Bin Maryam Book 1 Sadiya Kaoje

Author :  Humaira Bulama Category :  Read Hausa Novels

Chapter   5 / 30

12K to 15K   out of 87.6K words

kuɗi shiyassa kuke cutar duk wanda ku ka ga dama?, Ni Mahaifiyar Aliyu ce Ko kaɗan bana jin daɗin yadda yake rayuwa Alhaji kamai fa kana da ɗiya mata baka gudun Ayi musu Abinda Aliyu ke yiwa ɗiyan mutane? Ya kamata ka farka daga Nannauyan barci da a ke kasan Halin da ku ke ciki kaida Aliyu, wallahi Wallahi matuƙar kuka ci gaba da tafiya a haka wata rana Aliyu zai ɗauko ma Abinda yafi karfin ka da zaka gwammace mutuwar k........"

"Ke!" Laila ya daka mata wata irin tsawa gami da miƙewa tsaye yana faɗin ,"Dakata! Laila" ke har kiyi isar da zaki tsaya a gaba kina faɗamin baƙaken magana akan Aliyu Bazan lamunta a riƙa cin zarafin ɗana!"

Ya buga wawan tsaki ya juya ya fice daga falon, Mama ta rakashi da ido cike da Al'ajabi ta girkiza kai tare da share kwalla, lalle Alhaji ya yi nisa baya jin kira, wanda ya kama mata ya tsaya masa baya tabbas Akwai ranar nadama ta na jiye musu ranar da Duniya taza juya musu baya, ta jima zaune a wajen tana tunanin da ta san haka halinsa yake da bata Auresa ba babu Abinda Auren sa ya tsinana mata face bakin ciki....... tayi nisa sosai da tunanin Umma ta shigo falon tare da Hannatu yar kimanin shekara Bakwai a duniya, a hankali ta zauna kusa da ita tana sauke Ajiyar zuciya, "Maman Hanifa don Allah ki yi Haƙuri akan Abinda ke faruwa Tabbas Abinda Alhaji yake baya kyautawa tsakanin da Allah yana cutar da rayuwar Aliyu"

Ta rushe da kuka mai tsuma zuciya, Umma kwalla ta share har ga Allah tana tausayin mama, Hannatu ta matso kuka da ita tana faɗin ,"Mama! Kuka ki ke? Mama baki da lafiya na kira Daddy ya kaiki Asbiti, sai itama ta fashe da kuka harda shashsheƙa,Mama ta rungumeta tana faɗin ,"Autan Umma Nifa ba kuka nake ba Idanuna ne ke ciwo kingani tana faɗa tana share mata Hawaye, "Mama bari Naje na dauƙo Miki maganin ciwon Ido"

da gudu ta fice daga falon Mama da Umma suka bita da kallo, lokacin ɗaya suka sauke Nannauyan Numfashi,"Maman Hanifa don Allah ki Dena kukan ya isa"

"Na Dena Amarya"

Dai dai lokacin Hannatu ta dawo falon riƙe da Eye Drops tana faɗin ,"Mama kawo na saka Miki".

Ba musu ta ɗan ɗaga kanta sama Hannatu ta saka mata maganin tana Murmushi , "Yauwa yanzu zai deba ciwo"

"Thank you Hannah"

Umma ta ce yauwa je ki ce Aunty Sumayya ta tsefe Miki kai ko Anty Hanifa duk wanda kika gani, da sauri ta fice daga falon tana faɗin Umma zanje Saloon"



Umma taci gaba da janta da fira tana ɗebe mata kewa.



*******

Dada ta share kwalla da majina da ke zubo mata ba bu ƙaƙƙautawa ta ce,"Amman Aliyu bai kyauta muna ba yazo muna da siffa ta kamala ashe mugun nufi ne ransa, ALLAH ya saka Miki Murjanatu, ta dubi Murja dake kwance tana kuka, a hankali ta shafa kanta Muryarta a sanyaye ta ce,"duk mutumin kwarai ya yarda da ƙaddara mai kyau ko mara kyau mun ɗauki wannan Ƙaddara Allah ya yi Miki zaɓi na Alheri Allah ya baki wanda ya fi sa ki duk wata damuwa a ranki Allah zai saka Miki"

Sai a lokacin ranta ya ɗan yi sanyi ta mike zaune ta rungume Dada tana faɗin,"In sha Allahu Dada na gode sosai.......!"

*More comments and share pls!*

*Sadeeya Ka'oje ce 💋✍️*

💋𝐁𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐘𝐀𝐌💋

𝑵𝒂

𝑺𝒂𝒅𝒆𝒆𝒚𝒂 𝑲𝒂'𝒐𝒋𝒆

08149979652

https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj

𝑷𝒂𝐠𝐞 9-10

_____Sannu A hankali Murja ta Dena saka damuwa a ranta ta tattara su gefe ta aje, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi wa Dada da malam tanimu, A ɓangaren Tk ma sosai hakan ya yi masa daɗi zuwa yanzu ya fara rage shaye shayen da yake,

A Hankali a hankali kwanaki suka ci gaba da shuɗewa, cikin Aminci Allah zuwa yanzu Asad shekarsa Huɗu a duniya.

A Ɓangaren Aliyu kowa tunda ya saki Murjanatu bai koma yin Aure ba, Hakan ba ɓakin daɗi ya yi wa Mama ba, a ganinta Allah ya fara ƙarɓan Addu'arta,

Yau ta kasance Talata, Tunda safe Balaraba ta tashi da matsanancin ciro ciki, haka yasa aka wuce da ita Asbiti,

Suna tsaye Iya da Hamza cike da farin ciki mara misaltawa tare da Addu'ar Alkairi ga Dr Kamal da ya dauƙi Nauhin ciwon Balaraba, tunda A haihuwar Asad ya ke ɗawainiya da su tamkar dama can A kwai a laƙa a tsakanin su, tun a lokacin suka yaba masa, daɗin daɗawa tun isawarsu Asbiti Hamza ya kira shi daman sun ɗan saba da shi tun wani ciwo da Asad ya yi suka kawoshi Asbiti tun A lokacin ya ke da Number Hamza,

Kyakkyawan Albishir da ya yi musu na cewa ya ɗauƙi Nauhin Aikin da za'ayi Balaraba kyaune Apendis da za'a cire mata, "Kamal Mun gode sosai Allah ya saka da Alheri"

"Babu komi Mama in sha Allahu an jima kaɗan za'a shiga da ita wajen aiki, kuma in sha Allahu za'ayi shi cikin nasara zata dawo Normal kaman ma bata taɓa ciwo irin wannan ba"

Kallo suka riƙa binsa da shi cikin Al'ajabi da farin ciki marar misaltawa, bakinsu ya ƙulle sun rasa me zasu ce, Hatta Balaraba dake kwance tana binsu da kallo na musamman Dr Kamal, Ita kai tasan wani halin da take ciki,

Iya ta share kwalla da suka zubo mata, ba wai kudin ne suka rasa ba zuwa yanzu Alhamdulillahi babu Abinda suka rasa saboda tumaki Balaraba Allah ya sanya musu Albarka, a bangaren Hamza ma Alhamdulillahi zuwa yanzu Shagonsa ya daɗa bunƙasa kusanma duk jiyar tasu ba bu mai irin Shagonsa zuwa yana har ya kammala gidansa Aurensa ma baifi wata ɗaya da ya rage ba,

"Allah ya yi maka Albarka Kamaludden Allah ya kare ka Allah yasa ka gama da duniya lafiya Allah ya kareka daga sherrin maƙiya Allah yasa kafi haka ɗaukaka"

"Ba bu komi Mama Ai Balaraba kaman ƙanwace a gurina bana son godiya, fata na Adai Allah ya bata Lafiya yasa Ayi aikin cikin Nasara"

Ya faɗa yana kallonta da murmushi Kwance a fusakarsa Balaraba ta yi ƙasa da kanta tana Murmushi tun bayan abinda Aliyu ya yi mata bani ta tsani dukkan wani namiji ba musanman saurayi matashi amma har ga Allah Dr Kamal yana burgeta ta rasa da wane baki zata gode masa Murya a sanyaye ta ce,"Na gode ba ni da wata kalmar da zanyi maka godiya Allah ya saka maka da Alheri Allah ya faranta maka fiye da yadda ke ke faranta mana Allah ya......"

Ya ɗaga mata hannu da sauri yana faɗin ,"Ya isa haka tsakaninmu babu godiya an zama ɗaya Ummin Asad"



Murmushi ta yi tana sunkuyar da kai mugun kunya take ji idon ya kirata da sunan(Ummi Asad)

Ku shirya nan da Awa biyu za'a shiga da ita wajen Aiki"

Kaman yadda ya faɗa Awa biyu nan na cika aka shiga da Balaraba ɗakin da za'ayi mata Aiki, likitoci wajen guda huɗu ne a kanta ko wanne da Aikisa harda Dr Kamal, Iya da Hamza na zaune a waje suna binsu da Addu'ar samun nasara,

A ƙalla Saida suka shafe tsawon awa biyu sannan suka ga An Turo Balaraba akan gado ta kwance tamkar Matacciya iya zane ne kawai a jikinta Blue aka wuce da ita wani dakin na musamman da aka tanarda mata, Dr Kamal ya iso gare su fuskarsa dauke da Murmushi yana faɗin,"Alhamdulillahi aiki ya kammala da Alama akwai nasara ina sha Allahu zata warke"

Lokaci ɗaya Hawayen murna da farin ciki suka zubo musu Iya ta riƙa zuba Mishi Albarka,

Kuzo muje ku ganta saidai ba'a son hayani ko kaɗan kuma ba'a son A tasheta anfi son ta farka da kanta, da sauri suka nufi ɗakin

Ɗaki ne mai girma ga kyau gado biyu ne a ciki sai kujeru ukku da A.c bayan fanka da ɗan ƙaramin fredge a tsakiyar gadajen.

Bayan Awa ɗaya sai ga Dr Kamal ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo da kaya niƙi niƙi, a hankali Hamza ya mike ya ƙarɓa masa kayan,"Yauwa Mama ga wannan Aliyu Haƙuri ba yawa dai saboda na san a ƙalla zaku kai tsawo sati ɗaya kafin a sallameta, don Allah duk a Binda kuke buɓata kada ku ji Nauhin tambayata Ni ɗan ku ne kaman Hamza da Balaraba".

daga haka ya fice daga ɗakin,Iya da Hamza suka bishi da kallo, kana suka maida kallonsu ga kayan Hamza ya buɗe kayan shayi ne da fruit da kaji guda biyu da ƙaton flask ɗin shayi da na Abinci, Iya ta yi ta saka mishi Albarka.

*ASAD*

Zaune yake ya rabka Uaban tagumin kaman wani Babban Mutum kallo ɗaya zaka Mishi kasan cewa yana cikin matsananciyar damuwa Idanunsa cike da kwalla ya kalli Baba dake zaune kusa da shi Murya a sanyaye ya ce,"Baba ta shi ka kaini wajen Ummi na! Baba Ka kira Uncle Hamza ya zo Kaini wajen Ummi na"

Baba ya Kalli Asad dake zaune kusa da shi yana share hawaye, tausayin yaron ya cike a Zuciyarsa, tunda aka wuce da Balaraba Asbiti ya saka sukuni gabaki ɗaya a firgice ya ce ko karin safe ya ƙi banda kuka ba Abinda yake, "Ai na faɗa maka idon baka ci Abinci nan ba, ba inda zaka je"

Rau rau ya yi da ido Kwallar da ta taru ta zubo Mishi, yasa ta fin hannusa ya share, bai koma cewa Uffan ba illa kawai Ido da ya tsurawa Baba ko kyattawa ba shiyi, Baba ya Kallesa yana murmushi sanin Halin Asad ba zai koma yi Magana ba Abinci ma bazai ci ba har sai an cika mi shi burinsa, Baba ya shafi kansa yana faɗin Haba Asadullah fushi ka ke da ni?"

Dai dai lokacin Hamza ya shigo gidan yana murmushi, Kallo ɗaya Asad ya yi masa ya kwarda kai gefe tamkar bai gansa ba,"Hamza ya jikin Balaraba?"

"Jiki Alhamdulillah Baba"

da ga nan ya sanar da Baba irin hidimar da Dr Kamal ya yi mu su.

"Kai ma sha Allah, Allah ya saka mi shi da Alheri samun irin sa wannan lokaci a kwai matuƙar wahala, ka duba haka lokacin da Asad ya yi reshin lafiya shi ya ɗauƙi Nauhin komi, Allah yasa ya gama da duniya lafiya"



"Amin Baba"

Hamza ya kalli Asad da ke zaune ku sa Baba ya sunkuyar da kai ƙasa, "Asad! me ya sa meka?"



Baba ya yi Murmushi yana faɗin,"Wajen Balaraba ya ke son A kaishi, Bana son yaje wajen kasan idon ya ga Balaraba a halin da aka fita da ita a gida Zaiyi ta kuka, yanzu Haka komi baici ba tunda safe ba yadda banyi da shi ba"

Hamza ya kalli Asad yana murmushi cikin sanyi Murya yace,"Zo nan ɗan gidan Ummi Baba ne ya hanaka zuwa jen Ummi?"

A hankali ya gyaɗa kai ya na share kwalla, "To Kwantar da hankalinka yanzu zan kai ka wajen Ummi amma sai kaci Abinci zamu tafi ga fruit nan na zo maka da shi kai ɗai karka tsamma Baba"

"Uncle na ƙoshi wajen Ummi

zan tafi"

Baba ya girgizar kai yana faɗin ,"Lalle duk abinda yasa Asad reshe shan fruit ba ƙaramin Abu ba ne, Hamza ta shi ka kaishi wajen Mahaifiyarsa don ba zamu iya rigimar sa ba"

"Baba Likita ne ya ce Ba'a son a tashe har sai ta farka da kant......

"Uncle Wallahi ba zan yi Magana ba" ya faɗa cikin sauri,

"Ta shi kawai ku tafi Allah ya bata Lafiya ya ta shi kafaɗunta"

"Amin Baba"

Basu wani jima ba suka fice daga gidan,

Suna isa Asbiti kai tsaye suka wuce ɗakin da Balaraba ta ke kwance, a hankali Hamza ya buɗe ƙofar ɗakin suka shiga ya koma rufeta a hankali, Asad ya kalli Balaraba dake kwance saman gado tana bacci, gefen gado ya koma ya yi tsaye ya tsura mata Ido tsawon mintuna goma, A hankali ta fara buɗe idanunta da suka yi mata Nauhin Bishi Bishi ya riƙa ganin fusakar Asad a hankali ta ɗan ware idanunta tana Ambaton sunan Allah, Asad ya ƙarasa wajenta da sauri ya riƙe mata Hannu yana kiran,"Ummi! Ummi!! Ummi!!!"

Balaraba taji sautin Muryarsa a cikin Zuciyarta, "A...s..a...d...!"

ta kira sunansa cikin rawar Murya,

Hamza da Iya suka nufi wajen ta cikin sauri suna faɗin,"Balaraba kin tashi ya jikin naki? Baki jin komi?"

"H..a...m...m..a.! I.....ya!"

dai dai lokacin Dr Kamal ya shigo ya nufin wajenta,"Mama Allurar bata gama sakinta ba har yanzu, Ina dai fatan ita ta farka da kanta?"

"Ehhh"

Hamza ya bashi amsa,

"Karku damu zata wastsake in sha Allahu".

Kallo Asad ya yi da tuni wahaye sun wanke masa fuska, "Ka Dena Kaka kaji Ummi zata samu lafiya, ka ci Abinci ko?"

Hamza ya ce," Komi bai ci ba tun safe"



"Baka son Ummi ta Samu lafiya?"

"Ina so"

"To je ka ci Abinci kaji"

"A...s...a...d! Je kaci Abinci kaji"

Balaraba ta faɗa ido a rufe,

Murmushi su ka yi gabaki ɗayan su.

"Ni zan ta fi Allah ya ƙara lafiya!"

"Amin mun gode sosai Allah ya yi Albarka"

Sai bayan Awa biyu Balaraba ta sake farkawa, zuwa Yanzu Alhamdulillah ta farka da ɗan dama damanta sai ɗan abinda ba'a rasaba, Iya ta haɗa mata tea ta sha don Dr ya ce musu Abu mai ɗan ruwa ruwa zata riƙa sha na kwana uku sannan ta soma cikin Abu mai nauhi,tunda ta farka Asad ke manne kusa da ita,

a hankali aka Turo ƙofar dakin, Yan mata ne guda Ukku ta farkon riƙe da Basket ta biyun kuma riƙe da leda, suka shigo ɗakin suka durƙusa har ƙasa suka gaida Iya cikin girmamawa Iya ta amsa musu fuska a sake, "Mardiya Rahama Fiddausi kune tafe haka? Ya mamanku"

Mardiya da Rahama suka amsa, Lafiya lau suke, sunce a gaisheku juwa Anjima zasu shigo"

Iya ta kalli Fiddausi dake durƙushe kanta a sunkuye tana wasa da yatsun hannunta,"Fiddausi tashi mana ki zauna"

a hankali ta miƙe kai a sunkuye ta nufi wajen Balaraba cikin sanyi Muryar ta ce,"Adda Balaraba ya ƙarfin jiki"

"Alhamdulillah Fiddausi ya shirye shiryen buki?"

Murmushi kawai tayi tana kallon Hamza ta ƙasan Ido dake Binta da wani irin mayen Kallo tamkar wanda bai taɓa ganinta ba, Rahama da Mardiya suka ƙasaro wajen Balaraba,"Adda Balaraba ya jiki?"

"Da sauƙi sosai" ta faɗa tana Murmushi,



"Hamma Hamza Ina wuni" suka faɗa a tare,

"Lafiya lau ƴan ƙannena masu Albarka"

Fiddausi ta ɗago ta kallesa shima ita yake kallo a karo na biyu ta ɗago still ita yake kallo ta ɗan dalla mishi harara Lumshe idanunsa ya yi

5 / 30