Bin Maryam Book 1 Sadiya Kaoje

Author :  Humaira Bulama Category :  Read Hausa Novels

Chapter   10 / 30

27K to 30K   out of 87.6K words

jikinta na tashi. Murmushi ya kumayi yana cigaba da shafa jikinta. itako taƙi yarda su haɗa idanu sam.....

(Nidai na yi nan da alama Dr a m.......🤐🏃🏃🧐🤣🤣)

 

A hankali a hankali kwanaki suka ci gaba da shuɗewa ta ko wannen ɓangare Rayuwarsu na tafiya cikin Aminci Allah da rahamarsa, zuwa yanzu Adana shekarsa biyu a duniya Asad na da shekaru shidda da watanni......

*SUMAYYA*

Zaune take a falo tare ƴarta Noor ƴar kimamin shekara biyu a duniya hankali ta gabaki ɗaya ya karkata kan Noor dake wasa da abinci da suna ci ta ke, Wayar dake saman center table ta fara ringing har ta ƙatse bata ɗagaba aka karo na biyu ta koma yin ringing ta ko inda wayar take bata kalla ba, Saida wayar tayi Ringing har so huɗu amma ba'a ɗa ga ba,ƙarar shigowar saƙo da ta ji yasa ta nufi wajen wayar tare da dauka,

Fadila, shike sunan da ta ci karo da shi,

*Pls ka sameni a Safar Hotel room 66* shine saƙon da taci karo da shi.

Gabanta ya yi Masifar tsinkewa nan take jikinta ya soma ƙarƙarwa tamkar mazari, Idanunta sun ƙanƙance kamannita sun sauya Sai faman zirga zirga take daga karkon falon zuwa ƙarshe,cikin yanayin Nasir ya sameta, gadan gadan ta nufi wajensa ta cakumo wuyansa a fusace ta ce macuci Azzalumi Nasir kaci Amana me bana yi maka da har kane neman matan banza a waje Nasir yanzu zin........"

Kuka ya kwace mata harda shessheƙa,

Nasir ga baki ɗaya mamaki ya cika sa ya kalli Sumayya dake kuka tamkar ranta zai fita,"ke! Lafiya" ya tambaye cike da mamaki.

Sumayya ta ɗago da jajjayen idanunta murya a disashe ta ce,"Karka renamin Hankali mugu Allah ya isa tsakanin da kai Nasir wallahi Bazan yaɓa yafema b......."

tas!!! Ya ɗauke da mari mai masifar zafi Dif kunnuwanta suka ɗauke ta dena jin sautin komi sai "Dummmm!"

Noor ta fashe da kuka tare da komawa bayan Sumayy ta ƙamƙame jikinta waje ɗaya tana kuka mai cike da tsoro.

"Nasir ni zaka mara?"

"Don me ba zan mareki ba! ta ya zaki tareni kina faɗamin baƙaken magana"Ya faɗa cikin zafin rai.

Sumayya ta saki murmushi mai ciwo tana faɗin, Wallahi zama na da kai ya ƙare Nasir Bazan iya ci gaba da zama da mazina ci ba"

A ruɗe ya ce,"Sumayya wai mike damunki? Kina cikin Haiyacinki ko?"

ta ɗauƙi Noor ta wuce ɗakin tana kuka mai tsuma zuciya, kayanta ta haɗa Cikin akwati tare da na Noor ta fito,

Nasir ga biki ɗaya a ruɗe ya ke ya bi bayan Sumayya da kallon har ta fice daga falon, yana tsaye ya kasa ƙwaƙƙwaran motsi tamkar wanda aka dasa, tana kuka ta shiga motar ta zaunar da Noor a gaban sit ta ɗaura mata Bell ta fice daga gidan da matsanancin gudu tamkar wanda zata sama...........✍️

*More comments and share pls!*

*Sadeeya Ka'oje ce 💋✍️*

💋𝐁𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐘𝐀𝐌💋

𝑵𝒂

𝑺𝒂𝒅𝒆𝒆𝒚𝒂 𝑲𝒂'𝒐𝒋𝒆

08149979652

https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj

𝑷𝒂𝐠𝐞 19-20

_________Ringing ɗin wayar ta dawo da shi daga dogon Tunanin ya je, a hankali ya kalli inda yake jin sautin wayar saman kujera ya ganta da kyar ya tattaro ya ƙarfinsa ya nufi inda wayar take ya ɗaga ba tare da ya ce Uffan ba, daga can Ɓangaren Fadila ta ce,"Nasir ina ka aje wayar tun ɗazu ina kira baka ɗaga ba lafiya? na turama ma massages ba reply, tun ɗazu ina Hotel ɗin harma ta Haihu".tut! tut! ya ka she wayar yana sauke Nannauyan Ajiyar zuciya, da sauri ya miƙe tsaye ya nufi ɗaki ya ɗauki key ɗin motarsa ya fice da sauri ya nufi wajen Mota ya shiga a guje ya bar gidan, mai gadi ya bi bayan motarsa da kallo ya faɗin,"Allah dai ya sa lafiya Madam ta fita a wuje shima ya fita a guje". Ya maida gate ɗin ya rufe ya koma saman kuje ya zauna yana sauraren redio...

*SUMAYYA*

Ikon Allah ne kwai ya iso da ita gida, tuƙi take cike da tashin hankali ko gabata bata gani sosai, a gigice ta iso gida ta fito cikin mota riƙe Noor tana sharɓar kuka kaman ranta zai fita ta nufi Ɓangaren Mama," Mama da su Twins suka miƙe tsaye da saurin ganin yadda Sumayya ta shiga,"Sumayya lafiya?"

Mama ta faɗa tana nufo inda ta ke,

Sumayya ta rushe da kuka,"Mama Nasir ne!"

Cikin ta shin Hankali Mama ta ce,"Me ya faru da Nasir ɗin?"

Banda Kaka ba abinda Sumayya ke yi, Hankali Mama ya yi Masifar tashi,"Kinga Sumayya ki dena kuka nan ki faɗa min me ya samu Nasir ɗin,Ko sakin ki ya yi? ta faɗa Murya a sanyaye" ta girgiza kai.

"Mutuwa Ya yi?"

A karo na biyu ta girgiza ma ta kai.

"Don Ubanki ba zaki bani amsa ba, me ya samu Nasir ɗin?" Mama ta faɗa a tsawace, Murya na rawa Sumayya ta ce,"Ma...ma! Nasir Ma..zi...na....ci ne, wallahi bazan iya ci gaba da zama da shi ba! Mama don Allah ki ce ya sake ni" ta ƙarasa maganar tana share kwalla.

Mama ga baki ɗaya jijinta ya yi sanyi ta rasa ma me zata ce, Iya saninta da Nasir ba shi da wata matsala hasalima bai taɓa yin burwaba sai Sumayya amma ƴaƴan Yanzu baka shedunsu ka haifesu ne amma baka haifi hakinsu ba

"Zauna"

Mama ta yi Maganar tana nuna mata wajen zama, zama tayi Hanifa ta anshi Noor suka suka bar Falon daga Mama sai Sumayya kwai suka gare, Mama ta kalli Sumayya fuskarta duk ta sauya idanunta sun kumbura saboda Kuka, ta sauke Nannauyan Numfashi,"

"Kama sa ki ka yi?"

"A'a"

"Toh miye hujjar ki da zaki kira shi mazinaci?"

Sumayya ta zaiyanama Mama komi.

"Haba! Sumayya wallahi kin bani kunya da ilimin da wayonki kike abu tamkar jahila! Wallahi kin bani mamaki daga ganin text a wayar shi ne duk zaki bi ki tada hankalin a banza sai ka ce baki san halin mijinki ba, shike nan duk mai zuwa Hotel ɗan Iska ne? Maza ta shi ki koma ɗakin mijinki"

"Wai hayaniyar me na ji haka Laila?"

Mama ta kalli Daddy da Aliyu tuni har sun nemi wuri sun zauna suna jiran me Mama zata ce.

"Sumayya ce wai daga taga text a wayar Nasir shine ta kwaso ƙafa tazo wai Nasir neman Mata banza ya ke"

Daddy ya kalli Sumayya yana faɗin Ke! Gaskiya ne abinda Laila ta faɗa?"

"Gaskiya ne Daddy"

"Kiyi zaman a gida ba inda zaki je tunda bai san darajar ki da har ya ke neman matan banza a waje"

"Kaman ya ba inda zata je? Me ka ke nufi da hakan?"

Kaman yadda kunnuwanki suka jiye miki ba inda zata koma"

"Bafa sakinta ya yi ba!"

"Toh ai gwara sakin da irin wannan zaman cin amana wallahi bazan lamunta ba"

A fusace ya fice daga falon Aliyu ya masa masa baya, ta bisu da wani irin kallo mai cike takaici, "Ina wallahi bazai yiyuwa Sai kin koma ɗakin mijinki"

"Mama wallahi bazan iya zama da shi"

"Sumayya wai kina da hankali kowa, kisan hukunci matar da ta nemi mijinta ya sake ta? so ki ke ki koma ƙaramar Bazawa? ta shi maza masa ki koma gidan ki tun ban saɓa mi ki ba"

Sumayya ta fashe da kuka mai tsuma Zuciya,

"Mama ai da kin kaita kartayi driving a yanayin nan za'a iya samun matsala"

Hanafi ya faɗa cikin sanyi Muryar.

"ta shi maza muje"

da kyar ta miƙe tsaye ta ƙarɓi Noor hannu Hanafi, "je ɗaki ka ɗauko min Hijabi" da saurin Hanafi ya nufi ɗakin mama ya ɗauko hijabin ya miƙa mata kai tsaye suka wuce inda Sumayya ta yi parking ɗin motarta.....

Nasir tafiya ya ke kawai ba tare da yasan ina ya nufa ba, gabaki ɗaya ransa a jagule ya ke maganganu Sumayya sun tsaya mi shi a rai, har ya kama hanyar gidansu Sumayya sai kuma ya canza hanya ya nufi gidansu, yana isa ya zaiyanama Mommy duk abinda ya faru,

"Ina ita Sumayya ta ke ?"

"Wallahi Mommy ban sani ba"

"Kaman ya baka sani ba Nasir"

"Kirata maza kaji inda ta ke"

Number Sumayya ya kira yafi a ƙirga amma ba'a ɗa ga ba.

"Mommy ba ta ɗaga ba"

"To kai mi ye alaƙar da ita Fadila ɗin da zata ce kama ku haɗu a Hotel?"

Dai dai lokacin Dady ya shigo,"Aysha lafiya ya na ganku haka?" Mommy ta sauke Ajiyar zuciya kana ta zaiyanama Dady abinda ya faru....

Suna barin gida kai tsaye suka wuce gidan Sumayya Mama ta yi hon mai gadi ya buɗe mata gate ta shiga da motar,"Sannunku da zuwa Hajjiya"

"Yauwa Sannu" Mommy ta bashi amsa, tare suka nufi ƙofar falo Mama ta buɗe ta ji kofar a rufe,

"Shamsu Ina mai gidan ya ke? "Hajjiya ai kina fita shima ya fita"

Barin wajen suka yi suka shiga mota kai tsaye Mama ta wuce gidansu,

"Toh kai Nasir me ya sa baka yi mata bayani ba, kasan sha'anin mata sai a hankali"

"taƙi bani damar na yi mata bayani sai faman surfa masifa ta ke"

"Ai dole ta yi Masifa"Mommy ta bashi amsa tana harrarsa,

Dai dai lokacin kuma su Mama suka shigo Sumayya na biye da ita a baya,

"Assalamu alaikum, Yaya Anty ina wuninku"

"Wa'alaikum Salam, lafiya lau"

"Mommy Ina wunin ku"

Sumayya ta faɗa kai a sunkuye,

"Lafiya lau Sumayya ya gida"

"Lafiya lau"

"Gwaggo Ina wuni"



"Lafiya lau Nasir"

"Shi ba zaki gaida shi ba?"

Mama ta faɗa tana kallon Sumayya,

Sumayya ta dago da jajjayen idanunta ta sauke su a kan fuskar Nasir Murya a sanyaye ta ce ,"Ina wuni"

"Lafiya lau"

"Sumayya ki yi Haƙuri ki dena kuka Kinji"

"Haba Aunty Aysha miye a ka yi mata na kuka?"

"Miye ma ba'ayi ba"

Nasir ya yi saurin cewa "Wallahi Mommy abinda ta ke tunanin ba haka bane, "rufemin baki ko na sassaɓa maka"

Nasir yaza bakinsa ya yi tsit,

Sumayya taji wani irin sanyi ya mamaye zuciyarta,

"Haba Anty Aysha ki barshi mana ya yi magana"

Dai dai lokacin kuma Hajjiya ta shigo tana faɗin lafiya? na ganku nan kunyi cirko cirko?"

Mama ta zaiyanama Mama komi,

"Anya ko kunyi bincike akai, nasan Nasir bazai aika haka ba".

"Nasir wa ce Fadila?"

"Hajjiya Nurse ce abokiyar aiki na ina saman hanyar dawowa gida ta kirani tana da patient a hotel wata friend ɗinta ce tazo daga Abuja bukin wata ƙawarsu shine Labour ya taso mata a Hotel ɗin tana buƙatar taimakon gaggawa shine ta kirani na taimaka mata a matsayina na babban likita da nadawo gida na ci abinci na wuce ɗaki domin na watsa ruwa shine na bar wayar a falo to ni Wallahi na ma manta sam da muyi maganar da ita, shine ta yi ta kirana ta gayamin inda zan sameta ban ɗaga sai ta turomin text. Yana gama magana kira na shigo a wayarsa ya daga tare dasa speaker,"Hello Fadila"

daga can Ɓangaren Fadila ta ce,"Dr Nasir patient tana ta Bleeding sosai wallahi baby ya ƙiyin kuka nayi iya ƙoƙarina amma na kasa pls idon baka zaka samu damar zuwa ba katurom Nurse's ko motar Asibiti mu wuce Asbitin ina ga ma haka zaifi sauƙi" tana tsaka da magana Baby ya ƙyalla ƙara, "Alhamdulillahi baby ya yi kuka" ta faɗa cike da farin ciki,

"Okay gani nan zuwa" Nasir ya faɗa kana ya she wayar,

"To ba ga irinta nan kin tada hankalin a banza, miye umfanin haka?" Cewar Mama.

Sumayya ta sunkuyar da kai cike da kunya,

"Toh Alhamdulillahi tunda gaskiya ta bayyana Sumayya a riƙa kiyaye wa Kinji a rika kai zuciya nesa Allah ya ci gaba da baku zaman lafiya"

"Amin Hajjiya" Dady ta faɗa yana kallon Hajjiya,

"Oya ta shi maza kije ki nemi yafiyarsa tun ban ɓaɓɓallaki ba"

Ta miƙa jiki a mace ta nufi wajen Nasir murya a sanyaye ta ce,"kayi Haƙuri!"

Ya kawar da kai gefe yana faɗin,"Ba ko mi"

"Ayi ta haƙuri da juna Sumayya kinsan ya na yin aikin nan naku dole sai anyi cuɗanya, kai kuma don Allah komi ya wuce Karka ce zaka ɗauki wani mataki bayan kun koma gida"

"In Sha Allahu Hajjiya komi ya wuce"

"Allah ya yi muku Albarka"

"Amin ya rabbi"

"Ku ta shi ku tafi gida Allah ya tsare"

"Gwaggo muje na sauke ki gida"

"A'a Nasir bari na kira direba yazo ya ɗauke ni"

"to ki tafi ta motar Sumayya, tunda ga motata"

"Toh ba damuwa idon naje zan ba Hanafi ya dawo da ita"

Sallama sukayi musu kana suka wuce,har sun kai bakin ƙofa Noor ta ce,"Ba jan je gida ba zan zauna wajen Mommy"

tuni ta juya ta nufi wajen Mommy su kuma suka wuce, kai tsaye ya wuce da ita Safar Hotel, suna isa ya yi parking," ta fita ya juya baya ya ɗauki jaka sannan ya fito yana gaba tana binsa a baya har suka iso room 66 ya yi Knoking,"Yes shigo" aka faɗa da can cikin ɗakin, Sumayya ta buɗe ta shiga su biyu ne a ɗakin ɗaya na kwance saman gado ɗayan kuma na riƙe da Baby, ganin Dr Nasir yasa Fadila ta shi tsaye tana faɗin ,"Sannu da zuwa Dr"

Sumayya ta ji wani irin ƙolon ya tsaya mata a maƙoshi, ganin yadda fadila ke magana da Nasir,"Yauwa ga Sumayya nan zata taimaka Miki akwai in da zanje,

"Ai na maga zata iya tafiya"

"Kin tabbatar ba wata matsala?"

"Allah ba komi"

",Tah sai Anjima Sumayya kam tuni ta fice daga ɗakin sam Fadila bata kwanta mata sai ta ke ganin kaman akwai wani abu a tsakanin su wani irin kukan takaici ne ya taso mata.....

suna isa yayi parking sannan ya koma ya zauna ya jingunu da jikin kujerar yana jin yadda take kuka,

a zahiri mamaki yake itace da laifi itace da kuka kuma

har cikin ranshi yaji zafin marin da yamata ɗazu,

ajiyan zuciya ya sauk'e sannan yasa hannu ya d'an dagota ya jingina ta da jikin shi hannun ta ya kamo cikin sanyi ya cusa hannun kan k'irjin shi sai kuma ya kalleta a hankali yace." Kiyi haƙuri kinji"



sai kuma yayi shiru sannan yasa tafin hannun shi yana shafa fuskar ta a hankali yace.

"Kukan ki nasa zuciya ta tayi nauyi sabida sai inga kamar na k'asa rik'e amanar dana d'auka ne kiyi hak'uri ki gafar ceni banyi niyar tab'a lafiyar jikin kiba."

Murya na rawa ta ce,"me ya tsakanin ka da ita?"

Ya yi Murmushi yasan kishi ne ke ɗawauniya da ita.

"Wallahi tallahi ba bu komi tsakanin mu. Ki yadda da ni kinsan ba zanyi mi ki ƙarya ba, ta so muje cikin gida"

"Allah ba inda zanje sai na rana marin da kayi min"

"Toh shike nan muje ki rama"

Murya na rawa ta ce ,"ba inda zanje sai na rama".

Na yarda mu shiga saiki rama."

baki ta tura sannan tace "toh."

hannun ta yaja suka shiga cikin gidan ,

suna shiga ɗakin ta ya nufa da ita,

"Zan rama fa."

Ido ya tsura mata cikin mamaki ajiye wayarshi kan mirror sannan ya juyo a hankali yace.

"Toh zoki rama."

ta sowa tayi ta tsaya a gaban shi ta ɗan ɗago kanta tana kallon fuskar shi,shi kuwa kollon d'an tsawonta yake tunda ko fuskarsa in zata kalla sai ta daga wuya da kai,

kuma wai shine tana ikirarin tazo ta rama marin daya mata,

cikin ranshi kuwa jira yake yaga iya rashin kunyarta zata mareshin neko ƙaƙa

ganin tana ta ɗago wuya da k'afafun ta dan ta isoshi tsawo ta kasa,sai ya d'an rok'ofo kanshi ya sunkuyar dai-dai tsawonta cikin sanyi Muryar ya ce,"Rama"

fuskar shi ta tsurawa ido ta d'ago hannun zata dalla mishi.marin sai kuma tayi maza tayi ƙasa da hannun sai hawaye shar shar tamkar an kunna fomfo.

"Don kasan Bazan iya marinka ba shine zaka ce na rama"

murmushi yayi a ranshi yace.

"Gaskiyar bahaushe wata fuskar tafi k'arfin mari."

fahimtar da yayi bazata iya ramawan bane,

sai ya mik'o mata hannu zo nan matar Nasiru da famin me ki ke so?"

"goyo na ke so".ta faɗa cikin shogoɓa

"goɗai goɗai da ke zan goya"

"Allah sai ka goyani kona faɗa ma Mommy"

Ya lumahe ido, "zazzaɓi nakeji"

ta fashe da kukan taɓara tana bubbuga ƙafa irin yadda ƙananan ya suke,

"Shi kenan ya isa"

A hankali ya durk'usa ya mik'e tsawonshi kamar mai konciya sai kuma ya d'an taso ya k'afa hannun shi a k'asa sannan ya mik'e tsawonshi," zo ki hau"

Ba kunya ta ɗale sama tana Murmushi

yana kallon ta duk abin da takeyi,

a haka har

zuwa wani d'an lokaci sannan ya manna jikin shi kan lallausar carpet d'in ya kwanta yana maida numfashi akai akai,

itako murmushi tayi

10 / 30