Author : Humaira Bulama Category : Read Hausa Novels
Murja, a riki ce ya ce ,"M....e.....ki....kace? Sake faɗa Naji"
"Bana son warin turar......" ta miƙe da sauri ta nufi toilet tana sheƙa Amai kaman zata Amaye hanjin cikinta, da kyar ta gyara Jikinta ta fito toilet kallo ɗaya zaka yi mata kasan A wahalce take,
Wani irin kallon walaƙanci yake jifanta da shi,
Durowar dake kusan dashi ya buɗe ya fito da Pregnancy test strip tare da faɗin je ki kawo min fitsarin ki". Yadda ya yi maganar ba Alamu wasa, hakan yasa ta nufi toilet ba tare da ta kawo komi a ranta ba, sai dai ya nayin da ta ga Aliyu ya ɗan tsoratar da ita, jim kaɗan ta fito riƙe da ɗan ƙaramin cup ta miƙama Aliyu kana ta zauna gefen gado saboda jiri jiri da take gani. cikin ya nayin ƙama ya saka ɗan tsinken cikin fitsarin cikin Abinda bai gasa sekon talatin jan lati biyu suka bayya ɓaro ɓaro,
A fusace Aliyu ya juyo yana kallon, kallon da ya yi matukar tada mata Hankali,
"Cikin a gidan nan?"
Murja ta yi rau rau da idanu yana kallonsa,
“Murja ci ke ne da ke!?"
Murja ta sauke Ajiyar zuciya tare da Faɗin "Alhamdulillah! Allah na godema".
"Kije na sake ki saki Biyu"
A ɗimauce ta dago idanunta tana kallonsa cike da razana Abun yazo mata a bazata Muryarta na rawa ta, "me...... Ka......ce..... Aliyu..."
A tsawace ya ce ,"Abin da kunnanki ya jiye miki da shi na faɗa, tun Asali ban taɓa jin Sonki a raina ba, dama can sha'awarkice ta sanya na Aure ki domin na more hakan ta sanya na nemi Soyayyarki Amman zuwa yanzu soyayya ta ƙare domin na gama dake da baki yi cikin nan ba wata ƙil zan fara son ki a hankali, Amman kashh! Aiki gama ya gama".
Murja ta riƙa girgizar kanta cike da ɗimuwa a ganinta marki ne take ba gaske ba ne, Aliyu ne ke faɗa mata gugayen kalaman nan masu ɗaci haka, "Innalillahi wa'inna Ilaihir raji'un! Wannan wace irin masifa ce wane irin bala'i ne yake shirin faruwa da ita? Wani irin kuka ya kwace mata murya na rawa ta faɗin,"
"Aliyu kada ka yi min haka Don Allah idon ma wasa kace kace ka Dena don Allah karka yaudareni ka tausawa mareniyar ALLAH! Aliyu!Aliyu Don Allah ka janye furucin sakin nan!"
ta sake sakin wani kukan ya gyara tsayuwarsa sosai yana cewa,"Ba kuka zaki tsaya kina yi min ba Malama, gabaki ɗaya kinsan Ni bana gama biyu don haka tun wuri ki kama kank ki fice min daga gidan nan ki manta ma da kin taɓa son wani Aliyu A duniya".
Yana gama faɗin haka ya juya ya fice daga ɗakin.
Ya barta durƙushe a wajen tana kuka mai tsuma zuciya Hannayenta dafe da kanta dake tsakanin saramata kaman zai bare biyu, shi kenan Aliyu ya rabu da ita, yau ta shiga Ukku!!!"
Tafi ƙarfi Awa biyu durƙushe a wajen bata san inda kanta yake ba da kyar ta miƙe tsaye jiri jiri na ɗibarta ta tattara kayanta ta saka cikin A kwati ta fice daga gidan tana kuka, A kan idon malam Musu ta fice, girgiza kai ya yi tare da faɗin ,"Allah ya kyauta".
Cikin Sa'a tana fita ta samu Abin hawa ta shiga, Saida suka fita daga shiyar ta faɗa mishi inda zai kaita dafe da kanta da ƙirjinta da take jin kaman zai rabe biyu, saboda tashin hankalin da take ciki akan Binda Aliyu ya yi mata,
Koda Suka iso bata sani ba Saida mai Adaidaita ya yi mata magana kusan so Ukku shuru hakan yasa ya juyo ya sameta a sanƙare a gigice mai Adaidaita ya fito yana faɗin,"Innalillahi wa'inna Ilaihir raji'un!! Na shiga Ukku!! Jama'a ku taimaka min Wallahi bani na kashe ba! Lafiya lau tashiga keken Mai Adaidaita ga baki ɗaya ya firgice sai surutai yake na fitar Hankali, Samarin Shiya suka nufo wajensa gadan gadan, "Murjanatu ce ƙanwar Oga TK". Sai suka ruga da gudu wajen Oga TK, zaune suka samehi yana zukar taba tare da wasu samari dogo ne baƙi Amman ba sosai ba bakinsa duk ya yi bakin saboda shan taba idanunsa jawur da su, "Oga TK Murjanatu ta mutu a Adaidaita".
Da ƙarfi wanda aka kira da Oga TK ya mike tsaye tare da zaro yuƙa a jikinsa Baki a karkace yace ,"Murjanatu ta mutu a Adaidaita?"
Ya wuce da sauri sauran yaronsa suka mara masa baya,
Suna isa Oga TK ya kalli Murja dake sanƙare a wajen ɗaya, Ya runtse idanunsa Zuciyarsa na tafarfasa,
"Kai ka kashe min Ƙanwa? Yau saidai babarka ta Hai......."
Da kyar mai Adaidaita ya kwace kansa daga rikon da Oga TK ya yi masa yana faɗin ,"Wallahi daga Gesse pess I na dauƙota ita tace na kawo ta nan Saida muka iso na ganta a haka".
da ganin ganin yadda yake magana kasan ce wa a firgice yake,
Dada ta saka kuka tana faɗin,"Tukur ba hayaniya zamu tsaya Ni ba mu kaita Asbiti,"Dada shiga mu tafi"
Nan da nan suka shiga A daidaita suka nufi F.M.C. da ita suna isa aka karɓe ta sai yanzu suka lura da jinin da ke fitowa a jikinta, likitoci suka rufa a kanta domin ceto rayuwarta da Abin cikin, duk iya ƙoƙarin da likitoci sukayi domin ganin sun ceto Abin cikinta Abu ya gagara, sunsha wahala sosai wajen ganin Murja ta farfaɗo, ya ran TK suka riƙe mai Adaidaita da ya ɗauki ta suna zargin wani Abun ya yi mata shiyassa suka damƙe shi har sai ta farfaɗo, Bayan Awa Biyu Likita ya fito ya sanar sunyi nasanr ceto rayuwarta Amman Ana rasa Abin cikinta, ya ce su shiga su dubata don kuka take ta natsuwa sai surutai take da gudu suka wuce ɗakin da take Kwance tun kafin su iso suke jiyo ihunta tana faɗin ,"Aliyu ka cuceni kaci Amanata Allah ya yi min Sakayya Bazan taɓa yafe kama ba har duniya ta naɗe!".
"Dada ta damƙi kanta ta mata Addu'a a hankalinta a tashe da niyar ta Dena kuka sai kuma wani kukan ya kwace mata, Dada ta zauna a gefenta tana lallashinta, tana share kwalla ta ce,"Murjanatu kiyi haƙuri ki Dena kukan kiyi muna bayani mi ke faruwa, mai A daidaita sahu ne ya yi Miki wani Abu? Tk ya tambaye, kai ta girkiza ,"Yah Tukur ba ruwansa Aliyu ne!".sai ta sake fashewa da kuka,
"Dada Aliyu ya sake ni har saki biyu saboda na yi ciki".
Tk ya yi saurin cewa wane ciki bayan wanda ya ɓare?"
Dada ta yenke jiki ta faɗi babu Numfashi a tare da ita, Murja ma ta dake kanta da ya yi wata irin bugawa da jin Abinda Tk ya faɗa lululu! Ita ma sai gata ta sube saman gado ba Numfashi.
A ruɗe Tk ya ce,"Innalillahi wa'inna Ilaihir raji'un! Dada! Murjanatu!".
Dr Ne ya yi Nurse ɗin da ke tsaye a wajen umurnin ta yi sauri ta dauke ruwa a fridge da sauri ta ɗauki ruwan ta dawo ta buɗe ta zubawa Dada can ta buɗe idonta tana sauke Numfashi da kyar a hankali ta zubawa Murja ma ita ma ta buɗe idonta gami da warosu a take hankalinta ya dawo jikinta kalaman Tk sukaci gaba da ratsa kwakwalwarta "wanne ciki bayan wanda ya ɓare"
"Innalillahi wa'inna Ilaihir raji'un!!!"
"Me kika yi masa?".
Tana kuka ta zaiyana musu ko.
Dada ta share kwalla tana faɗin ,"Amman Aliyu nan Ya Sultan cika ɗan iska! Macuci Azzalumi! a she daman ba son ki yake tsakanin da Allah ba!, ALLAH ya saka Miki Allah ya bi mi ki Hakkin ki Murjanatu!, Kiyi haƙuri Kinji Allah yana tare da mai hakuri komi zai wuce".
Dada ta riƙa lallashinta, tare da faɗa mata kalamai masu sanyi.
"A fusace Tk ya ce ,"Wallahi saina ɗaukar mata fansa shi din ɗan gidan uban waye?"
"A'a Tukur ka gyalesa ba barshi da Allah shi zai saka mata,
"Haba Dada Kin fa san Murjanatu Amana ce a wajena taya zan kyalesa kaman yadda ta ɗan ɗani bakin ciki shima sai ya ɗanɗani fiye da nata, kai wallahi saidai Uwarsa ta haifi wani".
Murya a disashe Murja ta ce,"Ya Tukur don Allah ka gyalesa na barshi da Allah bana son ka ƙara komawa gidan Yari a kaina don Allah ina roƙon ka, bana son Ana jama iyayenmu magana kaga basa raye Addu'ar mu suke buƙata ba mu riƙa janyo musu magana Ana zaginsu Don Allah ka bar Aliyu da Halinsa na barshi da Allah shi zai kwatomin Hakƙina, Kuma don Allah ka Dena shaye shaye ya Tukur "
Tukur Ya share kwalla da ta zubo Mishi, duk duniya ba wanda yake so kaman Murja tun bayan da suka rasa iyayensu, su biyu ne a wajen iyayensu Dada itace mahaifiyar Babansu, halin rayuwa ne ta maida Tk dan shaye shaye saboda wahalar da suka sha a hannun kishiyar Mahaifiyarsu bayan rasuwar Mahaifiyar su sunsha a zaba sosai a hannunta Mummunan Tk da Allah ya ɗora mishi son Murja duk wata wahala yakan jureta saboda farin cikin murja, duk duniya bayan Maganar Dada da Murja baya jin Maganar kowa, akan ka taɓa murja gwara ka yi matsiyacin duka, komawar su hannu Dada ne Tk ya ɗan fara natsuwa duk da haka idon akan taɓa murja Zaiyi reshin kunya gab da Aliyu ya fara Soyayya da Murja Tk ya samu saɓani da wani abun har takaisu ga faɗa ya jima sa rauni sosai hakan yasa aka tura shi gidan yari na tsawon shekara ɗaya,
Murya a sanyaye Tk ya ce,"Zan Dena kin ji murja Nima bada son raina nake ba!"
Dada ta share kwalla saboda tausayi,"Allah ya yi muku Albarka!"
"Amin Dada"
Tk ya kalli ya ransa yana faɗin ku kyale mai ke ke nan ya wuce"
"An gama Oga"
Saida ta yi sati biyu a Asbiti sannan aka sallameta, ta rame tayi duhu kullum bata da Aiki sai kuka,
"Rabi'atu me zai haka mu roƙi yaron nan Aliyu ya maida Murjanatu ɗakin ta ki duba ga ki gani yarinyan nan tana cikin damuwa kullum cikin kuka take, Malam Tanimu na yi maganar yana kallon Dada,
"An ya Malam kana ganin zai yadda ya maida ta dakinta cewa fa. Ya yi Auren sha'awa ya yi ba sonta ya ba!"
"So ma nake Naji wane laifi ta aikata Mishi haka har da Zaiyi mata Saki Biyu"
"Ni dai a ganina da kabarshi"
"So nake muje muyi maganar gemo da gemo da Ni da mahaifinsa"
"Allah ya sa A dace"
"Amin"
Malam Tanimu ya nufi wajen Murja dake zaune ta rabka Uaban ta gumi,
"Zaki iya gane gidan su Aliyu ɗin?"
Cikin ya nayin damu ta ce zan gane"
"Shi ki ɗauko ma yafin ki muje"
Ita a tunaninta Aliyu ya maida Auren su,
Cikin hanzari ya dauƙi mafinta suka fice daga gidan Dada na musu fatan samun nasara.
Cikin Sa'a suka tatar da Daddy gida kasancewar yau Weekend ne, malam Tanimu yajin dadin samu Daddy a gida tunda shine ya nema sama Auren murja, Da aka sanar da Daddy ya yi baƙo kai tsaye ya ce a shigo dasu ɓangarensa tare da Mama, mama ta mike da niyar barin falon ya dakatar da ita,"ki yi zaman ki kawai"
Sallama sukayi suka shigo malam Tanimu ya gaida Daddy da Mama cike da izza ya amsa musu, Murja ma ta gaishesu, kanta a ƙasa,
"Malam Tanimu mi ke tafe da kai?" Ya yi ƙasa da murya ya ce,"Daman Aliyu ne ya saki Murmushi tsawon saki Biyu kenan da yan kwanaki Amman munji shiru ba wanda yazo bikonta sannan mun tambayeta ko ta yi masa wani laifin ta ce A'a".
Mama ta gyara zama cikin Wani irin yanayi tana kallon su, Daddy Babu ko alamun damuwa tare da shi ya ce,"Ai shi saki ba dole sai Anyi laifi ba ake yin sa!, Amman bari nakira Aliyu Naji"
Wayarsa ya ɗauka ya kira Aliyu,"Ka na Ina ?" daga can Ɓangaren Aliyu ya ce ," Ina gida Daddy"
"Ka same ni a gidan yanzu nan a kwai maganar da Za mu yi"kana ya kashe wayar,
Bayan mintuna goma sha biyar sai ga Aliyu ya shigo sanye yake da Jallabiya baƙa yana zuwa ya zauna kusa da Daddy ya ɗan Kwantar da kansa saman kafaɗarsa kaman yadda ya saba, yana ganin Malam Tanimu, amma ya nuna kaman bai sansu ba, tun A lokacin Malam Tanimu ya sha jinin jikinsa, Aliyu dake masa ladabi kaman wani sarki, yau a shi ne ya ƙi ko da gaida shi, Daddy ya kalli Aliyu ya ce ," wai sunzo ne suji dalilin da yasa ka samar musu ƴa ba tare da lafin komi ba"
"Ba tare da shayi ba ya ce,"Daman sai anyi Laifi ake saki?"
"Yanzu Aliyu Irin sakayyar sa zaka yi muna ke nan?".
Daddy ya yi saurin ɗaga masa hannu,"Tanimu ya isa haka taya zaka zo har cikin gidana kana gayama ɗana baƙaken magana, kwaɗayin ku ne ya za mu ku".
Malam Tanimu ya girgiza kai idanunsa sun kaɗa sunyi jazir saboda baƙin ciki," Shi kenan Alhaji daman mun zone saboda a sulhunta su ya maida matarsa daƙinta suci gaba da zaman haƙuri".
Aliyu ya miƙe tsaye yana faɗin ,"Wallahi Daddy da nasan a kan wannan maganar zaka kirani da banzo ba".
"Sarry my Son!"
"Daman na Aurenta ne domin na more kuma na samu Abinda nake so, me zan yi da ita?"
Cikin jikinta muka ku san yadda ku kayi da shi"
Falon ya yi tsit sai kukan Murja dake tashi, Malam Tanimu ya saki saki baki yana kallon ikon ALLAH cike da Al'ajabi bai taɓa zaton Reshin kunyar Aliyu ta kai haka ba, A yadda Aliyu ya zo masu da siffa ta kamala da mutunci a she abin bai kai zuci ba, tuni idanun Malam Tanimu suka ciki da kwalla ya kalli Aliyu kaman Zaiyi magana wani ƙaton Abu Mai ɗaci ya tsaya Mishi a maƙoshi,
Har ya juya zai tafi ya juyo yana kallon Daddy ya ce,"Kaiconka! Usman wallahi kayi asarar hali, kuma wannan gata da kake nunawa Aliyu sai ya kaiku ga halaka da sannu zakuga sakamakon ku kana ganin kai mai kuɗi ne ba zamu iya za da kai ba! Allah yana sama yana gani Allah ya yi ma Murjanatu sakayya akan cutar da Aliyu ya yi mana Allah ya bi mata Hakkenta".
Malam Tanimu ya damƙi Hannu Murja da ke kuka tana kallon Aliyu suka fice daga falon".
Aliyu ya za tsaki ya fice daga falon yana faɗin Ni wallahi Bazan ma ƙara Auren ƴaƴan latakkawan nan ba, Auren ma yanzu ya fita a raina, ya nufi Ɓangaren Umma,
"Mama ta sauke tagumin da tayi da hannu biyu taba share kwalla, kana ta kalli Daddy cikin wani irin yanayi ta ce ,"Alhaji" ya juyo ya kalleta cikin ƙoƙarin danne abinda ke ranta ta ce,"Alhaji wannan ba hanya da ka ke bi ba mai ɓullewa ba ce, wallahi ina mai ba ka shawara ka yi gaggawar gyara halinka da na Aliyu ka daina goyon bayansa akan zalunci da ya ke tun kafin ya gamu da Abinda zai sha masa kai gatan nan da kake nunawa Aliyu Ya yi yawa kana tutar da Rayuwarsa, Ka bi ka shagwaɓa shi yana lalata yaran mutane yana maidasu kanun zaurawa, saboda kana takarmar kana da