Author : Humaira Bulama Category : Read Hausa Novels
bi bayanta da kallo, yana jin zuciyarsa ba daɗi,
Duk a Binda ke faruwa akan idon su Iya, hakan yasa iya ta bi bayan Balaraba koda ta shigo ɗakin kwance ta sameta ta yi ruf da ciki tana kuka, A hankali iya ta zauna kuka da ita tana sauke Ajiyar zuciya,
"Haba Balaraba! Karki kasance ɗaya daga cikin bayin da suke butulci daga rahamar da Allah ya yi musu me ya saki kuka?"
Cikin shessheƙar ta ce,"Iya wallahi kukan kukan farin ciki ne na ke"
Iya ta saki murmushi.
"Amma kin sa haka da ki ka yi Asad bai zai ji daɗi ba, kin Asad yaro ne da ke gudun ɓacin ranki komin kanƙantansa don haka ki dena kuka yau ranar farin ciki ce a gare mu"
Balaraba ta share hawayen tana sakin Murmushi Iya ma murmushi ta sakar mata. tare suka fito daga cikin ɗakin suka zauna saman kujerar da ke fuskantar in da Asad ya ke zaune, a hankali ya sauko daga saman saman kujera ya durƙusa ƙasa cikin girmamawa ya ce,"Ummi ina wuni"
Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta Balaraba lokacin da taji sautin Muryar Asad, a hankali Lumshe idanunta ta buɗe a akan kyakkyawar fuskarsa Murya a sanyaye ta ce,"Lafiya lau, ya hanya?"
"Alhamdulillahi Ummi"
Hannunsa ya saka cikin Aljihu ya fito da wani ɗan ƙaramin Akwatin roba pink colour mai Masifar kyau ya buɗe shi, zoben Azurfa ne mai kyau da ɗaukar ido ya kamo hannun damanta ya zura mata zoben a yatsarta ta kusa da karami, cip cip zoben ya yi mata tamkar an auna, Balaraba a hanzarce ta kwace hannunta da ga rikon da Asad ya yi ma Hannunta yana gyara zaman zoben, da sauri ya ɗago ya Kalleta, da ita ta mai nuna da mutanen dake cikin falon. Ya yi saurin sunkuyar da kai lokacin da ya juya suka haɗa ido da dr Kamal da Uncle ɗin sa,
"To ni ina tsarabar tawa?"
Iya ta faɗa tana kafeshi da ido.
Akwatinsa ya buɗe ya ɗauko lambar yabo da sauran kyaututtukan da ya samu ya zamu saman tafin hannun Balaraba.
Falon ya yi tsit Hankalin kowa na akan Balaraba da Asad.
Fuskarta dauke ta farin ciki lokacin da ta kammala karatun ta miƙama Baba shima ya karanta kasancewar rubutun Arabic ne,
"Ma sha Allah!, Allah ya yi Albarka"
"Amin ya rabbi Ummi na gode sosai"
Abinci na musamman da Iya ta dafa misihi, Fiddausi ma ta haɗo nata da na Balaraba da tazo da shi daga gidanta ko wane Saida ya ci, tun kafin su kammala cin abinci mutane sun fara cika a gidan ƴan uwa da Abokan Azziki.
******* *******
Kusan kwana ukku sukayi suna fama da jama'a. Ranar da Asad ya shiga sati ɗaya da dawowa manyan manya Malamai jahar Kebbi suka shiryama Asad taro na musamman da za'a karramashi.
********
Sanye ya ke da shedda sky blue mai kyau da tsada sabuwa dal da ita ya ɗauko hularsa mai ratsin sky blue ya sanya sumar kansa ta fiffito gefen dama da hagu ya sanya takalmansa tsadaddi masu matukar kyau da agogon sa baƙi, ya fesa turarensa BLUE DE CHANAL, lumahe Idanunsa ya yi lokacin da ya shaƙi daddaɗan turarensa mai sanyi da saka natsuwa, kallon kansa ya yi ta cikin ƙaton madubin dake liƙe a waldurof ɗin sa ya gayra zaman hularsa yana sakin tattausar murmushi mai ƙara fuskarsa kyau da kamala.
"Asad! Kana ina? Fito mu tafi lokacin ya ƙure sosai"
Hamza ya faɗa yana buɗe ƙofar ɗakin,
Hamza ya tsaya Cak yana kallon Asad ta madubi, a hankali Asad ya juyo yana kallonsa fuskarsa dauke da Murmushi.
"Wow! Ma sha Allah, Tabarakallahu Ahsanul khaliqin!!Allah Yayi halitta awurin nan!! Hamza ya faɗa dai dai lokacin da yake kusantar in da Asad ɗin ya ke tsaye, yau zaka haɗa ƴan matan garin nan faɗa Asad, Allah kadai yasan zuciyoyin ƴan mata da zaka sace a yau" ya ƙarasa maganar cike da zolaya,
Asad ya sunkuyar da kai cike da kunyar Uncle ɗinsa, don shi Soyayya bata gabansa a yanzu har ya gama secondary school bai ta ɓa yi girlfriend ba, a maza ba da kowa ya ke hulɗa ba sai mutum ya kasance natsastse dake maida hankalinsa wajen karatu.
Hamza ya fito da wayarsa mai tsada ya dauƙi Asad hotuna masu kyau kana ya yi musu tare sanna suka fice daga ɗakin, tuni su Iya har sun fita suna tsaye wajen mota suna duk sunyi kyau cikin shigarsu ta Alfarma. suna fita bakin gate motar Dr Kamal na parking Hamza ya yi mishi Hannu ya juya a jere motocin suka hau saman titi kai tsaye suka wuce inda za'a gudanar da taron...
"Daddy Ina zaka je haka naga kana ta sauri lafiya?"
"Lafiya lau Aliyu zanje ne wajen wani taro mai mahimmanci da shek Jabir ya gaiyatan na wani yaro da yaci gasar Alqur'ani ta duniya jiya bayan salla jumma'a bani katin gayyata ya faɗa yana nuna ma Aliyu katin,
"Muhammad Asad Bin Maryam"
Ya furta sunan a hankali, ya yi da Zuciyarsa ya yi Masifar tsinkewa gashin jikinsa ya riƙa tashi, nan take yanayinsa ya sauya jikinsa ya yi sanyi, Zuciyarsa na mai mai masa sunan sam yaƙi fita a ransa.....
"Aliyu Lafiya?"
La....fi...ya lau Daddy"
Ya faɗa Murya na rawa"
"Ka tabbatar?"
Aliyu ya gyaɗa masa kai.
Ƙasa cewar Daddy sauri ya ke bai lura da halin da Aliyu ya ke ciki ba, har ya kai bakin ƙofa ya juyo ya kalli Aliyu ko zaka je mu tafi ba bazan jima ba"
A'a Daddy ba zan je ba"
Ya faɗa ido a rufe.
Daddy ya fice abinsa, ya kasa samun natsuwa a Zuciyarsa da sauri ya fice daga falon yana faɗin "zanje Daddy" tuni Daddy har ya shiga danƙareriyar motarsa mai kyau da tsada ganin Aliyu tafe yasa ya tsaida motar, Aliyu ya buɗe ya shiga sannan suka fice da ga gidan kai tsaye suka wuce inda za'ayi taron cikin ƙanƙanen lokaci suka iso, kusan lokaci ɗaya motocin suka iso..............✍️
(Na ce me ya hwaru? Jama'a ruwan birona ya ƙare 🤣🤣🤣 Ali ya ga Asad🤣🤣🤣)
*More comments and share pls!*
*Sadeeya Ka'oje ce 💋✍️*
💋𝐁𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐘𝐀𝐌💋
𝑵𝒂
𝑺𝒂𝒅𝒆𝒆𝒚𝒂 𝑲𝒂'𝒐𝒋𝒆
08149979652
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj
𝑷𝒂𝐠𝐞 25-26
_______kusan lokaci ɗaya motocinsu suka iso, Dr Kamal ne ya farayin parking sannan Hamza, Aliyu dake zaune cikin mota hankalinsa duk a tashe ya ke bugun Zuciyarsa ya tsananta sosai yasa hannunsa ya dafe satin zuciyarsa ya kwantar da kai gefen kujera ya rumtse idanunsa da ƙarfi, Daddy ya yi parking kusa da motar Hamza ya juyo yana kallon Aliyu, "Badai Bacci ka ke ba?"
"Shuru Aliyu baiko motsaba balle ya amma masa, A karo na biyu ya ce,"Aliyu mu ta fi"
A hankali ya buɗe fararen idanunsa da suka kaɗa sukayi jazir Murya a raunace ya ce,"Daddy mu tafi gida bana jin daɗi jiki na"
Hankali a tashe Daddy ya ce,"Aliyu mi ke damunka?"
"Daddy wallahi nima ban sani ba Zuciyata ta ke bugawa sosai tamkar zata fito"ya faɗa yana ɗora hannu Daddy saman ƙirjinsa.
"Subuhalillah!" Daddy ya faɗa a ruɗe yana janye hannunsa. Aliyu me same ka? Innalillahi!" da saurin ya juyarda a kalar motarsa suka bar wajen,
Dai dai lokacin su Dr Kamal suka fito daga cikin mota ya bi bayan motar Daddy ya da kallo har ta ɓace masa, a ransa ya ke mamakin me ya kawo Daddy wajen nan?.
A jere suka wuce cikin Hall ɗin ya sha ado na musamman, Shek Jabir na ganin Asad ya yi ma ɗan Agaji maganar ya kai Asad ɗin wurin zamansa na musamman da aka tanadar masa, ɗan agajin ya iso wajen da suke tsare ya raɗa masa a kunne, Asad ya juyo ya kallesu kana ya faɗa masu, ɗan agaji a gaba Asad na biye da shi baya har suka isa wajen da zai zauna, su iya ma suka nemi wajen suka zauna suna kallon Asad daga in da ya ke zaune.
Bayan wasu ƴan mintuna Aka buɗe taro da Addu'a, Hall ɗin ya yi tsit kowa ya natsu suna sauraren mahimman jawabai da shek Jabir ke yi, daga nan kuma suka fara gabatar da abin da ya tara su a ciki harda ɗaukar Nauhin karatun Asad da wasu manyan mutane sukayi duk ƙasar da ya so a fadin duniyan har ya kammala karatunsa kyauta, Shek Jabir ya ɗamƙama Asad makullin danƙareriyar motar sa mai kyau da tsada da katardun gida da kuɗaɗe masu yawa,
Su iya baki har kunne saboda Murna da farin ciki.
Haka taro ya watse lafiya bayan Anci an sha.....
*ALIYU*
Kai tsaye Daddy ya wuce da shi Asbiti domin duba lafiyar sa, bayan dr ya duba shi ya rubata maganin, daga Asibiti Daddy ya wuce pharmacy ya saya ma shi maganin suka wuce gida suna isa gida Daddy ya wuce da shi ɓangarensa da kanshi ya ɓalle maganin ya miƙa Mishi tare da ruwa, yana gama shan maganin ba jimawa bacci ya yi Awon gaba da shi.....
Bacci sosai Aliyu ya yi, ko da ya tashi Normal ya ke jinsa hakan ba ƙaramin daɗi ya yi ma Daddy ba....
*FOUR MONTH LATER*
Rayuwa ta yi daɗi ta ko wannen ɓangare yau satin Asad guda da barin Najeriya zuwa U.S....
*DADDY*
Zaune ya ke cikin danƙareriyar motarsa wata babbar macce na zaune a gefensa sanye ta ke da less mai kyau da tsada tana zuba kamshi, ta juyo cikin kissa da kisisina irin ta manyan mata ƴan duniya ta ce,"Honey! wai yau kam saura kwana na wa?"
Daddy ya saki tattausar murmushi mai kice da tsantsan farin ciki ya ce,"Sati biyu ko?"
"Allah satin biyun sunyi yawa yawa"
"To ya ki ke son a yi yanzu?"
"Kwai a maida shi one week na riga na kammala komi ranar Aure kawai na ke jira"
"Ba da muwa Allah ya nuna muna!"
"Amin Honey" tana faɗa tana rufe fuska........
________★★★
Yana gama parking ya nufi ɓangaren mama zaune ya sameta ,"Laila ki same ni a falo na" ya na kai ƙarshen maganar ya wuce zuwa Ɓangaren Umma ita ma a falo ya sameta zaune tana kallon Sunna tv,"Shukura ki sameni a falo na yanzun nan " kafin ma ta juyo har ya fice daga falon.
"Ikon Allah!" ta faɗa a hankali, kusan lokaci ɗaya suka iso a ɓangaren Daddy. zaune suka same shi kahan yasa suma suka zauna, kowa da abinda yake saƙawa a ran shi, Daddy ya yi gyaran murya yana kallonsu kaman yadda suma suke Kallonsa,"zan samu nera miliyan goma a account ɗinku!"
da saurin duka ɗago suna Kallonsa cike da mamaki, saboda bai taɓa yi musu irin wannan kyauta mai tsoka ba,
"Bayan wannan kuna akwai abinda kuke buƙata? Shuru ba wanda ta yi Magana, idon akwai abinda ku ke buƙata bayan wannan kiyi magana tun lokacin bai kure muku ba"
"Umma ce ta yi ƙarfin halin.cewa, "daman ina son na fara oder kayan kicin daga China ina Saidawa"
"Okey, ke fa Laila?"
"Ni ma ina son na riƙa saro kaya irin su less, Atamfa, Abaya, ina Saidawa"
"Zan tura kumu 20millions!, Allah ya kawo kasuwa mai Albarka"
Cikin tsananin farin ciki suka ce,"Amin!"
"Bayan nan baka buƙatar komi?"
A tare suka ce,"A'a"
"To nan da Sati ɗaya za'a ɗaura min Au....re!"
A razane suka ɗago suna Kallonsa nan take fara'ar su ta ɓace ɓat tamkar walƙiya,
Mama ta miƙe tsaye a fusace tana faɗin,"Aure Alhaji! Ina wallahi bazai yiyuwa ba wannan abin kunya har ina? tsoho da kai da jikoki zaka ce Aure za ka yi, ga wanda ya kamata kayima Aure can amma ba ka yi ba saboda baka san ciwon kanka ba, kai yanzu ko kunya baka ji ɗiyan ka suji labarin zaka kara Aure!, shiyassa ka sauya baka damu da mu ba daman wallahi na jima da gano inda ka dosa" ta ƙarasa maganar tana huci,
Umma ta ɗora daga inda ta tsaya,"Alhaji idonma mafarki ka ke kayi gaggawar farkawa da wane ido zamu kalli ƴaƴanmu? Yanzu kai da shekarun nan naka har zaka iya kula macce da sunan Soyayya, lalle ba shakka! Wallahi bazai yiyu ba bazamu yi kishi da ƴar cikin mu, haka kawai"
"Fusace Daddy ya ce ya isheku hakan,Aure kuma ba fashi sai an yi shi, Na dai ja muku kune, kowa ya tsaya iya matsayinsa in ba haka kun san saura"
Har Daddy ya fice Mama da Umma basu gama mamakin Daddy ba,
Umma ta kalli inda mama take zaune ta rabka Uaban tagumi,"Yaya yanzu haka zamu zuba ido muna kallon Alhaji ya yi Auren nan?"
"Uhmmm! to ya zamuyi Shukura? Bamu isa mu hana Alhaji Aure nan ba, tunda kiga ya dage sai ya yi kawai mu zuba Mishi ido duk abinda ya biyo baya shi ya jawa kansa, ba dai mun kwashi rabon mu ba, ko yanzu kasuwa ta watse ɗan koli yaci riba Allah bada zaman lafiya mu ai muna sunan matan Aure ne kwai yaushe rabo da wani abu ya shiga tsakanina da Alhaji"
*********
Lokacin da su Mama suka faɗama ƴaƴansu halin da ake ciki sun shiga damuwa sosai su a ganinsu kaman abun kunya ne ace kamar Daddy da ya ba shekar hamsin baya ace zai ƙara Aure Aliyu ma sam bai ji dadin abinda Daddy ya ke ƙoƙarin aikatawa, har tunkarsa sukayi da maganar akan ya janye daga karshe haɗe ya yi tare da iyayen nasu ya yi musu wonkin babban borgo ko kaɗan bai raga musu ba hatta Aliyu......
Sunaji suna gani aka daura Auren Daddy da Amaryasa Saliha, komai ya yi daɗi tsaknin Amarya da ango haka suka dawo tamkar saurayi da budurwa sai shan Soyayya suke da amarya Saliha, Saliha irin matan nan ne wayayyu da idon su ya buɗe sosai kuɗi ta gani shiyassa ta auri Daddy, Bazarawa race kusan Aurenta shidda Daddy shine na bakwai duk Auren da take bata taɓa haihuwaba hakan yasa yake cin Karenta babu babbaka. da kissa da kisisina ta saye Zuciyar Daddy....
Tunda Aka daura Aure Amarya ta tare a bangaren Daddy Su Mama suka dawo abin kallo Kwata kwata bai damu da su ba, tun abin na damunsu har ya zame musu jiki daga ƙarshe kusa tattara labarin Daddy gafe domin yanzu basu ko da lokacin kansu Business ɗin su suke hankali kwance saboda ciki gaban da suke samu a harka kasuwanci na su, Umma ta janyo sukanta daman duka ƴaƴan ƴan wanta ne duk kansu uwayensa ɗaya, haka suka riƙa gudanar da kasuwanci nasu bayan ko waccensu mijinta ya bata 5 Millions taja jari. Sai gaci cikin ƙanƙanen lokaci suka buɗe katon shago suka cika shi da kaya.
A ɓangaren Mama ma komi tare take da ƴaƴanta ita ma tuni sun bude shago mai girman gaske suka zuba ma'aikata.......
Asad tun bayan tafarfasa kusan kullum sai ya yi waya da iyayensa, wani lokaci na idon video call me sai suyi wajen awa ɗasu waya musamman ma ranar Weekend, Baida wata matsala a fanni karatunsa.......
Haka dai rayuwa taci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali,
*BAYAN SHEKARA GOMA SHA UKKU*
Da sassafe sanyi mai daɗin iskar damina Na kadawa gari yayi shiru sai sanyi mai ƙamshi dan ruwan da akayi aka ɗauke sai duhu duhu da ɗan yayehin ruwa da bai gama ɗaukewa ba, Kamar wacce akai wa dole haka ta bude manyan lussasun idanuwanta da suka rine suka sauya kala sakamakon dadewar da tai tana bacci Akan farincikin ta sauke idonuwanta wato mahaifiyata wacce ke zaune a saman tabarma da take kwance,
"Nainah yau ba zaki je tallan ruwa ba?"
hakan yasa ta tashi daga kwance da take ta fito daga cikin bukka tana hamma ba tare da ta rufe bakinta ba harta gama hamma, da hanzari ta nufi wani ɗan wuri da ka killace da shi da tsohon kwano duk ya hude ta yi fitsari ta fito ta yi Alwalla Jikinta na karkarwa saboda sanyi tana kammala Alwalla ta nufi ɗaki cikin sanɗa sanɗa saboda gida a jiƙe ya ke da ruwa. tana isa ɗaki ta ɗauki kuɗaɗɗen hijabinta ta saka ta kakbarta sallah, tana kammala sallah ta ɗaga Hannayenta sama tana Addu'a kamar ko yaushe,"Allah ka jiƙan Mahaifina Allah kasa ya huta Allah kasa Aljanna ce makomarsa! Allah ka jiƙan Kawuna Tukur Allah kayi Mishi rahama, Allah ka jiƙan Dada da Malam, Allah ka ƙarama mahaifiyata lafiya mai amfani!"
ta tofa Addu'a ta juyo tana kallon mahaifiyarta tana Murmushi,"Amma! Ina kwana?"
"ta gyaɗa kai tana Murmushi.
a hankali ta miƙe tsaye ta cire hitabin tare da sarkafe shi saman igiya dake ɗaure a ɗakin, ta ciro madubin roba irin mai hannun nan dake like saman zana ɗakin ta kalli fuskantar ta cikin madubin tana Murmushin da ya ƙara bayyanar da kyawonta demple ɗin ta suka lotsa sai faman Lumshe manyan Idanunta ta ke, tana kara godewa Allah kan ni'imar kyau da Allah ya yi mata ,Abu ne da ya ke bayyane, bata bukatar kowa ya kalleta ya fada mata cewar ta da kyau, kyau na hali ko