Author : Humaira Bulama Category : Read Hausa Novels
yake yin haka ba sai don son da yake Miki, kwana Ukku da suka wuce kafin wafuwar Al'amarin nan, Baba ya yi Marfinkin Aliyu ya sakeki sannan ya yi Miki korar walaƙanci, Wallahi Gabaki ɗaya bamu runtsa ba, Saboda hawan jininsa ya tashi ya tsananta sosai, tunda safe muka wuce dashi Asbiti, Baba ba samu Natsuwa har Saida kukayi waya dashi ki ka tabbatar mai da kina cikin ƙoshin Lafiya. Iya ma da kike ganin kaman ta sauya Miki badon komi tayi hakan ba sai don biji re mata da kika yi, da kinbi shawarar Iyayenmu ta tabbatar da hakan bai faru da ke ba!..."
"Hamma yanzu shikenan nan Rayuwa ta lalace?, Hannunsa yasa ya share mata Hawaye, Hamma shi kenan duk Abinda
Aliyu ya yi min ba wanda zai kwato min Hakƙina? Hamma yanzu haka za'a bar maza irin Aliyu a duniya suyi yadda suka ga dama ba wanda ya isa ya dakatar da su?".
"A'a Rayuwar ki bata lalace ba, zaman ki Bazawa ba shine ƙarshen jin daɗin ki ba, Ba gareki farai ba, don Haka ki cire duk wata damuwa a Ranki kodan cikin da ke jikin ki, Ki ɗauka a Ranki jarabawa ce komi zai wuce kaman ba'ayi ba, Hamma Nidai a ciremin cikin nan bana so!, Yadda na tsani Aliyu haka na tsani cikin nan".
"Ha ba! Balaraba taya zaki zubar da cikin nan da ya isa Haihuwa, kisan ki ke son Ki yi? da sauri ta girgiza kai, Miye laifinsa da kike son kashe tun bai shaƙi iskan duniya ba?, Ko Alama karki kuskura ki ce zaki zubar da ciki nan, kin san Me zaki Haifa? Kin sani ko shiƙadai ne ɗan da Allah ƙaddara zaki haifa a duniya daga shi ba wani? Kar laifin Mahaifinshi ya shafe shi, Kibar Aliyu da Halinsa duniya zata koya Mishi hankali, ki Kwantar da hankali ki cire duk wata damuwa a ranki, ki kula da kanki da ɗan cikin ki, idon kikayi haƙiru komi zai wuce kaman ba'ayi ba".
"Hamma ce wa fa ya yi na zubar da cikin ko na haifeshi bai damu ba, shi bai shirya zama Uba ba".
"Ki fi ta batun sa, in dai muna raye Aliyu zai gane kurensa, ke da ɗanki zaku za ku zama masa Wutsiyar Raƙumi, in sha Allahu, ALLAH zai ɗaga da darajjarki fiye da tunani sa. Kedai kwai Kici gaba da Haƙuri in dai muna da rai da lafiya kaman gobe ne farin cikin da walwalarki zata dawo".
Wani irin Sanyi ne taji a Ranta, ganin ta ɗan saki jiki sata ya rinƙa janta hira....
*ALIYU*
Washegari tunda sassafe ya wuce family House ɗin su, Alhaji Usman Marafa shine Mahaifin Aliyu, Asalinsa Buzu ne ɗan Nijer, Nema ya kawo sa Najeriya ya fara ne da Saida ruwa a bairo daga haka ya buɗe shagon kasan yana Saida kayan probitions sannu a hankali kasuwancin nasa ya haɓaka ya zama babban ɗan kasuwa mai zaman kasan, bayan wani ɗan lokacin ya koma karatu inda ya karanci harkar kasuwanci, daga nan ya soma Aikin gwamnati, kafin nan ya Auri Laila wanda ta kasance yar mai gidansa bayan Auren su Saida ta shafe tsawon shekaru Ukku sannan Allah ya basu Aliyu, Alhaji marafa ya dauki son duniya ya ɗorawa Aliyu, tun yana Yaro Alhaji marafa ya sagartashi, duk abinda ya ga dama shi yake baya tsoron kowa wannan Abin na matuƙar ƙonawa Laila rai tayi iya ƙoƙarin wajen gani Aliyu ya shiryu amman ina, wannan dalilin yasa tace In dai irin tarbiyyar da Alhaji marafa zai riƙa iyawa ƴaƴansa ta haƙura da haihuwa, Aliyu nada Shekara goma a duniya ta haifi yarta macce Sumayya, cikin ikon Allah ko Sumayya bata biyo halayen Aliyu ba, Sumayya na da shekara Huɗu Alhaji marafa ya Auri Shukura, kusan lokaci ɗaya suka haihu da Laila ta haifa masa yan biyu Hanafi da Hanifa, hajjiya Shukura ƴaƴanta Ukku Haroon,Abbas, Hannatu, dai dai gworgodo suna zaman lafiya....
Aliyu dogo ne fari tas kaman Mahaifinsa, ga manyan Idanu da dogon hanci, suma kansa baƙa wulik ta sauko har saman wuyansa, kyakkyawa ne Ajin farko. Duk da ya tashi sagartacce hakan bai haka shi samun ilimin na Allah dana zamani, Aliyu yaro ne mai ƙoƙari sosai ta ko wanne ɓangare, hakan yasa sauran Abokansa ke kiransa Aliyu Genius ( Ɗan Baiwa) Shekarunsa Ashirin da tana a duniya.....
Yana shigo kwanar da zata kai shi gidan su ya danna Hon ɗin matar sa, ɗa bi arsa kenan saboda baya son jira sai dai a jirasa, tun kafin ya ƙaraso mai gadi ya wangale masa gate a guje ya wuce cikin gida ya yi parking ya fito, gidan ne na Alfarma mai ɗauke da Ɓangare Ukku gida irin na zamani ko'ina a ƙawatashi da folawowi masu kyau da ƙamshi, a hankali ya nufi ɗayan Ɓangaren dake gefen daman sa,
"Mama don Allah kiyi sauri tun Yah Aliyu bai shigo ba taji shigowarsa yanzu zai zo duk ya shi mutane da iko kaman wani sarki, " Waton Gulma ta kika a gidan nan ko?, Wanna ya zama na farko ya zama na ƙarshe da zan sake jin sunana a bakin ki, Hanifa taja bakinta tayi gum kaman bata wajen, tasan halin Aliyu sarai baya son yayi magana a maida mishi koda ko shine da Gaskiya.
Zaman yayi saman kura ya dora ƙafa ɗaya saman ɗaya, Mama ta kallishe ta kawarda fuska gefe kaman bata san da zamansa a wajen ba, "Ina Kwana Mama".
"Lafiya". ta bashi Amsa a takaice
"Ke! Tashi ki haɗo min Breakfast".
"Ke! dawo ki zauna, Mama tayi maganar tana kallon Hanifa da ta gama da burcewa sai zarar ido take.
juyowa tayi ta kalli Aliyu da ya haɗe fuska kaman Hadari".
"Ma......m...a don Allah ki bari na ɗebo ma....sa". ta ƙarasa maganar Murya na rawa.
"Me ya ha na ka yin Breakfast a gida?".
"Na Saki Balaraba". Ya baya amsa kai tsaye ba tare da yaji shakkun ta ba.
Wata irin zabura Mama tayi cikin matsancin Gigicewa Mama ta ɗora Hannu biyu a ƙirji gani da juyowa da ido tana kallon Aliyu ta kasa furta komi sai kallon Aliyu take da ke karkaɗa ƙafa,
"Aliyu wacce Balaraba?,
"Mama Balaraba dai da kika sani".
"Aliyu kana da hankali ko wa?
Aliyu me ka ke son Maida kanka?
Aliyu ke san miye Aure?
Aliyu Allah ma da yace Ayi saki duk lokacin da akayi sai Al'arashi ya girgizar Aliyu me ka ɗauki macce?
daga ganin yadda take magana kasan a firgice ta ke..........
More comments and share pls!
*Sadeeya Ka'oje ce 💋✍️*
💋𝐁𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐘𝐀𝐌💋
𝑵𝒂
𝑺𝒂𝒅𝒆𝒆𝒚𝒂 𝑲𝒂'𝒐𝒋𝒆
08149979652
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj
𝑷𝒂𝐠𝐞 3-4
_____Da ganin yadda take magana kasan cewar a firgice ta ke, Mama ta zauna ta na kuka mai haɗe da surutai, "Innalillahi Wa Innalillahir rajiu'n! Ni Laila na ga ta kaina Aliyu ka saki Balaraba? Wa'iyazubillahi!" ta juyar da kallonta ga Aliyu idanunta sun ƙanƙance kamannita sun sauya,
Sumayya tuni ta fara kuka ta cusa kanta tsakanin cibiyoyinta Zuciyarta na wani irin tafarfasa da wani irin kunci saboda halinda Mahaifiyarsu take shiga, duk lokacin da ta shiga halin damuwa Aliyu ne Sila,
da kyar Sumayya ta mike tsaye ta nufin wajen Mama, ganin kwai ta yi Mama tayi wata irin Super ta dire saman Aliyu, "Laila!! Daddy Ya kira kira sunanta da ƙarfi, hakan yasa tai saurin juwa tana kallon sa, "ka shemin ɗaya zaki?".
Aliyu na gefe yana bin kowa da Kallon bai ce Uffan ba,da kyar Sumayya da Hanifa suka ɗaga Mama da ga wajen da take tana faman haƙi
Mama ta matse wasu zafafan Hawaye ta kasa cewa komi illa ido da ta zubawa fuskar Aliyu,ya yi misisi baya ko kallon ina take, Mama ta sunkuyar da kai Zuciyarta na wani irin raɗaɗi da ƙuna, sai kuma wani sabon kuka ya kwace mata, a zafafe Mama ta kwace daga rikon da Su Sumayya sukayi mata tana cewa,"ku barni na kashe Aliyu ko na samu sassauci daga raɗadin da nake ji akan sa, Daddy ya ƙara so wajenta da sauri ya riƙe ta gam ta kasata ƙarasawa wajen Aliyu, sai ta saka Kuka tana faɗin ,"Alhaji don Allah ka barni na kashe Aliyu bai da wani Amfani a wajena gara mutuwarsa da irin Allah ya isan da iyayen matan da yake yaura suka faɗi a kansa, Allah ya gani ina iyaka ƙoƙarina wajen ganin Aliyu ya natsu. Sai kuma taci gaba da kuka gaba daya sai falon ya yi shiru illa sautin kuka Mama da ke ratsa falon, daga Sumayya har Hanifa da Hanafi da shigowar kenan ido suka zubawa Aliyu shima ɗin kallon su yake fusakarsa babu ko gezau balle alamun firgici ko ruɗewa, Daddy yace "Lafiya wai me Aliyu din ya yi?
Sumayya ce tayi karfin halin cewa "Daddy Ya Aliyu ne ya saki Aunty Balaraba har saki Ukku!".
"Son da gaske ka sake ta?".
Babu ko ɗar ya gyaɗa kai ya ce ,"Yes Daddy na sake ta har saki Ukku! Cikin Jikinta ma nace ta zubar don ban shirya zama Uba a yanzu ba".
Mama ta doka Salati da ƙarfi gaske tana kallon Aliyu ɗin tace, Aliyu Kaji tsoron Allah ka Dena cutar ɗiyan mutane.
"Mama ni fa can dama ba sonta nake ba!,
Mama ta ringa girgiza kai cike da ɗimaucewa tana kallon Aliyu, "Aliyu cikin shekaru biyu kayi Aure ɗai ɗai har Aure Biyar me ka son maida kanka?
ta maida kallonta da Daddy don ta ga wanne irin hukunci zai ɗauka, babu wata da muwa a fuskar Daddy yace ,"Aliyu ta ya kayi sake Har ciki ya shiga tsakanin ka da ƙazamar yarin nan?".
Aliyu ya sosa kai yana murmushi ," Wallahi Daddy Nima ban san yadda kayi ba ta samu ciki har ya tsufa haka ban sani ba, Daddy ya yi murmushi kana yace ,"Ai kasan ita doguwar macce ba kasafai aka gane girman cikinta har sai ya girma musamman kuma cikin farin".
"Alhaji iya matakin da zaka dauka kenan wallahi kana cutar rayuwa yaron nan Allah saiya tambaye ka,
Ta ringa girgiza kai tana bin Aliyu da Daddy da wani irin mugun kallo mai cike da tsana.
Daddy yace ,"Ai ina ga wannan ba wata damuwa bace da zaki riƙa tada hankalin ga banza akan ƴaƴan talakawa da kwaɗa yin su ke zamu su da basu kawo kansu da hakan bata faru da su,
"Gaskiya ne Daddy, duk kansu kwaɗayi ne ya za musu musamman Lubna, Surayya, Munira, ƴa'yan matsiyata kawai".
Yana gama fadar haka ya fice daga falon cikin sauri yana hura iska daga bakinsa , su duka suka raka shi da ido har Mama da wani ƙaton Abu ya tokale mata maƙoshi ya kuma ƙi wucewa ganin take abin kaman a mafarki ko Al'mara. abubuwan suke faruwa ta runtse ido ta sake buɗewa sa ta saki kuka mai tsuma zuciya tana cewa,"Alhaji wallahi Abin da kake zalunce ne duk Abinda Aliyu yake kai ke daure masa Gindi Wallahi ina guce muku ranar da Duniya taza juya muku baya".
Sumayya da ke durƙushe a wajen tana kuka ta mike da sauri ta nufi wajen mama tana bata Hakuri tare dasu Twins da kyar ta mike tsaye ta nufi ɗaki,
tayi Nisa a cikin kuka ta yi ruf da ciki kaman wata ƙaramar yarinya, tunani duk ya kare mata yadda Rayuwar Dan ta zata kasance nan Gaba, Sumayya ta janyo ta Jikinta cikin rigar lallashi duk da cewa ita ma ɗin kukan ta ke yi ta ce,"Mama ba Kuka ya kamata muyi ba Addu'a Yah Aliyu yake bukata daga wajen mu, Mama wannan kuka ma da kike wani bala'i ne akan Yah Aliyu, Cikin Raunatattiyar murya mama ta.ce,"Sumayya do ke na yi kuka duk wata uwa ta gari ba zata so ɗan ta ya kasance haka ba, Wallahi ina tausayin Aliyu fice da yadda nake tausayi ku,"Mama dole ne duk wata uwa taji tausayi ɗanta".
"Mama koyi Haƙuri ki Dena kukan nan zaki sanyawa zucuyarki damuwa bayan wanda ki ke tare da ita, ki ringa Ambaton Innalillahi Wa Innalillahir rajiu'n! Komi ya yi tsakani yana tare da sauƙi, Babban tashin hankali ma shine taya zaki tun kari Daddy da maganar Yah Aliyu baya son laifinsa yaya ki ke ganin za'ayi?"
Kukanta ya tsananta ta kasa cewa komai.
"Nima ban san yadda zanyi ba Sumayya sai dai nayi da Addu'a Allah ya shirya min da Aliyu tare da Mahaifinsa!".
*ALIYU"
Yana fita daga Ɓangaren Mama ta nufi Ɓangaren Hajjiya Shukura (Umma) bayan sun gaisa ya wuce Ɓangaren Daddy ya zauna a tanfatsantsen falonsa ya sha kayan Alatu zama yayi ya dora ƙafa ɗaya saman ɗaya yana dannar wayar Hannusa, ya mike kenan zai fita Daddy ya shigo falon, " Ina zaka je? Ina son ka rani Unguwa".
Cikin sauri yace,"A'a Daddy a kwai inda zanje Bby Murja na jira na". Daddy ya yi Murmushi yana ce wa, "Angon Murja Aliyu ya yi Murmushi ya fice daga falon cikin sauri Ya shiga motar sa Hon guda Ya yi mai gadi ya buɗe mishi gate ya fice daga gidan da gudun gaske kaman wanda zai tashi saman,
Yana isa gida ya wuce dakinsa ya faɗa toilet tsala wankansa cikin ƴan mintuna ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya farar riga da wondonsa mai kyau da tsada baƙi ya ɗauko cambus ɗinsa baƙaƙe ya ɗaura a gogonsa mai kyau da tsada ya gyada sumar kasan tana ta kyalli da daukar ido, sai ƙamshin sassanyan turenshi da ke tashi, cikin sauri ya fito daga ɓangarensa ya nufi sabuwar motarsa da bata wuce kwana biyu da saye ba, mota ce mai masifar kyau da tsada ta zamani, ya ja ya fita Baba Musa ya buɗe masa gate ya cilla motar saman titi, kana ya saki tattausar wakar yana bin wakar Auta waziri (Ina kewar masoyiya) Aliyu kenan matarshin saurayi da ake ya yi ga kyau ga kuɗi ga iya kwalliya.
Kai tsaye ya nufi Gidan su Murja suma dai Marar karfine kaman su Balaraba, yana isa ƙofar gidan ya kira ta, bayan Mintuna biyu ya fito taci Ado sanye da farar sheda da bakin gyale sai ya zama kaman tamkar an ko sukayi,tayi kyau Abinda,
Ya tsura mata ido da shegen kallonsa yana murmushi ta burgeshi matuƙa ta muka dau hankalinsa fiye da kullum da ido ya yi mata mata nuni da ta karaso cikin ta kunta mai cike da tsanuwa ranta farikal don ta san ta farantawa Aliyu rai yau tana mamakin irin jararbar son da take masa wanda har take bijirewa iyayen Akan turbar da iyayen suka ɗorata na saka Hijabi saboda ta faranta masa, a hankali ta buɗe mota ta shiga sassanyan turarenta ya dagi Hancinsa ya Lumshe ido gami da kwallonta Murya can ƙasan maƙoshi ya ce," Ina son Kamshin turaren nan naki mai sanyaya zuciya, kiyi Masifar kyau baki taɓa yin kyau irin na yau ba".
Ta saki siririyar Dariya ba tare da ta ce komi ba, ya kunna motar gami da cewa muje kiga gari ko?". Murmushi ta sakar mai,
A guje ya bar ƙofar gidan su. Bai tsaya a ko'ina ba sai a sha'aban Super market ya yi mata seyayya mai yawa sosai sannan suka wuce Azbir Arena suka huta Saida da La'asar ya maida ta gida tare da tabbatar mata nan da kwana biyu Zai Turo iyayensa ayi maganar Aurensu, wani farin cikin ne ya lulluɓe Murja har ji tayi kaman ta rungumesa, yara unguwa ya rabawa suka suka shigar mata da kayan cikin gida.......
Kamar Yadda Aliyu ya faɗa bayan kwana biyu Daddy da wani Abokin sa, suka zo nema masa Auren Murja an tsaida magana nan da Sati biyu za'a daura Aure, duk wata hidima Aliyu ya ɗauke musu ita yace matarsa kwai yake buƙata idon An daura Aure yaba murja kuɗaɗen masu yawa domin tayi hidima, Mama sam tasa san wanar da ake toya ba, daga shi sai Daddy ke hidi marsu.
Yau Assabar A yaune kuma Aka daure Auren Aliyu da Murja, bayan Isha'i Amarya ta tare a ɗaƙinta. Sun kammala duk wani Abinda Shari'a ta Addini ya tanadar, Murja na kwance saman gado Aliyu zauna a gefenta wasu kwayoyi magani ya ciro daga Durowa ya ɓalli ɗaya ya miƙa mata tare da ruwa."Karɓi nan ki sha".
Cikin ɗan shakkunsa da take ganin ya ɗaure fuska tace ,"Miye wannan?".
"Magani ne".
"Amman Ni lafiya ta lau".
Ya ɗan sake fuska cike da yaudara yace ,"Kinga karɓi ki sha kinji bana son kiji Raɗadin da macce take ji a daren farko".
Hakan yasa ta karɓi maganin tasha, "Haa buɗe baki na gani kin sha?" ɗan karamin bakinta ta buɗe ya leka harda saka yatsarsa lungu da saƙo na bakinta don ya tabbatar.
"Good girl"
Ya faɗa yana murmushi.
A hankali ta dago tana kallonsa da dara daran Idanuwanta masu kwanta bata ce komai ba sai murmushi da ta yi cike da ƙauna tana matuƙar Kaunar Aliyu a ranta, na mijine da kowacce mace take da burin mallaka ya haɗa komi da take so, ga kyau ga iya