Bin Maryam Book 1 Sadiya Kaoje

Author :  Humaira Bulama Category :  Read Hausa Novels

Chapter   16 / 30

45K to 48K   out of 87.6K words

daga ta nufi gidan ƙawarta basu da wani nisa sosai suma dai talakkawa amma ba kamarsu ba gidansu bukka ukku ne sannan Bansu na aiki a wani Campany. tana isa gidan ƙarwar Tata Jamila ta rungume tana faɗin,"yau kin tuna dani?"

"A'a wallahi Jamila kinsan bani da lokaci kullum ina wajen talla, yanzu ma ban jima da dawo ba shine nace bari nazo mu gaisa"

"tun ɗazu kike faɗomin a rai, yanzun nan nake da niyar zuwa gidan ku"

Nainah tayi Murmushi tana faɗin,"Ina Inna da Baba?"

"Ina tana ɗaki Baba Kuma bai taso wajen Aiki ba"

A hankali suka wuce cikin ɗakin kwance suka same Nainah ta durƙusa har ƙasa tana faɗin,"Inna ina wuni"

"Lafiya lau Nainah ina Murjanatu?"

"tana gida"

"Ki gaisheta idon kinje gida"

daga haka ta fice daga ɗakin ta barsu, Nainah ta ɗauƙi littafin fin dake gefenta tana karanta abinda aka rubuta,"Jimilla Admus" Jamila ta kyalkyece da dariya tana faɗin "Jamila Adamu yake ba Jimilla Admus ba"

Nainah tayi dariya domin itama sunan ya bata dariya sosai, "Jamila wallahi ina son nayi karatu a rayuwata ina son nayi boko, ina son nayi karatun Addini amma ba hali, Abbana ya so nayi karatu kaman me amma babu hali gashi har Allah ya yi mishi rasuwa" ta ƙarshe maganar Kwalla na zubo mata.

Cikin sanyin Murya Jamila ta ce,"kiyi haƙuri Nainah komi zai wuce wata rana sai labari, in sha Allahu Allah zai cika miki burin ki nayi yin karatu"

"Ta ya Jamila?"

"Allah!"

"Kin gama Magana tunda ki ka ce Allah"

"Amman me zai hana ki canza sana'a Nainah ta yadda zaki tara kuɗi masu yawa da zaki ware wani abu daka ciki kina karatu, tun da ita makarantar Gwamnati baya da wani tsada, Uniform kawai zaki saya da littafai sai kudin P.T.A da ke biya shima bai wuce 500 ba"

"Kin kawo shawara mai kyau Jamila, sai dai ban san wacce sana'a zanyi ba a yanzu duka jarin ruwan nawa nawa ne? kuma ga lalurori abinda zamu cima wata rana gagararmu yake, yanzu haka so nake na tara kuɗi a gyara muna bukkarmu inda ke yoyo"

"Allah ya yi miki mafita na Alheri, damu ga baki ɗaya"

"Amin ya rabbi Jamila"

daga nan suka ci gaba da hira Jamila na koya mata karatu, sunyi nisa sosai a karatun suka ji saukar ruwa kaman a bakin kwarya,

Nainah ta miƙe da saurin tana faɗin,"Innalillahi ruwa Jamila wallahi na manta sam da hadarin nan"..

"Daman kin san ruwa tsakiyar damuna ba iska wani lokaci ma ko hadarin babu zakiji saukar ruwa"

"Jamila zanje gida wajen Nainah kinsan ba cikkaken lafiya ne da ita ba"

"Aa Nainah ina zakije cikin ruwan nan? ki ki duba ki gani yadda suke saukowa da ƙarfin Allah ko'ina ya yi dubu"

Hankalin Naina duk a tashe yake burin ta kwai ta ganta a gaban Amma"

Sou kusan Ukku Nainah tana yunkurin fita Jamila na kawota, daga ƙarshe ta saka mata kuka harda shashsheƙa, tsawon awa biyu da rabi ana sheka ruwa masu ƙarfin gaske. A na ɗauke ruwan Nainah ta fice daga ɗaki a guje ta nufi gidansu da lalabe da komi ta samu ta iso gidansu saboda hanyar cike ta ke da ruwa ga duhu da ya mamaye garin gabaki ɗaya, ko'ina tsit banda kukan kwaɗɗin babu abin ke ta shi,

tunda ta shigo gidan gabanta ke faruwa Jikinta na karkarwa saboda sanyi cikin wani irin yanayi da batasan na miye ta fara lalaben ƙofar shiga bukkarsu. dai dai lokacin kuma akayi wata irin walƙiya mai bala'in haske, dai dai lokacin kuma Idanuwanta suka sauka a kan Bukkarsu da rebinta duk ya zube ƴar gina kaɗan ta rage.

cikin matsancin gigicewa Nainah durƙushe a ƙasa tana wani irin kuka mai cike da tashin hankalin da fargaban abin Idanuwanta suka gane mata, a karo na biyu aka koma yin walƙiya mai haske hakan ne ya bata damar ganin wajen da kyau, hankali a tashe ta fara lalaben wajen tana kiran,"Amma" cikin rawar murya kusan mintuna biyar ta dauka tana abu ɗaya saboda tsantsin dake janta, can Hannunta ya sauka a kan hannun Amma a gigice ta riƙa sauke ginin a Jikinta ta ɗagota ta rungumeta a jiki ta fashe ta kuka mai tsuma zuciya, cikin ƙarfin hali ta shiga jijjigar Amma tana kiran sunanta,"Amma! Amma!! don Allah ki ta shi bani da kowa a faɗin duniyar nan sai ke! Amma don Allah ki buɗe idonki ki kalleni Nainahr kice" sai muka kukan yaci ƙarfinta, Kuka take Jikinta na karkarwa saboda sanyi gawani irin ciwon kai da zazzabin dake taso mata so take ta koma gidan su Jamila amma kuma bazata iya ɗagawa koda na daƙiƙa ɗaya ne tabar Amma a cikin halinta dake ciki. Tana rungume da ita tana kuka har garin Allah ya waye.

A gaggauce tayi Alwalla ta raɓe wani ɗan gefe da yasha iska tayi salla, tana gama salla ta nufi bakin titi da matsanancin gudu har tana faɗuwa saboda hanyar a jiƙe take har yanzu, tsawon mintuna goma tana tsaye a wajen kafin ta samu mai Napep, har ya tafi ya dawo murya na rawa ta ce,"Don Allah Asbiti zaka kaini amma sai mun ɗan shiga lungu can na ɗauƙi Mahaifiyata, "Gaskiya banza Iya shiga hanyar bata da kyau"

ta durƙusa har ƙasa tana haɗe Hannayenta kaman mai rogon gafara,"Bawon Allah don Allah kayi haƙuri ka taimakeni karna rasa Mahaifiyata ita kaɗai gareni"

Tana ƙarasa maganar tana share kwalla, tausayinta ya kama mai Napep,"mu tafi" ya faɗa yana kallonta,

" Na gode"

Kai tsaye suka wuce wajen Bukkar tasu, da taimakon mai Napep ɗin suka shigar da Amma ciki Nainah ta zauna tare da Kwantar da ita saman cinyarta tana hawaye, sai yanzu ta kare ma fusakar kallo duk ta kumbura ta sauya kammani tamkar ba kyakkyawar fusakar Amma ta ba, mahaifiyarta ita ce duniyarta, ta gwada kokarina akan ta tsagaita kukanta sai ta gano ashe ita ba ba Jaruma ba ce a gafen dauri, kai tsaye mai Napep ya wuce dasu Fati Lami. lokacin da suka isa emergency sai suka karbe ta cikin gaggawa, a sai a lokacin na tuna ba ko sisi a jikinta ta nufi wajen mai Napep tana zarar ido cikin ɗan rawar murya ta ce,"Uhmmm... Na wa... ne kuɗin ka?"

A bazata ta ji ya ce,"ki barshi kawai Allah ya bata Lafiya".

"Na gode sosai Bawon Allah, Allah ya saka maka da Alheri"

Ya ce,"Amin" kana ya ja Napep ɗin sa ya yi gaba,

Kasan cewar koda suka iso ana mopping ta ɗan raguɓe ga gina kamar sauran talakawa irinta wadanda suka tsaya suna jira a gama mopping din sannan su wuce, masu hannu da shuni kan da masu galihu wucewa kawai suke ba tare da an tsayar da su ba, masu aikin sai mika musu gaisuwa suke.

tana ganin an kammala mopping ɗin ta wuce idon Amma take kwance, wata daga cikin Nurses din da suke tsaye a ta daka mata wata irin tsawa data saka hantar ciki ta kaɗawa."Ke! ki ka fi kowa a nan ne da za ki tsallako ki wuce gurin be gama bushewa ba"

da sauri ta koma ina take tsaye ɗazu, alama idan ta sake yunƙurin take wajen za tai ta marinta.

wata Nurse ta nufo inda take tsaye tana ya mutsa fuska tana mata wani irin kallo mai cike da reni,ta kawarda kai gefe tamkar bata ganta ba,"ki je ki sai kati idon har kina son a duba Mahaifiyarki"

ta fice da sauri zuwa bakin titi ta hau majin zuwa Unguwarsu lokacin da suka iso ta nufi cikin bukkarsu mai mashin dinda ya kawo ya biya da kallo, tsaye tayi tana kallon sai yanzu ta lura a she harda ban ɗakinsu ya faɗi.idonta cike da kwalla, tana jin tausayin kansu, cikin sauri ta shiga namen Asusun can ta hangeshi gafen ginar da bata faɗi ba ta sauke Sassanyan Ajiyar zuciya tana godiya ga Allah, a hankali ta nufi wajen Asusun ta durƙusa a ƙasa ta ɗagashi da hannu biyu ta sake shi da ƙarfe nan ta ke ya fashe ta kwashe kuɗin ta zuba cikin pos sannan....

Suna isa Asbiti ta sallami mai mashin sannan taje ta biya kudin katin sai kuma aka ce likita na son ganina. Da sauri na nufi inda Nurse din ta nuna na tura kofar office din ta shiga hankalina a tashe fuskata duk hawaye ya bata ta,

"Wata mata mai farin kaya ta ce kana son ganina"

"What'sis your Name?"

Likitan ya tambayeta yana mata wani kallo daga sama zuwa kasa, duk wanda ya kalli sutura baya bukatar ta fada masa cewar ba mu da shi, tufafin da take sanye da su kawai sun wadatar su isarda sakon talaucin da suke tare da shi.

"Hey I'm toking to you"

Ya sake yin magana a garo na biyu,

Ya ɗan sauke Numfashi cikin hausarsa da bata fita sosai ya ce,"Ya sunanki?"

"Junainah Yusuf"

"Okey, Kai ka kawo Murjanatu Usman".

"Ehhh Mahaifiyata ta ce"

"Mamanka ya samu matsala a ƙashin bayanta saboda wani abu mai Nauhin da ya faɗo mata a baya, don haka sai anyi mashi aiki Kuma yana bukatar aikin cikin sauri"

Juyowa tai idonunta na zubar da kwalla ga girgiza masa kai dan bata ko iya magana saboda kukan da ta ke.

Kaje ma biya kudin da za'ayi mata aiki,

ta gyada masa kai.

"Bude baki kayi magana mana"

"Wallahi ba ni da su ban san inda zan samo ba, bani da kowa sai Mahaifiyata"

"Okay zaka iya tafiya idon ka samu kuɗi sai kazo a mata aiki"

Ta fice daga ɗakin zuciyarta na mata zafi, can bayan wani icce ta koma ta lissafa kuɗin duka duka dubu takwas da ɗari biyar ne. ta mike tsaye cikin kuzahari ta nufi wajen Zaliha mai abinci kasan cewar daga fati lami zuwa tasha ba wani nisa, tana isa wajen Zaliha ta rushe da kuka, da kyar Zaliha ta kallesa tare da tambatayar mike faruwa tana kuka ta zaiyanama komi, Zaliha ta sake Nannauyan Ajiyar zuciya, ta kalli Nainah da tausayin ya cikata,"kayi haƙuri Nainah Allah ya kawo muku mafita Allah ka Amma Lafiya, ta ƙirga 5k ta bata ga wannan ba yawa kaji in sha Allahu an jima zan shigo.

Nainah ta yi mata godiya sosai kana ta wuce,

Ƴan kudin da suka ragemata ta biya kudin magani da ruwa daka ƙara mata, Hankalinta ya tashi sosai lokacin da yamma ta gabato Amma bata ko matsa ba balle ta bude ido, . ga yunwa ta sata a gaba tana ta cinta ta gagara kai ko da ruwa a bakinta Shiru shiru babu wanda ya sake leko inda Amma ta ke kwance har bayan Isha'i,

Bayan ta gama salla Isha'i ta ɗaga Hannayenta sama nata kai kukan ga Allah,

tana zaune ta hango Amma na motsa har tana ƙoƙarin bude idanunta, da sauri ta mike tsaye cikin farin ciki,

"Amma! Buɗe idonki ki kalleni Nainah ce"

.Shiru bata amsa ba sai juya kan take kamar bata cikin hayyacinta,

Da sauri ta nufi wajen Nurse's,

"Don kuzo ku duba min Mahaifiyata ta farka Amman bata magana" ta faɗa cike da damuwa.

wani irin kallo kamar na kyama suka riƙa binta da shi, a hankali ta kalli tufafin jikinta sunyi Masifar ɗauɗa don jiya da Daddare duk birgimar da tayi a cikin lakar Bukkarsu kayan ne a Jikinta, sai dai ba da dauɗar ta ke a yanzu ba ta lafiyar Mahaifiyarta take.

"Wannan ƙazamar fa daga ina? Wallahi har ɗoyi take"

Ita dai bata ce musu uffan ba.

"idan kuma ba ka kula su ba ace ba ka yi aikin ka ba"

Sai sauran suka saka dariya, sai duk ta ji babu dadi amman hakan be hanakin sakin Murmushi ƙarfin hali.

Jiki a mace ta dawo wajen Amma ta zauna, har washe gari bata runtsaba kuma baci komi ba.

Wuraren ƙarfe goma na safe Zaliha ta shiga Inda muke tare da kular abinci da ruwa da kunu, ta saki murmushi farin cikin bayan mun gaisa ta tambaye ya mai jiki.

"Alhamdulillahi Anty Zaliha"

"Nainah amma yunwa kake ji ko?"

ta fashe da kuka tana faɗin,"Anty Zaliha tun jiya banci abinci"

"Subuhalillah! Haba Nainah ka Kyau ma kanka nna zama da yunwa?"

Kunun ta tsiyayamata a kofi ta zuba ruwa ta motsa sannan ta miƙa mata,"maza ƙarɓi ka sha"

Jikin Nainah na rawa ta ƙarɓa ta shanye shi kunun tas, Zaliha ta miƙa mata abinci da ta zuba a plate ,"Oya maza kaci"

"Na ƙoshi Anty"

"Oya muci tare"

"A'a na ƙoshi" Zaliha ta watsa mata harara ba musu ta saka hannuta suna ci tare Zaliha na janta hira har suka canye a binci tas,

"Na gode Anty Zaliha"

"Ya ake ciki batun aiki?"

"Sunce saina mawo kuɗi masu yawa sannan zasu dubata"

Zaliha ta suke Ajiyar zuciya kana ta miƙa mata kuɗi, "ga wannan jiya na faɗa ma mutanen shata abin da ya faru dakai shine suka haɗa kuɗin nan suka ce a baki dubu goma ne"

Nainah ta rungumeta Zaliha yana cin kyaunar na a ranta,"Na gode sosai Allah ya bar zumunci"

"Amin"

Ni zan zafi"

"Allah ya tsare"

ta bita da kallon kauna kauna irin ta wanda ya taimake ka a halin da kake da bukatar taimakon. A daren Amma ta farka sai dai tana yawan ƙorafin bayanta na ciwo sosai. Harda kunu ta sha a daren sai da tai tas ta ci ta koshi sannan na kwanta kan shimfidar da Anty Zaliha ta kawo mata.

Washe gari mutanen ta sha suka zo tare da Anty Zaliha da ta kawo muna abinci wasu daga cikinsu ko saninsu bata yi ba da zasu tafi suka ƙara bani 5k.....

Wasa wasa Saida suka shafe sati biyu a Asbiti,har zaman ya fara gundurarta ita kanta Amma da ke ciwon ta fara gajiya, kullum addu'ar Allah ya bata lafiya take bar asibitin, kullum nata kwance tsawon satin nan biyu kullum sai Zaliha ta kawo musu a bunci sau ukku a rana.

Ranar Amma ta tashi da matsanancin ciwon baya harda kukanta, Hankali Nainah ya yi Masifar tashi, ta shirya ta je gidan ƴan kwanan su da kayan aikin su masu amfani ta haɗa takai jari bola ta Saida aka bata 3k ta nufi pharmacy aka haɗa mota maganin ciwon jiki masu ɗan sauƙi ta bata Amma ta sha ko zata zamu sauƙin raɗadin da take ji.

Idon ta fito wajen sai ta zauna a ciki tai ta kuka, bata san abunda Allah ya tsara ba, ban san abunda zai faru gaba ba, Amma zata tashi ko ciwon zai yi ajalinta duka bata sani ba, zata rayu da ita na wani lokaci ko a'a duka bata sani ba. Iyakar abunda ta sani kuma ta ke da tabbaci akansa shine mutuwa kuma Allah baya barin wani dan wani, sai dai ta san twna son rayuwar Amma fiye da ta kowa duniya, ta rasa mahaifi shekara huɗu da suka shuɗe, sai ta ji kamar ba zata iya hakurin rasa Amma a yanzu ba.

Saida tayi kukanta mai isarta ta koma wajen Amma ta zauna a kujerar da ke fuskarta Amma, ita kuma tana daga

Kwance ta rame sosai sai sauke ajiyar zuciya take tana kallon mutane da ke kai kawo a cikin ɗaki, wani irin tausayinta Amma ne ya kamata da kuma tausayin kanta............✍️

More comments and share pls!



*Sadeeya Ka'oje ce 💋✍️*

💋𝐁𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐘𝐀𝐌💋

𝑵𝒂

𝑺𝒂𝒅𝒆𝒆𝒚𝒂 𝑲𝒂'𝒐𝒋𝒆

08149979652

https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj

𝑷𝒂𝐠𝐞 31-32

______"Amma" ta kira sunanta a hankali, a hankali ta juyo ta kalleta sai ta ga hawaye a idonta, ba ta damu da sharewa ba saboda tasan koda ta ga hawayen babu abunda zata boye mata.

"Amma"

"Mike damunki ?Wani gurin na miki ciwo? na kira likita"ta tambaya hankali a tashe ta komawa saman gadon asibitin inda take kwance ta zauna kusa da ita.

"Nainah yanzu idon na mutu baki da kowa a duniyar nan, ba mu da gida ba mu da komi Nainah, don Allah ki riƙe mutunci duk runtsi, kar wani ya yau dareki da sunan taimako ya keta kimi mutunci ki Nainah!"

Iyakar kokarin da tai shine ta rike kuka da hana hawaye taruwa a idonta, cikin rawar Murya ya ce ,"Zaki ji sauƙi Amma da ƴar da Allah, muci gaba da rayuwar mu kaman yadda muka saba"

Ta fada tana ina nuna mata kamar babu wata damu a tattare da ita.

"Amma na yanke shawarar mu koma gida, zan ci gaba da neman kuɗin da za'ayi Miki aiki. ki kwantar da hankalinki zan samu kudi zan biya a baki magani, kuma za ki warke za ki tashi, domin sun ce idan anyi miki aiki za ki samu sauki da yardar Allah"

Hawayen idonta ta share tana sauke ajiyar zuciya,

"Nawa ne kudin aiki?"

"Dubu hamsin"

ta mata karya saboda hankalinta ya kwanta, Amma ta lumshe ido hawaye suka sauko mata, a take ta ji duk wani kuka da ta ke kokarin dannewa ya tafi sai ta nemi rashin kuzarin ra rasa, wani karfi da shaukin neman mafitar inda zata nemi kudi...

kai tsaye Nainah ta wuce wajen Zaliha ta bata kuloli da ta kai musu abinci daga nan ta faɗa mata zasu koma gida ta nemi aiki koda aikataune, "To Nainah Allah ya baka Sa'a"

"Amin Anty"

"Ga wannan kayi kuɗin mashin ta bata 1k godiya sosai tayi mata sannan ta wuce, Kasancewar da

16 / 30