Author : Jiddah Barkum Category : Read Hausa Novels
wasu abubuwan ba, amma Mommy Haleema ma ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, ta dage sosai. An haɗa wa Inteesar turaruka iri-iri, turaren wuta, khumra, kullaccam, bakhour, da sauran kayan kamshi, musulmin daɗin ƙamshi dai ya mamaye gida tun kafin amarya ma ta shiga. Komai ta tanada domin ta tabbatar ’yarta ta fita kunya.
Yayyenta ma… kowa ya yi nasa bajintar. Adam ya kawo mata kayan ɗaki masu mugun kyau duk da Daddy ya mata komai amma shima sai da ya ƙara da nasa. Abubakar ya cika wardrobe ɗinta da sababbin kaya da takalma, handbags, jewelries kamar dai ya haɗa mata lefe ne. Khalil ya siya mata kayan electronics na zamani. Faruq, Saleem, Jaafar, Abdul, Alamin… kowa da irin gudummawar da ya bayar. Domin a wajensu… Inteesar ba ƙanwarsu kaɗai ba ce, ita ce farin cikin gidansu.
Abinda ya saukaka komai ba sabida dama tun farko an fara shirin aure, kuma ƙaddara ta gifta wacce ta rushe komai. Yawancin abubuwan da aka tanada tun wancan lokacin suna nan, an sake sabunta wasu, an ƙara sababbi, an kammala komai cikin ƙanƙanin lokaci. A ƙarshe… gidan amarya ya yi fes, ya yi tsit cikin ƙamshi da annuri, komai yana jiran isowar mai gidan.
Daren ranar da ya rage kwana ɗaya a kai amarya… ta gama yin sallar isha’i. Tana zaune a gefen gadonta. Aamaan yana kwance a cinyarta yana bacci. Tun da ta san gobe za ta bar gidan… ta kasa sakin yaron daga jikinta, ko kaɗan. Kullum idan ya yi barci sai ta aje shi, amma yau… ko bayan ya yi barci… har yanzu tana rungume da shi, tana shafa gashinsa a hankali, tana sumbatar goshinsa lokaci-lokaci, kamar tana ƙoƙarin haddace ƙamshinsa.
Ƙofar ɗakin ta buɗe a hankali. Mommy Haleema ce. Ta tsaya tana kallon yadda Inteesar ke rungume da Aamaan. Tun kafin ta yi magana… zuciyarta ta riga ta tausaya mata. A hankali ta ƙaraso, ta zauna kusa da ita, “Intee…” Inteesar ta ɗago, ta yi murmushi, “Mommy.” Mommy ta shafa gefen fuskar Aamaan, yaron yana barci cikin kwanciyar hankali, sai ta ɗauke idanunta ta kalli Inteesar, “ina son mu danyi magana.”
Inteesar ta ji gabanta ya faɗi, ta gyara zamanta, “tohm Mommy.” Mommy ta sauke numfashi, “ki sani tun yanzu… gobe… ba za ki tafi da Aamaan ba.” kalmar ta sauka kamar dutse a kan zuciyar Inteesar. Na ɗan lokaci… ba ta fahimci abin da Mommy ta faɗa ba, sai ta sake tambaya cikin sanyin murya, “…me kika ce?” Mommy ta kamo hannunta, “ba za ki tafi da shi ba. za ki bar shi a nan na ɗan lokaci.”
Nan take… idanun Inteesar suka cika da hawaye, ta matse Aamaan sosai a ƙirjinta, “a’a Mommy…” ta girgiza kai da ƙarfi, “a’a… don Allah… kada ki ce haka.” muryarta ta fara rawa, “dan Allah ki bar ni na tafi da shi.” Mommy ta dafa kafaɗarta, “Intee…” amma kafin ta ƙarasa… Inteesar ta fashe da kuka, ta rungume Aamaan har yaron ya ɗan motsa cikin barcinsa, “Mommy… ba zan iya ba. wallahi ba zan iya zama babu shi ba.” ta girgiza kai, “ya ya zan kwanta babu shi? ya ya zan farka ban ga fuskarsa ba? Mommy… kadaici zai kashe ni. haba Mommy… ni kaɗai zan zauna a gidan.” ta ƙara fashewa da kuka, “…ban san kowa ba. ki bar ni na tafi da ɗana.”
Mommy Haleema ta janyo Inteesar cikin jikinta, ta rungume ta kamar ƙaramar yarinya, “shhhh… ki yi haƙuri daughter.” ta shafa bayanta a hankali. Inteesar ta ci gaba da kuka. Mommy ta ɗan ɗago fuskarta, “kalli Mommy.” da ƙyar Inteesar ta ɗago idanunta. Mommy ta share mata hawaye, “ki tuna… Aamaan ɗanki ne. babu wanda zai taɓa rabaki da shi. babu.” ta sake dafa ƙirjinta, “ko da kin bar shi a nan… ba yana nufin kin rasa shi ba ne. ina son ki fara sabuwar rayuwarki cikin nutsuwa. ki saba da gidan, ki saba da zaman a can, ki saba da komai. daga nan… za mu kawo miki Aamaan.”
Inteesar ta girgiza kai, “yaushe?” Mommy ta yi murmushi mai taushi, “ba zai daɗe ba. in sha Allah… ba zai wuce sati biyu ba.” ta ɗan yi tunani, “ko idan ya ɗan ja… wata ɗaya kacal. sannan za mu kawo miki shi.” Inteesar ta sake fashewa da kuka, “wata ɗaya? Mommy… yayi yawa. yayi min yawa.” ta kalli Aamaan, “shi ma zai nemi Mamie ɗinsa. idan ya yi kuka fa?” Mommy ta kamo hannunta, “za mu kula da shi. ni zan kula da shi. yayyanki za su kula da shi. Shemau ma tana nan. babu abin da zai same shi.” ta yi murmushi, “kuma kin san Aamaan… duk inda yake idan ya ga ana sonsa… sai ya yi dariya.”
Inteesar ta yi shiru, sai hawayenta kawai ke zuba. Ta kalli fuskar ɗanta, yana barci cikin salama, ya ɗan motsa leɓbansa kamar yana mafarki. Ta shafa gashinsa a hankali. Wani sabon kuka ya sake ƙwace mata. Mommy Haleema ta rungume ta tare da Aamaan gaba ɗaya, ta riƙe su duka biyun a jikinta, ta lumshe idanunta, a hankali ta ce, “ki yi haƙuri daughter. wani lokacin… domin gina rayuwa… sai an fara da irin wannan sadaukarwar.”
Inteesar ta share hawayenta da bayan hannunta, da ƙyar… ta gyada kanta, “to Mommy…” muryarta ta yi ƙasa sosai, “zan yi haƙuri. amma… kullum zan kira a nuna min shi.” Mommy ta yi murmushi, “na yi miki alƙawari.”
A safiyar ranar da Inteesar za ta tare gidanta, suna durƙushe ita da Yaya Umar a gaban Daddy.
Inteesar sanye take da lafaya maroon mai tsananin kyau, an lulluɓe ta gaba ɗaya da ita, har fuskarta a rufe take. Amma… ko ba a ga fuskarta ba… an san tana kuka.
Umar kuwa… sanye yake da farar shadda mai tsabta, fuskarsa cike take da nutsuwa, amma idanunsa sun nuna irin nauyin da ke cikin zuciyarshi.
Mommy Haleema tana zaune a gefen Daddy, idanunta sun riga sun yi ja saboda hawayen da take ta dannewa tun safe.
Daddy ya daɗe yana kallonsu, sai ya sauke wata doguwar ajiyar zuciya, ajiyar zuciyar da ta fito daga can ƙasan zuciyarsa. A hankali… ya ɗora hannunsa kan Inteesar, ya shafa kanta cikin tausayi, muryarsa ta yi rauni sosai, “Fateema…” Inteesar ta amsa da ƙyar, “na’am Daddy…” muryarta ta dusashe saboda kuka.
Daddy ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci, sannan ya buɗe su, ya fara magana a hankali, “tun ranar da Allah ya ba mu ke… a matsayinmu na iyayenki… amanarki… da nauyin kula da ke… yana kanmu.” ya ɗan yi shiru, kamar yana tattara ƙarfin zuciya, sannan ya ci gaba, “mun yi iya ƙoƙarinmu. mun raina ki. mun tarbiyyantar da ke. mun so ki. mun kare ki. mun yi addu’a saboda ke dare da rana.” muryarsa ta sake karyewa, sai ya haɗiye wani abu mai ɗaci, “amma… a yau… …wannan nauyi… …wannan iko… …wannan amanar… ta sauka daga kanmu.” ya juya ya kalli Umar, sannan ya dawo da kallonsa kan Inteesar, “ta koma kan mijinki. daga yau… shi ya fi mu iko da ke.”
Inteesar ta ƙara fashewa da kuka. Daddy ya ci gaba cikin sanyin murya, “ina kuma son ki sani… duk irin halayen da za ki nuna a gidan aurenki… …ba ke kaɗai za a kalla ba.” ya nuna ƙirjinsa, “mu iyayenki za a kalla. mutane za su ce… Alhaji Kabeeru da Haleema haka suka tarbiyyantar da ’yarsu.” ya girgiza kai a hankali, “saboda haka… ki zama abin alfaharinmu. ki zama mace mai haƙuri, mai mutunci, mai biyayya ga Allah, mai kiyaye mutuncin mijinta.”
Inteesar ta ci gaba da kuka ba tare da ta iya ɗaga kanta ba. Daddy ya miƙa ɗaya hannunsa, ya ɗora shi kan Umar, “Umar…” “na’am Daddy.” muryar Umar ita ma ta yi rauni. Daddy ya kalle shi sosai, “ba zan yi maka doguwar magana ba. domin na san halinka, na san tarbiyyarka, na san zuciyarka.” ya yi murmushi mai rauni, “abu ɗaya ne kawai zan gaya muku ku duka biyu.” ya zuba musu ido, “ku zama sirrin junanku. kada ku bari wani ya san abin da ke tsakaninku. kada ku saka mutum na uku a cikin aurenku. idan kun yi farin ciki… ku yi tare. idan kun samu matsala… ku zauna ku warware tare. kada ku fita kuna kai korafi ga mutane. kada ku bari wani ya shiga tsakaninku. domin… yawancin gidaje ba matsalarsu ce ta rushe su ba. mutum na uku ne.” ya sake maimaitawa cikin ƙarfi kaɗan, “avoid third party. ko da kuwa mutumin yana da kusanci da ku. ko da kuwa ni ne. ko da Haleema ce. ko yayyanku ne. ko danginku ne. ku fara magance matsalarku da kanku. sai idan kun kasa… sannan ku nemi shawara.”
Ya sake sauke numfashi, muryarsa ta sake yin sanyi, “a yau… na ba ku amanar junanku. ku kula da juna. ku tausaya wa juna. ku zama suturar juna. dukkaninku… ‘ya’yana ne. rainona ne. tarbiyyata ce. kuma babu wanda ya fi wani a wurina.” ya sauke numfashi sannan ya dora, “Allah ya yi muku albarka. Allah ya ba ku zaman lafiya. Allah ya cika gidanku da rahama. Allah ya ba ku fahimtar juna. Allah ya sanya soyayya da tausayawa a tsakaninku. Allah ya kare ku daga sharrin mutane da sharrin shaiɗan. ameen.”
Mommy Haleema ce ta fara amsawa cikin kuka, “ameen ya rabb.” Umar ya amsa cikin rawar murya, “ameen.” Inteesar kuwa… ta kasa cewa komai, kukanta ya ƙara ƙarfi.
Nan take… ta matsa gaba, ta jingina kanta a kan cinyar Daddy, ta fashe da wani irin kuka mai tsananin ciwo, “Daddy…” kiran da ta yi masa kaɗai… ya karya zuciyar duk wanda yake cikin falon. Daddy ya dafe kanta, shi ma hawayen da yake ta dannewa… suka gagara, suka fara zuba a hankali. Ya ɗan lumshe idanunsa, sannan ya miƙe tsaye, ya kamo Inteesar, ya ɗaga ta daga ƙasa, ya rungume ta sosai, rungumar uba… mai cike da ƙauna, mai cike da tausayawa, mai cike da rabuwa.
Inteesar ta manne a ƙirjinsa, ta fashe da kuka fiye da, kamar ƙaramar yarinya, “Daddy… zan yi kewarka…” ta faɗa cikin kuka. Daddy ya rufe idanunsa, ya sumbaci kanta ta saman mayafin, ya shafa bayanta a hankali, “ni ma zan yi kewarki, Princess. amma… dole ce. wannan ita ce rayuwa. yau kin tashi daga gidana… domin ki gina naki gidan. kada ki taɓa manta… wannan gida… gidanku ne har abada. duk lokacin da kika buƙaci ubanki… za ki same ni.”
Mommy Haleema ta kasa ƙara daurewa, ta juya gefe, ta share hawayenta da gyalenta, amma duk da haka… sabbin hawaye suka ci gaba da zuba. Falon ya cika da shiru… sai sautin kukar Inteesar da ajiyar zuciyar Daddy. Lokaci ne da ya tabbatar wa kowa cewa… ko da aure sunnah ce… raba uba da ’yarsa… ba abu ne mai sauƙi ba.
Yaya Abubakar ya leko ya dubesu, “we are getting late, yakamata mu tafi, jirgi ba zai jira ba.” a hankali Daddy ya zare Inteesar daga jikinsa, ya miƙawa Umar hannu. Yaya Umar dake durƙushe ya tashi, sai Daddy ya kama hannunshi ya saka hannun Inteesar a ciki, Umar ya damke sosai. Daddy yayi murmushi wanda ya taho da wani siririn hawaye, sannan yace, “kuje Allah ya baku zaman lafiya.”
Sorry for the typos not edited
*KADDARAR ZUCIYA*
*CHAPTER EIGHTY-TWO: 82*
*A BEGINNING WRITTEN BY FATE*
*JIDDAH BARKUM*
———
Suka fito daga ɓangaren Daddy a hankali.
Hannun Umar yana damƙe da na Inteesar sosai, kamar an ce masa idan ya sake ta… wani abu zai same ta. Shi kansa bai san dalilin da ya sa yake riƙe da hannunta haka ba, sai dai zuciyarsa ta ƙi ya sake ta.
Inteesar kuwa… tun daga falon Daddy… ba ta daina kuka ba, sautin kukanta ya dauke, amma hawayenta… ba su daina zuba ba.
Har suka fito cikin compound. Motar da za ta kai su airport tana jiransu. Yaya Abubakar ya ƙaraso ya buɗe musu ƙofar baya.
Umar ya ɗan karkata, ya taimaka wa Inteesar ta shiga motar. Da ta zauna… ta sake sunkuyar da kanta, hawayenta suka ci gaba da sauka. Umar ya rufe mata ƙofar, sannan ya zagaya ya shiga gaban mota, kusa da Yaya Abubakar.
Mommy Haleema da Khalil suka tsaya a bakin veranda suna musu waving. Mommy ta yi murmushi… amma murmushin ya kasa ɓoye jajayen idanunta. Khalil kuwa… ya yi ƙoƙarin yin murmushi domin Inteesar kada ta ƙara rushewa.
Motar ta fara motsi a hankali. Inteesar ta waigo ta taga, ta ci gaba da kallon gidan. Gidan da ta taso, gidan da ta san komai a cikinsa, gidan da ta yi dariya, ta yi kuka, ta yi rayuwa. Har sai da motar ta fice daga gate, sai gidan ya ɓace daga ganinta. A lokacin ne… ta sake fashewa da kuka, ta rufe fuskarta da tafin hannunta. Ba wanda ya ce mata komai, domin kowa ya san… ba kalmomi take buƙata ba, lokaci take buƙata.
——
Har suka isa airport… Inteesar ba ta daina kuka ba. Da suka gama checking, aka auna kayansu, aka karɓi boarding pass, aka kammala duk abin da ya kamata, sai suka tsaya a wajen shiga cikin departure gate.
Yaya Abubakar ya juya ya kalli Inteesar, ya zuba mata idanuwa. Mutum zai rantse babu wani abu a zuciyarsa, amma idanunsa… su kaɗai sun isa su faɗi irin abinda ke zuciyarsa. Ya yi kama da uba… da yake miƙa ’yarsa zuwa gidan aurenta. A hankali ya matso kusa da ita, ba tare da ya ce komai ba… ya buɗe hannayensa. Inteesar ta faɗa jikinsa. Nan take… ta sake fashewa da kuka, ta rungume shi gam.
Abubakar ya lumshe idanunsa, ya fara bubbuga bayanta a hankali cikin sigar lallashi. Sai bayan wasu daƙiƙu… ya ce cikin sanyin murya, “Princess… ya isa haka. stop crying.” ya ɗan yi shiru, kamar yana jiran ko za ta rage kukan, amma sai ta ƙara manne masa. Ya sauke wata ajiyar zuciya, a hankali ya ɗan ciro ta daga jikinsa, ya ɗago fuskarta, ya share mata hawayen da suka cika kumatunta, sannan ya yi murmushi, “be a good wife… as you have always been a good sister…” “kina ji?”
Inteesar ta kasa magana, sai cikin kuka… ta gyada masa kai a hankali, “good.” ya shafa kumatunta cikin taushi, sannan ya saka hannu cikin aljihunsa, ya fito da wani ƙaramin akwatin velvet, irin akwatin jewelry. Ya miƙa mata. Inteesar ta karɓa da hannaye biyu, ta kalle shi, cikin murya mai cike da kuka ta ce, “thank you…” Abubakar bai ce komai ba, sai ya yi mata murmushi. Daga nan ya juya ya kalli Umar da ke tsaye a gefe yana binsu da kallo, ya matso kusa da shi, ya dafa kafaɗarsa, “ku tafi. an fara kiran passengers. Allah ya tsare hanya.” Umar ya jinjina kai cikin girmamawa, “ameen.” ya ɗan tsaya, ya kalleta, sai kawai tayi gaba ta fara tafiya. Umar ya bu bayanta a nutse zuwa departure gate. Mataki ɗaya, sai wani, ba tare da Inteesar ta waigo baya ba. Yayin da Yaya Abubakar ya tsaya daga nesa… yana binsu da ido, har suka ɓace daga ganinsa.
Jirgin daga Katsina zuwa Abuja… ya kasance cikin wani irin shiru. Shirun da ba wai saboda babu mutane a cikin jirgin ba… sai saboda mutanen biyu da ke zaune kusa da juna. Tun daga lokacin da suka zauna a kujerunsu… babu wanda ya ce wa ɗan uwansa ko kalma ɗaya.
Umar yana kallon window lokaci zuwa lokaci. Inteesar kuwa… tun da ta ɗaure seat belt… ta jingina kanta da kujerar, idanunta suna cike da gajiya. Ba ta da ƙarfin yin kuka kuma, ba ta da ƙarfin magana, ta dai zauna shiru. Jirgin ya fara tashi a hankali. Yayin da birnin Katsina yake ƙara ƙanƙanta a ƙarƙashinsu… Inteesar ta lumshe idanunta, ba ta san lokacin da bacci ya ɗauke ta ba.
…
Sai bayan jirgin ya sauka a filin jirgin saman Abuja. An kashe seat belt sign, mutane suka fara miƙewa ɗaya bayan ɗaya, ana buɗe overhead compartments, ana sauke jakunkuna, ana shirin fita. Inteesar kuwa… har lokacin tana bacci. Sai da Umar ya ɗan bubbuga gefen kujerarta a hankali. Ba ta ji ba. Ya sake bubbugawa cikin tausasawa. A hankali ta buɗe idanunta, ta ɗan kalli sama, sai hagu, sai dama, kamar tana ƙoƙarin tuna inda take. Da ta ga mutane suna fita… ta fahimci sun iso. Ba tare da ta ce komai ba… ta miƙe a hankali. Umar ya ɗauki handbag ɗinta, ya jira har ta gyara mayafinta, sannan suka fara tafiya suna bin sauran passengers, har suka fito daga cikin jirgin.
…
Da suka iso arrival hall… Umar ya tsaya gefe, ya ciro wayarsa, ya kira wani. Inteesar tana tsaye ɗan nesa da shi, saboda tazarar da ke tsakaninsu… ba ta jin abin da yake faɗa, sai dai ta ga yana magana cikin nutsuwa. Bayan ya gama… ya kashe wayar, ya juyo ya kalle ta.
… da idanuwansu suka haɗu… sai ta sauke kanta ƙasa. A hankali ya ce, “let’s wait a bit. Hashim yana hanya. zai zo ya kai mu gida.” Inteesar ba ta ce komai ba, sai kawai ta gyada kai. Suka sami wasu kujeru a cikin airport ɗin, suka zauna. Har yanzu… shiru ne tsakaninsu, kowa yana cikin tunaninsa.
Ba su yi mintuna biyar da zama ba… wayar Umar ta sake ringing. Ya ɗaga, “hello…” ya saurara na ɗan lokaci, sannan ya ce, “okay. we’re coming.” ya kashe wayar, ya miƙe tsaye, ya dubi Inteesar, “ya ƙaraso. let’s go.” ta miƙe ba tare da magana ba, ta bi bayansa a hankali. Har suka fito parking lot.
…
Wata baƙar mota ce can gefe, Hashim yana tsaye a jikinta. Da ya ga Umar… ya yi saurin ƙaraso, yana murmushi, “welcome back, bro.” Umar ya mayar masa da murmushi, “thank you.” Hashim ya buɗe boot, ya saka musu kayansu, daga nan ya juya wajen Inteesar. Ta ɗan sunkuyar