Author : Humaira Bulama Category : Read Hausa Novels
na halitta kyau na jiki ko na fuska, ita kanta idan na kalli madubi kyawota tsorata ta yake, hakika ita kanta ta san tana da kyau mai ɗaukar hankali, kyan dake hana ta shakaf a cikin al'umma, gashin kanta kadai idan ta sake ya sauko mutune har mamakin yadda take da gashi suke idon har ta sake shi saukowa ya ke har gadon bayanta gashi baƙi wulik mai tsantsi.
Ba sai na fada ba, duk wanda yasan Fulanin Asali yasan su da kyau da gashi sai dai a cikinsu ita din ma ta dabam ce a bangaren kyau.
"Amma yau ko za'ayi cikinkin ruwan nan tun da ba rana"
"ta ɗago ta Kalleta,"idon baki je tallan nan me zamu ci yau?"
"Shi kenan Amma bari na shirya na tafi"
Hijabinta dake sarkafe ta ɗauko ta saka ta saka tsofaffin ta kalmanta da dake ɗaure da tsumma ta gaba. a hankali ta fito daga bukka ta ɗauki farin boki mai marfi ta ɗaureyi da ruwa sannan ta buɗe tulu ta ƙirga ruwa kwara ishirin ta saka a robar ta rufe.
"Amma na tafi"
Allah ya tsare Allah ya kawo kawo kasuwa mai Albarka"
"Amin Amma"
Ta fada tana dariya ita kuma ya kaɗa kai ta fice tana murmushin domin ba lalle ba ne nayi ciniki kaman yadda ta ke fata.
ta saba tafiyar kasa, dan haka komai nisan guri baya damunta, tana tafe ina rare wakar fulatanci,"Laala saffta yofa Accata rena tamfata wai wai wai dalilama........."
Sannu a hankali take tafiya har ya iso babbar tasha Sir Yahaya, inda ya saba tsawa duk safe,
kamar kullum mutane suna ta kai kawo a gurin kama daga masu babura da masu napep da kuma masu motoci manya da kanana. ta nufi wajen wata bayarba mai Saida abinci da take zama wajenta kullum tana mata wonke wonke da da kai abinci idon an saye ita kuma tana Saida ruwan ta, kasan cewar yau akwai sanyi a garin bata yi wani ciniki sosai ba.
.Sai da yamma lis ta nufo gida a gajiye amman ba zata iya cire kudi na hau abun hawa ba, a ganina idan na hau kudin zasu ragu,
tana cikin tafiya bata ankara taji an watso mata ruwan saman da akai jiya da Daddare wadanda suke kwance a gefen titin sakamakon wucewar da wata motar tai da gudu tamkar zata tashi sama.
Wani irin haushi da takaici taji domin ba kadan ruwan motar ta jiƙe mata tufafi ba, bata ce komi ba taja siririn tsaki taci gaba da tafiyar ta a natse take tafiya har ta Iso unguwarsu dai dai wani ƙaton Super market ta idanuwanta sukai arba da kalar motar da wuce ta gabanta dazun ta bata mata tufafi, kuma wani abun dadi babu mutane a titi kasan cewar anata kiraye kiyayen salla maggariba
A hankali ta nufi wajen motar ta cikin dabara ta leƙa motar ba kowa
a ciki sannan ta kara matsawa tana kara tabbatarwa idan ita dince ko aa, kalar dai daya ce sabuntar ma daya ce a jikin number motar kuma an rubuta mata BIN MARYAM 327AW. da manyan haruffa tsabanin wacan da bata kula da number motar ba ma balle ma ta san me aka rubuta.
Wani ƙaton dutsi dage gabanta na ɗauka ta daddage iya ƙarfinta ta jefa ma glass ɗin motar.nan take motar ta fara kuka, da matsanancin gudu ta bar wajen zuciyarta na bugawa,ko ba komi burita ya cika
Ko ba shine ya bata mata tufafi ba be dame taba suma suji yadda ake ji.
Haka ta riƙa sauri tamkar wanda aka biyo, kaman anje ta juyo
ta juyo sai ta hango wata halitta mai kyau da daukar hankali da kuma ban tsoro tana kallona. Mutum amman a tsorace take da fuskarsa, sai dai kwarjininsa da haibarsa Nesa yake da ita amman fuskarsa gizo take mata tana kawo mata shi kusa kamar yana tsaye a gabanta. Annuri ne shimfide a fuskarsa, sai dai ba irin na masu dariya da sakin fuska ba, irin wanda annurin ya zame masa jiki yake bayyana kansa a duk lokacin da mai shi ya kalleka, kwarjinsa ya ƙara cika mata ido.
A take ta buɗe idonta ta hangi wajen da ya tsaye,fari ne ƙal wanda da ka ganshi kasan tabbas ruwa biyu ne Buzune, kuma zaka gane ya haɗa jini da Fulani.Wata iriyar shigace a jikinsa shiga mai ƙara daraja da kamala Fuskarshi nan ta fito ras sajenshi mai tsananin kyau yayi lib a fuskarshi sai sheƙi yakeyi, gashin girarsa ya komta lib a saman siraran idanunshi masu kyau da ɗaukar ido,
ta kumshe idanunta na nasu ƴan mintuna ta buɗe hango gurin da mutumen yake tsaye kamar anyi ruwa an dauke domin babu alamarsa balle shi din ya ɓace bat kamar be taba wanduwa a gurin ba. Wata kil ba mutum ba ne ta ayyana a ranta,
Samun kanta tayi da sakin tattausar murmushin ta Lumashe ido tana shakar kamshin turare mai shiga har cikin kwakwalwa da saka natsuwa,
ta risina ƙasa ta dauke kudi da suka zube tana dariyar kanta domin sai a yanzu abunda tai yake bata dariya na fashe gilashin motar mutane saboda mai motar ya watsa mata ruwan kazanta a jiki, wata ƙila ma ba shine ya yi ba.
Fuskarta ɗauke da murmushi har ta isa gida, zaune ta same ta gaban Murhu tana gasa masara guda huɗu,
"Amma ina kika samo marasa?"
"Saya nayi" ta bata amsa tana juya Masarar,
"Amma wallahi yau ba ciniki sosai nera ɗari nayi"
ta faɗa tana juye ragowar ruwa cikin tulu.
"Amma kinci Abinci?"
"Komi banci ba tun safe Nainah"
Daga can gaban murhun ta amsa mata kai tsaye. Wani abu ta ji ya tsaya a kirji wanda ya saba tsaya min a duk lokacin da Mahaifiyata ta yini da yunwa.
"Amma, akwai ragowar bireni da mukaci jiya da Daddare me yasa baki ci ba zaki zauna da yunwa bayan kinsan kinsa zama da yunwa baya baki lafiya"
"Koda na ɗauko biredin ya jiƙe kin san ɗakin yoyo ya ke"
ta turo baki tana bata fuska. Har ta gama gashin masarar ta gama fushi take da ita, sai dai hakan be hana ni cin marasarba,
Washe gari kaman ko wacce rana Saida haske rana ya leƙo ta kusuwar bukkan su sanna ta farka daga Nannauyan bacci, a maimakon ta tashi sai akwai ta ƙara dunƙulewe cikin yagaggen zanen gadonsu,"Nainah ta shi gari ya waye"
Haka ta fito daga cikin bukkarsu ta nufi can nesa da bukkarsu inda suke ba haya,
Bayan ta gama ta dawo na saka kasa na wanke hannuna sannan na saka sabulu, sai kuma na dora da alwala sannan na shigo dakin tai sallah asuba.
"ga ragowar masarar jiya can ciki kafin ki wuce wajen talla"
"Amma ki ci kawai idon na fita zan samu abin da naci".
"Babu inda zaki je sai Kinji masarar nan"
"Amma idon naci kefa?"
"Allah zai bani"
Haka ta turo baki ta bata fuska sosai kamar zatayi kuka, amman hakan be saka ta kyaleta ba, har sai da ta ci nasarar tana ta fushi daya kasa boye kyawon fuskata ta qwuqwuye masarar tas ta kora ruwa kana ta miƙe ta fice daga bukka ruwan ta lissafa masu ɗaya yawa bakan na jiya ba Kasan cewar yau akwai ɗan rana rana bakan jiya ba.
"Amma zan tafi, don Allah kar ki zauna da yunwa ki samu abinda kika saya da kuɗin jiya"
"Allah ya tsare, Allah ya kawo kasuwa Mai Albarka naina"
"Amin Amma" ta amsa tana Murmushi............✍️
More comments and share pls!
*Sadeeya Ka'oje ce 💋✍️*
💋𝐁𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐘𝐀𝐌💋
𝑵𝒂
𝑺𝒂𝒅𝒆𝒆𝒚𝒂 𝑲𝒂'𝒐𝒋𝒆
08149979652
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj
𝑷𝒂𝐠𝐞 27-28
______"Amin Amma" ta amsa tana Murmushi.a natse ta fice daga gidan yauma kamar kullum ƙasa take tafiya har ya iso tashar Sir Yahaya ta nufi wajen Zaliha bayorba,
"Anty ina kwana?" ta faɗa tana kallon Zaliha mai Abinci.
"Kana lafiya Nainah"
"Lafiya lau Anty"
"Kazo ka kaima Murtala direba abinci ka haɗa mishi da ruwa biyu"
Magana take mata amma dariya take mata saboda yadda take kiranta da namiji kamar yadda take yi ma ko wace mace idan kuma namijin ne sai ta mayarda shi mace, domin ita har yanzu hausarta bata gama fita ba. Sai itama tai dariya domin ta san abunda Nainah take yi ma dariya.
"Nainah ka renani ko? ka kwantar da hankali wata rana sai na fika jin hausa har fulatanci ma"
Yanzu ma dariyar ta ke,"kabar dariyan nan da kake ɗauki abinci Murtala direba ka bata".
"Tau Anty" tana faɗa tana ɗaukar abinci shinkafa da wake da miya da latas ta haɗa da ruwa biyu ta kaima sa, ya bata kuɗin Abinci da na ruwa tana isowa ta miƙa mata kuɗin Abincin ta ita kuma ta riƙe na ruwa.
haka ta riƙa kaima mutanen da suka sai abinci tana haɗa masu da ruwa, wuraren ƙarfe goma ta yi kwanke wanke bayan ta gama Zaliha ta zubata mata abinci ta shige ƙansa ƙaton tebur da Zaliha ke aje abinci kullum haka take tun Zaliha na dariyar ta har abin ya zame mata jiki, kasan cewar teburin lulluɓe ya ke da Leda irin wanda ake shimfiɗawa a ɗaƙi, ta ya za'a ta wangale baki a tana cikin abinci a irin wannan wajen da mutane ke cike,
(Kusan Fulani a kwai kunya 😍🤩)
tana gama cin abinci ta fito ta ɗauraye plate, haka ta yini a tasha bayan La'asar ta yi wonke wanke ɗan sauran abinci da ake ragewa a plate ta haɗe shi wajen ɗaya ta zuba a leda ta ɗauraye plate ɗin duka sannan, Saida yamma lis ta baro tashar cike da farin ciki ta seda ruwanta duka ga kuma a binci da Zaliha ta bata, daman wani lokaci idon bata Saida abincin ta duka tana bata ragowar.....
tana cikin ta fiya dai dai shagon ta hangi mota mai lambar jiya tayi parking a wajen, a hankali ta nufi wajen motar tana kallon cikinta juyowar da zatayi ji da bugu abu, da ƙarfi ta rumtse idanuta ɗan ƙaramin bakinta na motsawa ita karan kanta bata san me take faɗin ba, wani irin tsoro ne ya rufeta a wajen,tsoro ne irin wacan tsoron daya kamata jiya a lokacin da hangoshi tsaye yana kallonta, banbancin wacan karon da wannan a jiya murmushi da ta yi yau kuma kwalla ne a idonta tsoro da fargabar abunda zai mata. Lokaci daya taji an fisgota da Masifar ƙarfi wanda hakan ya bata damar sauke Nannauyan Numfashin da ban san tana rike da shi ba sai a yanzu.
"Ke! Malama wani irin dabbanci ne haka? mutum yana son ya shiga motarsa kin tare nasa hanya matsiyatan banza ƴan maula"
Wani dake tsaye gefen shagon ya faɗa yana tunkuaro inda take tsaye.
ta buɗe idanunta tana kallon Mutumen dake tsaye a gabanta yana cire jacket din jikinsa ya bar White t-shirt saboda ta dan shafe shi kadan lokacin sukayi karo da juna cike da kyankyami ya bude bayan mota ya saka jacket din ya rufe ya dawo mazaunin gaba ya zauna yana goge hannunsa da tissue yana ya mutsa fuska saboda ya rika rigar data shafi gefenta kadan....
tab ɗijam! wato duk tsayin da yake yana kallonta jiran yaje na bashi guri ya shiga motarsa ne, amman ba zai iya yi mata magana ba, wata kila maganar wahala take masa ko kuma yana kyamar furta kalmar bani wuri na shiga motata, ita dai
da kallo ta bi motar sai a yanzu ta lura da number motar ita ma *BIN MARYAM* ne rubuce a jikinta, sai dai wannan motar ba irin wacan ta jiya ba ce.
(Ba dai Asad ɗin mu na gargajiya ya dawo ɗan birni yanzu? Kaji maza jinin Ali gadanga, jama'a! Muje zuwa yanzu aka fara wasan😍🤣🤣)
"Matsa can kona ɓaɓɓallaki, baku da aiki sai maula daga kunga Mota mai tsada kuzo kuna wani marairaicewa Allah na sake ganin ki wajen shagon nan sai na karya Miki ƙafa na ga da uban da zaki sake zuwa nan, salon ɗai ki zamin tsiya *BIN MARYAM*ya dena zuwa wajen nan"
ta share Kwallar da ta zubo mata, ba komi yafi baƙanta mata rai ba kaman zagin mahaifinta da ya yi,"Ai kaine ɗan maula kuma na Barka da Allah da zagin Mahaifina da ka yi"
Kasan cewar mai shago ya yi nisa sosai baiji abinda ta faɗa ba. haka dai ta ƙasara gida zuciyarta ba ba daɗi,ganin Amma ta ya kawarda duk wata damuwarta.
"Amma na" ta kira sunanta lokacin da ta iso wajen da ta ke zaune,
"Amma kinci Abinci?"
"Na sha gari da shuga"
tayi Murmushi,
"Amma muyi salla muci Abinci, Amma yau na seda ruwa wan duka" tana ƙasara maganar tana miƙa mata kuɗin da basu wuje ɗari takwas ba,
Bayan sun gama sallah maggariba da Isha'i ta juye musu Abincin cikin tasar sunaci suna hira har suka kammala,
"Amma kin san jiya naga Aljani"
Amma ta yi Murmushin,
"Amma wallahi Aljani ne ni ban taɓa maganin mutum mai kyau kamarsa ba"
Amma ta yi dariyar ƴarta da yarinta ke ɗawainiya da ita, "taya mutum zai ga Aljani ya kwana lafiya Nainah?"
"Amma wallahi Aljani ne" nan siffanta ma Amma kamninsa,
"Kenan kema Aljanar ce"
"A'a kam Amma" ta faɗa tana dariya,
"Idon kyaune ai kin fisa kyau"
"Amma don baki gansa ba ne shiyassa ki ke faɗin haka"
"Mutum ne ki ka gani Nainah ba Aljani ba ai su Aljannu ba su da kyau"
"Amman ba ance suna rikiɗa su dawo bil adam ba, ance ma ko wacce irin siffa suna iya komawa"
"Gaskiya ne Su Aljannu suna riƙi ɗa su dawo ko wacce siffa mutum, maciji, mage, kare, komai ma suna dawowa"
Nan take Jikinta ya soma karkarwa sigar Jikinta na tashi,"Amma mu bar hirar nan don Allah har tsoro ya kamani kinsa ranar da Daddare da na fito fitsari naga wani kare gato baƙi kwance a tsakiyar gida"
Don ta Kwantar mata da hankali ta ce,"Ai wannan ba Aljani ba ne su ai basa barin ka gane su"
"Kuma fa haka ne Amma don har nayo fitsari na dawo yana kwance a wajen ko motsi baiyi ba" basu wani jima ba suka shige bukkarsu suka rufe suka Kwanta Nainah ta shiga can bayan Amma ta rungumeta....
Washegari ma haka ta farka ranta fari tas Zuciyata kal kamar yadda ta saba tashi a ko wace safiya ta Allah duk kuwa da irin rashin da suke da shi. Tun tashinta haka suke rayuwa har Allah ya karɓi ran Mahaifinta,
Tayi Alwalla ta yi Sallah ta ɗaga Hannayenta sama tana Addu'ar da ta saba yi kullum tunda ta fara wayo Amma ta faɗa mata ta riƙa yima iyayenta da ƴaƴanta abin kyaunar Addu'a da kakanninta bayan rasuwar mujinta wanda ya kasance Mahaifin Nainah ta riƙa Mishi Addu'a, tun daga lokacin kuma take sasu cikin Addu'a...
"Amma ina kwana?"
Lafiya lau Junainah!" ta Kirata da ainahin sunanta.
Ta saki tattausar murmushi tana jikin daɗi a duk lokacin da Mahaifiyarta ta Kirata da ainahin sunanta da take jinsa na musamman kodan ba'a cika kiranta da sunan ba,
"Amma Yaukam ruwan basu da yawa idon na Saida zan saye wasu na dawo dasu...."
tayi mata Addu'ar da ta saba yi a koda yaushe.
"Amma ki sai abinci da kuɗin jiya karki zauna da yunwa Kinji"
"Naji Adawo lafiya"
"Allah saya Amma" kana ta fice daga gida tana rera waƙar fulatanci...
**********
Kasan cewar ruwan nata basu da yawa sosai yau kuma da wuri da ta Saida bata bari tashar ba Saida ta yi ma Zaliha wonke wanke ta ɗiba mata Abinci sannan tayi mata sallama, bakin wani shago ta tsaya ta saye ruwa leda biyu kana ta kama hanyar gida....
dai dai zata tsallaka titi Wata baƙar mota mai bakin gilashi, ta zuge gilashin motar tana kiran,"mai ruwa"
sai fuskar mutumen nan na jiya da shekaranjiya ta bayyana, wata matashiyar budurwa zaune a gefensa,"mai ruwa kawo" ta sake kira a karo na biyu.
ta nufi wajen ta da sauri kaman zata faɗi wani abu ne take riƙe dashi cikin roba fari ƙal da ɗan ƙaramin colalin roba shima fari ya bin cikin robar ya zube mata a jiki.
"Bani ruwa"
Jikinta na rawa ta bude Ledar ruwa ta miƙa mata ta ƙarba ta miƙomata ɗari biyar sabuwar dal da ita. Ina kafin na faɗa mata babu canji mutumen ya ɗaga gilashin motar.
dan da alama bata isashe shi kallo ba, traffic kawai yake jiran a sake ya ja motarsa yanar wajen da gudu....
Afra ta juya tana kallon Nainah wacce ta koma gafen titi tana kallon motarsu.
"Wannan ya zama na farko ya zama na ƙarshe da zaki sauke gilashin motata ki yi magana da wani saman titi"
Ya fada ba tare da ya kalleta ba, tsif tai kamar babu ita a cikin motar, ta san halin Asad sarai dan haka bata sake yunkurin sake yin wata maganar ba har suka isa bakin gate din gidasu. Bata