Bin Maryam Book 1 Sadiya Kaoje

Author :  Humaira Bulama Category :  Read Hausa Novels

Chapter   21 / 30

60K to 63K   out of 87.6K words

ta turomin Account number ɗinta, Umma ta faɗa mata duk abin ya ce suna gama wayar ta Turo Account number ɗin ta Asad ya tura mata 100k ta kira ta riƙa zuba Mishi ruwan Albarka....Kai tsaye Asad ya wuce kamfaninsa saboda akwai wani abu da Zaiyi mai matukar mahimmanci so yake idon ya gama ya wuce gidan Mansura ta kaishi gidan su Nainah.

*NAINAH*

Da tunanin samun mafita ta kwana har garin Allah ya waye, bata samu baccin kirki ba saboda tunani da kuma nishin da Amma take yi. Bayan ta gama salla ta kunna kara ta tafasa ruwan zafi ta haɗa mata tea ,ita ma ta kasa cin komai. Sai da ta tabbatar ta koshi sannan na fito da ita na gyara mata jikinta na sake gyara dakim na saka Hijab ta ta fice daga gidan tana tafiya batare da tasan ina ta nufa, dai dai lokacin ta iso wani ƙaton kamfanin mai kyau, haka kawai ta ji bari ta shiga ciki ta nemi aiki koda shara da mopping ne ko Allah zai sa ta dace.

Ta buga gate mai gadi ya leƙo yana faɗin,"boyar Allah Lafiya?"

"Don Allah aiki nake nema koda shara da mopping ne"

"Ki yi haƙuri boyar Allah akwai masu aiki cike"

"Don Allah Bawon Allah ka taimaka min Mahaifiyata ta ce bata da lafiya shine nake neman aiki domin na saya mata magani".

Mai gaɗi duk sai ya ji tausayinta,"muje wajen Oga Allah yasa a dace"

"Amin"

Ya fada yana nufar cikin kamfanin.ita dai tana tsaye kusa da gate din har ya shiga ciki sai ta hango Asad ya fito sanye da kananan kaya sunyi Masifar yi masa kyau daga can ya tsaya yana kallonta kamin ya ya doso inda take tsaye............✍️

More comments and share pls!



*Sadeeya Ka'oje ce 💋✍️*

💋𝐁𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐘𝐀𝐌💋

𝑵𝒂

𝑺𝒂𝒅𝒆𝒆𝒚𝒂 𝑲𝒂'𝒐𝒋𝒆

08149979652

https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj

𝑷𝒂𝐠𝐞 37-38

______Me yasa zaki tafi batare da sani na ba?"

"Daman halam zaman ka nake? ba zan zauna idon za'a walakantani saboda halal ɗina"

"Idan kuma ke kika samu matsala?"

" jiya ba tai bacci ba saboda azabar ciwo, bata iya tashi komai a inda take take yinsa bata gane kowa ni ma da nake yarta bata gane ni ba, kuma ba mu da inda za mu babu wanda zai taimaka mana ina son mahaifiyata bana son ta mutu"

ta karasa maganar tana kuka mai karfi daman tun da ta soma maganar hawaye ke sauko mata. Shi ma hawayen ta gani a idonsa sai yai saurin daga kansa sama ya zuba hannayensa aljihu yana cizon leɓensa.

Duƙawa tai a wajen saboda kukan da ya ci ƙarfinta, ya bar ta a wajen ya nufi wajen motarsa be dade ba sai ga shi ya dawo rike da gorar ruwa masu sanyi dayan hannunsa kuma rike da tissue, ya nufo inda take, tissue ya fara bata tare da ya ce mata komai ba, ta karba ta share hawayenta sannan ya bude gorar ruwa ya miƙa mata, Karba tai ta sha rabin ruwan ta sauke Sassanyan Ajiyar zuciya ta aje goror ruwa a kasa ta miƙe tsaye a hankali ta ɗago sai taga ita yake kallo bai ko kyaftawa, ta kawar da fusakarta gefe tana share kwalla.

"Ina Mahaifiyar ta ki?"

"Tana gida?"

"Wane gida"

" gidan ƙawata bukkarmu ta faɗi shine mahaifinta ya bamu bukkar ɗaya muna zama duk wata muna biyansa dubu biyar"

Shiru yai be ce komai ba har na ɗan wani lokaci idonsa na a kanta bata san abunda yake kallo a jikinta ba.

"Muje Office ɗina ki zauna kafin na kammala wani aiki"

Yana fadar hakan ya juya da niyar komawa ciki sai kuma ya juyo ya kalleta ganin ta tsaya a gurin ta ki bin bayansa.

"Bazan je ko'ina ba"

Ta fada ta turo baki ba tare da ta kalleshi ba. Matsowa yai kusa da ita sosai kamar zai hade jikinsu gabanta ya soma faduwa kamshin turarensa ya cika mata hanci sai ta ɗan matsa baya tana kallonsa ido,

"Bana son gaddama,"

Yadda ya yi maganar kaman yana bata umurnin,

Kara tubo masa baki tai ta juya sai ta ji ya fisgota da mugun karfi juyo da ita suna fuskantar juna

"Wuce ki shiga na ce"

Ya fada cikin muryar dake nuna bacin ransa yana zare mata ido.

"Haka kawai zan shiga ciki, ni ba ƴar iska ba ce"

Cikin daga murya ta yi maganar har Mai ma'aikatan Kamfanin suka juyo suna kallonsu Matsowa yai da fuskarsa yana fitarda numfashi da karfi.

"Ke! ba ƴar Iska ba ce amma ki ke bin Deedat ku tafi cikin gari?"

Yana fadar hakan ya sake ta da karfi har tana ture baya kamar zata fadi, sannan ya juya ya koma ciki ya ta a wajen tsaye. Juyowa tai tana kallon mai gadi,"Don Allah waye Ogan wajen nan?"

Mai gadi ya yi Murmushi yana faɗin,"ai shine mai wajen"

ta bar wajen cikin rashin jindadin domin haka ta bata cin ma ruwa ba, daman nasan indai shi ne za ko zai sai ya wulakantanta tunda dan wulakanci ne. Har ta kama hanya sai kuma ya juya na koma saboda bacin ran daya same ni gate din ta buga da karfi mai gadin ya sake leko ganina ya bude min karamar kofar.

Da sauri ta nufi ciki shiga ƙofar da taga ya shiga, ta riƙa buga ƙofar da ƙarfi, mutane suka taru a wajen suna Kallonta security kuma suna ƙoƙarin fitar da ita amma taƙi.

A haukace take ,"faɗin ka fito ka biyani kudin da Deedat ya bani, mugu kawai Azzalumi Wallahi sai Allah ya saka......"

Bata karasa ba ya bude kofar tai yi shiru kaman ba ita ba, hannunsa rike da waya da kuma keys din mota, kamshin turarensa duk ya cika gurin shi kuma ya yi mats fadi a ido tsoronsa ya cika zuciya, ba kuma tsoro kar ya dake ta ba, yana da wani irin kwarjinin da ke saka mutun tsoro na rashin dalili. Yana tsaye jikinnkofar daga ciki ita kuma tana daga waje idonsa a kanta kamar yana hararata kuma ba harararba. Juyowa tai ta sauko daga gurin na nufi gate ta fice abuna ba tare da ta kara cewa komai ba, shi ma kuma be ce min ba, hanya ta biyo ta tunanina kala kala na ciwon Amma neman maganinta Da karfi aka faka mota gabanta sai na ga an turo ganbun motar an bude shi, sai ta ga Asad ne a ciki yana kallon wani gurin, ba zai iya cewa na shigo ba saboda bakin girman kan tsiya, idan ma ta shiga bata san inda zai kaita ba, sai akwai tai gaba abunta ta barshi a gurin. Sai ya kara cin gabanta da motar ba tare da ya yi mata magana ba ita ma ta kara yin gaba, sai ya fito daga cikin motar ya biyo bayanta ya fisgo kafadar Hannunta ya dawo da ita ya saka ta cikin mota da karfi ya rufe motar ya zagayo gefensa ya shiga ya hau titi ba tare daya kalleta ba.

"Ka sauke ni mugu kawai"

Ta fada tana saka dayan hannunta ta murza inda ya riƙeta cikin kukan da ta fara tun a lokacin daya riƙota ya saka ta cikin mota domin ba karamin riko ya yi ma ba don har yanzu tana jin ciwo a guri. Wayarsa ya ciro ya kira ta sakata a speaker sannan ya ajeta samman cinyarsa yana tuƙi ringing ukku aka ɗaga.

"Ya Asad ina kwana?"

"Lafiya lau"

"Ina da patient ne ambulance nake so yanzu nan"

"Subhanallahi waye ba lafiya? Yah Asad?"

"Baka santa ba"

"Wani guri ka ke zan saka a turo maka yanzu?"

Sai yai shiru be ce komai ba, jiran yake tai magana ita kuma bata sammaci hakan ba tun da taga ko kallonta be yi ba.

Shin shuru Adnan ya ce,"Yah kana jina?"

"Idon na isa gurin zan turama da Address ɗin"



"Okay"

Sannan ya kashe wayarsa, ba tare da ya kalleta ba ya ce ina ne Unguwar ku?"

"Takalau"

Kai tsaye ya wuce can bayan sun iso ta nuna Mishi gida, ya yi parking sannan ya tura ma Adnan Address ɗin ta fice daga cikin motar ta wuce bukkarsu ta ƙara gyarama Amma jikinta ta saka mata hijabi, cikin ƙanƙanen lokacin ƙatuwar motar Asibitin ta iso a Jikinta An rubuta *BIN MARYAM*

ta zauna kusa da ita tana ta kallonta kamar bata gane ta ba har yanzu. Tana jin lokacin da motar asibitin ta tsaya sai na ji muryar maza biyu sun doso Bukkarsu

“Ina marar lafiyar take?”

“Gata nan”

Ta fada da sauri ina mikewa tsaye sai suka shigo suka dauki Amma suka fita da ita zuwa cikin motar asibitin Inna da Jamila suka tsaye suna kallon su.

"Ni ina zan shiga?"

Ta tambayi mutanen da suka shige cikin motar. Sai na ji muryar Asad yana fadin.

"Zo ki shiga nan"

Da sauri na nufi motar ta shiga daman bata rufe ba, shi ma kuma jin kai ya hana shi rufewa. Da ta shiga motar sai yai mata keys suka bi bayan mutane sai da muka fara nisa sai na ga sun bi hanyar Gesse shi kuma ya dauki hanyar G.R.A.

"Ya naga ka canza hanya? ka kaini wajen Amma na!"

Ta fada ta shirin fashewa da kuka.

"Bana son Surutu"

Shine Kawai abunda ya fada ba tare daya kalleta ba ya cigaba da tukinsa ita kuma na cigaba da kuka har suka isa Ga.R.A, wata hanyar ya biyo inda manya gidaje na alfarma, bakin wani katon gate ya tsaya. Da suka shiga harabar gidan sai ta ga manyan motoci guda biyar a fake kusa da ta farkon ya faka tashi motar ya bude ya fita ba tare da ya ce mata komai ba. Ita na bude ta fito ta tsaya gurin motar tana hawaye gaba daya tsoro ya gama kamata dan a nata tunanin wata kila ma tsafi yake. Da Hannu yai mata alama da na wuce ciki ita kuma ta lake kafaɗarta alamar ba zaba din ba, gaba yai abunsa ya barta bar a gurin tana karewa gidan kallo, yafi gidan su Umma kyau nesa ba kusa ba tana hawaye, gidan be min kama da na yan yankan kai ba amman bata da tabbacin ba cutar da zai yi ba, gashi kuma ya saka an tafi da Amma waya sani ko sani abun za a mata. Karar bude kofar falon taji kamar yadda ta ji lokacin da zai shiga, sai na hango wata farar mace ta fito daga falon ta doso inda take tsoro ne ya kamata a zatona wani abun zata mata ta ƙame jikinta waje ɗaya.

"Ƴata ki dena kuka Kinji zo muje ciki"

ta sa hannu tana share mata hawaye.

"Ina nan ya kawo ni?"

"Gidan iyayensa ne"

"Mahaifiyata tana asibiti ya saka an tafi da ita ban san abunda zai mata ba, bana cikin kwanciyar hankali har sai naji halin da Mahaifiyata ta ke ci"

"Ba cutar da ita zai yi ba, ki aminta da mu Wallahi ba za mu cutar da ke ba, kuma in sha Allahu Mahaifiyarki zata samu Lafiya"

sai ta rumgume ta tana kuka. Shi kuma ya fito daga falon ya nufo inda suka ta yi zaton ko wani abun zai fada mata sai ta ga ya bude motarsa ya shiga.

"Ummi zan tafi Asbitin"

"Okay, duk abin da ake ciki ka sanar da ni"

"Okay Ummi"

Ya fada yana kallonta daga cikin gilashi motar. Sannan taja Hannunta ta nufi hanyar falon da ita, da suka shiga ciki sai taga wannan budurwa ta da ta ba bata 500 saman hanya.

"Sannu da zuwa"

Kai kawai ta gyada musu ta zauna a kujerar da matar ta zaunar da ita Sannan ta zauna kusa da ita ta rike Hannayenta

"Dan Allah ki daina kuka Wallahi raunana min zuciya kike idan kina kukan nan sai ki saka nima kuka"

"Afra Shiga ciki ki hada mata ruwan wanka”

"Aa ba zan yi wanka ba, na fi son naje asibitin kusa da ita hankalina zai fi kwanciya"

"Za a kula da ita za a mata duk abunda take bukata idan ma kinje ba wani abun za ki mata ba, kuma ba cutar da ita zai yi ba taimakonta zai yi"

"Afrin je ki haɗa mata ruwan wonka masu ɗumi"

"To Ummi"

Tana rumgume a kirjinta tana fitarda numfashi a hankali, ta jidadin rumgumar da tai mata rabon dana kwanta jikin Amma a haka har ta manta amman yau wata uwar ta rungumeta ta yi kuka a jikinta ba tare da ta nuna mata kyama ba. Ko da yake ba a fuska da hali ake gane mugun mutum ba.

"Tashi muje ciki Kiyi Wonka"

"Ummi bari na kaita ɗaki na,ai nama santa ita ce wanda ranar da Ice cream ya zube a jikina na sai ruwa a wajent, kin gane Ni?"

A hankali ta gyaɗa mata kai alamar na gane.

Hannunta ta rika ta tashi tsaye taja ta har cikin dakin dan madaidaici mai gado daya da da madubi da durowa guda ukku ɗakin ya yi kyau sosai.

"Ya sunanki halam?"

"Junainah Amma ana kirana Nainah"

"Nice Name, sunana Aysha Amma Afra ake cemin mu ƴan biyu ɗaya sunanta Laila( Afrin) na ɗan fita tsawo ita ko ta fini jiki"

Nainah ta yi Murmushi.

"Shiga ciki sai ki yi wankan bari na kawo miki tufafin da za ki saka"

"Na gode"

Na nufi bandakin cikin tsoro domin ni har yanzu zuciyarta bata natsu da su ba, a dayan bangaren kuma na kasa aminta cewar Asad ba cutar da Amma zai yi ba. Bata wani dade gurin wankan ba ta gama ta dauki zane ta daura ta fito tsoron gashina har gadon bayanta, zaune ta samu Afra saman gado riƙe da kaya

"Ma sha Allah"

Ta fada tana kallonta sai kuma ta aje kayan hannuna ta nufo bayanta tana taba gashinta.

"Nainah da gaske gashinki ne? ko dai kari kikai"

"Na wa ne"

"Ma sha Allah, ga mai can saman madubi da kaya nan saman gado"

Ta fada tana fita daga dakin. Abaya ce baƙa da under wears sabbi sai dan karami dankwali baki. Sai da ta fara saka kayan ciki sannan na saka abayar ta daura dankwalin a fito da tsoron gashinta baya ta zauna kasa, gudun kar ta zauna a saman gadon ya zama laifi komai bata shafa ba duk kuwa da tulin kayan kwaliyar da suke dakin, Kofar dakin aka turo sai ga Ummui ta shigo dauke da plate da kofi.

"Nainah ta shi ki zauna sama gado mana ki ɗauka nan tamkar gidan ku ne, Ki ci abinci kinji ki kwantar da hankalinki ki yarda da mu ba zamu taba cutar da ke ba, kuma mahaifiyarki zata samu lafiya ta warke In Sha Allah"

"Bana jin yunwa, ni wurin Amma na zanje, don Allah ku Kaini wajen Mahaifiyata ko zan samu Kwanciyar hankali, Asad mugune" nan ta labarta mata tun farko haɗuwarsu

Wasu yawu ta hade da karfi tai mata murmushin ƙarfin hali.

"Ba ki fahimce shi bane, amman za ki sanshi nan gaba kadan"

Bata sake cewa komai ba bayan hawaye da ta share tana murza yatsun hannunta ta rasa yadda zata yi zuciyarta ta aminta cewar ba cutar da Amma Asad zai sake yi ba.

*ASAD*

Kai tsaye yana barin gidan Ummi ya wuce *BIN MARYAM HOSPITAL*

duk wani abu da ake ma patient kamin a shiga da shi ganin likita shi yai kama daga karba kati da kaiwa a bude file. Sannan ya kira Dr Yasir ya fada masa cewar ya kawo ta har an shiga da ita ciki, ba bata lokaci Dr Yasir ya iso asibitin sai da Asad yai masa bayanin cewar matsalar ƙashin baya ne sannan ya shiga dakin da aka kaita ya soma bata taimakon gaggauwa shi da wani likitan. Bayan sun fito Dr Yasir ya saka wasu nurses din suka kaita akai mata hoto a aka debi jininta sannan ya canja mata daki aka kaita wani dakin na musamman.

"Sir ya akai aka bar matar nan haka? Ciwon nan yana kokarin cinye ta?"

Lokacin da suka jero suka fito daga Ɗakin ne Dr Yasir ke masa wannan tambayar.

"Ina fatan dai zata samu sauƙi?"

"Zata samu mana, amman dole Saida taimakon Dr Adnan kasan ƙorarrene ta fanni ƙashi tunda Dr Sapwan yana India daman sune likitocin da suka fi kwarewa wannan fannin"

"Abu ya zo da sauƙi" cewar Asad. Don Allah ayi ƙoƙarin ayi mata aiki yau"

"Okey Sir, amma yau aiki bazai samu ba saboda tana buƙatar jini da ruwa shine abunda ta fi bukata, to mun saka mata ruwa jinin kuma na saka a bincika idan kawai wanda yai daidai da nata"

"Ka gwada nawa mana idan zai yi, sai a saka mata"

Dr Yasir ya kalleshi. cike da mamaki,

" ina son rayuwar matar na ko me za ayi pls!"

",In Sha Allahu Sir daga gobe zuwa jibi in sha Allahu za'a mata aiki cikin nasara kuma zata dawo dai dai da yardar Allah"

Asad ya sauke Nannauyan Numfashi kana ya ce,"muje a gwada jinin"

Tare suka juya suka zuwa lap a can aka gwada jininsa da na Amma aka ga zai shiga sai ya kwanta aka cire gora biyu a jikinsa aka sannan ya taso ya fito Dr Yasir ya bashi gangon madara da maltina ya sha.

Kai tsaye ya wuce office ɗin Adnan ya yi masa bayanin komi sannan ya wuce gida, Ummi ta haɗa

21 / 30