kyautawa kanki sannan ta fita. Hajara ta cigaba da kwalliya suna hira
tace ke ni fa Sahabi ya dage sai nayi karatu. Yace zai rinka yi min lesson kafin a fara WAEC don har ya
biya min kudin a wata makarantar. Zuhra tayi dariya zaiyi asarar kudi da lokaci kenan. Baki fada masa
kina sahunmu bane? Bana son wulakanci wallahi tunda na fahimci yana son nayi karatu na soma
dagewa. Wannan karon mutum shida na doke harda ke. Zuhra ta daga hannu alamar jinjina kaga su
Fropesa Hajara kenan. Hala irin su Ligan dinnan zai nema miki. Kanwar Hajara da ke tsakar gida sai
dariya ta leko ta taga...Yaya Zuhra kin fiye abin dariya. Wai Ligan...Legal ake cewa. Zuhra ta hade fuska
tace in ba tsoro ba ki shigo dakin nan ki fada mana kiga yadda zanyi dake. Marar kunya kawai. Hajara
ma dai dariyar take ta dauko dankwali zata daura. Sai da ta daura wani dakal dakal din mayafi
karami. Ta daure shi da ribbons har biyu manya sannan tayi dauri. Daga karshen daurin ta zaro wani
ribbon din mai gashi dogo daga jikinsa ta makala taga ya zauna sosai sannan ta tura shi a jaka. Duk
abinda take idanun Zuhra kyam a kanta. Tace Hajara gashin doki kika koyi sawa? Da sauri Hajara ta
toshe mata baki. To sarkin karadi kada ki fada da karfi sai na fita zan saka. Zuhra tace wallahi babu
kyau kuma kema kin sani. Ga acuci kin dora wannan wari ma ya isheki. Hajara tace ke ba yau zan saka
ba fa. Yanzu ma gidan Anti Faiza zani tayata aikin abincin da zasuyi a makotansu. za'ayi party ne a
gidan. To gobe zansa idan zaa wurin party din. Zuhra tace happy bazday tuyu zasu yi? Oho nima ban
sani ba. Tace dai yan gayu ne a gidan. Zuhra tace duk da haka bani gashin na kona ko na fadawa
Mama.

Da kyar Hajara ta bata ribbon din. Za ta fita Zuhra tace ke kamar kwailin kike ko, kinga fuskarki kuwa?
Sai yanzu na lura. Hajara ta dora hannu a ka. So kike dai Mama taji tayi fada kike wani daga murya.
Kuma bleaching ake cewa ba kwailing ba kalmar ko dadin ji babu. Tana murmuahi tace wani mai na
samu mai dan kyau na gyaran fata. Kinsan tunda biki ya matso gara na shafa na dan washe. Zuhra dai
tabe baki tayi...wallahi Hajara ki kiyaye sabon Allah. Ga acuci, ga bleaching ga karin gashi. Shi Sahabin
zaki ha'inta da farin karya ko danginsa. Naga dai duk a unguwar nan kuka tashi to meye basu sani ba.
Karasa hada jakar tafiyarta tayi tace to malama zuhra idan kin gama waazin ki zo ki rakani bakin titi.
Kuma wallahi kika fadawa su Mama sai munyi fada. Zuhra tace mun dade bamuyi ba...ni akan irin
wannan ba sai dai aji kanmu ba. Lokaci guda kika tsiri irin wadannan abubuwan kawai don zakiyi
aure. Hajara tace to in kinji haushi kema ki fitar da miji mana. Ran Zuhra ya soso ta dan yi murmushi
miji dai Allah ke bayarwa. Kuma da yardarSa idan na tashi aure sai na sami miji na gani na fada. Daga
nan tayi tsaki ta fita Hajara na kiranta tana bata hakuri. A tsakar gida suka tarar da Mama tace har
anyi fadan ne kajin Mama? Ku zo nan...suna harare hararen juna suka durkusa gaban Mama. Tace duk
naji abinda kuke fada. Ke Hajara akan an fada miki gaskiya kike gayawa yar uwarki magana ko? Duk

canjin halin da kika koya yan kwanakin nan ina lura dake. Shiru nayi so nake farin naki yafi haka yawa
sannan nasa yayyanki maza suci ubanki a gidan nan. Zuhra ta kwalo ido....lah Mama kema zagin kike
yi. Mama tace ban kuma ce kiyi ba, nima kuskure ne. Ta cigaba da yiwa Hajara fada kije gidan Yayar
taku ki dawo zanyi maganin rawar kan nan naki. Ita ma ba kyaleki zata yi ba kin sani sarai. Idan na
sake jin kuna fada kuma ni daku ne. Ki wuce ki rakata ta hau adaidaita tace da Zuhra. Sum sum suka
tashi suka fita. Zuhra ke rike da jakar kayan amma har suka je titi ko tari basuyi wa juna ba. Sai da
adaidaita sahun ya fara tafiya Hajara ta leko tana dagawa Zuhra hannu. Itama dagawa take tana
tambayarta yaushe zaki dawo. Hajara tace sai yanzu zaki tambaya? Kwana goma zanyi.....Zuhra harda
dan hawaye ta koma gida. Irin wannan fadan sun saba yin shi da Hajara. Sai dai suna sake haduwa
zancen ya wuce kenan.
[25/09 3:14 pm] Inna��: AL'ADUN WASU🗿4



Batul Mamman(Mrs)💖





Hajara na sallama gidan yayarta ta hadu da babban dan Anti Faiza Abba zaune a bakin kofar gida.
Hannunsa ta gani a nade alamun gyaran karaya ko gocewar kashi. Yana ganinta ya rungumeta A dan
tsorace tace Babana me ya sami hannunka? Yace fadowa nayi daga kan babur din Baba. Ba dai hatsari
kukayi ba ko ta tambayeshi suna shiga cikin gidan. Yace a'a jiya ne da daddare na hau sai na fado. Anti
Faiza na jin muryarsu ta fito tana mata sannu da zuwa. Tace kafin ki fara korafi jiya abin ya faru ni
kuma bana son tadawa Mama hankali sai ya dan ji sauki. Hajara tace ba komai Allah Ya sauwake.
Sauran yaran uku suka zo suna mata sannu da zuwa. Mai bin Abba ce ta kalli Hajara da kyau sai tace
Anti Hajara kinga fuskarki tayi fari, kafarki kuma baka. Ko kema mai bleaching ce irin ta fim dinnan....

Gaban Hajara ya fadi, Anti Faiza ta bar raba kayan wanki da take yi tace bazaki make mata baki ba
kina jin abinda take fada. Nabila ta ce Allah ki kalli kafarta da fuskarta ki gani. Anti Faiza ta taso zata
kaiwa Nabila duka sai taga Hajara na jan siket dinta tana kara rufe kafa. Anti Faiza tace su fita tana
mata wani kallo. Gaba daya cikin Hajara ya duri ruwa. Tun kafin ta tambayeta tace wallahi Mama tayi
min fada dazu kuma bazan kara yi ba. Anti Faiza tace da kina hauka ne kika fara shafe shafe. Ta fizge
jakar kayan Hajara ta zazzageta a wurin tana duba kayan tana fada. Hajara a hankali ta gode Allah da
Zuhra ta karbi ribbon din mai gashi a jiki. Anti Faiza kuwa ta kare mata tas sannan tace ke da Zuhra
kuke yi ko? Hajara tana matsar kwalla tace a'a ni kadai ce. Ba wani nan, abokin barawo ai barawo ne
kuna tare wata rana zata koya ne. Ta fara laluben wayarta. Zan kira Umma ince a turo min ita ko zuwa
asabar ne in ja muku kunne da babban baki. Ba don hannun Abba ba ai gidan zani na hada ku. Wato
kun girma zaku nunawa duniya baku da mafadi. Ita dai Hajara sai bada hakuri take.

Bayan kwana biyu Zuhra na zaune kan karamar kujera a kofar kitchen Umma na ciki tana duba miya
da yar karamar fitilarta gwamnati ta gaza. Zuhra ta rike ciki ta fara waka.

Dan kanzo
Iya ko dan dago dago
Iya yunwa bata da hankali
Iya yunwa taci mutum tara
Iya.....

Umma tace Zuhra ko in miko miki kwano ne? Ta washe baki Umma kin gama girkin. Umma tace a'a
wai da ki

1 / 40