Bin Maryam Book 1 Sadiya Kaoje

Author :  Humaira Bulama Category :  Read Hausa Novels

Chapter   1 / 30

1 to 3K   out of 87.6K words

💋𝐁𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐘𝐀𝐌💋

𝑵𝒂

𝑺𝒂𝒅𝒆𝒆𝒚𝒂 𝑲𝒂'𝒐𝒋𝒆

https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj

𝑷𝒂𝐠𝐞 1-2

_____"Aliyu! don ALLAH kayi haƙuri ko don cikin dake jiki na!, Aliyu idon ka koreni yanzu ina zan je cikin daren nan?. "Wallahi sai kinbar gidan Bazan iya zama dake ba!".

"Innalillahi na shiga Ukku! Aliyu yau da bakin kake kiran na tafi na bar ma gidan ka? Mena tare maka?

Aliyu Ni Balaraba kake kora?".

Wani irin mugun kallon ya watsa mata tamkar ya yi tozali da kashi cike tsana kafin ya daka mata wata uwar tsawa ya na ce wa.

"Na ce ki fice min da ka gida tun da ba ubanki ya gina shi ba!".

Jikinta Gabaki ɗaya ya dauƙi rawa cike da tsoro matsanancin da fargaba, ya sake daga mata wata tsawa cike da hargagi,"nace ki fice min daga gida, bari kiji ki saurareni da kyau Ni Aliyu daga yau babu Ni ba bu ke Balaraba,duhu ya yaye daga idanuna an yi walƙiya na ganki a yanzu tsirara nake kallonki, kije na sake saki Ukku!".

"Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n lahaula wala ƙuwwata Illah billahil aliyul Azhim Hasbunallahu wani'imal wakil Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan minha" sune Adduo'in da take iya maimaitawa afili da kuma ranta.

Tashin hankali jiri da buguwar Zuciya su ne suka same ta a lokaci guda, cikin wani irin watsanancin tashin hankali,"shi kenan Murja kinyi nasara akan Aliyu kin shiga tsakanin mu. ta raba Ni da wanda yake shirin in ganta Rayuwata da soyayya da tausayi da kulawa, a yau Soyayya da tattalin da yake nunamin sun koma zazzafar ƙiyayya,mai muni. Wai yau ni Aliyu ke jifa da waɗannan miyagun kalamai masu zafi.

Kuka take rusawa harda shashsheƙa muryarta ko fita sosai ba ta yi tana cewa,"Haba Aliyu Me yasa kake ƙoƙarin cutar da ni? Me nayi kama zakayi irin wannan Sakayya?".

Sai muryarta ta yi rauni tana ci gaba da kuka," ka gayamin Aliyu wane laifi na aika maka?Aliyu idon baka ji tausayi a wannan hali ka nake ciki wa gareni da zai nuna tausayi a kaina bayan ALLAH!, Aliyu ka tuna Auren Soyayya mu kayi bana ƙiyayya ba!.Aliyu yanzu don ka tara abin Duniya shine zaka guje ni? "Bari jiki na gaya Miki ban taɓa jin son ki a raina ba! Na Aure kine saboda kyawunki na mori surar jikin. Baki da wani Amfani a wajena yanzu, cikin dake jikin ki kisan yadda ki ka yi dashi don ni ban shirya zama Uba a yanzu ba,idon Kinga dama ki haifeshi ko ki zubar ya rage naki".

Ya ƙarasa maganar ya na ya mutse fuska.

Ta sake rushewa da kuka mai tsuma zuciya,Aliyu ya kalleta yana sakin maƙetashin Murmushi, na gama dake har abada ba za ki taɓa samun kulawa daga gare ni".

Ƙasa ta durƙushe tana kaka tana faɗin ,"Aliyu ka cuceni kaci Amana ta, Macuci Azzalumi!".Tas! tas!! tas!!! taji saukar zazzafar Mari. da ƙarfi ta mike tsaye ba zato ba tsammani yaji saukar Zazzafar Mari a fuskar sa. Murya a disashe ta ce,"Ban yi lalacewar da ɗa namiji irinka zai mare ni na kyaleshi", tai magana tana nuna shi da yatsa. Aliyu ga baki ɗaya jikinsa ya yi sanyi,ko a marki bai taɓa zaton idon ya daki Balaraba zata iya ramawa ba, Bama Balaraba bayan mahaifiyarsa ba wani ma haluki da ya taɓa marinsa, da ƙarfi ya yunƙura zai mareta tai saurin riƙe Hannu sa tana faɗin "ko a lama karka kuskura. ta sauke hannusa da ƙarfi har Saida ya bada wani sauti ƙat,"Balaraba Ni zaki mara?,"

"Aliyu Abinda da yafi Mari ma zan Aika ta maka muddin kace zaka ta ɓa Lafiyar jiki na, Aliyu kaine mutum na farko da ya fara sani na zubar da hawaye na a Rayuwa,Sannan kaine mutum na farko da ya fara karya min Zuciya ta a rin mutanen da na yarda dasu a rayuwa ta,Bazan yi maka mummunan fata ba, Amman kasan da cewa duk mutumen da kaiyi sanmadiyyar zubar Hawayen sa kaima naka zubar Hawayen ka na tafe".

A fusace ta wuce ɗaki ta ta haɗa kayanta cikin A kwati ta fice daga ɗakin tana share hawaye, ba tare da ta sake kallon inda Aliyu yake tsaye ba ta fice daga falon, a farfajiyar gidan tai tsaye tana kallon lungu da saƙo na gidan, gida ne na Alfarma mai ɗauke da Ɓangaren biyu, Numfashi taja mai zafi kana ta fesar.ganinta tafe yasa mai gadi ya nufi wajen ta gadan gadan yana faɗin, "Ranki ya daɗe ina zuwa cikin raden nan?". ya tambaye tana mai nuna tausayi a kanta, "gidan mu zanje".

"Ranki ya daɗe dare ya yi sosai kusan 12:30 yanzu". ya faɗa yana kallon A gogon Hannu sa, Ranki ya daɗe koda kin fita ba zaki samu abun hawa, kuma ɓata gari na nan ta ko'ina za su iya cutar dake. Idon ba damu don Allah ki koma ciki cikin gida".

Kallon sa tai hawaye na zuba a fusakarta "Baba Musa wallahi ko gawata bana fatan ta a shigar da ita gidan Aliyu mutumen da ya yaudare ni ya lalata min Rayuwa me zan koma nayi a gidan sa, wallahi tallahi kaji rantsuwar ɗan Musulmi nida gidan Aliyu har Abada. Yadda nake jin tsanarsa a raina wallahi zan iya kashe indon muka kasan ce a wajen ɗaya". Baba Musa ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciya.

"Baba Musa son ALLAH ka buɗe min gate na wuce bana son na ƙara koda Minti ɗaya a cikin gidan nan Zuciyata zata buga".

"Ranki ya daɗe idon ba damuwa muje na kaiki gidana ki kwana idon gari ya waye sai ki wuce gida, Hankali zaifi kwanciya akan ki kama hanya a matsayin ki macce".

Sosai taji daɗi yadda Baba musa ya nuna tausayi a kanta, ɗakinsa ya koma ya ɗauki fitila da sanda sannan ya fito ya ɗauki A kwatinta suka fice daga gidan, tafiyar mintuna goma sukayi, suka iso gida, ɗan ma dai-dai cin gida mai ɗauke da ɗakuna Biyu suna isa ƙofar gida ya kira Matarsa Ubaida ta buɗe musu ƙofa saboda ta ciki aka rufe ƙofar, bayan mintuna Biyu ta iso tana buɗe ƙofar idanunta suka sauka kan Balaraba dake tsaye, Mamaki fal a fuskar Ubaida ta kalli Baba Musa ta kalli Balaraba,"Baban Nana lafi..... da sauri Baba Musa ya tari Numfashinta "Kinga kaita ciki tana buƙatar hutu". A kwatinta Ubaida taja zuwa cikin gida Balaraba tabi bayanta, kai tsaye Ubaida ta wuce da ita ɗakinta, ta sauko da yarta Nana yar kimanin shekara Huɗu a duniya za Kwantar da ita ƙasa, Balaraba tai saurin da Katar da ita,"Ai da kin barta saman gado ƙasa ya isheni".

A'a kam taya zaki kwanta a ƙasa? Anty Balaraba".

"don Allah ki kwanta saman gadon nan kodon Cikin dake tare dake, bari Naje na rufe gida, ba tare da taji me zata ce ba ta fice daga ɗakin, "Baban Nana Nifa a tsora ce na ke, anya ma Anty Balaraba zata iya kwana a gidan nan? ɗakin da ba A.c Balle fanka"

"To ya Za tayi, Kaddarorin Rayuwa ne ba yadda ba zasu soma dan Adam ba, ALLAH dai ya bamu ikon cin jarabawar duniya".

"Amin Baban Nana".

"Karɓi nan gobe A saya mata koko da ƙosai ta samu na karyawa".

cikin ladabi da ƙarɓi kuɗin tare da yimai godiya. Bayan ta fiyarshi ta rufe gida ta wuce ɗakin.Nana da ta bari kwance ƙasa ta tarar da ita saman gado.

"Anty Balaraba don ALLAH ki tashi a ƙasa nan ki koma saman gado",

"A'a Ubaida kibarni a ƙasa nan na kwanta taya zan kwanta saman gadon Baba Musa, ki barni ka wai a nan, nafi jin daɗin kwanciya a ƙasa".

Balaraba. A daren kasa bacci ta yi duk sanda ta juya Aliyu take gani ta riƙa tariho Soyayyarsu ta baya har kawo yaudarar da butulci da ya yi mata, a yanzu Kum shine mutum da tafi tsana a duniya,

Assuba fari Balaraba ta fito daga ɗakin tai Alwalla ta fara nafila kamin ta gabatar da Salla Assuba, ta saba da wannan ɗabiyar tun tana ƙarama da Askar ɗin safe da na maraice duk da kasancewar tana da ƙananan shekaru hakan bai sa na watsar da koyarwa Iyayenta, Balaraba ko kaɗan bata wasa da Salla ko wacce sallah tana yinta cikin lokacin ta duk abinda take komi mahimmancin sa idon lokacin salla ya yi takan da Kawar da shi har sai tayi salla, Addu'oi safe da maraice ba su wuce ta a bin har ya zame mata jiki. Idon bata yi sai taji bata cikin natsuwa.

Saida Rana ta fara fitowa Ubaida, ta tada Nana tayi Sallah, tana gama salla ta miƙa mata jug da kudin da Baba Musa ya bata," Kije wajen Inna mai koko ta baki kokon ɗari Ukku ƙosai ɗari ukku ta ƙara Nera ɗarin Akan kuɗin da Baba Musa ya bata.

Wutan Murhu Ubaida ta kunna ta ɗora ruwan zafi, tana zaune a wajen har ruwa suka tafasa ta juye a bokiti ta surka dai dai yadda mutum zai iya yin Wonka, ta sake cika tukunyar ta maida saman wuta, ta wuce Bayan gida, Zaune ta tarar da Balaraba ta ɗan jin gida da bango bacci ya fisgeta, har zata juya taji Murya Balaraba tana faɗin ,"Maman Nana An tashi lafiya?"

"Lafiya lau Alhamdulillahi, ga ruwan Wonka can na kai miki ban ɗaki, da kyar ta mike tsaye jijinta duk ya yi tsami saboda kwanciyar da tayi a ƙasa, kayan Jikinta ta cire da daura zane ta saka hitabi ta wuce ban ɗaki, tana fita Ubaida ta gyara dakin tsab, tana zauna Nana ta shigo,"Nana kin daɗe yau kam". cikin ɗan tsamin baki irin na yara da basu kware da magana ba ta ce,"Mama mutane Sunyi waya a jen saida nabi ya yi"

Ubaidah tayi Murmushi tana Kallon yarta, " mutane sunyi yawa ake ceba ba waya ba, Layi ake cewa ba ya yi Kinji"

Balaraba ta shiga ɗakin tana Murmushin da kasan na ƙarfi hali ne kwai take,

Fita Ubaida ta yi daga dakin tare da Nana don ta samu damar kimtsa Jikinta, bayan Mintuna biyar Ubaida ta shigo zauna ta sameta tana naɗe kayan da ta cire, ta sanya doguwar riga ta shadda hakan ya ƙara fito da ƙaton cikinta, sosai rigar tayi mata kyau, "Anty Balaraba ga kayan kari nan tayi maganar tana nuna mata jug ɗin koko da ƙosai, "kaman ko ta san tana buƙatar Abici saboda wata irin jahilar yunwa taje ji har jiri jiri take ji, abin cikin sai shure shure yake kaman zai fasa cikin ya fito. "Ki zauna muyi karin a tare".

"A'a Alhamdulillahi".

"Nana zo nan mu karya kinji".

"A'a na ƙoti "(ƙoshi)

Fita Ubaida tayi daga ɗakin, daga ita sai Nana da ke bata labari". Saboda akwai sabo mai ƙarfi tsakanin ta da Nana da Ubaida wani irin lokacin idon taje kaima Baba Musa Abinci takan shiga wajen Balaraba suyi hira wani lokaci har aiki take mata. Duk Aure Auren Aliyu bai taɓa Auro macce kirkin Balaraba ba da son mutane duk da tana kaima Baban Nana Abinci hakan Baisa Balaraba ta dena bashi ba,

sosai tasha kokon da ƙosai, sunyi mata daɗi musamman koko da take jin tsami tsamin sa,

Ƙarfe tara da rabi Baba Musa ya shigo gidan, bayan sun gaisa ya sanar da Balaraba ga keke nan na jiran ƙofar gida. "Na gode sosai".

"Miye na godiya Ranki ya daɗe?".

Kayanta Ubaida ta fito dasu ta miƙa ma Baba Musa ya fita dasu waje, ta ciro 5k cikin handbag ɗin ta, ta miƙama Nana gashi kisai Alawa ko".

"A'a Anty Balaraba ra don Allah ki bari kudin nan sunyi yawa".

"Wallahi banza karɓa ba". ta faɗa cikin gaskiya da gaskiya.

Godiya sosai Tayi musu da irin karamci da kulawa da suka nuna akanta, suna tsaye a ƙofar gida har Saida suka Dena ganin mai keke.

Mai keke bai sauketa a ko'ina ba sai a ƙofar gidan su, gida ne irin na talakkawa, tana sauke kayanta dai dai lokacin wani kyakkyawan Saurayi da bai wuce shekara Ashirin da biyar ba, sanye da farar Jallabiya, kusan kamammi su ɗaya da Balaraba, ya nufo wajenta da sauri yana faɗin ,"Balaraba Lafiya da sassafe haka? Ina Aliyu?".

Kaman abinda take jira ke nan ta fashe da kuka mai tsuma zuciya. "Hamma Aliyu ya sake ni!".

"Me kika ya masa?".

"Miwaɗaimo komi,(Ban masa komi ba)

Kayan ta ya shigar dasu cikin gida,

"Hamza Ba ƙuwa mukayi?".

"A'a Iya Balaraba ce".

"Daga subaka? Jam waddi mo"( da sassafe? Lafiya me ya kawota?)

Sumi sumi ta shigo cikin gidan kaman wadda kwai ya fashe a ciki.

Kallon ta iya tayi daga sama zuwa ƙasa tana taɓe baki, har ƙasa ta duƙa da kyar saboda halin da ta ke ciki tace,"Iya ina Kwana?".

"Lafiya, mi ya kawo gidan tunda safe haka?"

"Murya wa naje ji haka?"

Ya yi maganar yana a je biyar dake hannun sa, da ɗan sauri sauri Balaraba ta nufi wajensa ta rungumesa,"Maryam! Ya kira Ainihin Sunanta wanda shi kadai ke kiranta dashi. Malam Ahmadu farin mutum ne, dago ɗan siriri Baida jiki sosai, kana ganinsa kasan Bafulatanin Asali ne. Matarsa ɗaya Saudatu, da ƴaƴan sa Biyu Hamza da Maryam wanda suke kira da Balaraba, Balaraba daguwa ce fara Sal, gashi har gadon baya, Siriri ya kusan kamannnta ɗaya da malam Amadu, Balaraba ta, taso cikin so da kyaunar iyayen ta, Musamman malam Amadu da bai san ida zai a jeta ba, Balaraba Shekarunta goma sha tara A duniya,

"Ki yi A hankali baki ganin yadda ki ke, ya faɗa yana ƙara rungumeta, A hankali ta sauke Sassanyan Ajiyar zuciya,

"Baba Ina kwana?".

"Lafiya lau, ina mijin na ki?".

"Baba Aliyu ya sake ni". ta faɗa tana kuka,

"Innalillahi wa'inna Ilaihim rajiu'n!, Me kika masa?".

tana kuka ta zai yana musu komi,

"Daman Abinda ke faɗin Akan rayon nan gaskiya ne?"

"Ai ga irinta nan, Abinda ake gudu ya faru, ba yadda banyi da Balaraba akan karta Auri yaron nan tayi banza da magana ta, ba wanda bai san Halin yaron da Auri saki yake Amman duk da haka tace ta Amince yanzu wa gari ya waya?, Kinbi son Zuciya kinyi abinda ya sha Miki kai, da Ƙananan shekarunki kin ɓata rayuwar ki, ya sakoki da ciki, daman irin wadannan rana zata zo da bata da wata Amfani a wajenki da kinbi Magana da kan bai faru dake ba, duk da Mutum baya gujewa kaddarsa".

zamewa Balaraba tai ƙasa tana kuka tana faɗin ,"Iya don ALLAH ki gafarce Ni, nayi da nasani na reshin bin maganar ki, Hawaye ta share kaman yadda Iya ma ta share hawayen ta, "Iya don ALLAH ki yafe min kona samu Rahamar Ubangiji".

Hamza ya share Hawayen da suka zubo Mi shi.

"Maryam ki Dena kuka kinji duk wani ɗan Adam baya gujewa kaddarsa, ya faɗa yana nuna tausayi akan ta, ta shi ki je ɗaki ki huta ALLAH ya yi zaɓi na Alheri ya sauke ki lafiya".

Haka Ranar ta yini cikin kunci da baƙin ciki, daga ita har Iya cikin damuwa suka kwana har garin ALLAH ya waye. tayi Nisa Sosai daga dogon Tunanin da taje, hakan yasa bata ji Shigowar Hamza ba. "Balaraba! "Taji shigar sunanta har ƙoƙon ranta, sai dai ba ta ɗ'ago ba ta amsa da "Na'am Hamma".

Zama ya yi suka da ita suna fuskantar juna, cikin tausasa Halshe ya ce, "Balaraba ke! Yanzu ba ƙaramar yarinya bace, duk da kasan cewarki mai ƙananan Shekaru, ya kama ki cire damu a ranki tunanin da kike ba shi zai maida Aliyu a wajenki ba, Haƙiƙa Balaraba kin tabba Babban Kuskure a Rayuwar ki na bijirewa Baba da Iya da ki ka yi, Baba ya goyi bayan ki ne kwai don farin cikinki Amman ba don yana son Auren nan ba, Balaraba kowa a faɗin farin nan ya san Halin Aliyu da irin ɗaurin gindi da yaje samu daga wajen Mahaifinsa na lalata Rayuwar ƴaƴan mutane musamman talakkawa irin mu marar galihu, Soyayyar Aliyu ta ruɗeki ta sa kin bar mazaje na gari kin zaɓi Azzalumi da bai san kimar macce ba, kin san irin son da Baba ya ke mi ki, Amman duk da Haka kika kasa gano Reshin son Auren ki da Aliyu, tun da aka ɗaura Auren ki, ki ba bar gidan nan kullum Baba cikin tunanin wanne hali kike ciki, Kullum Addu'ar sa Allah ya kareki daga sherrin Aliyu karya ya maida ke ƙaramar Bazawa, a kullum da tunanin ki yake kwana da shi yake tashi, kiran ki da kike ganin inayi a kullum Baba ne ke sani na kira yaji ko ba wata Matsala,ba don komi

1 / 30