Author : Humaira Bulama Category : Read Hausa Novels
tana nuna masa kofar fita. Hawaye shar suka wanke fuskar Deedat tuni yai mutuwar zaune.
Kasa cewa komai Deedat yai sai kallon Umma yake hawaye na sauko masa kamar ba shi ba. A fusace ta bar masa gurin ta haye sama dakinta. Ya dade zaune a gurin sannan ya mike tsaye ya nufi part dinsu, keys bude dakin ma daker ya iya sakawa ya bude yana shiga ya zube a falo zaune saman kananan cushion dinsa.
Abunda ya faru ne ya tsaya masa a rai, ta ina ne be kyautawa Ummy ba? Miye illar abunda yai? Har ga Allah be ga da inda yake da wata matsala ba, Ummy ta nuna masa son kai, kuma maganar da ya fada mata babu laifi a ciki, ta sani sarai yana son Nainah taya zata juyar abun akan Asad saboda yana danta? Ya sani be kyautawa Nainah ba, har ta furta kalmar tsana a gareshi ba, wannan babin kam ya yarda yayi kuskure amman da wanne zai ji rashin goyon bayan Ummy ko kuwa yanke masa hukunci da mari da Umma tai, ko kuwa auren Nainah da Asad zai yi? Anya ma zai iya zai iya kallon Nainah da Asad a guri daya bayan shi ya fi cancanta ya zauna da ita? Domin shi ya ce yana son ta kuma yana da tabbacin tana son sa.
A daren be yi bacci ba duk kuwa da irin gajiyar da ke tattare da shi Ta ina zai shirya da Nainah? Asubar fari ya fita daga gidan zuwa masallaci be dawo ba sai bakwai da rebi na safe, kamar zai wuce part dinsu sai kuka ya shigo part din Umma, Daddy ya samu tsaye a tsakiyar falon yana kai koma, jiki a mace ya nufi wajensaya durƙusa har ƙasa ,"ina kwana Daddy".
Tas! Tas!! Ya wonke kyakkyawar fuskarsa da lafiyayyun mark har guda biyu, da sauri Deedat ya mike tsaye dafe da kuncensa hawaye masu zafi na silalo masa.
,A she baka da tunani Deedat?
"Daddy don Allah Kiyi haƙuri"
Ban taɓa tunani haka daga gare ka ba, so hauka ne Halam?"
"Wallahi wannan ya zama farko kuma ya zama na ƙarshe, idon wani abu ya sake shiga tsakanin ka da Balaraba na reshin daɗi in mai tabbatar ma da cewa zan cireka daga cikin jerin ƴaƴana"
A razane Deedat ya juyo yana kallonsa fuskansa jiƙe da hawaye ya ɗuka har ƙasa yana mai neman gafarar mahaifinsa.
A fusace Daddy ya fice daga cikin falon zuwan Ɓangaren Iya.
" ina kwana Umma"
Ta yi kamar ba ta ji shi ba sai cigaba tai da aikinta.
"Umma yah Deedat na gaisheshe ki"
Baby ta fada a zatonta bata ji abunda Deedat yace ba ne.
"Na ji ai"
Ta fada ba tare da ta kalleshi ba. Shi kuma ya mike tsaye cikin rashin jindadi ya fice daga falon.
**** *****
BAYAN KWANA BIYU
Asad na zaune a office ɗinsa yana dannar wayar aka turo mishi saƙo ta WhatsApp da ɓakuwar number kaman ba zai buɗe ba sai kuma ya buɗe video, Video Nainah ne a sirara tare wani saurayi suna aika baɗala, daga ita har shi babu mai tufafi a jikinsu............✍️
Alhamdulillahi anan na kawo ƙarshen Book
1
.
END OF BOOK
(Tashin hankali me ke shin faruwa da Nainah?🙆🙆🙆?
Ga mai buƙatar ci gaban labarin zai biya ƙuɗi 500 kacal ta wannan Account Littafin *BIN MARYAM* na kudine akan 500 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652. Nagode🤗