Kaddarar Zuciya Book 2 Complete JIddah Barkum

Author :  Jiddah Barkum Category :  Read Hausa Novels

Chapter   8 / 40

21K to 24K   out of 117.5K words

ta kama hannunta, Nana ta matse shi a hankali, “kada ki tafi… ina son ki kasance tare da ni.” Umar ya sauke numfashi, duk da cewa zuciyarsa tana son shiga tare da matarsa… sai ya gyada kai cikin fahimta, ya kalli Inteesar, “go with her.” Inteesar ta gyada kai. Nurse ɗin ta fara tura wheelchair ɗin zuwa cikin labour ward, Inteesar na tafiya a gefenta… riƙe da hannun Nana da ƙarfi. Yayin da Umar ya tsaya a bakin ƙofar… idanunsa na binsu har suka ɓace daga ganinsa. A karo na farko cikin shekaru… ya ji mintuna kaɗan na iya zama kamar awanni, kuma babu abin da zai iya yi… sai addu’a.

Umar ya tsaya a bakin labour ward, idanunsa suna kan ƙofar da aka shigar da Nana. Lokaci ya fara tafiya a hankali, mintuna suna wucewa… amma a wajensa… kamar sa’o’i ne. Ya kasa zama, ya kasa tsayawa wuri ɗaya, sai yawo yake yi daga wannan gefen corridor zuwa ɗayan. Lokaci zuwa lokaci kuma… yana ɗago hannayensa sama, “ya Allah… ka sauƙaƙa mata, ya Allah… ka bata haihuwa mai sauki.” Asuba na gab da ketowa, hasken fitilun cikin asibitin ya gauraya da hasken safiyar da ke fara bayyana ta cikin manyan tagogin corridor. A daidai lokacin… ƙofar labour ward ta buɗe, wata nurse ta fito cikin sauri tana cire safar hannunta. Da sauri Umar ya miƙe tsaye, ya ƙarasa gabanta cikin tashin hankali, “sister…” ya kira da sauri, “how is she?” nurse ɗin ta ɗan kalleshi, “kai ne kawo Mrs. Nana Aseeya?” da sauri ya gyada kai, “yes… she’s my wife.” ta yi ɗan nod, “okay, please come with me, the doctor would like to speak with you.” Gabansa ya sake faɗuwa. Ba tare da ya yi wata magana ba… ya bi bayanta, har suka isa ofishin likitan. Nurse ɗin ta turo ƙofar, “doctor… her husband is here.” Likitan ya ɗaga kai daga takardun da ke gabansa, “thank you.” nurse ɗin ta fita. Likitan ya nuna kujerar da ke gabansa, “please… have a seat.” A hankali Umar ya zauna, yana jin bugun zuciyarsa yana ƙaruwa da kowace daƙiƙa.

Likitan ya ɗan duba bayanan da ke gabansa, sai ya ɗago ya kalli Umar, “Mr. Umar…” ya fara cikin nutsuwa, “your wife is in labour, but we’ve discovered that your baby is in a breech position, wato jaririn bai juya kansa zuwa ƙasa ba, ƙafunsa ko mazauninsa ne suka fara zuwa hanyar haihuwa maimakon kai.” Umar ya haɗiye yawu. Likitan ya ci gaba, “she also started bleeding before active labour began, kuma ta fara zubar da jini tun kafin naƙudar haihuwa ta fara sosai, wanda ba abu ne da ake sa ran gani a irin wannan lokaci ba.” ya sauke numfashi, “unfortunately, she has already lost a significant amount of blood, abin takaici, ta rasa jini mai yawa kafin ma a kawo ta dakin haihuwa.” ya ɗan yi shiru kafin ya ƙara da cewa, “as a result, her blood pressure has become elevated, saboda hakan ne hawan jininta ya ɗan tashi sama da yadda ya kamata.” ya haɗa hannayensa, “at this point, the safest option for both your wife and the baby is an emergency caesarean section, wato dole mu yi mata tiyatar gaggawa domin fitar da jaririn, saboda hakan shi ne mafi aminci gare ta da kuma jaririn.” kalmar ta sauka kan Umar kamar dutse. Likitan ya ci gaba, “however, we cannot take her into surgery until we bring her blood pressure under better control, amma ba za mu iya shigar da ita ɗakin tiyata ba har sai mun fara saukar da hawan jininta zuwa matakin da zai kasance lafiya. operating while her blood pressure is dangerously high would increase the risk of serious complications, idan muka yi mata tiyata yayin da hawan jininta yake da yawa, hakan na iya jawo manyan matsaloli masu haɗari ga rayuwarta.”

… sai daga baya ya ce, “we’re doing everything we possibly can, muna yin duk abin da ya dace da duk ƙarfinmu. our team is already working to stabilize her blood pressure, likitoci da nurses suna aiki yanzu domin su saukar da hawan jininta ya dawo daidai. we’ve also prepared blood in case she needs a transfusion during or after surgery, haka kuma mun tanadi jini idan har ta buƙaci a ƙara mata yayin tiyatar ko bayan an gama.”

Shiru ya mamaye ofishin. Umar ya zuba wa likitan ido, kafin ya furta cikin murya mai rawa, “doctor… what do you suggest? me kake gani zaayi? what should we do now?” ya girgiza kansa, “please… all I need is to save my wife. if there’s anything… anything at all… please do it. I don’t care how much it costs. I’m ready to spend my last kobo… just let my wife be fine.” muryarsa ta fara karyewa, ya haɗe hannayensa cikin roƙo, “please, doctor… save her.” Likitan ya kalli Umar na wasu daƙiƙu, ya ga tsantsar tsoro da ƙaunar da ke cikin idanunsa, sai ya yi magana cikin kwantar da hankali, “Mr. Umar… we’re doing everything we possibly can. our team is already working to stabilize her blood pressure. we’ve also prepared blood in case she needs a transfusion during or after surgery, duk abinda yakamta ayi zaayi.” ya ɗan matsa gaba, “but right now… amma kafin nan… I need you to be strong, ka nutsu ka zama jarumi. your wife needs us to stay focused. we’re going to do everything within our power… …to save both your wife and your baby.” Umar ya runtse idanunsa, wasu zafan hawaye suka zubo a karon farko tun da suka iso asibitin. Ya ɗaga hannayensa sama a hankali, lips ɗinsa suka motsa ba tare da sauti ba, “ya Allah… la yukallifullahu nafsaan illa wus’aha.”

Umar ya ci gaba da kallon takardar da ke hannun likitan, yana jin kamar kalmomin da ke rubuce a kanta sun haɗe masa wuri ɗaya. Likitan ya miƙa masa alƙalami, “you need to sign the operation consent form, kana buƙatar ka saka hannu a takardar amincewa da yin tiyatar.” ya ɗan yi shiru kafin ya ƙara da cewa, “once her blood pressure comes down to a safer level, we’ll take her straight to the operating theatre for the emergency caesarean section, in sha Allah.” Umar ya sauke idanunsa kan takardar, yatsunsa suka ƙara rawa. A rayuwarsa… babu wata takarda da ta taɓa yi masa nauyi irin wannan, takardar da zai sanya hannu… ba wai saboda wata kasuwanci ba, ba wai saboda wani aiki ba, sai dai saboda rayuwar matar da ya fi so a duniya. Ya haɗiye yawu da ƙyar, da hannun da ke rawa… ya karɓi alƙalamin. Ya ɗan lumshe idanunsa na daƙiƙa guda, “ya Allah… kai kaɗai ne masani, ka kiyaye min ita…” a hankali… ya saka hannu a wurin da aka nuna masa. Da ya gama… sai ya miƙa takardar ga likitan. Likitan ya karɓa, ya dubi sa hannun na ɗan lokaci, sai ya ɗaga kansa, ya taka har inda Umar yake, a hankali ya ɗora masa hannu a kafaɗa, ya ɗan bubbuga kafaɗar tasa cikin ƙarfafawa, “stay strong, ka zama jarumi. we’ll do everything we can, za mu yi duk abin da za mu iya domin ceton ta. please pray for her, ka ci gaba da yi mata addu’a.” Umar ya gyada kai, amma ya kasa cewa komai, makoshinsa ya cika. Likitan ya juya… ya fice cikin sauri domin ci gaba da shirye-shiryen tiyatar, ƙofar office ɗin ta rufe. Umar ya zauna na wasu daƙiƙu yana kallon ƙofar, sai ya ja wani dogon numfashi, ya shafa fuskarsa da tafin hannunsa, kafin shi ma ya miƙe a hankali, ya fito zuwa corridor ɗin asibitin…

Da ya taka corridor ɗin… sai ya yi kacibus da Inteesar. Ta tsaya a gefe, sanye cikin doguwar rigar bacci da hijabinta. Fuskarta… ta kumbura sosai, idanunta sun yi jawur… alamar kuka mai yawa. Tun daga lokacin da nurses suka karɓi Nana… ba ta daina zubar da hawaye ba. Da ta ɗaga kai… idanunta suka haɗu da na Umar. Ba ta yi tambaya ba, amma kallonta kaɗai… ya isa ya bayyana abin da zuciyarta ke son ji, “Yaya?” Umar ya tsaya cak, ya kasa matsawa, ya kasa magana. Na wasu daƙiƙu… suka tsaya suna kallon juna. Inteesar ce ta fara karya shirun, muryarta na rawa, “…Yaya? Yaya Nana fa…? me likita ya ce?” Umar ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci, kafin ya buɗe su a hankali, ya sauke numfashi mai nauyi, “suna son su yi mata tiyata…” ya faɗa da ƙyar. Inteesar ta zaro ido, “tiyata?” Umar ya gyada kai a hankali, “baby ɗin… …ya juya ba yadda ya kamata ba. sannan…” ya haɗiye yawu, “…ta yi losing blood sosai.” Inteesar ta dafe bakinta da hannu, hawayen da take ƙoƙarin dannewa… suka sake zubo mata, “innalillahi wa inna ilaihi raji’un…” ta furta cikin sanyin murya. Umar ya jingina bayansa da bangon corridor, ya ɗaga kansa sama, idanunsa sun yi ja. Karo na farko… Inteesar ta ga kamar Yaya Umar ya gaji, ba gajiyar jiki ba, gajiyar zuciya. Ta matso kusa da shi a hankali, ta tsaya gabansa, cikin murya mai cike da tausayawa ta ce, “Yaya… Yaya Nana za ta fito lafiya, baby ma zai fito lafiya, in sha Allah. let’s keep praying.” Umar ya kalleta, ya yi ƙoƙarin yin murmushi, amma murmushin… ya kasa bayyana. Sai kawai ya ɗaga kansa sama, ya lumshe idanunsa, lebbansa suka fara motsi cikin addu’a… yayin da corridor ɗin asibitin ya sake yin tsit, sai ƙarar takun nurses da na’urorin asibiti kaɗai ke ratsawa… kowannensu na jiran lokacin da ƙofar ɗakin tiyata za ta buɗe.

Bayan kusan awa biyu… lokaci kamar ya tsaya cik. Agogon da ke manne a bangon corridor yana ci gaba da tafiya… amma ga Umar… da Inteesar… kowane dakika kamar shekara guda yake ji. Inteesar na zaune kan kujera, hannunta biyu haɗe wuri guda, lips ɗinta na motsi cikin addu’a, “…ya Allah… ka sauƙaƙa mata… …ya Allah… ka kare min Yaya Nana.” hawayen da ta goge sau ba adadi… sai dai suna ci gaba da zuba. Umar kuwa… tun bayan da ya fito daga office ɗin likita… bai sake zama ba, kawai yana tsaye… idanunsa a kulle kan ƙofar theatre. Babu wanda ya yi magana, sai ƙar AC, da kuma sautin kayan aikin asibiti daga nesa. Can… … ƙofar theatre ta buɗe a hankali. Wasu nurses biyu suka fara fitowa, dukkansu sanye cikin surgical gowns, masks a fuskokinsu, suka wuce ba tare da sun ce komai ba. Bayan su… sai wani likita ya fito, ba shi ne likitan da ya yi magana da Umar da farko ba, wani ne daban. Ya cire surgical cap ɗinsa, ya sharce zufar da ke goshinsa da bayan hannunsa, sai ya sauke wani dogon numfashi. Bayan wasu daƙiƙu… sai ga likitan farko shima ya fito, fuskarsa cike take da gajiya, da wani irin tausayin da ba sai an faɗa ba. Ya ɗago idanunsa, kai tsaye suka sauka kan Umar. Umar bai motsa ba, kawai ya tsaya… yana kallon likitocin, zuciyarsa na bugawa da ƙarfi, har yana jin sautinta a kunnuwansa. Inteesar kuwa… ba ta ma kalli likitocin ba, hankalinta gaba ɗaya yana kan ƙofar theatre, idonta na jiran ganin lokacin da za a fito da Nana, ko tana kan bed, ko tana barci saboda allurar tiyata, ko dai meye… matuƙar ta ganta, hakan ya ishe ta.

Likitan ya matso kusa da Umar, ya tsaya gabansa. Na wasu daƙiƙu… ya kasa cewa komai, sai ya runtse idanunsa na ɗan lokaci, kafin ya buɗe su a hankali, ya ce cikin sanyin murya, “very sorry, Mr. Umar… ina matuƙar baƙin cikin sanar da kai, Malam Umar…” ya haɗiye yawu, sannan ya ci gaba, “we couldn’t save her, ba mu samu nasarar ceton matarka ba.” kalmar… ta faɗi cikin corridor ɗin kamar wata ƙar aradu. Likitan ya sauke numfashi, “unfortunately… we also lost the baby, abin takaici… mun rasa jaririn ma.” ya girgiza kai cikin tausayi, “her blood pressure became critically high… hawan jininta ya yi matuƙar tashi… …and because of the severe bleeding she had before surgery… …sannan saboda yawan jinin da ta zubar tun kafin a fara tiyatar… …her body couldn’t hold on any longer, jikinta bai ƙara iya jurewa ba.” ya sauke idanunsa ƙasa, “she passed away before we could begin the operation, Allah ya karɓi rayuwarta tun kafin mu samu damar fara tiyatar.” ya sake kallon Umar, idanunsa cike da tausayawa, “we’re deeply sorry, muna matuƙar baƙin ciki. please accept our condolences, muna mika maka ta’aziyyarmu. Allah ya ba ka haƙurin jure wannan rashi.”

Shiru… mai nauyi, mai kashe zuciya, ya mamaye corridor ɗin. Umar bai ce uffan ba, bai motsa ba, idanunsa kawai suka tsaya kan fuskar likitan, kamar bai fahimci abin da aka faɗa masa ba, kamar kwakwalwarsa ta ƙi karɓar kalmomin. Sai… a cikin shirun nan… aka ji wata ƙara mai ƙarfi, TIMMMM!!! kamar wani abu mai nauyi ya bugi tiles ɗin corridor. Da sauri… Umar da likitocin suka juya. Inteesar ce… kwance shimfiɗe a ƙasa, wayarta ta faɗi gefe guda. Idanunta a rufe, ta sume gaba ɗaya. “nurse!” wani daga cikin likitocin ya yi saurin ƙwala kira, “quick! bring a stretcher! da sauri! ku kawo gadon ɗaukar marar lafiya!” nurses suka yi tsere zuwa gare ta. Yayin da Umar… har yanzu… yana tsaye a inda yake, ba don bai ji abin da aka faɗa ba… ba kuma don bai ga Inteesar ta faɗi ba… sai dai saboda a wannan lokacin… duniyarsa gaba ɗaya… ta ruguje cikin daƙiƙa guda.

Sorry for the typos not edited

*KADDARAR ZUCIYA*

*CHAPTER SEVENTY-THREE: 73*

BEHIND THE DEAD BODY

*JIDDAH BARKUM*



Nurses suka fito da stretcher cikin gaggawa, suka ɗaga Inteesar daga inda ta faɗi sumammiya, da sauri suka nufi Emergency Unit da ita.

Amma… Umar bai motsa ba, har yanzu yana tsaye a wajen… kamar mutum-mutumi. Idanunsa suna kallon ƙofar theatre ɗin, amma ba ya ganin komai, kunnensa sun daina jin sauti, zuciyarsa kuma ta yi wani irin sanyi da ba zai iya misaltawa ba. Komai yana masa kamar mafarki, mafarki mafi muni da yake ta roƙon Allah ya farka daga gare shi. “Ba zai yiwu ba…” zuciyarsa ta maimaita, “Nana ba za ta mutu ta bar ni ba… ba za ta tafi ba…”

A daidai wannan lokacin… ƙofar theatre ɗin ta sake buɗewa da ƙarfi. Wata nurse ta fito da gudu, fuskarta cike da tashin hankali, “doctor!” likitan da ke tsaye kusa da Umar ya waigo da sauri. Nurse ɗin ta ƙaraso tana haki, “sir… the baby is alive, he’s showing movements, we repeated the scan just now… we can still save the baby!” yaron yana da rai, mun sake yin scanning yanzu, kuma mun ga yana motsi, har yanzu akwai damar mu cece shi!

Kafin ta gama rufe bakinta… Umar ya zabura, kamar wanda aka watsa wa ruwan ƙanƙara, idanunsa suka buɗe sosai. A karon farko tun bayan jin labarin mutuwar Nana… bakinsa ya motsa, “Dr…” muryarsa ta fito cikin rawar da ba ta taɓa fitowa daga gare shi ba, “…please…” ya haɗiye yawu da ƙyar, “help me… save my baby, please doctor… save my baby.” don Allah… ku ceci ɗana, don Allah likita… ku ceci jaririna. Likitan bai ɓata ko daƙiƙa ɗaya ba, ya juya cikin gaggawa, “prepare the theatre immediately! ku shirya ɗakin tiyata nan take! move! ku yi sauri!” nurses suka ruga da gudu suka bi bayansa.

Sai lokacin ne… Umar ya fara fahimtar girman abin da ya faru. Kalaman likitan… “we couldn’t save her…” suka sake amsawa a cikin kunnuwansa, “ba mu samu nasar ceton matarka ba…” jikinsa ya fara rawa, numfashinsa ya ƙule. Ya zaro wayarsa daga aljihunsa da hannun da ke karkarwa, ya shiga neman number ɗin… Mommy Haleema ❤️ yatsunsa ma suka gaza danna screen yadda ya kamata saboda rawar da suke yi. Da ƙyar ya danna, wayar ta fara ringing.

A wannan lokacin… hasken asuba ya fara bayyana a sararin samaniya, agogo ya nuna… 6:15 AM. Ringing ɗaya kawai… ta ɗaga, “assalamu alaikum…” muryarta ta fito cike da nutsuwa, “Umar?” sai dai… da ta ji yadda numfashinsa yake fita… zuciyarta ta buga. Nan take ta miƙe tsaye daga kan sallayarta inda take zaune tana jan tasbihi bayan idar da sallar asuba, “Umar?” ta sake kiransa cikin firgici, “lafiya?” ya yi shiru… sai sautin numfashinsa mai nauyi. Daga ƙarshe… cikin wata irin murya mai cike da rauni, ya kira, “…Mommy.” ta ƙara firgita, “na’am Umar, me yake faruwa?” ya runtse idanunsa, hawayen da ya daɗe yana nema suka zubo a karon farko, “Mommy…” ya fashe da kuka, “…wife…” ya kasa ƙarasa maganar, “Mommy…” ya sake maimaitawa cikin kuka, “…my wife…” muryarsa ta karye, “my wife is gone…”

Mommy Haleema ta tsaya cak, tasbihar da ke hannunta ta zame ta faɗi ƙasa, “innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” ta dafe ƙirjinta, “Umar!” ta ɗaga murya cikin tashin hankali, “ka faɗa min me yake faruwa! me ya samu Nana? ka yi magana mana!” Umar ya yi ƙoƙarin magana… amma kalmomin sun ƙi fitowa, sai kuka kawai… kuka irin na mutumin da duniya ta rushe masa cikin lokaci ɗaya. Babu abin da Mommy Haleema ke iya furtawa… sai, “innalillahi wa inna ilaihi raji’un…” ta maimaita sau ɗaya… ta sake maimaitawa, kamar zuciyarta ta kasa karɓar abin da kunnuwanta suka ji. Da ƙyar ta haɗiye kukanta, ta dafe ƙirjinta da hannu ɗaya, sannan cikin murya mai rawar jiki ta ce, “Umar… ka… ka nutsu kaji.” ta yi shiru na ɗan lokaci tana ƙoƙarin daidaita numfashinta, “sannan… ka na ina yanzu?” daga ɗaya ɓangaren… sai sautin numfashinsa mai nauyi, numfashin mutumin da zuciyarsa ta riga ta tsinke, cikin rarrabewar murya ya ce, “…muna asibiti…” ya yi shiru, “…Mommy.”

Mommy Haleema ba ta sake cewa komai ba, a hankali ta sauke wayar daga kunnenta, yatsunta har yanzu suna rawa, ta kashe wayar. Ba tare da ta tsaya tunanin komai ba… ta nufi ƙofar ɗakin da sauri, tashin hankalin da ke cikin zuciyarta ya hana ta jin komai. Kai tsaye… ɗakin Daddy ta nufa. Da ta isa bakin ƙofar… sai ta tsaya,

8 / 40