Bin Maryam Book 1 Sadiya Kaoje

Author :  Humaira Bulama Category :  Read Hausa Novels

Chapter   25 / 30

72K to 75K   out of 87.6K words

kiran da sukaji Sadiya ta yi har so Ukku Jumayma!Jumayma!! Jumayma!!!" cikin zafin nama suka juyo suna masu sassarfa kamar zasu tashi sama.

Kwance take kamar bata Numfashi, Sadiya tsugunne yayin da Ammy ta tallafi kanta tana mai duddubata ko zata iya gane wani abu, kallo ɗaya Bappa ya yi mata kwalla ta zubo Mishi daga idonsa, ya sanya hannunsa ya dauko yana dannawa don ya fahimci akwai bugun Zuciyarta, da sauri ya miƙe tsaye ya nufi. Wajen fridge ya dawo ruwa ya yayyafa famata da alama dogon suma ta yi. ya buɗe gorar ruwa ya tsiyaya a hannunsa ya yi bismilla ya watsa mata ruwa a fuskarta kusan sau ukku sannan tayi wani dogon Numfashi, lokacin ɗaya suka sauke Nannauyan Numfashi, "Ku ɗauke ta mu tafi Asbiti." Cak Ammy ta ɗauke suka sanya ta a mota, kai tsaye suka wuce da ita Asbiti.

Likita ne ya fito sanye da fararen kaya ya doso wajen da suke tsaye sunyi zugum," Dr lafiya? me ke damunta?."Ya faɗa cikin damuwa.

Dr ya ba shi hannu suka gaisa daga bisani ya fara jera masa bayanin kamar haka.

"Babu wata matsala dake damun wannan yarinya baya ga damuwa da ta saka a cikin Zuciyarta,munyi Aune Aune da gwaje gwaje Amma Lafiyarta lau,sai dai zuciyarta dake cike da damuwa mai yawan gaske, saboda haka dole ne a riƙa faranta mata ranta da duk abin da ta ke so, saboda haka zuwa anjima kaɗan idon ta huta zamu sallameta." Ya faɗa yana mai rissanawa da girmamawa,"Allah ya bata Lafiya."

Bayan awa ɗaya aka sallameta kaman yadda likita ya faɗa, kasancewar sun samu tabbacin reshin ciwo a Jikinta............✍️

More comments and share pls!

*Sadeeya Ka'oje ce 💋✍️*

💋𝐁𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐘𝐀𝐌💋

𝑵𝒂

𝑺𝒂𝒅𝒆𝒆𝒚𝒂 𝑲𝒂'𝒐𝒋𝒆

08149979652

https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj

PAID BOOK

Littafin *BIN MARYAM* na kudine akan 500 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652. Nagode🤗

Anty Hauwa🤩

Maryam Ɗangiwa 🤩

Aysha Muhammad 🤩

Ina matukar godiya Allah ya saka da alheri Allah ya bar zumunci 🤲❤️🤸

𝑷𝒂𝐠𝐞 43-44

_______Babu wani canji a yanayinta saima abin da ya ƙaru domin a yanzu ne ta tsunduma cikin kogin damuwa da tashin hankali,bata bacci duk iya tsayin dare tana tunanin mutum ɗaya wanda ta ganshi a filin jirgi na Sokoto, sai dai kuma bata taɓa Sanin ina zata nemo shi ba, ta rasa inda zata ganshi wanda Tunanin hakan yana sata cikin tashin hankali mara misaltawa, ta tsani komi a duniya ba ta son komi, matsalar a'a ɗaya ce yadda iyayenta suke tada hankalinsu akan ta, damuwarsu tamkar suna ƙara jefa ta ne cikin matsala,tafi son su barta ta yi ta tunanin, tana jin daɗin yawan tunani duk da takan ɗanɗana baƙin cikin da takaici da ɓacin rai na rashin sanin taka manmen inda zata ga wannan mutum, kyansa mai yawa ne ga kuma yawan tunaninsa da take.

Zaune take a falo sanye da doguwar riga ta less tayi Kyau sosai duk da reshin kwalliyar da bata yi ba, amma zaka iya tabbatar da kyauta sai dai kamar kullum tun da ta shiga wannan hali idonta jawur suke saboda aikin kukan da take, duk san da ta miƙa duniyar tunani ta tuna kyakkyawar fuskarsa da ta kanji so da tsatsanin kaunarsa, ta yi nisa sosai cikin ɗanɗanon so, ko menene ya kamani to haƙiƙa dai shi ne so, "lallai nayi ganganci da na gaza fahimtarsa a rayuwa sai dai ya ƙaru ina zan samo wannan mutum da ya zagaye min Zuciyata tare da sarƙafe ta? Ina zan gan shi? Waye shi? me ya sa ba kasa manta da shi? Anya zai so ni kaman yadda na ke son shi? ba ni da madafa, so ya kamani ina ganinsa ya min ƙuna a cikin Zuciyata.

Jumayma ce ke duk wannan tunanin, Hankalinta ya yi Masifar ta shi matuƙa, ina amfani wannan, lalle yau na yadda kalmar so tabbas so gaskiya ne, wani irin ɗaci da fargaba da faɗuwar gaba suka kamata, wani irin sarawa kanta ya yi wanda ya sanya cikin ƙanƙanin lokaci ta fara fita haiyacinta, da kyar ta tashi hannuwanta da de da kanta ta yi cikin ɗakinta ta haye saman gadonta,ta ja bargo ta rufe nan take wani irin zazzafan zazzaɓi ya rufe ta Jikinta sai karkarwa ya ke kaman mazari, a hankali take nishi saboda wani irin zafi da Jikinta ya ɗauka ga wani irin numfashi mai zafi da take fesarwa, ta kwanta ne kawai ba wai don ta yi bacci ba, kasancewar sani bacci ya daɗe da ƙaura ce mata tun tsawon watanni huɗu da suka shuɗe, haka ta raba yini tana saƙe saƙe a zuciyarta

Tana kwance ta jiyo murya Sadiya na gaisawa da yannenta wani irin daɗi taci ya mamaye zuciyarta, ta ɗanyi murmushi mai kama da yaƙe tana mai ƙoƙarin ta shi dake kwance da ta ke, cikin sanyi murya ta ce ,Adda Nazlah sannuku da zuwa yau she ku ka zo?"

ga baki ɗayan su suka zauna saman gado suna faɗin,"Jumayma tunanin me ki ke haka? Har muka shigo baki sani ba."Jumayma ta yi shiru ba tare da ta ce komi ba, Adda Aysha ta ce,"Amman dai ba ki da lafiya ko? naji jikinki da zafi sosai."



ta kawar da zance tana faɗin,"Adda Aysha sannu da zuwa."

"Ki ba ni amsar tambayata"

"Lafiya lau nake Adda" ta faɗa ta kyar, a hankali ta shi tana tafiya da kyar ta nufi falo bata jima ba ta dawo Hannunta riƙe da tray ɗauke da ruwan goda da lemu ta zuba musu cikin cup ta basu suna sha suna hira wanda hirar tasu daga Nazlah sai Aysha ne yi, domin Jumayma tuni ta faɗa duniyar tunani, Aysha ta taɓata a karo na biyu ta na faɗin Lafiya ki ke ko Jumayma?"

"Lafiya lau Adda"

"Hmmmmmm!....."

******* *******

Satin Baba Musu biyu a Asbiti aka sallameshi a ranar kuma Ummy ta damƙa mishi makullin gida mai kyau da tsari tsabar farin ciki har Saida sukayi kwalla, gida ne mai kyau ɗaki ukku da falo duk wani abu dake ake buƙa acikin gida Ummy ta sa Asad ya tana dar musu da shi tun daga Abinci zuwa bubuwan buƙata na yau da kullum sannan da jari kusan 200k, Baba Musu ma bai barshi hakan nan ba ƙofar gida Asad ya buɗe masa shagon yana Saida shadda da su Atamfa.. Ummy da kanta ta kaisu har gidansu, bayan kwana biyu Maman Nana ta je gidan mijin Nana ta ɗauko jikokinta suka ci gaba da zama tana kula su. tun daga lokacin rayuwarsu ta sauya suka dawo suna rayuwa mai kyau da tsabta, lokacin lokacin Ummy na kai musu ziyara tare da Alherai masu ɗimbin yawa....

*NAINAH*

Wasa wasa sai da Amma ta shefe tsawon wata ukku a Asbiti tana jinya, ranar da suka cika wata ukku da sati biyu a ranar aka sallameta.

da kafafunwanta take tafiya, Ummy na tare da ita yayinda Nainah da Afra suka yi gaba suna tafiya, motar Adnan suka shiga Ummy da Amma kuma suka shiga motar Asad. Ta yi zaton gidan Su Jamila zasu nufa domin sauke su acan sai ta ga an nufo gidan Ummy. Asad ne ya budewa Ammy mota da kansa ta fito tana takawa a hankali tana bin bayan Ummy wacce ta wuce gaba zuwa cikin falon. ta lura da yadda Amma take karewa ko'ina gidan kallon, wata kila ita ma ya burge ta kamar yadda ita ma gidan ya burge ta a farkon zuwanata

A falon suka zauna Ummy ta murmushi ta ce,"Nainah daga yau nan zaku ci gaba da zama in sha Allahu.idan kin dan huta za ku koma Bq na saka an gyara muku can za ku zauna ke da Amma kuma Yayan su Afra yace Saka Nainah makaranta nan kusa sai ta fara zuwa islamiya, ta bokon ma za a samu wanda zai fara koya mata a gida kamin a saka ta makaranta"

Bata san lokacin da idonta ya cika da kwalla ba, na dade ina jiran zuwan wannan ranar da zata koma makaranta ta samu ilimi, amman bata samu ba. Kallon Asad tai sai naga yana danna waya yana murmushi kadan suna hada ido ya murtuke fuska kamar be taba yin dariya ba,"Allah ya saka da Alheri"

ta fada murya kasa kasa. Be amsa mata ba sai ma dauke kansa da yai daga barin kallonta ya kalli wani gurin can dabam.

Amma ta ce ,"An gode Kana ta hidima da mu, bayan nema mana magani yanzu kuma kun kawo mu gidanku kuma za ku saka Junainah makaranta? Abunda muka dade muna buri tare da Mahaifinta, bamu taɓa haduwa da mutane masu kirki da sanin darajar dan 'adam ba irinku, taimakon da kuke mana ya yi yawa"

Cewar Amma tana hawaye kamar yadda Nainah ma ke yi. Ummy ta yi murmushi tana faɗin,"Ba komai ai yi ma kaine, lokacin sakarwa zai zo lokacin da zan nemi wani abun daga gareki ina fatar ki amsa min da hannu biyu"

“Zan karba miki ko minene a duniyar nan, matukar ina da iko da karfi akansa, ku ne mutanen da kuka taimake mu, ban taɓa mafarki haduwa da ku ba, kuma ba ku taimake ni dan ku samu wani abun daga gareni ba"

Amma har yanzu hawaye take hawayen jindadi da farin ciki. A nan suka sukaci abinci sai da suka koshi sannan Afra ta raka su zuwa Bq din, wani bangare ne na gidan da aka kawatashi sam ba zaka dauka cewar Bq bane sai idan an fada maka, Ɗaki ne da falo da ban ɗaki a ciki, komi an zuba musu a ciki.

Da yamma Afree na zaune wayarta ta yi Ringing ta ɗaga tana sallama,"Ya Deedat ya gida?" daga can Ɓangaren Deedat ya ce,"Lafiya lau, halam an sallai su Nainah na je asibiti ban gansu ba"

"Ehhh ɗazu da safe aka sallamesu suna nan gidanmu"

"Okay ki Kai mata waya Please ina son zanyi magana da ita"

"To Yaya"

Asad dake zaune duk sai yaji ransa ya yi mugun baçin zuciyarsa har wani zillo ta ke,hankalinsa na can gurin Nainah da Afreen ta kai mata waya, kamin ta dawo duk ya takura, ji yai ba zai iya hakura ba ya tashi ya fice daga falon gaba zuwa Bq, a gurin aje motoci ya samu Afreen tsaye tana jiran Nainah dake can gefen ta gama wayar ta bata wayarta.

"Ke! kar Deedat ya sake kiran wayarki ya ce ki bawa Nainah ki kai mata"

"Toh Yaya"

Ta amsa da sauri tana gyada masa kai. Ya nufi inda Nainah take zaune wayar a kunnenta tana murmushi hannu kawai ya mika mata alamar ta bashi wayar, sai ta tsaya kallonsa ba dan ba ta fahimce shi ba sai dan jira take sai ya furta.

"Bani wayar"

Ya furta a fusace sai ta mika masa tana kallonsa da fararen idanuwanta masu kamar madara ta turo masa baki alamar ta ji haushi, katse kiran yai sannan ya nuna ta da wayar.

"Karki sake waya da Deedat a cikin gidan nan"

Bata ce masa komai ba bayan idon da ta sakar masa shi kuma ya juya ya koma gurin Afreen ya mika mata wayarta sannan ya bude motarsa ya shiga ya bar gidan a guje.

Duk abunda suke Ummy na hangensu ta tagar kitchen murmushi tai tana ta kallon yadda Nainah ta turo baki, ta sani da ace wata ce a cikin kanensa ta turo masa baki yau sai ya fasa bakin nan amman da yake Nainah ce gashi ya tafi ya kyaleta, yadda Asad yake nuna kishinsa akan Nainah ta sani sarai son Nainah yake ba wai yana gudun shigarta wani halin ne kawai ba, sai dai shi din be san yana yi ba. Shigowar Afreen kitchen din yasa Ummy barin jikin tagar ta kalleta tana murmushi.

"Ummy kin ga Ya Asad da fusata wai kar na sake bawa Nainah wayata su yi waya, gashi tun ɗazu Ya Deedat kirana ya ke"

“Ina ganin duk abin da ya faru idan ya sake kira kice ni ya kira a wayata zan bata su yi magana"

"To Ummy"

Lokaci ɗaya suka fice daga Kicin ɗin.

*ANTY AMARYA*

"Anty wai yanzu shikenan haka zamu kyale lamarin nan? Anty wallahi bazan iya haƙura da Asad ba, kullum wutar son shi ƙara ruruwa ta ke a cikin Zuciyata ban taɓa son wani ɗa namiji kaman yadda nake son Asad shine mutum na farko da na fara so kuma shine mutum na ƙarshe bazan ƙara son wani mahaluki ba bayanshi, ina son shi fiye da yadda nake son kaina, Anty don Allah ki ceto rayuwa wallahi idon na rasa Asad ki sani nima zaki rasani reshi na har abada ko miye zanyi domin na mallaki Asad!"



ta ƙara maganar tana kuka mai ban tausayi, rungumeta Anty Amarya ta yi tana share mata Hawaye tana faɗin,"Ki Kwantar da hankalin ki Ramla in sha Allahu in dai Ina raye sai kin Auri Asad ko da ko zan rasa duk abin da na mallaka!"

"Anty kullum haka ki ke faɗi, gashi har ina gab da rasa Asad"

""Ki ƙara haƙuri Kinji ki bani nan da ɗan wani lokaci komi zai dai dai ta in sha Allahu, tunda yanzu Nainah ɗin tana gidan Balaraba komi zai zo da sauƙi"

Ramla ta tashi zaune daga kwance da take tana kallon Anty Amarya,"Da gaske tana gidan Ummy? Amma ya aka yi ki ka sani?"

"Nima shekaran jiya nake samun labarin"

"Yaushe zamu je gidan Anty?"

"Sai gobe"

"Wallahi sai nayi sanadiyyar barin ta gidan"

tana kai ƙarshen maganar ta wuce ɗaki tana wani irin irin murmushi, da Kallo Anty Amarya ta bita har ta shige cikin ɗaki.

*NAINAH*

Da wani irin mugun kallo mai cike da tsantsan tsana tabi Asad da shi, bata san dalilin son nuna isa da yake mata ba, ‘abunda yake mata ko kanensa baya ma haka, saboda su suna wayar be taba hana su ba sai ni’ Haka ta tunzure baki ta nufi Bq din su ta jin haushin karbe wayar da Asad yai domin ban gama waya da Deedat ba, kuma tana son ta tambayeshi yaushe zai zo, Amma ya zo ya karbe wayar.

Haka ta yini ranar cikin ɓacin rai, bayan Isha'i Afreen ta kawo musu abincin su mai rai da lafiya, tuwon semonvita da miyar ɗanyar kuɓewa da taji kifi da nama da man shanu suna cin abinci suna hira har suka kammala, Bayan Amma Nainah ta kwanta ta rungumeta kaman zata shige bayanta ta baccin tai cikin kwanciyar hankali har safe...

Washegari bayan sunyi salla suka koma bacci sai wuraren karfe 8:30 suka tashi Nainah ta gyara musu ɗaki tayi shata da mopping duk da bani dauɗa ya yi ba ta, ta Wonka bayi sanna Amma tayi Wonka tana fitowa Nainah ta shige toilet ɗin domin ta yi Wonka koda ta fito tuni Amma ta shirya har an kawo musu Breakfast lafiyaiyar masa da ferfesun ganda da kunun Aya.

Bayan sun kammala Nainah ta tattara kayan zuwa Ɓangaren Ummy a falo ta same su kai a sunkuye ta ce,"Assalamu alaikum, Ummy ina kwana"

"Lafiya lau Nainah, ya jikin Amma?."

"Da sauƙi sosai Ummy"

"Ma sha Allah, Allah ya ƙara sauƙi"

"Amin Ummy"

Sannan ta gaida su Adnan kana ta wuce Kicin ta aje kulolin ta dawo falo, dai dai lokacin kuma Dr Kamal ya fito sanye ya ke da Jallabiya hannunsa ɗauke da Laptop, har ƙasa Nainah ta durƙusa ta gaishe shi ya amsa mata fuska a sake.

"Abba Ina kwana" suka haɗa baki wajen gaishe shi

"Lafiya lau"

Zama ya yi ya ɗora ƙafafuwansa saman center table dake tsakiyar Falon sanna ya ɗora laptop ɗin saman cinyoyinsa yana dannawa,

"Ummy ko a kwai wani aiki da za'ayi?" Cewar Nainah.

"Ba wani aiki"

"Nainah pls ki gyara min ɗakina" Adnan ya faɗa"

tun kafin Adnan ya rufe baki Nainah ta nufi ƙofar ɗakin sa.



Kaman wanda aka jefo ya fito daga cikin ɗakin sanya da ƙananan kaya blue jeans da plaid shirt mai ratsin blue sosai kayan suka yi masa kyau.tuni Nainah ta shige ɗakin.

"Ummy..."

Ya kwala mata kira ta nufo wajensa da saurin tana faɗin,"Lafiya?"

"Ummy kar yarinyar nan ta sake shiga Ɗakin Adnan da sunan gyara masa daki, miye amfanin Afra da Afreen?idan ba zasu gyara masa ba ya hakura da gyaran kawai"

"To miye idon ta gyara masa ɗaki?"

"Ni dai a ga ni na kaman bai da ce ba tun da ba muharramarsa ba ce"

Da mamaki Ummy ta kalli Asad.

"Wani Abun Adnan ɗin ya ta ɓa yi mata?"

"A'a Ummy"

"To miye hujjar ka da zaka ha nata shiga ɗakin sa"

"Saboda ba muharramarsa ba ce ko mi zai iya faruwa."

"Ya Asad ni ba dan iska ba ne ka fi kowa sanin haka"

Asad ya watsa masa harara da rinannun idanunsa da suka sauya launi iya ja saboda ɓacin rai.

"Kai baka iya kyautatawa kowa zato? A yadda kaga dama haka kake son taka mutane? Ba zai yiyu ba Wallahi idan zaka taka kowa yadda kake so ta ba a gidan nan ba sam bazam lamunta ba"

"Wai hayaniyar me nake ji ?" Cewar Abba, Asad lafiya?"

"Ba

25 / 30