Kaddarar Zuciya Book 2 Complete JIddah Barkum

Author :  Jiddah Barkum Category :  Read Hausa Novels

Chapter   12 / 40

33K to 36K   out of 117.5K words

yi sallah, sannan ta shiga bathroom ta yi wanka. Bayan ta fito, ta nufi gadon da Abdallah yake kwance yana ta bacci cikin kwanciyar hankali. Ta yi murmushi a hankali, “good morning Aamaan…” ta ɗauke shi cikin kulawa ta kai shi bathroom, ta yi masa wanka cikin ruwan ɗumi, ta shafa masa baby lotion mai ƙamshi, sannan ta saka masa wata red baby romper mai ƙayatattun silver stones a ƙirji, tare da ƙaramin farin socks da snickers fari mai kyau wanda ya dace da kayan jikinsa.

Tubarkallah… yaron ya ƙara girma sosai, idan mutum ya gan shi, da wuya ya ce watanni shida ne kacal a duniya. Yana da ƙiba mai kyau, garin jiki, da fuskar da kullum take ɗauke da annuri irin ta mahaifiyarsa. Ta taje ƙaramin gashin kansa a hankali, ta shafa masa baby oil, sai ta ɗauke shi ta sumbaci goshinsa, “handsome boy ɗin Mamie…”

Daga nan ta shiga shirinta. Ta saka wata doguwar red gown mai ɗauke da sparkling crystal stones a ƙirji da hannaye, kayan sun zauna a jikinta cikin matuƙar kyau. Ba ta yi kwalliya ba, amma fuskarta fes take, kyawunta na fitowa a zahiri duk da alamun baƙin cikin da ke cikin idanunta. Ta yi normal rolling da veil ɗin, ta fesa turarenta sannan… ta ɗauki handbag ɗinta, ta ɗauki key ɗin mota… sannan ta ɗauki Abdallah a kafaɗarta. A hankali suka fara saukowa daga stairs.

A falo… Mommy Haleema, Khalil da Umar ne zaune. Kamar sun haɗa baki… duk suka ɗaga kai lokaci guda suka kalle su. Khalil ya yi dariya, “kai boss man!” ya faɗa yana kallon Abdallah, sai ya ƙara da cewa, “yanzu fa idan na miƙa hannu nace, ‘zo wajen uncle Khalil,’ wallahi sai ya tara min dukkan ƴan Katsina a gidan nan.” Inteesar ta harare shi, “ko da zai zo ma… ba zan ba ka shi ba.” Khalil ya ƙyalƙyale da dariya, “ai ko kin ba ni ma ba zan karɓa ba, wa ya kai ni taɓa wannan ƙaramin shugaban?”

Umar… tun farko yana zaune shiru yana kallonsu, ba tare da ya sani ba… wani sanyin zuciya ya ratsa shi. Tsawon watanni… a yau ne karo na farko da ya ji falon gidan ya ɗan yi masa kama da gida. Inteesar ta juya ta kalli Mommy, “Mommy… mun tafi.” Mommy Haleema ta miƙa hannu, “taho ɗan ƙauye…” Abdallah kuwa… da sauri ya ƙara manne kansa a kafaɗar Inteesar, ya ƙi ko kallon Mommy. Khalil ya sake fashewa da dariya, “Mommy! ki rufa mana asiri da yaron nan.” Mommy ita ma dariya ta yi, “ni ma ba ɗauka zan yi ba, ya karya min cinya.” Khalil ya girgiza kai, “ai Mommy… har kunnuwanmu sai sun daina jin magana saboda kukansa idan Inteesar ba ta kusa.” Inteesar ta kasa riƙe murmushinta. Mommy ta ce, “toh, ina za ku je kuma yau?” Inteesar ta zaro ido, “Mommy! jiya fa nace miki yau zan je na yi wa Aamaan siyayyar abubuwan amfani, da yawa sun fara ƙarewa.” Mommy ta dafe kanta, “oh… na manta.” sai ta yi murmushi, “kayan wannan tsohon za a je siyowa shiyasa na manta kenan.” Khalil ya ƙara kwashewa da dariya, Inteesar ma ta yi dariya, har Umar… wanda bai ce komai ba tun da aka fara hirar… sai da murmushi ya suɓuce masa.

Inteesar ta ce, “ni dai Mommy… sai mun dawo.” har ta juya za ta fita… sai Umar ya kira a hankali, “Inteesar…” ta tsaya, ta waigo. Ya zaro wallet ɗinsa ya fito da ATM card ya miƙa mata, “gashi… ki yi amfani da shi.” Inteesar ta girgiza kai, “a’a… Yaya Abubakar ya riga ya turo min kuɗin da zan yi wa Aamaan siyayya tun jiya.” Umar ya ci gaba da kallonta, “ki karɓa.” ta yi shiru, ya sake cewa cikin nutsuwa, “you might see something else you’ll like for him… ki saya masa.” Inteesar ta san idan ta ci gaba da musu ba zai karɓa ba, sai ta karɓi card ɗin, “nagode.” ta saka shi cikin handbag ɗinta, sannan ta juya ta fita. Umar ya bi bayanta da kallo… har sai da ƙofar ta rufe. Daga nan… a hankali ya sauke kansa ƙasa.

*KADDARAR ZUCIYA*

*CHAPTER SEVENTY-SEVEN: 77*

*THE SECOND CHANCE*

*JIDDAH BARKUM*



Inteesar ta buɗe ƙofar motar ta, sannan cikin kulawa ta saka Aamaan a cikin rear-facing infant car seat, kujerar musamman da ake ɗaure jarirai a mota domin kare lafiyarsu. Ta tabbatar ta ɗaure belt ɗinsa yadda ya kamata, sannan ta shafa kumatunsa a hankali, “good boy…” ta faɗa tana murmushi.

Daga nan ta zagaya ta shiga driver’s seat, ta kunna motar, sannan ta fice daga gidan cikin nutsuwa.

Kai tsaye ta nufi Katsina Royal Galleria, wani katafaren shopping mall na zamani da ya shahara wajen sayar da kayan yara, tufafi, kayan wasa da sauran kayayyakin more rayuwa.

Da ta isa… ta samu parking mai kyau, ta ajiye motar sannan ta fito. Ta zagaya bayan motar, ta cire Aamaan daga car seat ɗinsa ta rungume shi a kafaɗarta. Yaron kuwa yana ta kallon ko’ina da manyan idanunsa masu kama da na mahaifinsa.

A hankali suka shiga cikin mall ɗin. Inteesar ta ɗauki cart, sannan ta fara zagayawa sashen kayan jarirai. Baby wipes, diapers, baby lotion, powder, baby shampoo, body wash, feeding bottles, pacifiers, baby cereals, formula milk, baby towels, bibs, baby shoes, socks, sabbin kaya masu laushi… duk abin da Aamaan yake buƙata… ba ta bar ko guda ba.

Da ta gama nan… sai ta wuce sashen kayan wasa. Nan ma… ta ɗauko masa teddy bears, talking toys, musical toys, educational blocks, baby walker toys, da wasu kayan wasa masu launuka iri-iri da suka dace da shekarunsa. Aamaan kuwa… duk lokacin da ya ga wani abin wasa mai haske sai ya miƙa hannu yana son ya taɓa shi. Hakan ya sa Inteesar yin dariya a hankali, “Aamaan… duk kana so ne?” sai ya yi wata ƙaramar dariya. Ta kasa hana kanta murmushi.

Bayan ta gama siyayya… ta nufi wajen biyan kuɗi. Duk abubuwan da ta saya… ba ta taɓa ATM card ɗin da Umar ya ba ta ba. Kuɗin da Yaya Abubakar ya turo mata tun jiya sun wadatar mata sosai.

Bayan ta gama payment… ma’aikatan wajen suka taimaka mata suka ɗauki dukkan shopping bags ɗin har zuwa wajen motarta. Ta buɗe boot ɗin motar, suka tsara mata komai cikin tsari, ta yi musu godiya, “thank you.” “you’re welcome, ma’am.” da suka tafi… Inteesar ta rufe boot ɗin motar.

Sai ta ɗago kai tana shirin shiga mota… amma… ta tsaya cak. Wata baƙar mota ce ta ajiye a bayanta… har ta toshe mata hanyar fita gaba ɗaya. Ta ɗan yi shiru, ta sake dubawa, babu ta yadda za ta iya fita, dole sai an matsar da motar. Aamaan har yanzu yana jikinta, ba ta so ta tsaya a wajen cikin zafi da yaron. Sai ta nufi security guard ɗin mall ɗin, “please…” ta faɗa cikin ladabi, “could you help me find the owner of that vehicle? it’s blocking my way.” security ɗin ya bi inda take nuna da ido, nan take ya gyada kai, “to Hajiya, bari na duba.” ya juya cikin sauri yana neman mai motar.

Inteesar kuwa… ta koma bakin motarta, ta jingina da jikin motar cikin nutsuwa. Aamaan yana kwance a kafaɗarta yana wasa da ƙaramin yatsansa… ita kuma… ta tsaya tana jiran a matsar da motar domin ta samu ta koma gida.

Security ɗin ya dawo da sauri, “Hajiya…” ya kira cikin girmamawa, “gashi nan… mai motar yana zuwa.” Inteesar ta ɗaga kanta, “okay, thank y—” maganar ta tsaya a maƙoshinta. Idanunta suka sauka kan mutumin da ke tahowa a hankali. Aliyu… gabanta ya faɗi. Tun bayan abin da ya faru… ba ta sake ganinsa ba, ba ta sake yin magana da shi ba, yau ne karo na farko da suka sake haɗuwa. Na ɗan lokaci… idanunsu suka haɗu. Sai dai… Inteesar ta kawar da nata idanun tamkar ba ta taɓa saninsa ba, ta juya kai tsaye ta nufi motarta.

A hankali ta buɗe ƙofar baya, ta kwantar da Aamaan cikin infant car seat ɗinsa, ta ɗaure masa belt yadda ya kamata, ta rufe ƙofar. Sannan ta zagayo zuwa driver’s seat. Hannunta na shirin buɗe ƙofar motar… sai Aliyu ya ƙaraso, ya tsaya gabanta. Fuskarsa cike take da mamaki, da kuma wata irin yanayi ko kunya ne. Na wasu daƙiƙu… ya kasa magana, sai daga bisani… ya furta cikin sanyin murya, “Inteesar…” ba ta ko kalle shi ba, ta sake kai hannu za ta buɗe ƙofar motar. Da sauri… Aliyu ya ɗora hannunsa a kan murfin ƙofar. Hakan ya sa Inteesar ta janye hannunta da sauri, ta ɗago kanta. Fuskarta babu ko ɗigon murmushi, ta haɗe gira, “sorry, malam.” ta faɗa cikin sanyin murya mai sanyi amma cike da tsauri, “ni matar aure ce.” ta ɗan dakata, “lafiya ka tsaya haka a gabana?”

Aliyu ya tsaya cak, kalaman nata suka bugi zuciyarsa kamar guduma. Inteesar ta ci gaba ba tare da ta ba shi damar magana ba, “mota kawai aka ce ka matsar, ka ba ni hanya in wuce.” shiru ya ratsa tsakaninsu. Aliyu ya buɗe baki da ƙyar, “aure…” ya maimaita cikin rawar murya, “…kin yi aure?” ya faɗa yana kallonta kamar bai gaskata abin da ya ji ba.

Inteesar ta ɗan kalle shi, kallon da babu komai a cikinsa face rashin son ɓata lokaci, “idan ba za ka matsar da motar ba…” ta faɗa cikin natsuwa, “ka sanar da ni, zan nemi wata hanyar fita.” Aliyu ya kasa cewa komai, kawai ya ci gaba da kallonta, yadda take tsaye… da yadda ta canza gaba ɗaya. A hankali… ya ja da baya, har yanzu idanunsa suna kanta. Sai ya juya ya shiga motarsa, ya kunna engine, ya matsar da motar daga hanyar.

Da hanya ta buɗe… Inteesar ta shiga motarta, ba ta sake kallonsa ba, ta kunna motar. Cikin daƙiƙa kaɗan… ta fice daga parking lot ɗin da wani irin gudu.

Aliyu kuwa… ya tsaya jingine da motarsa, idanunsa suka bi hanyar da motarta ta bi… har sai da ta ɓace gaba ɗaya daga ganinsa. Ya lumshe idanunsa a hankali, sai ya sauke wata doguwar ajiyar zuciya, “…kin yi aure…” ya maimaita a hankali. Kalmar ta fito daga bakinsa… amma ta sauka ne kai tsaye cikin zuciyarsa. A karon farko… ya ji kamar ya rasa ta har abada.



A yammacin ranar… falon gidan ya yi tsit, iska mai daɗi na ratsawa ta labulen tagogi. Inteesar na zaune a ƙasan carpet ɗin falon, ta jingina da kujera. Sanye take da doguwar rigar cotton mai laushi, green colour, wacce ta ƙara fito da hasken fuskarta. A kanta kuma akwai ɗan ƙaramin mayafi da ta yafa cikin sauƙi.

Aamaan kuwa… yana zaune ne a kan cinyarta, sanye yake da farin singlet da ɗan ƙaramin wandon shan iska mai blue colour. Tubarkallah… yaron ya ƙara ƙiba da annuri, da alama ko kaɗan bai san wata damuwa ba.

Inteesar ta gama ba shi abinci kenan, yanzu kuma… lokacin wasansu ne. Ta riƙe ƙananan hannayensa biyu tana murmushi, “Aamaan…” ta kira cikin shagwaɓa, ya ɗago ya kalleta, sai ya yi mata wata irin dariya ya bangale bakinsa gaba ɗaya. Ita ma ta yi dariya, taɓa hancinsa a hankali, “ka ce…” ta ɗan tsaya, “ma… mie…” ta faɗa a hankali tana jan kalmar, kamar yadda ake koya wa yara magana. Aamaan ya ƙyalƙyale da wata irin dariya mai daɗi.

Inteesar ta sake gwadawa, “ma…” “mie…” “ka faɗa mana… ma… mie…” sai dai… maimakon ya maimaita abin da take koya masa… sai ya ɗauke hankalinsa gaba ɗaya, idanunsa suka koma wani waje, yana kallon wani abu da matuƙar sha’awa.

Inteesar ta bi inda yake kallo, ashe… Yaya Khalil ne tsaye a bayan kujera, yana yi wa Aamaan alama da yatsansa, ya ɗora yatsa a bakinsa, “ssshhh…” sannan yana girgiza masa kai, kamar yana cewa, “kar ka faɗa.” Aamaan kuwa… sai ya sake fashewa da dariya.

Inteesar ta zaro ido, “Yaya Khalil!” ta faɗa tana hararsa, “me haka kuma?” Khalil ya kasa riƙe dariyarsa, ta nuna shi da yatsa, “ina koya masa magana… kai kuma kana hana shi.” Khalil ya riƙe ciki yana dariya, “haba! kin ji na ce wani abu ne?” Inteesar ta turo baki, “ban so.” ta faɗa kamar ƙaramar yarinya, sannan ta rungume Aamaan a ƙirjinta, “Aamaan… kar ka kula uncle Khalil, zan koya maka idan mun koma daki.” Aamaan ya lumshe idanunsa a jikinta, ya kwanta lip a ƙirjinta yana wasa da mayafinta.

A saman stairs kuwa… Daddy yana tsaye tun ɗazu yana kallon duk abin da ke faruwa. Ya kalli Inteesar, ya kalli Aamaan, sai kuma ya kalli Khalil. Wani sassanyan murmushi ya bayyana a fuskarsa, murmushin da ya fito daga zuciya. A hankali ya sauke numfashi, “alhamdulillah…” ya furta a hankali. Ba tare da ya katse musu annashuwarsu ba… ya juya cikin nutsuwa… ya koma ɗakinsa.

Yamma ta yi. Bayan an idar da sallar magariba… Alhaji Kabeeru ya zauna a cikin ƙaramin sitting room ɗinsa. Wurin ya yi tsit, sai ƙamshin turaren wuta da Haleema ta kunna yake yawo a cikin ɗakin. Ya jingina da kujerarsa, idanunsa suna kallon window amma zuciyarsa tana wani wuri dabam. Na wasu daƙiƙu… sai ya ɗaga murya cikin nutsuwa, “Abubakar…” Yaya Abubakar da ke zaune a gefe ya amsa, “na’am Daddy.” “ka kira min Umar.” “to Daddy.”



Bayan mintuna kaɗan… ƙofar ɗakin ta buɗe a hankali. Umar ya shigo, sanye yake da farar jallabiya mai sauƙi. Fuskarsa bata buna damuwa ba, ba kuma ta nuna farinciki ba, tsaka tsaki. Duk da cewa watanni shida sun shuɗe… har yanzu akwai wani irin shiru da ya mamaye rayuwarsa. Da ya ƙaraso… sai ya durƙusa a gaban Daddy cikin cikakkiyar girmamawa, ya sunkuyar da kansa, “assalamu alaikum Daddy.” “wa alaikumus salam.” Daddy ya amsa cikin tausasawa, sai ya zuba masa ido, dogon lokaci… bai ce komai ba, yana kallon Umar ne kawai, kallon da uba yake yi wa ɗansa idan zuciyarsa ta cika da tausayinsa. Shi kansa Umar ya fara jin wani irin bugun zuciya, bai san abin da Daddy yake son faɗa masa ba.

Sai daga ƙarshe… Daddy ya sauke numfashi a hankali, “Umar…” a hankali Umar ya ɗago kansa, “na’am Daddy.” muryarsa ta fito a sanyaye. Daddy ya gyara zamansa, “ina son mu yi magana, magana mai muhimmanci.” Umar ya gyada kai cikin biyayya, “ina sauraronka Daddy.” Daddy ya ɗan yi shiru, kamar yana tsara kalamansa, ba ya son ya yi kuskure, domin ya san zuciyar da yake magana da ita har yanzu tana ciwo. A hankali ya fara, “yau… tsawon watanni shida kenan da rasuwar Nana.” kalmar kaɗai… ta isa ta sa fuskar Umar sauyawa, idanunsa suka sauka ƙasa. Daddy ya lura, amma ya ci gaba, “alhamdulillah, na yi farin ciki da yadda ka karɓi ƙaddar Ubangiji. ba ka yi kuka da Allah ba, ka yi haƙuri, ka ci gaba da rayuwa.” ya ɗan yi shiru, sai ya ƙara da cewa, “ko da na san… har yanzu kana jin zafin rashinta.” Umar bai ce komai ba, sai ya haɗiye wani abu mai ɗaci. Daddy ya ci gaba cikin nutsuwa, “amma rayuwa… ba ta tsayawa saboda mutuwar mutum, mutum yana tafiya, rayuwa kuma tana ci gaba.” ya ɗan jingina bayansa, “shi ya sa… ina ganin lokaci ya yi, ka koma bakin aikinka, ka ci gaba da rayuwarka, ka sake shiga cikin mutane, ka daina zama kai kaɗai da tunani.”

Sai ya sake yin shiru, kalmar da ta biyo baya… ita ce ta fi nauyi, “kuma… ina ganin lokaci ya yi… …da zaka sake yin aure.”

Shiru, shiru mai nauyi ya mamaye ɗakin. Umar ya ji kamar numfashinsa ya tsaya, bai ɗago kai ba, bai motsa ba, kamar mutum da aka zuba wa ruwa. Daddy ya lura, amma bai matsa masa ba, ya ba shi lokaci. Sai bayan wasu daƙiƙu ya sake kiransa, “Umar…” “na’am Daddy.” muryarsa ta fito da ƙyar.

“ka san ba na tilasta maka komai, kuma ba zan taɓa tilasta maka aure ba. amma ina magana ne a matsayin uba, a matsayin mutumin da ya fi ka shekaru, a matsayin wanda ya san rayuwa.” ya yi murmushi mai ciwo, “ni ma na taɓa rasa matar da nake so, na san yadda ciwon yake, na san yadda dare yake tsawo, na san yadda mutum yake jin kamar rayuwa ta tsaya.” sai ya ɗaga idanu ya kalli Umar, “amma… ba haka rayuwa take ba, rayuwa tana ci gaba.” sai ya yi shiru, ya ɗan matsa gaba, “Umar… ka tuna shekarun baya… lokacin da ka zo neman Fateema?” Umar ya ɗan ɗago kai, gabansa ya faɗi a hankali ya furta, “na tuna Daddy.” “ka tuna lokacin da na ce… ‘ba zan ba ka Fateema ba’?” “na tuna.” ya sake faɗa cikin sanyi. “ka tuna dalilin?” “na tuna Daddy.” Daddy ya gyada kai, “na ce… ba zan haɗa ‘ya’yana biyu… Inteesar… diyata, da kuma Nana… diyar ɗan’uwana… ƙarƙashin inuwa ɗaya ba. ba don bana son ka ba, ba don ban yarda da kai ba, sai don zuciyata ba ta amince ba.”

Sai Daddy ya yi shiru, ya lumshe ido, “Allah ya yi wa Aseeyah rahama.” “amin.” Umar ya amsa cikin sanyin murya. Daddy ya buɗe idanunsa, “ba ni na rubuta ƙaddara ba, Allah ne.” sai ya sauke numfashi, “yau… wannan dalilin da ya sa na hana ka Fateema… …ya ƙare.” kalmar ta sauka kamar dutse, zuciyar Umar ta buga da ƙarfi, numfashinsa ya ɗan rikice. Daddy ya ɗan karkata kansa, ya kalle shi ido cikin ido, “ina tambayarka ne, ba na matsa maka, ba na kuma tilasta maka.” ya ɗan yi shiru, sannan cikin murya mai cike da hikima ya tambaya, “har yanzu… …kana da ra’ayin Fateema?”

Kalmar ta tsaya a cikin ɗakin, shiru ya sake mamaye komai, sai bugun zuciyar Umar… da ya fara ji kamar kowa yana iya jin sautinta.

Sorry for the typos not edited

*KADDARAR ZUCIYA*

*CHAPTER SEVENTY-EIGHT:

12 / 40