Bin Maryam Book 1 Sadiya Kaoje

Author :  Humaira Bulama Category :  Read Hausa Novels

Chapter   7 / 30

18K to 21K   out of 87.6K words

Zuciyata tun lokacin da Hamza ya sanar da ni cewa ba ki da Aure"

Tun a lokacin nake fama da sonki, ga shi yana nema ya yi min Illa.

Abubuwa da da suka ja Hankalina game da ke,Na dade ban ga macen da ta tara abubuwan da ake so ga mace tagari irinki ba kin haɗu ta kowanne fanni lokacin ɗaya Allah ya sanya min ƙaunarki a raina tare da tausayin ki,

Sunana Kamaludden Aminu shekaru talatin da shidda, mu Ukku ne a wajen Mahaifiyar mu, Kamal, Nasir sai ƴar Autarmu Zainab, Na taɓa yin Aure shekaru Biyar da suka shuɗe, amma Allah ya yi mata rasu wajen Haihuwa tare da abin cikinta tun daga lokacin kuma ban sake yin Aure ba"

"Allah ya jiƙanta da rahama"



"Amin"

"Wallahi Balaraba Aurenki nake son nayi, manufata a gareki Alheri ki manta da Abin da ya faru dake a baya ki ɗauka hakan na daga cikin ƙaddarorinki kuma ki san bawa bai wuce kaddarsa ina son ki fuskanci sabuwar rayuwa, nasan kin san halina a yi ɗan zaman da mu ka yi, ya ki ka gani Maryam!, Don Allah kada jiki Nauhina ki faɗa min gaskiya abin da ke cikin zuciyarki".

Kunya da farin ciki suka haɗu suka cika a Zuciyata, duk da shakkun da take yi akan ƙara yin soyayya da wani ɗa namiji tun bayan makauniyar Soyayya da ta yi da Aliyu, amma yanzu tana da ya ƙinin halin Dr Kamal ba ɗaya da na Aliyu ba, a iya ɗan zaman da su ka yi da shi ba zata ce ga wa Ai'bunsa ba

Lallal wani halin ga Allah baiwa ne ,Dr kamal ya cika ɗan Halak in dai ba butulci ba ta ya zata ce ba ta sonsa mutane da tuntuni ya dade da samu muhimmin matsayi a cikin Zuciyata,

Ta yi shuri cike da tunanin ta kasa ƙwƙƙwaran motsi balle ta ce Uffan, ta kuma kasa ɗagowa ta ta kallesa tunda ta fuskanci hakan ya ke so ku kunyarsa take ji sosai, Dr Kamal ya tausasa Murya idanunsa akan yatsun Hannayenta da take wasa da su zara zara da su farare tas da su sun sha jan lalle,"Maryam kiyi magana mana kin barni ciki zullumi da fargaba, wallahi Maryam duk sanda nazo gidan ku da niyar bayyana mikin sirri Zuciyata nake zuwa, amma tsoro da fargaba ke hanani faɗa sai na tafi da abin a raina saboda ban san irin ƙarɓar da za ki min ba, in jin tsoron reshin amincewar ki, daga ƙarshe naga ɓoyewar ba shi da wani Amfani shi yassa yau na yi ta maza na sanar da ke.

Na san cewa idon na rasa ki Maryam na yi reshin mace tagari, sai dai na yarda na Amince da cewa komi nufi na Allah ne, matar mutum kabarinsa kuma Allah shi ke cusa so a zuƙatan bayinsa ba zan ji haushinki ba don kin ce ban yi Miki ba, zan yi yaƙi da Zuciyata na danne son ki, don Allah Maryam ki buɗe baki kayi magana"

Kalamansa sunyi matukar tasiri a Zuciyata sun kuma ƙara masa girma da ƙima a idanunta, babu Abin da zata cewa Allah sai godiya ya yi mata kyakkyawan sauyi da miji nagari abin so,

Cikin sanyi Muryar ta ce ,"Dr Babu abin da zance, ba zan iya kwatanta Alheri da karamcin da kayi min a rayuwa, tausayi da imaninka sun baka muhimmin matsayi a Zuciyata tuntuni,samun irinka a wannan zamani sai an tona masu yin Abu don Allah ba don wata manufa ba, duk macen da ta sameka a matsayin miji a bokin rayuwa Kuma uban ƴaƴanta to tabbas ta gama dacewa duniya da lahira, halayenka abin so da koyi na yadda kai ɗin wata Rahama ce a gare ni,Allah ya aikomin lokacin da ban taɓa zato ba a lokacin da nake jin cewa bazan sake rayuwar Aure ba, bana son na sake irin makauniyar Soyayya da zata Kaini ga bijirewa iyayen ba, sai gashi a lokacin da na cire tsammani ka ɓullo gareni da kyakkyawar niya idon na ce bana sonka Dr nayi butulci,

Na gode Dr da ƙaunarka a gare ni, ba ni da abin da zan saka maka da shi illa idon na zamo matarka zan dongwama wajen faranta maka har ƙarshen Rayuwata"

Ji ya yi tamkar ya rungumeta saboda murna da farin ciki,bakinsa ya ƙi rufuwa ya kasa natsuwa wata sabuwar ƙaunarta ta fizgesa Balaraba ta ko'ina ta haɗu yadda take tsara lafuzanta ma kwai abin so ne, don ya sake samu tabbacin ƙauna daga gare ta ya dubeta cikin sanyi Murya ya ce,

"Na ji daɗi sosai Maryam da abin da ya fito daga bakinki na kuma gode kwarai da gaske sai dai ina son don Allah ki gaya min da bakinki shin ki na so na, soyayya ba ta dole ko kunya ba,ko kuma saboda abin da nayi miki za ki ce zaki Aure ni babu sona a cikin ranki".

Ta yi saurin girkiza kai tana cewa,"Ko ɗaya Dr tuni Zuciyata ta kamu da sonka tun lokacin da na gane kai ɗin namiji ne nagari abin so mai kyawun hali da iya mu'amala ka san kwayun hali na sanya a so mutum kyawawan halayenka sun taimaka wajen jefa Zuciyata cikin ƙaunarka"

tsabar farin cikin ji ya ke tamkar ya rungumeta, shi kaɗai ya riƙa tsuma ya rinƙa jifanta da Kallonsa mai kashe Zuciya Murya can ƙasan maƙoshi ya ce ,"Na gode sosai, kin sake cika Zuciyata da tarin farin ciki mara misaltawa ke ma ɗin Kyawawan halayenki na ɗaya daga cikin Abin da yaja hankalina akan ki, domin ke ɗin mace kwarai ce da wane namiji zai yi kwaɗayin mallakar ki a matsayin uwar ƴaƴansa bayan tsantsan kyau da Allah ya baki harda kyawun sur......"

Ta yi saurin rufe fuskarta tana dariya tare da faɗin ,"Banda zuga fa"

Dr Kamal ya sake katseta da ,"Gaskiya ce babu maganar zuga ke kyakkyawa ce ta ko wanne Ɓangare, Allah dai ya kika muna burinmu, in sha Allahu za ki same ni bai baki kulawa da tattali da Soyayya har Abada ba zaki yi da nasanin Aure na ba, idon ba da muwa nan da wata ayi bukin mu ina son a haɗeshi da Auren ƙanena da za'ayi"

"Wannan tsakanin ka ne da Baba Ni dai na gama nawa"

"Auww haka ma zaki ce?"

"To me zance bayan wannan?".

"A shirye na ke ko yanzu banƙi a ɗaura muna Aure ba, bana bukatar komi Matata kawai nake buƙata,kin san matsalar gauro wallahi a matse nake sheƙa Biyar Haba! Ki tausawa ɗan Bawon Allah"

Ina ma ƙasa ta tsake ta shige kwai ta huda saboda kunya, Hannayenta biyu ta sa ta rufe fuskarta, "wai kunya ta ki ke ji?, gwara ki ajiye kunyar nan tun yanzu ni da nake son mu gina sabuwar Rayuwa da zata ɗore har abada, idon munyi Aure zamu riƙa Kwana wajen ɗaya muci abinci a plate ɗaya na baki a baki muyi Wonka a tare muyi girki ta re".

duk maganar nan da yake Fuskar Balaraba a rufe take, "Ohh ni Kamaludden yau na samu suruka, tunda ba zaki magana ba zan ta fi Saida safe"

Jin haka yasa ta janye Hannayenta amma ta ƙi yadda su haɗa ido, shi ko sai kallonta ya ke yana Murmushi, "Ki ga yama Baba zan shigo Mu gaida gobe in sha Allahu".

"Allah ya kai mu"

"Amin My Dear!"

Tana tsaye a ƙofar gida har sai ta dena hangen motarsa, A hankali ta sauke Ajiyar zuciya tare da Rungume Hannayenta tana saki tattausar murmushi.

Da gani yadda yake tuƙi kasan yana cikin tsantsan farin ciki, yana isa ƙofar gida ya yi parking a wajen gidan ya fito ya wuce ciki, ƙaton gida ne mai matukar kyau da tsari Ɓangare biyu, Kai tsaye ya wuce Ɓangaren dake gefen daman sa, a hankali ya buɗe ƙofar ya shiga Idanunsa ba su sauka a ko'ina ba sai a kan Aliyu da ke zauna saman kujera ya ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya yana riƙe da Mug da dayan hannusa ɗayan hannu kuma na riƙe da tsadaddiyar wayarsa yana dannawa cike da ƙorewa,

Dr Kamal ya ɗan murza idanunsa ya buɗe akan fuskar Aliyu, cike da mamakin ganin wanda bai taɓa tsammanin ga ba, ya ƙara sa cikin haɗaɗɗen falon da sha kayan Alatu ya nemi waje ya zauna yana kallon Aliyu, "Hajiya wai Aliyu ne ko idanuna ne ke min gizo?".



Wata kyakkyawar tsohuwa dake zaune kusa da Aliyu ta killi Dr Kamal ta ce,"Aliyu ne Kamal ba gizo ba".

"Haba! Ni wonder yau Aka tashi da sanyi sanyi Ashe comrade Aliyu ne zai zo, Wallahi Hajiya rabon da nasa Aliyu a idona kusan shekara biyu kenan, muna gari ɗaya Wallahi Aliyu sam baka da kirki"

Aliyu ya Kallesa ya taɓe baki,

"Iyakarka kenan ban dai buga ga re ka,

"Malam kana cika min kunne da surutu"

Hajiya ta kallesu ya yi Murmushi tana faɗin,"ku kan dai ba ku rabuwa da rigama duk kuka haɗu sai kunyi rigama"

"Hajiya Wallahi Aliyu ya rena ni, kusan sheka biyu na ba shi, amma ki duba yadda yake sako min magana kaman wani ƙanensa"

dai dai lokacin Sumayya ta fito ɗaki tare da Zainab ƙanwarsu Dr Kamal har ƙasa suka duka suka gaida Dr Kamal,"Yah Kamal sannu da zuwa"

"Yauwa my Sister's"

Ya faɗa fuska a sake,

"Sumayya ina Gwoggo Laila?"

"Tana Ɓangaren Mommy"

dai dai lokacin kuma Su Mama suka shigo falon,

"Gwaggo Ina wuni"

Dr Kamal ya kaɗa cikin girmamawa,"Lafiya lau Kamal ya Aika?".

"Alhamdulillahi gwoggo ina su Twins?"

"Suna Ɓangaren Anty Aysha ta re Nasir"

"Gwaggo a she tare ku ke da Comrade"

Mama ta kalli Aliyu dake zauna,ita kam ma bata san da zuwan sa ba,

"Wai Aliyu ne can Zaune?"

Cewar Mommy,

"Shine Mommy"

Dr Kamal ya bata amsa,

"Ikon Allah wallahi rabon da na ga Aliyu a gidan nan har na manta"



tare suka ƙarasa cikin falon suka zauna,

"Ina wuni"

ya faɗa ba tare da ya ɗago ya kallesu ba,

"Lafiya lau Aliyu ya kwana da ya yawa?".

"Lafiya lau"

ya ɗan ɗago ya kalli mama, ita ma shi take kallo,"Mama! Ina wuni"

"Lafiya"

ta bashi amsa a sanyaye,

dai dai lokacin Su Twins da suka shigo tare da wani kyakkyawan saurayi kamanninsu ɗaya da Dr Kamal sai dai shi ya fi Dr Kamal yarinta, ga baki dayan su suka haɗa bakin wajen gaishe su,"Yah Kamal Yah Aliyu Ina wunin ku"

Kamal ne kawal ya amsa musu, Aliyu kam ko kallon inda suke bai yi ba,

"Sumayya ke kam ki ce wajen Nasir ki ka zo".

"Sumayya ta rufe ido cike da kunya ta ce,"Aa wallahi Yah Kamal"

Ai basai kin rantse ba, ke da gidan ku yarinyar da aka yaye a gidan nan".

"tunda haka ne ga ga ɓangaren ta can sai ta tare"

Sumayya ta kalli Nasir ta sunkuyar da kai ƙasa ta na Murmushi,

"Bana son sa ido fa kana ta kuramin ƴa da yawa"

"Wace wainaar kike toyawa ƙamshi ya shika ko'ina a gidan nan"

dariya sukayi gabaki ɗayan su banda Aliyu, dottijawa ne guda biyu sanye da Jallabiya, Dr Kamal da Nasir kuka miƙe tsaye suka taimaka ɗan dottijon ya zauna saman lallausar kujera chaise lounge dake cikin falon ya ɗan shin giɗa gareta riƙe da sandarsa agefe,"Bappa" sannu da zuwa suka faɗa a tare,

"Dady sannu da zuwa"

"Yauwa Twins Sumayya kuna lafiya?"

"Lafiya lau Uncle"

"Uncle sannu da zuwa"

"A'a wai Aliyu ne nake gani haka?"

"Shi ne Dady"

"Ikon Allah!, Aliyu ya kwana dubu"

"Alhamdulillahi Uncle"

"Yaya Sannu da zuwa"

"Yauwa Laila ya mai gidan ki?"

"Lafiya lau ya ke"



"Ma sha Allah, tun yaushe kuka shigo Hlm?"

"Bayan maggariba"

Bayan sun gama gaisawa Dr Kamal ya yi gyaran murya tare da faɗin,"Dady na samu matar Aure har mun dai dai tsakanin mu manya kwai suka rage shi shiga"

"Bappa ya ɗago yana faɗin,"ma sha Allah, ko kai fa Ina yarinyar ta ke, "Bazawa race Bappa amma tana da Hankali da natsuwa sosai".

Aliyu ya ɗan ɗago ya Kallesa yana taɓe baki,

Ina son idon Abubuwa suka dai dai ta a haɗa Aurenmu da na su Sumayya domin samun sauƙi"

"Haka ma za'ayi in Sha Allahu" cewar Hajiya, Allah ya tabbatar da Alheri"

"Amin Hajiya"

Mama ta faɗa tana Murmushi,

Sauran ƙanne suka taya shi

maurna da fatan Alheri...........✍️

*More comments and share pls!*

*Sadeeya Ka'oje ce 💋✍️*

💋𝐁𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐘𝐀𝐌💋

𝑵𝒂

𝑺𝒂𝒅𝒆𝒆𝒚𝒂 𝑲𝒂'𝒐𝒋𝒆

08149979652

https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj

𝑷𝒂𝐠𝐞 13-14

_______Sauran ƙanne suka taya shi

maurna da fatan Alheri,

"Na gode sosai, Gwoggo zan tura miki kuɗi ki haɗa min kayan lefe da kayan ɗaki"

"Me ya samu kayan gidan"

"Gwaggo kayan sun tsufa"



"Ina wani tsufa Kamal ba sheka biyu kenan da ka sauya kayan gida ba? zanje gidan na duba duk Abin da ya kama a sauya sai A sauya shi, tunda ɗaki huɗu ne sai aka tsoffin kadaje a ɗaki biyu, biyun kuma sai kasa sabbin kaya"

"Gwaggo aiki duka ɗaku nan da falo akwai kaya a ciki kuma duk sabbine ban jima da canza su ba"

"To tunda haka ne ba sai an sauya ko mi ba"

"Ita Amarya ta saka nata ina?"

"Ai na ɗauke mata komi saboda iyayenta ba masu ƙarfi ne ba"

"Tunda haka ne A sauya kayan Babban falo ya isa, Lefe kuma na ɗauke ma ni zan haɗa tawa gudummawar kenan"

"A'a gwaggo karmuyi haka da ke pls"

Mama ta yi Murmushi tana faɗin ,"Ka re na kenan?"

Ya yi saurin girkiza kai yana faɗin ,"A'a wallahi gwaggo, na gode sosai Allah ya saka da Alheri"

Suka amsa da "Amin"

"Gwaggo idon an cire kujerun falo na aba Sumayya gudummawa ta kenan a matsayin na na Babban Yayan Amarya" ya ƙara sa maganar cike da zolaya,

Gabaki ɗayan su suka sanya Dariya, Mama ta ce,"An ko gode kaga sabbin da a ka yasa mata sai abaka kai kuma"

Nan ma suka sake yin dariya,

Mommy ta kalli Mama ta ce,"Sannu da ƙoƙari Allah ya saka da Alheri"

"Haba Aunty Aysha miye na godiya Kamal Ɗa nane idon banyi masa ba wa zanyi wa? Kamal tamkar ɗan da na haifa ne da ni da Ubansa Uwa ɗaya uba ɗaya"

Hajiya ta ce,"Mahaifiyarsa kuma Babbar Aniyarki"

Mommy da mama sukayi Murmushi,

Aysha da Laila tare suka taso tun suna yara tare suka yi Primary da University ko da yaushe suna tare komin irin ɗaya kaman ƴan biyu,ko Hutu suka samu a makaranta giɗa suka suke hutunsu gidansu Laila ko gidan su Aysha, da haka har Soyayya ta shiga tsakanin Aysha da Aminu tun daga lokacin kuma Laila ta koma kiran Aysha Anty saboda Aminu kusan lokaci ɗaya akayi Auren. kuma har yanzu ƙawancen su na nan ba abin da sauya sai dai su da suka manyanta,

"Zainab Hanifah ku je ku ɗauko abinci"

tare suka mike zuwa Ɓangaren Mommy ɗin Hanafi ya mara musu baya, kuloli ne n Alfarma kusan kuda Ukk suka aje su a tsakiyar falon,tuwan shinkafa ne da miyar kuka ta musamman sai soyayyen Naman kaji, haka suka ci Abinci cikin nishaɗi da farin ciki banda Aliyu,

Bayan sun gana cin Abinci su Zainab suka tattara wajen,Hira suka ɗan taɓa kafi nan Mama tayi musu sallama,"Hajiya zamu tafi, Anty Aysha, Yaya, Bappa, Saida safenku"

"Laila har zaku wuce?"

7 / 30