Author : Humaira Bulama Category : Read Hausa Novels
dayan hannunsa aljihu.
"Asad ya ce miki wani abu kaina ne? Ya ce miki ni dan iska ne?"
ta yi ƙasa da kanta tamkar bata ji me ya ce ba
"Allah ne shedata ni ba dan iska ba ne ni, tun na ke a rayuwata ban taba aikata zina ba, dan kuma na ce ina son ki ba laifi ba ne"
Dagowa tai ta kalleshi sai ya sakar mata murmushi ya nufi kofar fita daga falon ya bar ta tsaye ya fice da ga Falon.
"Afra ɗauko Abinci mu wuce Asbiti Adnan ya kira ya ce mahaifiyar Nainah ta farka"
Kai tsaye suka wuce Asbitin, tana jin bata ji daɗin yanayin da ta ga Deedat ba,sam kalamansa ba su mata dadi ba. Bayan Direba ya yi parking motar ya suka fito suka nufi cikin asibitin, kusan mutane duk wadanda ya Kalleta so ɗaya sai ya sake Kallonta wasu har da sakar mata murmushi suke. Ita dai tana biye da Ummy har suka isa cikin dakin da Amma take, Adnan suka samu a ciki da Dr Yanusa suna duba Amma wacce ki kwance idonta bude tana kallon mutane, Ummy ce ta karasa cikin yayinda Junainah na tsaya bakin kofa kallonta ta kasa karasawa tsoro da fargaba ta ke kar ta je kusa da ita tace bata gane ni ba, Adnan ya sakar mata murmushi ita kuma idonta na kan Amma har ta fara hawaye.
"Shigo mana Nainah"
Cewar Adnan daker ta iya daga kafarta ta fara takawa cikin dakin, karar sautin takalmin kafata ne yasa Amma ta kalli inda ta ke wani abun mamaki sai ta ga Amma ta sakar mata ta murmushi,wani irin daɗi ta ji ya lulluɓe ta da sauri ta karasa kusa da ita tana ta kallonta kamar wanda ta sheka bata ganta ba.
"Amma!...."
"Na'am Junainah!...."
Kwata Kwata ta manta da aiki aka yi mata, ta ɗagota da niyar ta rungumeta tana kukan dadi, bata manta ni ba ko da ta manta komai ni bata manta ni ba, sai da Ummy ta dago tana dariya ta ce.
"Karki ji mata mana ciwo yi a hankali"
Na kalli Adnan tana hawayen farinciki ta ce.
"Alhamdulillahi Allah na gode ma Yaya Adnan Amma bata manta komi ba!"
"Bata manta komai ba sai dai ki yi mata fatan samun lafiya mai ɗorawa"
"Alhamdulillahi!+³ Allah na gode ma" ta faɗa har so Ukku lokacin da ta ɗago daga sujada. Kallo ɗaya zaka mata kasan tana cikin tsantsan farin ciki a wannan lokaci bata da wani buri da ya wuce samun lafiyar Mahaifiyarta kuma Alhamdulillahi Allah ya cika mata birninta da alama muka yanzu ta doro hanyar samun lafiyar.
"Ummy na gode sosai Allah ya saka muku da Alheri Allah ya yi muki sakayya da gidan Aljannar Fiddausi"
Murmushi tai ta na faɗin
"Ba komai ai yi wa kaine Nainah Allah ya ƙara mata lafiya"
"Amin Ummy........"
*ASAD*
Daga wajen aiki ya wuce gidan Ummy duka kanensa suna zaune tsakar falon suna kallon a tare suke gaishe shi ya amsa musu da dan sakin fuska sai dai ba Sosai ba ya nufi dakin mahaifiyarsa. Zaune ya same saman lallausar carpet tana riƙe da littafin Addu'oi tana karatu ta ɗan juyo tai ta amsa masa sallamar da yai tana kallonsa."Wa'alaikassalam"
"Ummy ina wuni?"
"Lafiya lau ina ka aje wayarka ina ta kira baka ɗaga, ina fatan kaje Asbiti? Mahaifiyar Nainah ta farka kuma anyi nasara bata manta komi ba kaman yadda likita ya faɗa."
"Ma sha Allah Alhamdulillahi! yanzu da na ke son na leka, ban sani ba ko za a wuce da wani abu shiyasa na biyo"
"Nainah tana cikin farinciki sosai yau"
Ya dada fadada murmushinsa shi kansa ya jidadin jin hakan balle kuma da aka ce masa Nainah tana farinciki, ya gyara zamansa yana kallon Ummy ya ce.
"Allah ya ƙara mata lafiya"
"Amin, Deedat ya fada min cewar kana takura masa akan Nainah ya fada min sonta yake kuma son Aure idon Abubuwa sun lafa yana son ya gabatar da iya a wajen iyayensa"
Asad ya kalleta da sauri mamaki kwance a fuskarsa karara,
"Shi Deedat din ya fada miki haka Ummy"
“Eh yace ya fada mata hakan tun a gidan Iya"
"Me kika ce masa?"
"Na fada masa ita yanzu ba soyayya ne a gabanta ba, domin mahaifiyarta babu lafiya, wata kila kalaman nawa ba su masa dadi ba,koda na fito mu tafi Asbitin ya wuce ko sallama bai min ba,kuma ban jidadin hakan ba ko kaɗan"
“Miye abun rashin jindadi a ciki Ummy ki fita batun sa kawai Ai gaskiya kika fada masa mahaifiyar yarinya ba lafiya ban dan rashin tunani ba har ya dube ta ya fada mata yana son ta? Kuma yarinyar nan yanzu abunda take bukata ilmi, bata san komai akan addinta ba, yarinyar da bata iya banbance wanda a muharraminta da wanda ba muharraminta ba ko mahaifiyarta ta samu lafiya ai ilmi shine Farko abunda take bukata a yanzu"
"Talla ta ke i kaga ba lallai ne ace tana zuwa makaranta ba,ni kaina na fada masa hakan ne saboda na san be kamata yai mata maganar a yanzu ba, komi a hankali ake binsa"
"In banda reshin hankali irin na Deedat ta ya da ganin yarinya kace kana sonta baifa son kowa a familyn ta"
"Wannan duk ba matsala ba ce tunda dai ga Mahaifiyarta komai zai zo da sauƙi, ni da kai na idon abubu ya taso zan shige mata gaba , kuma ni mai masa komai ce Allah dai ya dai ya tabbatar muna da Alheri "
'Ba Amin ba'. Ya faɗa a zuciyarsa'
"Idon kuma bata son shi fa?"
Ya fada yana mikewa tsaye domin shi sam baya son maganar ma Kwata kwata
"Mi zai sa ba zata so shi ba, miye Deedat ya rasa? ya na da duk wani abu da wacce ta ke son mallaka ga ɗa na miji, Asali, tarbiyya, kyau, ilimi, hankali, Addini, kuɗi, sanin ya kamata, bayan wannan akwai wani abu da ba shi da?"
"Zan ta fi Asbitin sai na dawo"
"Allah ya tsare"
"Amin Ummy"
Kana ya fice daga ɗakin zuwa inda ya yi parking motarsa ya shiga ya fice kai tsaye ya wuce Asbiti, Har ya isa asibitin be daina jin haushin Junainah ba shi ya rasa wace irim yarinya ce da har zata tsaya ta saurareshi, wace amsa ma ta bashi ? Wannan karon ba kamar yadda ya saba shiga dakin ya shiga ba, da sallama ya shiga tsabanin baya da sai dai ya tura kofar ya shiga a haka ba tare da sallama ba. Ladiyo ta amsa masa Junainah na zauna saman gadon da Amma take tana ta mata fira baki har kunne. Da wani irin far'a marar misaltuwa Junainah ta kalleshi kyau da tai da far'ar data haska fuskarta sai ta tasa gabansa faduwa a karon farko. Ba laifi ya saki fuska sai dai ba sosai ya karasa gurin Amma yana mata ya jiki.
"Mama ya jiki na ki?"
A hankali Amma ta juyo tana kallon sa, gabanta ya yi Masifar tsinkewa lokacin da ta yi Arba da fuskar Asad, fuskar da bata zata taɓa manta da ita duk da shekaru sun shuɗe, ta nuna shi da ɗan ya tsaya yana Murya na rawa ta ce,"Ali...yu!"
"Nainah ta juyo tana kallonta mamaki ƙarara shimfiɗe a fuskarta ta ce,"Asad ne sunansa ba Aliyu ba!"
"Asad kuma? A'a Nainah wannan Aliyu ne ba Asad ba!sai ta je ganin abun kaman a mafarki, Kodai da gaske Aliyu ne? ya bi yi bayanta sai ta ke ganin kaman lokacin da ya sake har ta yi jinya a Asbiti, ",Aliyu ka biyo bayana na ne domin ka ƙarasa ni? duk irin cin Amana da tozarci da kayi min a gidan bai ishaka ba har sai ka biyoni a inda nake ka ƙara sa ni, duk halinda na shiga Aliyu kai ne sila, kai silar rugujewar farin ciki na ka son ba sona kane ba me ya sa zaka yaudareni mugu Azzalumi Wallahi ƙarshe bazai kyau ba! Hakƙina ba zai bari ka gama da duniya lafiya ba, kasa na rasa abin cikina duk saboda kai Aliyu!" ta ƙasara maganar tana kuka mai tsuma Zuciya,
Junainah ta fashe da kuka mai ƙarfi tana faɗin,"mugu me ka aikatawa Mahaifiyata? me yasa a duk lokacin da ka raɓemu sai wani mugun Abu ya same mu ka ka fice daga ɗakin nan bana son ganin ka!"
Asad ya ya ɗaga ya kalleta cike da mamaki ya sake kallon Amma dake kwance har yanzu ta na kuka mai ban tausayi.
"Wani Abun ta ce na aika mata?" Asad ya faɗa a sanyaye.
Nainah bata tsaya saurarensa ba taci gaba da tambayar Amma,"Amma me ya aikata miki? Amma daman kin san shi?"
"Aliyu! ne wallahi, me yasa zaka dawo cikin rayuwata so ka ke ka kasheni tun lokacin na bai yi ba? na tsaneka Aliyu!"
"Na shiga Ukku! na lalace! Asad hankali ya kwanta? ina farin cikin Mahaifiyata bata manta da komi kaman yadda Ya Adnan ya ce" ta faɗa cikin tashin hankali ita a tunaninta Amma ta samu matsala ne a kwakwalwa har take irin waƴan nan surutai,
Wata uwar harara Asad ya watsawa mata daman wani bakin haushinta yake ji na rashin dalili. A fusace ya fice daga ɗakin ya nufin ya wajen motarsa ya shiga, ikon Allah ne kawai ya kai shi gida domin wanin irin tuƙi yake mai kama da na ganganci, saboda ɓacin rai
Bayan ta fitar Asad da kyar Nainah da ladiyo suka shawo kan Amma ta dena kuka, Nainah na zauna kusa da ita ta riƙe hannu ɗayan hannunta kuma ta nata share mata hawaye,"Amma daman kin san shi? ya taɓa yi miki wani abu ne?"
"Aliyu! ne bazan ta ɓa manta da fuskarsa ba!"
"Amma wannan fa Asad sunan shi ba Aliyu ba"
"Haba Nainah ta ya zaki ce min wannan ba Aliyu ba ne wani ne can dabam?"
"Amma gaskiya ne Nainah ta faɗa Miki sunansa Asad ɗan matarda ta wuce ne ɗazu, sai dai idon kama ce?"
"Amma gaskiya ne ta faɗa Asad sunansa ba Aliyu ba" Nainah na faɗi hakan ne domin Hankali Amma ya kwanta.
Washegari Ya farka da wuri saboda be samu kwanan ba har garin Allah ya waye, akwai gajiya sosai a tare da shi amman ko da wasa bacci be ziyarci idonsa ba. Bayan sallah asuba ya dawo dakinsa ya zauna, idonsa na masa nauyi na rashin samun bacci da be yi ba jiya, a yadan bangaren kuma tunanin Nainah ya cika masa zuciya, baya jin zai iya janye ya bawa wani damar daukarta a matsayin mata bayan shi ya fi kowa cancantar ya malleketa tun Idanunsa suka yi arba da mata masu kyau masu aji masu natsuwa da hankali ya so mata da yawa saboda kyau amman be taba ganin wacce hankalinsa ya kwanta da ita kamar Nainah ba, kyauwonta ya dauki hankalinsa sosai be taɓa jin son wata kamar Nainah ba, wani bangare na zuciyarsa yake jinta dabam, ta ina ma zai iya yafe ta a zuciyarsa idan har ya yarda yace zai yafeta hakan na nufin ya zama ragon maza kenan. Kurciyarta kyawunta na daga cikin abunda yasa yake sonta💋
A hankali ya nufi gaban ƙaton madubinsa ya tsaya yana ta kallon kansa, a zahiri kansa yake kallo amman a baɗili tunanin mafita yake, har ga Allah yana son Junainah shi a yanzu ma yaji yana bukatar aure daman rashin samun wacce tai masa ne yasa shi be maida hankali gurin auren ba, amman yanzu ya yana jin son aure sosai a ransa, kuma yana matukar jin kaunar Nainah a Zuciyarsa.
"Wannan shi ne karo na farko daya kamata na mallaki abunda na ke so, wannan shine lokacin ya da ce da zan tsayawa kaina da kaina, ba zan iya barin wannan ta wuce ni ba, idan har ba zata so ni to be kamata ta so Deedat ba, idan har zan iya hakura na kyaleta to ko ba sonta na ke da gaske ba!"
Magana yake da kansa yana kallon madubin dakinsa, yana jin wayarsa na ringing amman ya ki ya duba mai kiran ma balle ya daga. Toilet ya shiga yai wanka yana fitowa ya shirya cikin kananan kaya sannan ya dauki wayar yana duba miss calls din da Ummy ta jera masa, kiranta yai da dayan layinsa da be cika kiran mutane da shi ba.
"Ummy ina kwana"
"Lafiya lau, ƙarfe nawa ne jirgin naku zai ta shi?"
"2:30"
zaka shiga kafin ka wuce ko daga office zaka wuce?"
"Office zanje yanzu,zuwa 12:30 zan shigo"
"Okay"
Sannan ya kashe wayar yana sauke Ajiyar zuciya. Yana fita ya nufi ɓangaren Umma ya gaisheta daga nan ya yi mallama domin daga wajen aiki zai wuce Abuja, ta yi mishi Addu'ar a dawo lafiya. sannan ya wuce wajen iya, zaune ya same saman Darning suna karyawa tare da Baba, da Baby, ya gaishesu sannan Baby ta gaida shi a gaggauce ya sha tea sannan ya yi musu Sallama ya wuce office, kaman yadda ya faɗa 12:30 nayi ya yi Sallama da mutanen Company kana ya barma Deedat sakon Ayyukan masu mahimmanci da zaiyi kafin ya dawo.
Yana isa gidan Ummi ya ci abinci sannan itama ya yi mata sallama ya wuce ya so ya biya Asbiti amma ganin lokaci yana neman ya kure masa yasa kai ya wuce Airport 2:30 dai dai jirginsu ya ɗaga zuwa Abuja.
*********
*ASAD*
Satin Asad ɗaya a Abuja ya tattaro ya dawo, saboda gabaki ɗaya hankalinsa da tunaninsa suna wajen Nainah abin da ya Kaishi ma bai samu daman gudanar komi yadda ya kamata ba a kullum da tunanin Nainah ya ke kwana da ita yake tashi, hakan yasa ya dawo dole ba don ya so ba. ranar da ya dawo a ranar Deedat ya wuce Abuja saboda ya ƙara sa aiki da Asad bai samu damar ƙarasa wa ba.
*NAINAH*
Alhamdulillahi cikin satin ɗaya Amma tana ta samun lafiya,a yadda ta ke ganin ta samu sauki a yau kawai ta gode Allah ba adadi, domin idan abun ya daure a haka Amma ta dauko hanyar samun sauki sosai, Da dare Afra da Afreen suka kawo musu abincin dare sosai suka so ta bi su zuwa gida amman ta ki, ko ba komai na san Amma zata fi sakewa idan ta gan ta zata fi sakewa ita ma kuma hankalinta zai fi kwanciya idan ina ganinta duk kuwa da na san ba wani maganin zata iya mata ba.
****** ****** *****
*BALARABA*
A hankali ta yi parking motarta gefen titi ta fito kai tsaye ta nufi wajen wani mutum dake zaune saman keke irin ta guragu wata mata na tsaye a bayansa, "Baba Musa!" ta fa dai dai lokacin da ta ƙara so wajensu, mutum da aka kira da Baba Musu ya ɗago ya kelleta, akaro na biyu ta sake cewa,'tabbas sune" sai ta fashe da kuka tana faɗin,'Baba Musu me ya same ka? Maman Nana me ya faru da shi?"
"Boyar Allah wace ce ke!"
"Balaraba ce tsohuwar matar Aliyu" ta faɗa hakan ne domin su gane ta.
"Allah sarki! rayuwa kenan Anty Balaraba ashe zamu sakin ganin ki?"
"Me ya samu Baba Musa?"
"Ba shi da lafiya"
"Kusan duk lokacin da na biyo hanyarnan sai na ganku, Zuciyata na raya kune sai Allah ya kadda na tsaya, shekarun baya bar gidan naje amma ban same ku ba na tambayi makwota sunce ba su san inda kuka koma ba, tun daga lokacin nake roƙon Allah yasa na ganku, Alhamdulillahi kuma Allah ya karɓi Addu'a ta, bari na kira motar Asibiti a wuce da Baba Musu domin yana buƙatar ganin likita"
Nan take ta kira Adnan ta faɗa masa inda take, bayan Mintuna goma sai kaga motar ɗaukar matar lafiya sun iso suka ɗauƙi Baba Musa suka wuce dashi Maman Nana ko ta shiga matar Ummy ta mara musu baya.
Suna isa Asbiti Aka soma ba Baba Musa agajin gaggawa saboda yanayin jikinsa na tsufa.
Maman Nana ko faman godiya ya ke Ummy, "Ina Nana halam?"
Maman Nana ta yi zugum cikin wani irin yanayi ta ce,"Nana Allah ya yi mata rasuwa wajen Haihuwa shekara biyar da suka shuɗe"
"Innalillahi wa'inna Ilaihir raji'un! Allah ya gafarta mata Allah yasa ta huta!"
"Amin ya rabbi"
"Ya bayan Rabuwa?"
"Alhamdulillahi, mun gode Allah"
"Ai a lokacin ina ta sauraren ko zanji labarin Haihuwar ki amma shuru" Ummy ta yi Murmushi yana wasa da key ɗin motarta."tun yaushe Baba musu ke fama da ciwon nan?" Ummy ta jefo mata tambatayar.
Maman Nana ta sauke Nannauyan Numfashi kana ta ce," kusan sheka goma kenan yana jinyarnan munyi yawon Asbiti amma ba wani ci gaba haka maganin hausa ma ba kalar da ba yi ba amma sauƙi yana wajen Allah, dole muka haƙura saboda halin talauci ga reshin muhalli Abubuwa dai sai godiyar Allah"
Ummy bata bar Asbitin har Saida ta tabbatar da komi ya dai dai sannan ta wuce gida,
"Ummy sannu da zuwa"
"Yauwa"
"Ummy Yah Asad yazo baki nan Amman yace an jima zai dawo, Daddy ma ya dawo har ma ya sake fita"
"Okey"
Kana ta wuce ɗakinta ta watsa ruwa, bayan Isha'i ko sai ga Asad ya sake dawo wa bayan sun gaida Ummy ta sanar dashi Baba Musa da aka kwantar a Asbiti.
"Ayya Allah ya shi lafiya"
"Amin ya rabbi, ina buƙatar gida zan mallakama Baba Musa saboda wani taimako da ya yaɓa min wanda Bazan taɓa mantawa ba."
"Okay Ummy......"
AFTER THREE WEEKS
***** *****
Gaba kiɗayansu suka waigo don son ganin mi ke faruwa, saboda ihun da