Author : Jiddah Barkum Category : Read Hausa Novels
kare zuciyarsa daga ƙarin lalacewa.”
Inteesar ta ji hawaye masu zafi sun cika idanunta. Ta dafe baki da hannunta, muryarta na rawa ta tambaya, “...Doctor, yana cikin haɗari ne?”
Likitan ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya amsa cikin gaskiya amma cikin kwantar da hankali, “Ba zan ce yana cikin haɗari a wannan lokacin ba, domin mun samu mun daidaita yanayinsa. Amma idan ba a kula da wannan matsalar tun yanzu ba, lokaci na iya zuwa da zai yi mana wahalar cetonsa.”
Kalmar ƙarshe ta sauka a zuciyar Inteesar kama dutse. Ta sunkuyar da kanta, a karon farko ta ji tsoron rasa Umar ya mamaye zuciyarta fiye da yadda ta taɓa zato.
Likitan ya miƙe tsaye, ya kalli Inteesar cikin tausayi. “Alhamdulillah, yanzu yanayinsa ya daidaita. Mun ba shi magungunan da suka dace, bugun zuciyarsa ma ya fara dawowa yadda ya kamata.”
Inteesar ta saki wata doguwar ajiyar zuciya, kamar an ɗauke mata wani babban dutse daga ƙirjinta. Sai dai kafin ta yi wani yunƙuri, likitan ya sake cewa, “Amma...” Kalmar ta sake sa gabanta faɗuwa. Ya ci gaba cikin nutsuwa, “kar ku bar shi shi kaɗai, musamman cikin dare. Saboda irin magungunan da muka ba shi, da kuma yanayin da ya shiga, ba mu san yadda jikinsa zai amsa ba cikin sa’o’i na farko. Idan ya ji ciwon ƙirji, ko numfashi ya fara masa wahala, ko ya sake faɗuwa, ku dawo da shi nan take.”
Inteesar ta gyada kai cikin sanyin jiki, “In Sha Allah, Doctor, za mu kula da shi.”
Likitan ya yi mata ɗan murmushi, “Allah Ya ba shi lafiya.”
“Ameen,” ta amsa a hankali, sannan ta juya ta fita daga office ɗin.
⸻
Da ta fito, ta tarar da Yasmeen zaune a bakin corridor. Tun daga nesa idanunta suka sauka kan Inteesar, nan take ta miƙe tsaye, fuskarta cike da tashin hankali.
“Me Doctor ya ce?” ta tambaya da sauri.
Inteesar ta ɗan tsaya, ta sauke numfashi, sannan ta ce cikin sanyin murya, “Akan ciwon zuciyarsa ne, shi ne ya sa ya samu attack.”
Yasmeen ta bita da kallo kamar bata yarda ba, kafin ta sake tambayar wani abu, ƙofor Emergency ta buɗe. Nurses biyu suka fito suna turo kujerar marasa lafiya da Umar ke kai. Dukansu suka juya da sauri, idanun Inteesar suka sauka a kansa.
Umar ya buɗe idanunsa kaɗan, amma har yanzu kasala ta bayyana ƙarara a fuskarsa, kamar wanda aka kwashe masa duk wani ƙarfi. Yasmeen ta yi saurin yin gaba, ta buɗe ƙofor bayan motar. A hankali nurses suka taimaka masa ya shiga, suka zaunar da shi a back seat. Ya jingina bayansa da kujera, ya lumshe idanunsa, numfashinsa na sauka a hankali, kamar duk wata magana tana masa nauyi.
Inteesar ta tsaya tana kallonsa na wasu daƙiƙu, sai kuma ta shiga ta zauna kusa da shi. Ba ta ce komai ba, kawai ta ɗan juya kai, idanunta suka sauka a kansa ta gefen ido. Ta ga yadda fuskarsa ta yi fari, da yadda numfashinsa yake fita a hankali, wani irin tausayinsa ya sake cika mata zuciya. Ta runtse idanunta, ta juya ta kalli window.
Yasmeen ta zauna a driver’s seat ta kunna motar. Mai gadin asibitin ya buɗe musu gate, motar ta fice daga harabar Ezamiye Hospital. Babu wanda yake magana, sai ƙarar engine da kuma numfashin Umar mai nauyi, da ya cika motar da wani irin yanayi na tsoro.
Bayan isarsu gida, da ƙyar ya rufe ƙofor motar, ya jingina da ita na ɗan lokaci, kafin ya fara taku cikin nutsuwa. Takunsa a hankali yake yi, kamar kowane mataki yana cin masa ƙarfi. Ya shiga cikin falon, bai zauna ba, kai tsaye ya nufi stairs, hannunsa riƙe da handrail ɗin gefen matattakalar. Yana hawa mataki ɗaya, sai ya tsaya ya sauke numfashi, sannan ya ci gaba.
Inteesar na tsaye tana binsa da ido har sai da ya ɓace daga ganinta. Ta sauke wata doguwar ajiyar zuciya. Yasmeen ma, tun daga lokacin da suka fito daga asibiti, ba ta sake cewa komai ba, ta yi shiru kawai, ita ma ta juya ta haura sama.
Nan take falon ya sake yin tsit. Inteesar ta ƙarasa bakin sofa ta zauna a hankali, ta zuba tagumi, idanunta suna kallon waje ɗaya, amma ba abin da take gani. Kalaman Doctor ne kaɗai suke ta maimaituwa cikin kanta, “Yana buƙatar kulawar matarsa...”, “Kar ku bar shi shi kaɗai cikin dare...”.
Ta runtse idanunta, ta ɗan yamutsa fuska, ta gyara zamanta kamar wani abu yana yawo a ƙafafunta. Da farko ta ɗauka gajiya ce, sai dai ba a jima ba ta ji kamar wani abu ya fara zuba a jikinta. Gabanta ya faɗi, “Period,” ta furta a hankali, ai dama lokacinsa ya kusa.
Da sauri ta miƙe ta haura sama zuwa dakinta, ta buɗe drawer, ta ɗauko pad da niyyar ta saka. Amma da ta shiga toilet, sai ta tsaya cak, idanunta suka buɗe kaɗan. Ba period ba ne, abin da ta gani ya ba ta mamaki, kawi gani tayi tana leaking ba tare da ta san daga ina ba. Ta tsaya tana kallonsa, ta yi ƙoƙarin tuna wani abu, ko akwai abin da ya faru, ko akwai dalili, amma ta kasa tuna komai. Sai kawai ta kunna ruwan ɗumi, ta yi tsarki cikin nutsuwa, sannan ta fito ta zauna bakin gadonta.
Shiru. Sai wata zuciya a hankali ta fara rada mata, “Go and check on him...”
Ta ɗago kai, idanunta suka sauka kan agogon bango, 11:45 PM.
Ta yi shiru, “Yanzu?” ta tambayi kanta. Sai kuma zuciyar ta sake cewa, “Doctor ya ce kar a bar shi shi kaɗai...”
Ta sauke numfashi, a hankali ta miƙe, ta gyara hijabinta ta tabbatar ya rufe ta sosai, sannan ta nufi ƙofor ɗakinta. Ta buɗe ta a hankali har ta isa gaban ɗakin Umar, sai ta tsaya. Ta dade tsaye a wajen, hannunta na kan handle ɗin ƙofor, tana tunanin ta shiga? Ko kuma ta koma? Ai ya ji sauƙi, watakila yana barci, kada ta dame shi.
Sai dai kalaman Doctor suka sake dawo mata, “Kar a bar shi shi kaɗai...”
Ta lumshe idanunta, a hankali ta yi knocking sau ɗaya. Shiru, ba amsa. Ta sake knocking karo na biyu, har yanzu shiru. Gabanta ya ɗan faɗi.
A hankali ta tura ƙofor, ta shiga. Idanunta suka fara yawo cikin ɗakin, baya ciki, sai dai ta ji sautin ruwan daga toilet.
Ta tsaya a inda take, idanunta suka fara yawo cikin ɗakin. A karon farko tun da ta tare a gidan nan, shi ne karo na farko da ta shiga ɗakin Umar. Numfashinta ya tsaya na ɗan lokaci. Ɗakin ya zarce yadda take zato, faɗi ne mai cike da natsuwa. Katifar Persian mai launin ash da silver ta mamaye kusan dukan floor ɗin. A tsakiyar ɗakin akwai wani babban king-size bed mai launin charcoal grey, an shimfiɗa fararen Egyptian cotton bedsheets masu sheƙi. Pillows guda shida ne a jere, dukkansu a daidaitacce kamar ba wanda ya taɓa kwanciya a kansu.
A bayan gadon, headboard ne mai tsayin gaske, an yi shi da soft leather mai launin black. Gefensa akwai bedside tables guda biyu, a kansu akwai crystal lamps masu haske irin warm golden light. Hasken ɗakin gaba ɗaya ba mai ƙarfi ba ne, soft ambient lighting ce mai sa zuciya ta natsu.
A gefen window, dogayen curtains masu launin cream da dark grey ne, an ɗaure su da silk ropes. Window ɗin kuma glass ne daga ƙasa har sama, ta cikinsa ana iya hangen fitilun birnin Abuja suna walƙiya cikin dare.
A wani gefen ɗakin akwai ƙaramin lounge, sofas biyu masu launin navy blue, tsakaninsu akwai marble center table, a kai an jera wasu books, laptop, komai yana wurinsa. Ba wata hayaniya, ba wata tarkace. Ƙamshin ɗakin ma ya bambanta, ba turare mai ƙarfi ba, sai wani haɗaɗɗen kamshi na sandalwood, da oud, da ɗa vanilla mai sanyi, kamshin da ke ba ɗakin wani irin nutsuwa.
Inteesar ta kasa ɗauke idanunta, ta ji kamar ɗakin yana bayyana irin halin mai shi: tsari, nutsuwa, tsafta, da kuma wani irin kaɗaici da ba kowa zai gane ba.
Sai a lokacin ta sake jin sautin ruwan shower daga toilet, ta maido hankalinta wajen ƙofor toilet ɗin, ta tsaya shiru, ba tare da ta san dalilin da ya sa zuciyarta ta fara bugawa da sauri ba.
Inteesar na nan tsaye a wajen, numfashinta ma kamar ya tsaya. A hankali ƙofor toilet ɗin ta buɗe, Umar ya fito. Daure yake da wani farin luxury bath towel mai laushi a ƙugunsa. Ruwan da ya fito daga wankansa har yanzu na sauka a kafaɗunsa da ƙirjinsa a hankali. Gashinsa ya ɗan jike, ɗigon ruwa na bin gefen wuyansa yana saukowa zuwa ƙirjinsa. Saboda yawan motsa jiki, six packs dinsa sun bayyana a sarari ƙarƙashin hasken ɗakin.
Inteesar, kamar wacce aka kunna mata remote, kai tsaye ta ɗaga kai, idanunsu suka haɗu. Lokaci ya tsaya mata na wasu daƙiƙu. Da sauri ta sauke kanta ƙasa, gabanta ya yi wani irin faɗuwa, ta ji kamar ƙananan tsutsotsi suna yawo a duk jikinta. Zuciyarta kuwa bugunta ya sauya gaba ɗaya, ta fara matse kafafunta a hankali. Hannayenta suka rike gefen hijab dinta ta matse shi sosai, sai kuma ta saki hijabin, ta fara wasa da yatsunta kamar tana son cire su daga jikinta. Ba ta san inda za ta kalla ba, ba ta san me za ta ce ba.
Umar kuwa, tun fitowarsa idanunsa suna kanta, yana kallon yadda ta rikice, yadda ta kasa ko ɗaga kai. Ya ƙaraso tsakiyar ɗakin a hankali, baka jin komai sai ƙarar AC, ɗigon ruwa haryanzu na sauka daga jikinsa. Daga ƙarshe ya katse shirun cikin wata sassanyar murya.
“Ba ki yi barci ba?” ya tambaya, idanunsa na kanta.
Inteesar ta ɗan jinjina kai, da ƙyar ta buɗe baki, “Uhmm, dama zuwa na yi na ji ko za ka ci wani abu.”
Umar ya kalli ɗan mitsitsin bakinta, bakin da ya yi ta masa rashin kunya ɗazu, sai wani ɗan murmushi marar ƙarfi ya bayyana a gefen lips ɗinsa. Ya ɗan matsa kusa kaɗan, ya sake kallonata, cikin sanyin murya ya ce, “Dare ya yi, ba na cin abinci idan dare ya yi haka.”
Inteesar ta ɗan ɗago kai na ɗan lokaci kaɗan, sai ta sake sunkuyar da kanta. Wallahi ji take kamar ƙafafunta ba za su iya ɗaukarta ba, jikinta kuwa sai wani irin yam yammm yake mata, ba ta ma fahimci dalilinsa ba. Ta gyada kai kawai, “Toh...” ta furta a hankali, sannan ta juya da niyyar fita.
Sai kawai ta ji yace, “Ouch...” Muryar Umar ta katse ta. Ya ɗan riƙe gefen cikinsa, fuskarsa ta ɗan sauya.
Inteesar ta firgita, da sauri ta juya, “Yaya!” Ta ƙarasa gabansa da sauri, “What happened?” ta tambaya cikin tashin hankali. Ba tare da ta sani ba, ta kama hannunsa.
Umar ya runtse idanunsa kamar wanda ciwon ya sake dawo masa, ya ɗan sunkuyar da kansa, numfashinsa ya yi nauyi, sai cikin wata murya ƙasa-ƙasa, kamar ma irin shagwabar nan zai yi, ya ce, “...Marataaaaa...” Ya ja kalmar a hankali cikin wata siga da ta sa tsikar jikin Inteesar ta miƙe.
Sai ta dan tsaya still, idanunta cike da fargaba. Abin da ya faɗa mata a asibiti ya dawo mata gaba ɗaya, “Kar ku bar shi shi kaɗai...”, “Idan ya sake jin ciwo...”. Gabanta ya sake bugawa da ƙarfi. Ta ɗago ta kalli fuskarsa, ta rasa ko ta kira Yasmeen, ko ta taimaka masa ya zauna, ko kuma su sake komawa asibiti.
Ba tare da ta sake tunani ba, Inteesar ta ƙara riƙe hannunsa, “Yaya, a hankali,” ta faɗa cikin tashin hankali.
Umar yana ɗan jingina da ita, ko da ba dukan nauyinsa ya ɗora mata ba, suka taka a hankali zuwa bakin gadon. Sai dai hakan kaɗai ya isa ya sa bugun zuciyarta ya sake rikicewa. Da ƙyar suka isa bakin gadon, ta taimaka masa ya zauna, sai ta durƙusa a gabansa, fuskarta cike da damuwa.
“Yaya, mu koma asibitin,” ta faɗa cikin sauri, “dan Allah. Dare ya yi sosai, ciwon ya dawo, muje kafin ya ƙara tsananta,” muryarta har ta fara rawa kamar za ta yi kuka.
Umar ya lumshe idanunsa, ya sauke numfashi a hankali, sannan cikin wata murya mai rauni, kamar wanda ya shekara yana fama da jinya, “A’ah,” ya girgiza kai kaɗan, “idan na kwanta zai ragu. Ni idan bacci ya ɗauke ni, shi kenan.”
Inteesar ta tsaya tana kallonsa, ta ga yadda fuskarsa ta sauya da yadda yake magana da ƙyar, sai zuciyarta ta sake narkewa. Ta gyada kai a hankali, “Toh, kada ka motsa,” ta faɗa cikin sanyin murya.
Sai ta fara gyara masa kwanciya, ta ɗaga pillow ɗin, ta jujjuya shi da kyau, ta saka masa shi a bayansa cikin kulawa. Umar ya buɗe idanunsa kaɗan, ya tsaya yana kallonta. Yadda take ta faman rikicewa saboda shi, yadda ta manta da komai, sai shi kaɗai a gabanta, wani shegen murmushi ya suɓuce masa na gamsuwa, na jin daɗi.
A dai-dai lokacin, Inteesar ta ɗago, idanunsu suka kusa haɗuwa. Da sauri ya maida fuskarsa kamar zaiyi kuka, ya sake ɗan yamutsa fuska, “Ouch...” ya furta yana dafe gefen cikinsa.
Inteesar ta firgita, “Subhanallah!” ta faɗa da sauri. Da hannunta ta gyara pillow ɗin sosai, “Ka jingina da kyau.” Ta taimaka masa ya kwanta a hankali, sai ta janyo duvet ta rufe masa jikinsa har ƙirji, ta gyara gefensa kada sanyi ya shiga.
Ta ɗan matsa baya, ta tsaya tana kallonsa, ba ta san abin da ya kamata ta yi ba. Ta ɗan cije leɓenta, hannayenta a haɗe waje guda, idanunta suna yawo tsakanin fuskarsa da magungunan da ke kan bedside table. Ta tuna kalaman Doctor, “Kar ku bar shi shi kaɗai cikin dare.”
Sai ta sake kallonsa, numfashinsa yana fita a hankali, ya lumshe idanunsa kamar yana ƙoƙarin yin barci. Inteesar ta sauke ajiyar zuciya, a hankali ta ja ƙaramin chair da ke kusa da gadon ta zauna a kansa. Ta jingina bayanta, ba tare da ta sani ba idanunta suka ci gaba da binsa, kamar tana tsoron ko daƙiƙa ɗaya ta ɗauke idanunta kutoka gare shi, wani abu zai sake faruwa.
Umar ya buɗe idanunsa kaɗan, ta gefen ido ya kalli Inteesar. Har yanzu gabadaya hankalinta yana kansa. Tun daga lokacin da ta zauna, ba ta ko ɗan kau da idanunta daga gare shi ba, ko ya motsa kaɗan sai ta firgita, ko ya sauke numfashi sai ta matsa kusa.
A hankali ya lumshe idanunsa, sai kuma gaba ɗaya ya kifa akan cikinshi kamar wanda wani ya wuntsila shi. Hannayensa biyu suka kama cikinsa, ya danne shi da ƙarfi. Numfashinsa ya rikice, ya fara saukewa da sauri kamar mai fama da cutar asthma. “In... hah...” ya ja numfashi da ƙyar.
Inteesar ta firgita matuƙa, “Yaya!” ta faɗa da ƙarfi. Da sauri ta hau gadon, ta yaye duvet ɗin, ta kama kafaɗarsa tana ƙoƙarin ɗagashi. “Haba! Yaya! Mu koma asibiti, dan Allah. Ina tsoron dare,” muryarta ta karye, hawaye suka fara gangarowa ba tare da izini ba. Ta sake girgiza shi, “Yaya ka buɗe ido, please, mu tafi.”
Umar ya buɗe idanunsa da ƙyar ya kalleta, cikin wata murya mai rawa kamar wanda ciwo ya cinye gaba ɗaya, “Ba... ba komai, Princess. I... I will be fine.”
Inteesar ta fara girgiza kai da sauri, “A’a, a’a, ba zan yarda ba. Muje asibiti, please, kada ka ƙara magana.”
Sai kuma jikinsa ya fara karkarwa, haƙoransa suka fara bugun juna, wallahi babu wanda zai ce ba zazzabi ne ya kama shi ba. Ya matse idanunsa, cikin wata irin murya mai sanyi ya furta, “...Sanyi... sanyi nake ji, Princess...”
Inteesar ta ƙanƙame da rikicewa, “Ya Allah!” Da sauri ta janyo duvet ɗin da niyyar ta ƙara rufe masa jiki.
Amma kafin ta kai, sai Umar ya kamo hannunta da ƙarfi ya janyo ta. A take ta faɗo jikinsa, numfashinta ya tsaya, ta zaro ido sosai. Kafin ta ankara, ya riga ya lulluɓe jikinta da hannayensa, ya matse kansa a ƙirjinta kamar ƙaramin yaro da yake neman mafakar mahaifiyarsa.
Muryarsa ta fito a raunane, cikin rawa sosai irinta mara lafiyar dake tsananin jin jiki, “Hug me, Princess...” Ya sake matse kansa a jikinta, “Wayyo, zan mutu, ki yafe min...”
Inteesar ta daskare, gabanta ya buga da ƙarfi, hannayenta suka tsaya a sama, ba ta san inda za ta ajiye su ba. Ta ji yadda jikinsa yake rawa, ta ji yadda numfashinsa yake bugawa da sauri a ƙirjinta, hawayenta suka ƙara zuba.
“Yaya,” ta kira cikin kuka, “kada ka faɗi haka, don Allah. Ba za ka mutu ba, In Sha Allah ba za ka mutu ba.”
Da rawar hannu, a hankali ta ɗora hannunta ɗaya a bayansa, ɗayan kuma ta shafa kansa cikin lallashi kamar yadda Mommy Haleema take yi mata idan tana cikin damuwa. “Kada ka tsorata, ina nan, zaka ji sauki,” ta faɗa cikin muryar kuka, ba tare da ta san cewa kalaman da take faɗa domin kwantar masa da hankali, su ne suke ƙara sanya murmushi ɓoye a zuciyar Umar ba.
Ya ci gaba da danne kansa a ƙirjinta kamar wanda zafin ciwon ya turnuƙe gaba ɗaya, numfashinsa yana fita da ƙyar. A hankali ya sake furtawa cikin wata murya mai rauni, “...Hug me tight... Princess... Sanyi...”
Da jin kalmar “Sanyi”, Inteesar ba ta yi wata-wata ba. Da sauri ta ƙara matse shi a jikinta, ta zagaye bayansa da hannayenta biyu, ta rungume shi tsam kamar tana tsoron duk zafin da yake ji ya koma jikinta. Hankalinta ya gama tashi, ba ta taɓa ganin Umar cikin irin wannan hali ba tunda ta san shi. Ta san abu ɗaya, Yaya Umar mutum ne mai tsananin juriya, ko ciwo yake ji ba kasafai yake nuna shi ba. To idan har yau ya kai ga wannan halin, tabbas ba ƙaramin ciwo yake ji ba.
Hawaye suka sake cika mata ido, ta ɗora haɓarta a kansa tana shafa bayansa cikin lallashi. “Kada ka damu, zai wuce. In Sha Allah zai wuce,” ta faɗa cikin rawar murya.
Umar bai ce komai ba, sai ya ɗan yi shiru yana sauke numfashi a hankali. Har yanzu yana manne tsam a jikinta kamar idan ya sake