Bin Maryam Book 1 Sadiya Kaoje

Author :  Humaira Bulama Category :  Read Hausa Novels

Chapter   26 / 30

75K to 78K   out of 87.6K words

komi Abba....."

"Kaman ya ba komi, me aka masa?" Abba ya fa ɗa yana kallon Ummy" nan ta zaiya Nana komi"

"Abba ya saki murmushi tare da faɗin,"Ai gaskiya ya faɗa ba muharramarsa ba ce kin san sheɗan komi zai iya faruwa.

"Am.... ma.....ai..." Ya isa pls kira Nainah ɗin ta fito, Ba musu Ummy ta kwala mata kira,"Nainah..."

"Na'am Ummy"

"Barin gyaran ɗakin nan Afra zata ƙara sa"

Asad be sake cewa komai ya nufi falo ya zauna a sofar da ke kusa da kofar yana ta huci kamar wani kaman wani baƙin kumurci....

Abba ya kalli Ummy ya ce,"Abin da ki ke bai da ce ba kina ja Mishi reni a wajen ƙannensa."

"Ai shine ba ya riƙe girmansa taya zai riƙa shiga abin da bai shafe sa ba, ni ban san me yasa ya kwana gidan nan ba"

"Yaro da gidan Ubansa"

"To wallahi ya fita har kar ƴaƴana idon ba haka ba zan ɗau mummunan mataki a kansa, ya bi duk ya takura basu da sakewa idon ya na kusa, shi sai ka ce ta kurasan a ke"

"Wai me ya yi zafi haka Ummy Asad?"

Ummy ta dalla mishi harara tana ji gaba da jininta sai da ta yi mai isarta sannan Dr Kamal ya ja Hannunta suka wuce ɗaki....

Bayan la'asar Su Ummy na zaune a falo suna kallo har da Amma, Anty Amarya ta shigo tare da Ramla,"maraba da baƙi Anty Rashida ke ce a gidan namu yau?"

ta Kirata da Anty badon ta girmeta ba sai don tana matsayin matar ƴaƴanta, Har ƙasa Ramla ta durƙusa ta gaida Ummy.

Fuska a sake Ummy ta amsa mata.

Dai dai lokacin Nainah ta fito daga ɗakin Afree, Cak ta tsaya tana kallon su, suma ita suke kallo Ramla sai hararta ta ce, A hankali ta ƙaraso cikin falon tana faɗin ,"Ina wunin ku"

Suka amsa mata ba yabo ba fallasa.

"Hajjiya zan tafi" Amma ta faɗa tana ƙoƙarin barin falon, "Ai da kin zauna matar yaya nace yan gida ne duka.



"Bari kawai na tafi" Ummy ta batun magana Anty Amarya ta katse ta ta ce,"Ummy Asad ki barta ta tafi"

Amma kam tanu ma ta fice daga falon,

"Nainah kawo musu ruwa"

"Ai a ƙoshe muke daga gidan wata friend ɗin ta nake nan bayan layin ku shine na ce bari na biyo mu gaisa"

"Allah sarki aiko na gode, kwanan nan nake waken zuwa gida, Allah bai ƙaddara ba."

"Ai ko wa dai kin ɗan jima baki je gida ba"

"Ramla ya makaranta?"

"Alhamdulillahi Ummy"

"Ai ta gama karatu kusan wata Biyu ma kenan" cewar Anty Amarya.

"Ma sha Allahu,Allah ya taimaka ya bada Sa'a, sai Aure yanzu kam ko?"

Ramla ta sunkuyar da kai alamun kunya. Ummy ta yi Murmushi.

Daga nan kuma hira ta ɓarke tsakani Ummy da Anty Amarya har zuwa lokacin sallah maggariba sannan Ummy ta wuce da ita ɗakinta domin ta yi Salla

Ramla kuma ta wuce ɗakin Afra tayi Alwala ta kabbarta salla,

"Innalillahi wa'inna Ilaihir raji'un Me zan gani haka? Afra waya shigo ɗakin nan bayan na shiga toilet?"

"Lafiya me ya faru?"

"Zoben zinarina da na aje saman mirror ban ganshi ba"

"Zoben Zinari?"

"Ehhh zan shiga toilet na cire shi tare da abin hannu yanzu na duba ban Ganshi ba"

"Da ina falo naga kaman Nainah ta shigo ɗakin nan Amma bana tunani zata ɗauƙi zaɓen sai dai idon faduwa ya yi ƙasa"

"Wallahi bai faɗi ba sai da na tabbatar ya zauna da sannan na shiga toilet kuma a tsakiyar mirror na ajeshi ba gefe ba balle a ce ya faɗi"

"Anty Ramla ki duba dai da kyau maybe ya faɗi ƙasa baki gani ba"

Nan take Suka hargitse ɗakin wajen neman zobe lungu da saƙo na ɗakin ba inda ba su leƙa ba, ba zobe ba labarin sa,

Ana cikin haka Ummy ta shigo dakin tana faɗin,"Ramla ki fito ku wuce Anty Rashida na jiran....." Maganar ta maƙale mata a baki ta tsaya Cak tana kallon Afra da Ramla ,"Lafiya? Me samun ɗakin?"

Afra ta faɗa mata abin ke faruwa.

"Ramla kin tabbatar kin a je zobe?"

Murya na rawa Ramla ta ce,"Wallahi Ummy da hannuna na aje shi saman mirror"

"Ikon Allah"

Ana cikin haka Nainah da Afreen suka shigo ɗin, da mugun sauri Ralma ta nufi wajen Nainah ta kama wuyar rigarta tana faɗin ,"Bani zobe na da kika ɗauka"

Da wani rin mugun mamaki Nainah take kallon Ramla,"wane Zobe?"

"Anty Ramla don Allah mubi a bin nan a hankali" cewar Afra.

"Ɓarauniya na ce ki bani zoben da kika ɗauka"

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, ni kuma? ban ɗauka ba, Wallahi ban dauka ba"

"Waya shigo ɗakin nan bayan ke?"

Hawaye ya fara mata zuba tamkar an kunna fonfo

"Anty Ramla wallahi ban ɗauka Miki zobe ba, kuma da kike maganar na shigo dakin nan zuwa nayi na ɗauki hijabi na, don Allah karku min haka wallahi ban taɓa yin sata ba"

Ummy ta yi saurin kiran Nainah dake kuka kamar zata ranta zai fita,

"Nainah ki Dena kuka, Ramla ki sake ta, nawa ki ka saiyi zoben naki? a biya ki"

"Ɓarauniya nan ma Saida ki ka kai halin na ki ko, Ɓarawo dai bai ji daɗin duniya ba", cewar Anty Amarya.

"Ummy na rantse da Allah ban ɗaukan mata zobe ba"

"Nainah ina son ki fada min gaskiya, na san baki taba min karya ba, ke kika ɗauki zoben?"

"Ummy..... wallahi ban ɗauka ba!" ta faɗa marya na rawa.

"Munafuka wazai ɗauki zoben bayan ke, Ai tsintacciyar mage bata mage"

"Rashida ya isa!"

Ummy ta faɗa cikin tsawa.

Basu an kara ba kwai suka ji ihun Nainah koda suka juyo Ramla na kai mata duka ta ko'ina a jikinta tana faɗin Ɓarauniyar wallahi sai kin fitomin da zobe na"

Sai kuma ta tsaya Cak daga dukan Nainah da take ta fara tsalle tana ihu tana soshe soshe kaman wata marar hankali kuka take sosai mai haɗe da ihu, cikin ƙanƙanen lokaci ta fara fita haiyacinta gabaki dayan zuka zuba mata ido suna kallon ikon Allah.

"Innalillahi wa'inna Ilaihir raji'un na shiga ukku na lalace" haka ta riƙa sambatu.

Hankalin Anty Amarya ta yi Masifar ta shi ganin halin da kanwarta ta ke ci, kan kace kabo Ramla ta fara yaga kayan jikinta sai ga zobe ya fado kasa, ga manya manyan kuna baƙaken ƙirrin manne a jikinta ta ko'ina

"Innalillahi wa'inna Ilaihir raji'un!! KunamuA jikin Ramla"

Da sauri Afree ta nufin wajen da zoben ya faɗin ta ɗauka tana faɗin "wannan ai shine zoben da aka nema"

Nan take kunamun suka ɓace ɓat a jikin Ramla kaman anyi ruwa an ɗauke, da matsanancin gudu ta fice daga daga dakin Anty Amarya ta mara mata baya.....

A fusace Ummy ta juyo tana kallon Afra da Afreen tana faɗin,"Ba na hanaku yin ƙohi ba?"

"Ummy wallahi ba mu ne ba!"

"Kaman ya ba kune ba waye ƴan biyu a gidan bayan ku..............✍️

An yanka ta tashi 😂😂😂😂😂😂

More comments and share pls!

*Sadeeya Ka'oje ce 💋✍️*

💋𝐁𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐘𝐀𝐌💋

𝑵𝒂

𝑺𝒂𝒅𝒆𝒆𝒚𝒂 𝑲𝒂'𝒐𝒋𝒆

08149979652

https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj

PAID BOOK

Littafin *BIN MARYAM* na kudine akan 500 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652. Nagode🤗

𝑷𝒂𝐠𝐞 45-46

______"Na ce su waye ƴan biyu a gidan nan bayan ku? Na hanaku yin ƙoyin nan Amma ba zaku dena ba ko? Kun maidani mutuniyar ban za ko?" da ganin yadda take maganar aka a hasale take.

"Ummy wallahi ba ni ce sai dai idon Afra ce" Afreen ta yi maganar tana nuna Afra.

Da sauri ta girgiza kai tana faɗin ,"Ummy wallahi ba ni ce ba"

"Karku renamin da hankali"

"Afra ta ce ,"Wallahi tallahi+³ ba ni ce ba" kaman yadda Afra ta rantse haka ita ma Afreen ta rantse kan cewa ba ita ta ai kata ba.

Afreen ta ce,"Ummi Allah ne ya nuna mata abin ta, wata ƙila ma kunamun sun jima a jikin bata sani ba"

",Allah ya Kyau ta"

"Amin Ummi"

gaba ki ɗaya suka nufi wajen da Nainah take durƙushe tana kuka. Ummy ta rungumeta a jikinta tana share mata hawaye tana faɗin ,"Kiyi haƙuri Kinji Nainah,"

"Ba komi Ummy"

"Yauwa yar Albarka" Ummy ta faɗa tana shafa kumatunta.

"Ta shi muje ki wonke fuskarki, sannan kar ki bari Amma ta fahimci wani abu ya faru".

"Toh Ummy"

Har bakin toilet ɗin Ummy ta kaita ta wonke fuskarta sannan suka wuce falo, wayar Afreen dake Ringing yasa ta nufi wajen da wayar take da sauri ta ɗaga tana faɗin ,"Ya Deedat ina wuni?" daga can Ɓangaren ya ce,"lafiya lau, Ina Nainah? ina son magana da ita"

Afra ta zaro ido tunawa da gargaɗin da Asad ya yi mata, sai ta fara inda inda tana ,"Ya Deedat daman...." Ummy tayi sauri cewa Bata wayar".

Afra ta miƙa ma Nainah wayar ta koma can gefe tana magana, dagani yadda ta ke maganar kasan cewa tana cikin farin ciki.

dai dai lokacin Asad ya shi go falon, fuska a ɗaure kamar ko yau she, kai tsaye ya wuce wajen Nainah.

Cikin tsawa ya ce,"Ba ni wayar"

Bata ba shi ba ta tsaya tana kallon sa ya sake daka mata tsawa.

"Ki ba ni wayar na ce....!"

A razane ta mika masa wayar idonta na kokarin cika da hawaye.

"Gashi"

Dagowa yai ya kalleta kamin ya kai hannu ya karbi wayar ya buga ta da kasa iya karfinsa a take wayar ta watse Nainah kuma tai ihu tai baya Jikinta na rawa a zatonta wani abun zai mata.

"Karka sake daka mata tsawa balle kuma ka ce zaka nuna nata dan yatsa, bata jidadi a wani gurin ba ba zaka zo nan ka hana ta ba, abunda kake yi ma kannenka da kowa ita ba zan daukar maka ba, don haka ka kiyaye ni"

Ummy ta fada tana nuna shi da yatsa cike da jin haushin yadda ya yima Nainah, dafe kansa yai a gurin har yanzu gumin bacin rai ne yake sauko masa.

Duk abin ke faruwa kafin watsewar Wayar Deedat na sauraren su......

*DEEDAT*

Ransa be taba baci kamar yau ba, ya rasa dalilin daya saka Asad yake shigar masa hanci, iyakar abunda ya sani yana son Nainah saboda tana kyau kuma ya san ba haramun bane son mace mai kyau Nainah ta kai mace da za a kalleta a so ta, daman ya dade yana son aure mace mai kyau, bayan so na aure ba shi da wata manufa ga Nainah amman yadda Asad yake masa ya sashi jin haushi sosai,a yanzu ne ya shirya taba ta ko kebewa da ita da kuma neman aurenta domin ya lura kamar Asad yana kishi ne, ba taba ta ko kebewa da ita kawai ba ya dauki alwashin har Runguma da kiss sai ya mata a gaban Asad sai dai idan mutuwa zan yi ya mutu idan kuma ya fusata shi sai ya yi mai gaba daya daman dai aurenta zai yi dan haka yana jin ko kaiwa yai a jikinta ba wani abun ba ne face samun damar da zai saka duk wani da zai masa karan tsaye ya amince da aureta dole.......

"Baba na!"

Ummy ta kira shi da karfi jin tana ta kiransa kadan be amsa ba yana can wata duniyar yana tunani. Kallonta yai sai yai murmushi, murmushi da ke ƙara ma kyakkyawar fuskarsa kyau da kamala.

"Na'am Ummy"

"Ina ta magana baka ji ni ba, lafiya dai?"

"Ba lafiya ba Ummy, abunda Asad yake min ne bana jindadinsa akan yarinyar nan don Allah ki gaya masa ya dena"

Ummy ta zauna a kujerar dake kusa da tashi.

"Mi yake maka? Baba na"

"Ummy bana da halin nai magana da yarinyar ko na kebe da ita sai ya saka zargi, kuma wallahi Allah ya sani bana da wani manufa akanta bace na aurenta da zanyi.

Da mamaki Momy ta kalleshi.

"Aure kuma? Baba na"

"Eh Ummy na taba fada mata tun a lokacin da take gidan Iya ina sonta,ina son ta Ummy dan Allah ki shige min gaba"

Ya fada yana wani marairaicewa kamar zai saka kuka.Maganar sam ba tai ma Ummy dadi ba sai dai ba zata muna nuna masa ba.

"Baba na yarinyar nan yanzu ba soyayya ko aure ne a gabanta ba, ta mahaifiyarta take duk dai Alhamdulillahi ta samu lafiya.

"Na sani Ummy, ni ma ban yanzu nake nufi ba, sai hankali ya kwanta, ke kadai zan iya rikewa domin ke nake da tabbacin za ki share min hawaye na"

"In Sha Allah ni mai maka komi ce Baba na".

"Ummy ina Nainah ta ke?"

"Tana ɗaki". da ga zaune da take ta kwala mata kira sai gata ta fito tana dan sauri sauri sai. ta tsaya Cak tana kallon wanda bata yi tsammanin ganinsa a dai dai wannan lokaci ba,

"Ƙaraso mana"

Cewar Ummy tana Murmushi.

A hankali ta ƙara so cikin falon ta zauna Ummy kuma ta wuce ɗakinta tabarsu.

"Beauty ya jikin Amma?"

"Jiki Alhamdulillahi"

"Ma sha Allah" Ya fada yana murmushi ita kuma ta yi kasa da kanta,

"Junainah.. Sauda dama nakanji Zuciyata tamkar zata fashe, amma sai na kasa ɗaukar ko wane irin mataki, ya na yin Sonki ne ya cika Zuciyata yanzu kuma so yake ya fasata don Allah kiji tausayina duk runtsi karki gujeni wallahi ina sonki Nainah son da ban taɓa yiwa wata halitta ba"

Wani irin sanyi jikinta ya yi saboda kalamansa sunyi Masifar kayar mata jiki.

"Ga wannan" ya faɗa yana miƙa mata wani ɗan ƙaramin kwali mai kyau ya sha ado.

"Ki buɗe ki gani"

Ta dago na kalleshi.

"Bude kwalin pls

Ta bude kamar yadda ya bukata wani kyakkyawan zobe ta fara cin karo da shi,

"Ban san size din yatsunki ba amman na san Zaiyi miki, "Zoben minene?"

"Na zinari ne"

Wani tsoron ta ji ya kamata daman tunda taga yanayin zoben ma dauka cewar na zinari ne, sai dai rashin sanin hakikanin zinarin yasa bata yi saurin yenke hukunci ba har sai da ya fada mata.

"Ni ko Azurfa ban taɓa sakawa ba balle zinari"

"Kisa a ranki daga yau kin fara kenan, ke din ai matar manya ce Nainah..."

"Amman....!"

"Pls Karki ce komai Nainah ki saka dan Allah!"

Bude akwatin zoben tai ta fiddo daga ciki, sai da ta kalli Deedat sannan ta saka zoben tana hade yawu gabanta na bugawa da mugun karfi. Wani irin abu ta ji ya ratsa ta, wata irin daraja da daukaka suka cika mata ido, saurin cire zoben tai hawaye na sauko mata masu Masifar zafi.

" Ya Deedat Ba zan iya sakawa ba ka yi hakuri don Allah"

"Nainah ba zan cilasta ki ba amman ki aje shi a gurinki, zaiyi Miki amfani anan gaba"

ta gyada kai tana share hawaye.

"Zan wuce sai da safe"

Murya na rawa ta ce," Állah ya tsare"

"Amin"

Yana fita ta fashe da wani irin kuka.

ji kamshin turaren Asad wani irin turare mai kwnatar da hankali da saka nishadin ruhi,tana jindadin shakar kanshin sosai fiye da komai a yanzu. Da sallama ya shigo falon bata amsa masa ba ta miƙe da sauri ta fice daga falon garin saurin da take ta buge shi kwalin zoben ya faɗi bata bi ta kansa ba ta fice da gudu zuwa Bq.

Da wani irin kallon tuhuma ya biya kafin ya juyo inda kwallin yake ya durƙusa ƙasa ya ɗauki kwallin yana juya shi, yana mamakin ina ta same shi saboda ya gane kwallin miye......

"Waya bata zobe?"

Shine abunda ya fara zuwa masa a rai, Deedat ya fara tunanin sai kuma yake ganin kamar ba zai yi wannan shirmen ba, da sauri ya fice wajen zuwa wajen motarsa ya shiga...

Da tunanin wanda ya bata zoben ya kwana a ransa, washegari misalin ƙarfe takwas da rabi na safe ya shirya cikin kananna kaya ya nufo dinning area, rasa yai mi zai a gurin sai kawai ya koma ɗaki ya dauko keys din motarsa ya shiga ya dauki hanyar gidan Ummy. Nainah ce kawai a falon tana gyara Ummy kuma tana kitchen, ba karamin dadi ya ji na samun Nainah ita kadai a falon ba, daman yana son ya tambaye wanda ya bata zoben.

"Ina kwana"

Ta dan risina tana gaishenshi be amsa ba har ya karaso kusa da ita.

"Kina da wani a ranki wanda kike so? Fada min karki baye komai?"

Wani kallo tai masa kamar bata fahimci abunda yake nufi ba

"akwai wanda kike so a ranki?" Ya jefo mata tambatayar a karo na biyu.

"Ya Deedat.....!"

Da mamaki ƙara a fuskarsa ya sake jefo mata wata tambatayar.

"Deedat kike so?"

Ta yi shiru bata sake cewa komai ba. Sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro kwalin zoben ya nuna mata.

"Shi ya baki wannan zoben"

Sai tai shuru bata ce komai ba.

"Yanzu ke har kin san soyayya?"

“Ba son sa na ke soyayya ba, kawai dai ina jindadi idan na tuna dan zaman da muka yi lokacin da nake gidansu, a koda yaushe yana ƙoƙarin wajen sani farin ciki"

"Waya baki zoben?"

tana ƙoƙarin

26 / 30