Author : Humaira Bulama Category : Read Hausa Novels
Jumaimah taja numfashi ta re da fadin ,"Ya Allah".
Daga bisani ta ce da Zaitun lokacin da kuke makaranta ta taɓa yin haka?"
"Gaskiya Ammi ban taɓa ganinta cikin wannan hali ba tun ta shi da ita ban taɓa ganinta cikin irin wannan damuwa ba sam bata irin haka ba bakinta ba ne, wallahi bana son jarrabarwar mu ta fito Jumaimah na cikin wannan hali saboda kar ya taɓa karatunta
Adda Aysha ta ce ,"Ammi yanzu haka za'a zuba ido ? Gaskiya a san abin yi."
Adda Nazlah ta ce ,"gaskiya Kam ya kamata a san matsalar don a yi maganinta". Da wannan shawara suka watse kowa jikinsa a sanyaye.....
*NAINAH*
lokacin da ta bar falon da kuka ta fito zuciyarta cike da jin haushi Asad da tasan cewar hana tafiyar zai yi da tun farko ban fada masa ba. Gurin Amma ta dawo lokacin tana wajen zaune ita kuma ta wuce dakin ta hau kan katifa na kwanta tana ta kuka a hankali dan bata son Amma ta ji. tana in lokacin da Ummy ke gaisawa da Amma.
"Ina Nainah take?"
"Yanzun nan ta wuce tana ɗaki"
"Ko ta yi fushi ne saboda na ce ba a a gidan Iya da ita ba?"
"Ina na ne gidan Iya kuma?"
"Gidan Iyayena, ɗazu nake faɗa mata yan nenta zasuje can gidanmu shine ta ce zata bi su,amman yanzu Yayansu ya zo ya ce ba za a je da ita ba, wai ba zata je ta barki ke kaɗai ba"
"Ai Nainah haka take da kafiya ba kaman yar uwarta ba! Ita ba ruwanta ga zurfin ciki kaman haifinsu".
"Daman Nainah na da ƴar Uwa?"
"Ehh Nainah yan biyu ne"
"Ina yar uwarta take?"
"Tun suna yara yan shekara huɗu ta ɓata har yau kuma labarinta amma ina ji a jikina tana raye"
"Ku yan wani gari ne?"
"Ni Asalin yar zogirmane amman anan birnin Kebbi na ta shi, ga baki ɗaya"
"Mahaifin Nainah na raye?"
"Shekara huɗu kenan da rasuwarsa, Mahaifin Nainah mutumen kirki ne ba shi da matsala ga ibada da tausayi da taimakon na kasa da shi, ina Alfahari da shi a matsayinsa na mijina kuma uban ƴaƴana ina fatan yadda na kasance matar a nan duniya na zama matarsa a lahira"
"na jidadin da aka samu Nainah ta hanyar aure, shine babban farin cikina"
"Ta Aure aka haifesu Uba kuma na gari da ko wacce ƴa Zatayi Alfahari da shi, ina jin daɗin sosai idon na tuna Yusuf shine uban ƴaƴana".
"Kin taɓa wani Aure halam kafin Yusuf?"
"Na taɓa Auren wani Azzalumi ma yaudari maci Amana". Ali.......!"
Bata ƙasara ba Asad Ya iso wajen yana faɗin,"Ummy Don Allah a ramin key ɗin motarta ki".
"Lafiya me ya samu motar taka?"
"Wallahi tun ɗazu nake ta data taƙi tashi"
"Kodai ta samu matsala ne?"
"Ummy lafiya lau da na shigo da ita gidan nan kuma sabuwar mota ce"
"Ai ƙarfen nasara ba shi da tabbas"
"Ummy tayi ma Amma sallama sannan ta wuce cikin gida ta dauko key ɗin mota ta ba Asad ya tadata itama taƙi tashi"
"Ummy Kinga ita ma bata ta shi ba"
Kawo mu gani Ya miƙa mata key ɗin ta tada motar sai gata ta shi,
"Bari naje da ita gida sai na ba direba ya maida Miki".
"Okay"
Yana shiga mota taƙi kashe kanta ya kunna ta ƙi ta shi. A hasale ya fito cikin motar yana faɗin ,"wai me hakan ya ke nufi?"
Ummy ta karɓi key ɗin motarsa ta nufi inda ya yi parking ta buɗe ta shiga ta yi mata key ta tashi mamaki ƙarara a fuskar Asad Ummy ta fito ya shiga tana shiga mota ta kashe kanta🤣🤣
Wasa wasa Saida Ummy ta tada motocin gida duka suna ta shi amma da zaran Asad ya shigo sai su ka she kansu, daga karshe ta yenke shawarar kai shi gida ta dawo da mota ta tada mota lafiya lau Asad na shiga mota ta mutu.
(Haba Nainah!🤣🤣🤣)
"Ummy bari kawai na hau Keke na tafi gida".
Ya nufi gate mai gadi ya yi juyin duniya gate da buɗe ya ƙi buɗewa da ƙaramar ƙofa da gate duk sun ƙi buɗe wa."
A hasale ya dawo wajen da Ummy take tsaye tana dariya ƙasa, saboda ta gano in da matsalar take.
"Jirani ina zuwa"
Kai tsaye ta wuce Bq har cikin ɗaki in da Nainah take kwance tana kuka, "Autana ta kira sunanta a hankali".
"Na'am Ummy".
"Ki yi haƙuri ki bar Yayanki ya tafi wajen Aiki ana jiran a office".
"Ummy ai ban hana shi tafiya ba". ta faɗa a shogoɓe.
"A'a Autana karmuyi haka dake, ki yi haƙuri kinji".
Sai ta saki murmushi, ganin haka yasa Ummy ta juya ta fice daga ɗakin tana dariya ƙasa ƙasa...
tana isowa ta miƙa Asad Key ɗin motarsa tana faɗin, "Allah ya tsare, Mai gadi buɗe masa gate. da mamaki ya bar gidan Abu sai ka ce Film.....
Yana tafiya bada jimawa ba Sun Afreen suka wuce gidan gidan Iya har Bq suka je suka ma Amma da Nainah Sallama sannan suka wuce.
Washegari H.M ɗin makarantar ya kira Asad ya sanar da shi Copper ɗin ta samu lessons a wani gida don haka bazata samu damar zuwa sai dai idon yana buƙatar Namiji.
Da yamma suna zauna a waje Adnan yazo gidan Nainah.ta bishi zuwa wajen da ake parking ɗin motoci zaune ta same shi riƙe da littafai. ta gaishe shi ya amsa mata fuska a sake.
ya soma tambaya inda ta tsaya a karatuna na boko daga nan ta gane cewar malamin boko ne.
"Aji nawa ki ka tsaya a makaranta?"
"Ni ban taɓa zuwa ba makaranta ba"
"Kin iya karanta hausa?"
"Eh na iya amma kaɗan kaɗan
"Turanci fa?"
"Ban iya ba"
Ya rubuta wani abu a takarda ya bata ya ce ta karanta,
Ta soma karanta ta sai dai ta yi tana gargada wani gurin kuma sai ya gyara min idan na fadi wani abun ba daidai ba sai yayi ta mata dariya, bayan ta gama ya bata turanci ya ce ta karanta sai n
Ta kafaranta da hausa ba tare da san ma'anarsa ko fassararsa ba, nan ma ya sha dariya sosai ita kanta tayi dariyar kanta domin duk turancin da ya nuna mata da hausa na ke karanta shi. Suna cikin haka Asad ya fito tare da Ummy ashe yana cikin gidan bata sani ba. Mutumen ya shiga masa bayani
"tana da kai kuma ta yi kokari sosai, yanzu hausar ce za a dora ta akai sai kuma turancin da zamu fara daga farko domin shi tace bata iya komai a ciki ba"
"Good"
Ya fada fuskarsa ba yabo ba fallasa, sannan ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudin masu yawa nya mikawa mutumen.
"Ga wannan idon wani abun ya taso zan nema ka".
Mutumen ya yi masa godiya sosai sannan ya wuce.
"Me ya faru kuma?"
Bayan ya wuce Ummy ta tambaya.
"Ya cika sakewa bana son namiji mai sakewa da mace sosai"
Ya fada yana kallon Nainah.
"Ba na ce ki daina fitowa haka ba?"
Na wonke su basu bushe ba"
"Wuce ki sako Hijabi"
"Ba su bu she ba
Ta fada ta turo baki. Ya dalla mata Harara Ummy ta ce," Su kaɗai ne shijaban halam?"
"Ehh"
"Je daɗin Afra ko Afreen ko ɗauko hijab ku tafi Unguwa"
"Toh Ummy" sannan ta wuce cikin gida ba jimawa ta dawo sanye da hijab pink color ya yi mata kyau sosai.
, ko da ta dawo yana cikin mota ya bude front seat da alama ita yake jira, shiga tai ta zauna da gangan ta ki rufe motar sai ta ya mika hannunsa ya janyo ganbun ya rufe sannan ya soka taka motar daman tuni aka bude masa gate.Ba su yi wata lafiya mai nisa ba, suka iso gaban wata katuwar makarantar islamiya, wani irin dadi ne ya lullubeta ta kalleshi da sauri.
bude motar ya nufi wani bangare na makarantar ya barta a ciki, be dade ba ya dawo ya bude mata murmushi motar da kansa na fito ga tsaya a kusa da shi ya wani hade rai irin kar na ga damarsa din nan, wani malamin ne ya zo ta takardu ya ya tambayi sunana da sunan Baba lafiya ta da sauransu sai ya rubuta a form din hannunsa da ya bukaci number waya sai Asad ya bada tasa.
"Shikenan yanzu sai uniform za a siya mata da kuma hotonta da za a laka a jiki file ɗin ta"
"Akwai Uniform ɗunkakke"
"Okay a bata set biyar"
Be tambayi nawa ba yake ba kawai ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudin masu yawa ya mikawa mutumen.
dan Allah ka saka ido akanta bata iya komai ba, tun daga farko za a fara koya mata"
"In sha Allahu ba ka da matsala, ba ri na dauko mata uniform din”
Komawa yai cikin makarantar ya dauko uniform din cikin ya miko mata ta karba tana murna kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha. Sannan ta koma cikin motar shi ma Asad ya zagayo ya shigo yayi mata key.
“Na gode Allah ya saka maka da alheri”
Be amsa ko inda na ke be kalla ba, ita kuma bata damu ba farincika ya gama cika zuciyarta gaba daya, daga ilslamiyar ya wuce da ni gurin daukar hoto aka dauki hotonta aka ba shi, fiye da kudin hoton ya bawa mutumen, abunda ta lura da shi idan zai maka alheri ko ya baka hakkinka sai ya ninka maka ko kuma ya baka abunda ya fi yawan nawa, ta yi zaton daga nan gidan za su koma sai ya nufi Mall da ita bata taɓa shiga shagon ba tun da take ganinsa sai dai kawai ta bi an wuce
Yana gaba tana binsa a baya sai rabon ido take tana kallon kayan shagon ta kalle kalle da kansa yake zabon kayan ciki, yawanci dogayen riguna ne na abaya da riga da skirt na kanti, sai takalmi masu kyau da mayunka shafawa na gyaran jiki, sai da ya biya kudin sannan suka saka masa a mota muka fito muka shiga motar ya dauki hanyar wata plaza da ita wannan karon a motar ya barta ya shiga ciki domin be bude mata mota ba don ta fito kamar yadda yake mata, ita kuma na zauna a cikin motar har yayi abunda zai yi ya fito wani na riko masa manyan ledodi.A bayan mota aka saka masa musu sannan ya shigo motar yana cin wani abu mai kamar chocolate , ya ci kusan rabi sannan ya miko mata sauran sai ta karba ta saka gefen hijab ta goge yayun bakinsa sannan ta ci, ido ya saka mata yana ta mata kallon rainin wayo sannan ya tashi motar suka kama hanyar gida ana kiran sallah magariba.
A harabar gidan ya faka motarsa ya bude boot din ita kuma na bude na fito rike da uniform dina zata wuce bq sai ta ji ya ce.
"Wa zai ɗaukar Miki kayan dake ciki?"
Da saurin ta dawo ta dauki kayan zuwa falon Ummy.
"Kayan ku ne ke da Mama"
Ta zaro ido tana bude baki.
"Da gaske?"
"Da karya"
Ya fada ba tare da ya kalle ta ba ya rufe boot din ya nufi Ɓangaren Ummy wani tsalle tai na dire ranta fes, a gaskiya yau Asad ya burge ta domin ta kura shi ma yana da mutunci kamar Deedat sai dai Deedat ya fishi son mutane da far'a. Amma ma ta yaba sosai da kayan da kuma halin Asad daman tun suna asibiti take ta yabonsa tana ganin kirkisa sosai, wannan karon har da cewat tana mamakin yadda hake ga hidima da ita haka. Bayan sallah isha'i Amma ta ce ta je na masa godiya kuma na ce ita ma tana masa godiya. Rigar jikin na cire ta saka daya daga cikin abaya da ya siya mata na saka na yafa mayafinta sannan na nufi part din rigar sai kyalkyali take ko'ina na jikinta.
Da sallam ta tura kofar falon ta shiga, sai Ummy ta amsa mata da far'arta Asad yana zaune saman Sopa ya hade rai sosai kamar an masa wani abu, tana juyowa sai ta ga Deedat tsaye yana sakar mata murmushi.
"Yah Deedat sannu da zuwa"
"Yauwa Beauty na"
Ya fada yana kallon yadda rigar ta karbe ta abun ka da farin mutum ya saka babaken kaya.
"Kin yi kyau sosai rigar ya karɓe ki
Ya fada yana murmushi.
"Eh dazun Asad ya siya min ita shine nazo nayi masa godiya.
Ina zoben da na baki...?"
Bata amsa shi ba tai saurin fisge hannunta tana kallon Asad hankalinta a tashe kamar wacce za ayi ma wani abu.
"Deeeeedat.......!"
Asad ya daka masa tsawa a cikin muryar da shi kan shi be san yana da ita ba."
"Kar sake kuskuren yabon kyauwuta balle ka ce zaka kai dan iskan hannunta ka taba ta, wannan ya zama na farko kuma na karshe".
Nan take Yanayin fuskar Deedat ta canja sosai.
"Ke wuce ki bani wuri" Asad ya faɗa a hasale.
Tayi kaman bata ji abin da ya ce ba.
Magana Asad yake ma Deedat cikin tsawa yana nuna shi da yatsansa kwayar idonsa gaba daya ta canja zuwa ja kamar ba shi ne da farin ido ba, shi kan shi Deedat sai da gabashi ya fadi domin ya razana sosai da yanayin da ya ga Asad Kamar kyalftawar walkiya haka Nainah ta bace bat a cikin falon kamin ta isa Bq har da gudunta, ganin irin tsawar da Asad yai ma Deedat da yake kanensa kuma dan'uwansa to ita kan ta san nata dukanta zai yi. Da sauri Ummy ta fito daga kitchen tana kallonsu, jin yadda falon gaba daya yake amsa muryar Asad har yanzu be janye yatsansa daga nuna Deedat da yake ba sai rawa yatsan yake kamar zai da ki Deedat da hannunsa.Wani irin abu yake ji yana masa yawo cikin jini wanda be taba jin irinsa ba, duk wani kishin Nainah da yake a can baya na yanzu ya ninka shi ninka shi, ya yaba kyauta ya janyo hannunta ya rike, da irin kallon da yai mata da kalamansa na har lokacin Deedat be iya cewa komai ba banda kallon kallon da suke da juna shi da Asad.
"Kun samu matsala wallahi shine nan akan macce kun maida kanku kaman kanurka baku da aiki sai faɗa"
Asad ya juyo ya kalli Ummy
"Ummy Ki fada masa ya daina shiga gonata"
"Kaman ya In daina shiga gonarka ko ka daina shiga gonata?, Don an yaba kyau Nainah anyi magana da ita ko taba ta miye matsalar ka da wannan?"
"Idon kana ganin ba matsala ba ce ka sake ga ni"
Asad ya fada yana sauke yatsansa sannan ya fice daga falon zuwa Bq.
"Tabbas zan sake ko"
Deedat ya fada a fusace yana bin Asad da wani irin kallo.
"Don Allah ku ba zuciyoyin ku haƙuri"
"Banda renin hankali Ummy miye ruwansa da ni? Naga dai ba shi da alaka da ita kamar yadda ni ma ba ni da, kuma son Nainah na ke son ta na ke be isa ya hana hakan ba..."
"Ka yi hakuri Baba na zan masa magana"
Maganar da Ummy ta masa ce ta saka ya zauna saman kujera yana ta huci da mamakin yadda Asad yake son masa fin karfi.
cikin wani irin yanayi ya nufi Bq
be taba jin kanshi a cikin irim wannan yanayin ba kamar yau. Ji yake kamar ba zai jure wani ya kara yabon kyau Nainah ba, ko da mace ce balle namiji. Yana shiga bq din Nainah ta ruga da gudu tana ihu ta yi bayan Amma da ke zaune ta boye gabanta sai faduwa yake ta yi zaton ko dukanta Asad ya zo ya yi, duk da bata tsoronsa a yanzu amman tana tsoron yanayin da ta ganshi a yanzu. Yayi kokarin sauke fushinsa ya dan saki fuska sannan ya isa bakin kofar dakin da Amma take ciki ya tsaya ya cire takalminsa sannan ya shiga, risinawa yai har kasa kamar jiya ya gaishe ta ya mata ya jiki ta amsa masa fuska a sake Nainah na bayan Amma zaune tana dan lekoshi ya kawar da kai.
"Mama don Allah kar a sake bari Nainah ta fita tsakar gidan nan babu mayafi a jikin, kin ga akwai aljannu masu shiga jikin mutum"
"In sha Allahu zata riƙa sawa, mun ga kaya mun gode sosai Allah ya yi Albarka"
"Amin"
Yana amsawa da amin ya mike tsaye yana watsawa Nainah wata muguwar harara domin mugun haushinta yake ji, ita kuma ta murguda masa baki ta kara shigewa bayan Amma.
Yana fita ta fito daga bayan Amma ta zauna tana turo karamin bakinta.
"Wai shi baya son ya ga wani na min far'ah ko muna wasa ko magana, ya fi son ya gan ni cikin bacin rai, idan yaga wani ya sakar min fuska sai wani haɗe fuska kaman hadari mtsssss...!
"Nainah tunda ba ya so ai sai ki daina, namiji baya jindadi idan yana Son mace yaga wani namijin na kula ta................✍️
More comments and share pls!
*Sadeeya Ka'oje ce 💋✍️*
💋𝐁𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐘𝐀𝐌💋
𝑵𝒂
𝑺𝒂𝒅𝒆𝒆𝒚𝒂 𝑲𝒂'𝒐𝒋𝒆
08149979652
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj
PAID BOOK
Littafin *BIN MARYAM* na kudine akan 500 kacal , me