Kaddarar Zuciya Book 2 Complete JIddah Barkum

Author :  Jiddah Barkum Category :  Read Hausa Novels

Chapter   34 / 40

99K to 102K   out of 117.5K words

“Wannan kam zan cinye kudadenka wajen shopping.”

Ya kalli fuskarta. “Idan kina farin ciki... komai yana da sauƙi.”

Sai ta yi masa kallon da ya sa ya ɗan yi shiru. Ya ci gaba da gungurawa.

*🇮🇩 Bali, Indonesia*

Green forests. Private villas. Waterfalls. Rice terraces. Spa. Quiet beaches.

Ta lumshe ido. “Wannan ma yana da nutsuwa. Haka nake so.”

Ya gyaɗa kai. “Na sani.”

Sai ya nuna mata wani shafi. “Ga wasu kuma.”

*🇫🇷 Paris* – don romantic dinners da Eiffel Tower.

*🇮🇹 Italy* – Venice gondola rides da Lake Como.

*🇲🇺 Mauritius* – fararen rairayin bakin teku da resorts masu zaman kansu.

*🇸🇦 Makkah & Madinah* – domin su haɗa hutun soyayya da ibada.

Ya kashe scrolling ɗin. Sannan ya sauke tablet ɗin kan cinyarsa. Ya sake kallonta.

“To... wace kika fi so?”

Inteesar ta yi shiru na ɗan lokaci. Ta sake kallon hotunan. Daga ƙarshe ta ce cikin murmushi,

“Da zan zaɓa... na fara da Makkah da Madinah.” Ta ɗan yi dariya. “Sai kuma Maldives. Sannan Turkey.”

Umar ya yi murmushin gamsuwa. “Excellent choice.”

Ya ɗan matse hannunta. “To shi ke nan. Za mu fara da Umrah. Sai mu wuce Maldives. Daga nan...” ya ɗan yi mata wink, “mu ƙarasa Turkey. Infact duka ma zamuje.”

Inteesar ta yi saurin ɗaga kai tana kallonsa. “Da gaske?”

Ya kama hannunta ya haɗa yatsunsu. “Da gaske. Ina so in zagaya duniya tare da ke. Ba saboda ƙasashen ba... sai saboda duk inda nake, idan kina tare da ni, a nan ne gida na.”

Inteesar ta yi shiru. Ta matse hannunsa cikin nata. Ta jingina kanta a ƙirjinsa tana murmushi.

“Ni ma... ko ina ne, matuƙar tare da kai nake, zan ji kamar na isa gida.”

Umar ya sumbaci saman kanta cikin taushi. Ya ƙara rungume ta.

Tablet ɗin kuwa ya ci gaba da nuna hotunan kyawawan wuraren da suke shirin gina sabbin abubuwan tunawa tare.

---

Not edited

*KADDARAR ZUCIYA*

*CHAPTER NINETY-SEVEN: 97*

FOREVER TOGETHER

*JIDDAAH BARKUM*

———

Inteesar ta yi shiru na wasu daƙiƙu, kanta kwance a faffadan ƙirjin Umar. Tana jin bugun zuciyarsa yana bugawa daidai da nata.

A hankali, cikin siririyar murya mai cike da kunya da gaskiya, ta ce,

“I love you so much… Yayaaa…”

Umar ya tsaya cak. Kamar bai yarda da kunnuwansa ba.

Da sauri ya ɗan janye ta daga jikinsa, ya riƙe kafaɗunta da hannayensa biyu yana kallon fuskarta.

Inteesar ta ɗan karkatar da kanta gefe cikin kunya, tana murmushi mai laushi, idanunta cike da soyayya.

Ya sauke numfashi a hankali.

“…Da gaske kina sona?”

Muryarsa ta fito ƙasa sosai, cike da mamaki da fargabar rasa amsar da zuciyarsa take jira.

Inteesar ta sake murmushi. Ba tare da ta ce komai nan take ba, ta koma ta kwantar da kanta a ƙirjinsa, ta zagaye bayansa da hannayenta.

Sannan cikin nutsuwa ta ce,

“Eh… ina sonka.”

Ta ɗan yi shiru kafin ta ƙara da cewa,

“Ina matuƙar ƙaunarka, Yayaaa… ƙaunar da ko ni kaina ban san iyakarta ba.”

Kalaman nata suka sauka kai tsaye cikin zuciyar Umar.

Ya lumshe idanunsa. Hannunsa ya zagaye ta sosai, ya matse ta a jikinsa tamkar yana tsoron kada wani ya ƙwace masa ita.

Sai ya furta cikin rawar murya,

“Alhamdulillahil-ladhi bi ni’imatihi tatimmus-salihat…”

Ya ɗan yi murmushi, idanunsa na cika da ƙwalla.

“Na gode Ya Allah... na gode da Ka sa ta so ni. Na gode da Ka bani Jewel ɗina.”

Ya sumbaci saman kanta cikin taushi.

“Wallahi Jewel... ko yau Allah Ya karɓi raina, zan tafi cikin farin ciki. Saboda... na riga na cimma burina mafi girma.”

Inteesar ta ƙara manne masa. Shiru ya mamaye tsakaninsu. Sai sautin numfashinsu kawai.

Bayan wasu daƙiƙu, Umar ya sake magana.

“Kinsan wani abu?”

Ta ɗaga kanta kaɗan. “A’a...”

Ya yi murmushi mai ɗaci.

“Da dare... shekaru da yawa... ban cika iya bacci ba.”

Ya ɗan ɗaga kai yana kallon sama kamar yana sake rayuwa cikin tsoffin kwanakin.

“Sau da yawa ina fita balcony... ina tsaye ina kallon taurari.”

Ya yi murmushi mai ciwo.

“Ina jin kamar yadda nisan sama da ƙasa yake... haka nisan samunki yake.”

Ya shafa gashin kanta cikin kauna.

“Amma ashe... Allah tun tuni Ya riga Ya rubuta cewa wata rana... za mu zauna ƙarƙashin inuwar aure.”

Ya sake rungume ta. A wannan karon da wani irin ƙarfi.

Sannan ya yi shiru na wasu daƙiƙu, kamar yana haɗiye wani abu mai ɗaci.

Can kuma ya ce,

“Sau da yawa Nana Aseeyah tana samuna tsaye da tsakar dare.”

Muryarsa ta fara rawa.

“Za ta tambaye ni... ‘Har yanzu tunanin Inteesar kake yi ko?’”

Ya yi murmushi cikin hawaye.

“Sai ta ce... ‘babe... je ka yi alwala. Ka yi nafila. Allah zai sauƙaƙa maka.’”

Ya lumshe idanunsa.

“Haka kawai... ba taɓa yi min faɗa ba. Ba taɓa ce min in manta da ke ba.”

Inteesar ta ji wani irin zafi ya ratsa zuciyarta. Hawaye suka fara zubo mata ba tare da ta goge su ba.

Umar ya ji su suna sauka a ƙirjinsa. Sai ya ƙara matse ta.

“Karki yi kuka...”

Amma ita kuka kawai take yi.

Bayan ta ɗan natsu, Umar ya shafa bayanta a hankali. Sai ya tambaya cikin sanyin murya,

“Ranar nan da kuka fito daga kitchen... Nana Aseeyah me ta faɗa miki a ɗaki?”

Inteesar ta sauke ajiyar zuciya. Sabbin hawaye suka sake zubo mata. Ba ta goge su ba.

Cikin rawar murya ta ce,

“A kitchen... ta ce min... na daure... na aure ka.”

Muryarta ta sake karyewa.

“Ta ce...”

Ta kasa ƙarasawa. Kuka ya ƙwace mata.

Umar ya share hawayen da ke fuskarta. Ta haɗiye kukanta kafin ta ci gaba.

“Ta ce... tunda ita har yanzu Allah bai ba ta haihuwa ba... watakila idan na zo... ni zan haifa mana yaran da ta daɗe tana mafarki.”

Da ta gama faɗar hakan, ta fashe da kuka mai tsanani.

Umar ya sake rungume ta da dukkan ƙarfinsa. Shi ma idanunsa suka cika da ƙwalla.

A wannan lokacin, ba wai kawai yana jin tausayin Nana Aseeyah ba ne, yana jin nauyin irin girman zuciyar matar da ta fi son farin cikinsa a kan nata.

Sai ya ɗago idanunsa sama cikin sanyin murya ya ce,

“Allah Ya saka mata da Aljannatul Firdaus... ita mace ce da ba zan taɓa mantawa da alherinta ba.”

———

*Kwanaki biyu suka gudu* cikin sauri tamkar walƙiya, inda kowace daƙiƙa ta kasance mai cike da zallar soyayya, kulawa, da kuma sabon shauƙi da ya mamaye tsakanin ma'auratan. Gidan ya canza launi gaba ɗaya. Dukkan wata katanga ta kunya da fargaba ta ruguje, ta bar gurbinta ga wani lallausan aminci da ke ƙara dankara soyayyarsu.

A yanzu haka, gaba ɗaya gidan ya ɗauki sabon salon shirye-shirye. Shirin tafiya honeymoon suke yi na musamman. Yaya Umar ya tsara cewa za su fara gudanar da ibadar Umra a ƙasa mai tsarki domin su miƙa godiyarsu ga Allah SWT tare da neman albarka a cikin sabuwar rayuwarsu, kafin daga baya su ƙarasa sauran ƙasashen da suka tsara za su ziyarta.

*Daren yau shi ne daren* da ke gab da ranar tafiyarsu. Sanyin AC na ratsa faffadan falon nasu mai cike da alfarma da ƙamshi mai daɗi.

Inteesar na zaune a kan lallausan dogon sofa sanye da wata doguwar rigar barci ta cotton mai taushi. Yayin da Yaya Umar ke kwance, ya ɗaura kansa a kan cinyoyin nata cikin wata irin natsuwa da nuna cewa nan ne cikakken comfort zone ɗinsa. Idanunsa a lumshe suke luff, fuskarsa ɗauke da sassanyan murmushin da ke nuna tsananin gamsuwa. Numfashinsa na fita a hankali. Ba barci yake yi ba, yana can yana jin daɗin yadda lallausan hannun Inteesar ke yawo a cikin sumar kansa, tana tusa yatsunta a hankali tana sarrafa gashin, wanda hakan ke ƙara kashe masa dukkan jiki.

Shuru-shuru kake ji a falon, sai kawai sautin numfashinsu da ke gaurayuwa.

Can sai ga wayar Inteesar ta ɗauki ruri a gefe. Ta ɗan leƙa screen din wayar, sunan "Mommy" ya bayyana radau.

Wani lafiyayyen murmushi ya mamaye fuskarta. Da sauri ta ɗaga kiran ta danna a kunne.

“Mommy naaa!” ta faɗa cikin muryarta mai cike daɗi da raunin shagwaɓa.

Mommy Haleema ta amsa kiran cikin matsananciyar fara’a da kulawa. Suka gaisa cike da farin ciki da nuna kewar juna. Inteesar har ta sami damar yin magana da Aamaan, tana sauraron kalaman gwarancinsa na yarinta da yake yi mata, wanda hakan ya sanya ta fashe da wata lallausar dariya mai sauti.

Yaya Umar da ke kwance a cinyarta ya ɗan ƙara lumshe idanunsa, yana sauraron sautin dariyarta wanda ke ratsa zuciyarsa kamar wata rera waƙa.

Bayan sun gama gwaranci da Aamaan, Inteesar ta maida wayar ga Mommy, suka ci gaba da tattaunawa.

Cikin hanzari da nuna ɗoki, Inteesar ta ce:

“Mommy, gobe fa In Sha Allah za mu yi tafiya. Kuma ina dawowa, kai tsaye Katsina zan sauka...”

Mommy Haleema ta saki wata gajerar dariya ta jin daɗi.

“Masha Allah, Princess. Ubangiji Allah Ya kiyaye hanya, Ya tsare ku, Ya kuma dawo da ku lafiya.”

“Amin, Mommy na.”

Mommy ta yi shiru na wasu daƙiƙu, sannan ta gyara muryarta, ta dawo da ita cikin wani irin yanayi na nutsuwa da zalla manufa. Cikin sanyin murya ta ce:

“Princess... yanzu kinyi wata shida da aure ko? Saura wata shida da suka rage mana gaba ɗaya, ko kuwa?”

Wata irin sarƙewa ce ta sarƙe makoraron Inteesar gaba ɗaya. Cikin rashin fahimta da kuma ɗaukar jiri, ta ce:

“Mommy... wanne watanni shida kuma?”

Mommy Haleema ta gimtse dariyar da ke ƙoƙarin subuce mata a ɗayan ɓangaren. Sannan cikin takaitacciyar murya mai nuna tabbatar da zance ta ce:

“Princess, kin manta yarjejeniya da alkawarinmu ne? Idan har kika cika shekara ɗaya cif a gidan nan, zan raba ki da Umar gaba ɗaya na dawo da ke kusa da ni.”

Gubbbb!

Gaban Inteesar ya faɗi da wani irin mugun ƙarfi da sautin da ta ji har cikin kwaran jikinta. Wani irin sanyi mai zafi ya rufar mata lokaci ɗaya. Har hannunta na hagu da ke cikin gashin Umar ya tsaya cak ba tare da ta sani ba. Ta saci kallon Umar da ke kwance a cinyarta.

A daidai wannan lokacin gaba ɗaya, Yaya Umar ya riga ya ji sarai dukkan kalaman da Mommy ke faɗa ta cikin speaker tun daga kalmar farko har zuwa ta ƙarshe. Domin kusancin da ke tsakanin fuskarsa da wayar yana da yawa sosai.

Jin maganar raba shi da Jewel ɗinsa bayan shekara ɗaya ya sanya shi jin wani irin shock ya dake shi. Nan take ya ɗan buɗe kyawawan idanunsa waɗanda suka riga suka sauya launi kaɗan, ya kafeta da su yana jiran sauraron abin da zai biyo baya.

Inteesar ta rikice gaba ɗaya, lissafinta ya fita daga tsari. Ta rasa abin da za ta ce wa Mommy. Gashi gaba ɗaya ba ta son Yaya Umar ya ji amsar da za ta bayyana, duk da cewa ta riga ta tabbatar a ranta ya ji dukkan abin da ake cewa.

Cikin ruɗani da saurin neman mafita, ta fara pretending da canza sauti:

“Hello... Hello Mommy? Kina jina kuwa? Gaskiya banajinki gaba ɗaya... Hello? Network ɗin gaba ɗaya ya ɗauke, Mommy...”

Tana gama rarraba kalaman nan cikin sauri, ta danna end call ta katse kiran gaba ɗaya. Ta sauke wayar ta ɗora ta a gefen kujerar, tana fitar da numfashi sama-sama.

Yaya Umar ya zame kansa a hankali daga kan cinyarta. Ya tashi ya zauna daram a kan sofa ɗin, ya gyara zamansa da kyau gami da fuskantar ta gaba ɗaya. Idanunsa waɗanda suka yi zurfi cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara suka tsaya karaf a kan fuskarta.

Kallon ya kasance na tsanaki, kallo mai cike da tuhuma, bincike, da kuma wani irin raɗadin da ya kasa ɓoyewa.

Inteesar ta tsinci kanta cikin matsananciyar marairacewa da rashin gaskiya. Ta kasa ɗaga idanta ta kalli fuskarsa. Sai ta fara sosa kanta da yatsun hannunta na dama, tana wasa da gefen rigarta cikin tsoro da inda inda.

Umar ya tsare ta da idanu gaba ɗaya. Bai ce da ita ko uffan ba, kuma bai janye idanunsa ko na daƙiƙa guda ba. Wannan shu'umin kallon da yake jifa da shi gaba ɗaya ya birkita mata lissafin ƙwaƙwalwarta. Ya bar zuciyarta tana harbawa da ƙarfi tamkar za ta fito fili.

Ganin irin zazzafan kallon tuhumar da yake jifanta da shi, wanda ke ratsa kowace jijiya ta jikinta, ya sanya Inteesar jin duk wata dabara tata ta ƙare. Cikin tsananin ruɗani da rashin sanin madafa, ta fara in-ina, muryarta na rawa sosai yayin da hawayen gaskiya suka cika mata idanu.

“Yaya... wallahi... wallahi ba ni ce na ce ba!” ta shiga rarraba kalaman da sauri, tana fatan ya fahimci tsantsar gaskiyar da ke zuciyarta.

“Mommy ce ta faɗa mini ranar... ta ce idan har ba na son zama da kai, to na yi haƙuri na zauna na tsawon shekara ɗaya guda, daga nan sai ta zo ta tafi da ni ta raba mu. Amma wallahi, thummal wallahi Yaya ba ni na ce ba... tsakanina da Allah nake faɗa maka!”

Tuni Yaya Umar ya fahimci ainihin bakin zaren dake faruwa, kuma ya gano inda kullin yake tun farko. Sai dai, ganin yadda ta firgice ya sanya shi yanke shawarar tsananta fushinsa domin ya ƙara fuzgo ainihin abin da ke can ƙasan zuciyarta.

Ya sake haɗe girar samansa da ta ƙasa. Fuskarsa ta yi tsam tamkar bai taɓa yin murmushi ba. Cikin wata irin daƙuƙashiyar murya mai ban tsoro da nuna zallar raɗadi, ya ce:

“Wato... ashe tsanar da kike mini ta kai matsayin da har lissafin watanni da kwanakin da suka rage miki ki rabu da ni kike yi, ko, Inteesar?”

Yana gama faɗar haka, sai ya ɗora hannunsa na hagu a saitin ƙirjinsa. Ya dafe da ƙarfi gami da runtse idanunsa da suka sake yin ja wur. Yana fitar da nishi da sauri-sauri tamkar wanda zazzafan ciwon ƙirjinsa na dā yake ƙoƙarin tashi a take.

Ganin yanayin da ya shiga ya sanya Inteesar jin dukkan duniyar ta juya mata gaba ɗaya. Ba tare da wani tunani ba, ta miƙe da sauri ta matso kusa da shi sosai a kan sofar. Ta sa hannayenta biyu ta riƙe nasa hannun da ke ƙirjinsa, ta rungume shi da dukkan ƙarfin jikinta, tana kuka na ainihi.

“Wallahi Yaya ban tsane ka ba! Don Allah karka ce haka... Ranar da daddynmu ya ce ya ɗaura mana aure, lokacin da muka je ɗaki ina kuka, a lokacin ne fa Mommy ta faɗa mini haka... Amma yanzu sam ba haka ba ne!”

Umar ya ɗago idanunsa da suka riga suka yi luff saboda dabarar ruda ta. Amma sai ya sake canza sautin muryarsa zuwa mai cike da gunji da kishi:

“Ba ni yarda ba... kece kika nuna ba kya sona tun farko. Kuma kece kika sa aka yi wannan maganar... shi ya sanya ta ce za ta raba ki da...”

Kafin ma ya ƙarasa furta kalmar da zai ƙara ɓata mata lissafi, Inteesar ta cire dukkan wata ragowar katanga ta kunya da tsoro da ke tsakaninsu. Ta matso da fuskarta da sauri, ta haɗe bakinta kai tsaye a kan nasa. Ta danne lips ɗinsa gam ta hana shi ƙarasa maganar da yake yi.

Maimakon ta janye, wannan karon sai ta canza salo gaba ɗaya. Ta sa dabarun da ta koya daga gare shi kwanakin nan. Ta fara sarrafa lallausan labansa cikin wani irin zazzafan shauƙi da rarrashin da ya sanya Yaya Umar yin luff gaba ɗaya kamar ba shi ne ke masifa yanzu ba. Ya saki hannunsa daga ƙirjinsa, ya bar shi ya zame daram a kan sofar, yana karɓar kowane sanyayyen sumba da take juyawa a kan lips ɗinsa cikin amincewa.

Inteesar ba ta bar shi ya numfasa ba, kuma ba ta janye ba. Sai da ta tabbatar ta sarrafa shi gaba ɗaya, ta kwance masa dukkan wasu notoci na kansa tsaf, ta bar daukacin jikinsa yana karkarwa da tsimi na musamman a tsakiyar falon.

A hankali Inteesar ta janye bakinta daga nasa, tana haki sama-sama, yayin da dumin numfashinta ke dukan fuskarsa. Idanun Umar sun riga sun kaɗa sun yi ja wur. Sai dai wannan karon ba na fushi ba ne, zallar zazzafan shauƙi ne da kishirwar da ta fara ruruwa a ƙirjinsa.

Bai ba ta damar yin wani tunani ba, kuma bai ba ta damar sauka daga jikinsa ba. Cikin zafin nama ya sa fafadan hannayensa biyu ya ɗage ta cak jikinsa gaba ɗaya. Ya miƙe tsaye daga kan sofar falon. Inteesar ta saki wani ɗan gajeren nishi, ta ƙanƙame wuyansa tsam yayin da yake takawa cikin sassarfa da natsuwa ya nufi master bedroom ɗinsa da ita, yana barin hasken falon ya rage a bayansu.

Suna shiga cikin ɗakin, sanyin AC da daddadan ƙamshin turaren wuta na Oud da ya gauraye da iskar ɗakin suka daki fuskarsu. Cikin dabara ya shimfiɗa ta a tsakiyar lallausan gadon, ya yi rumfa a kanta, yana bin kowane sashe na fuskarta da wani irin kallo mai ratsa tsokar zuciya.

“Jewel...” ya kira sunanta cikin muryar raɗa da ta dishe gaba ɗaya saboda zazzafan yanayi.

“Tunda kika fara bude mini wanann shafin... to yau ba za ki tsira ba. Dole ne ki ƙarasa sauran shafukan gaba ɗaya a nan.”

Inteesar ta ji wani irin abu yana ratsa mata daukacin jijiyoyin jikinta. Wannan karon, dukkan wani shingen kunya sun narke sun bace. Soyayyar Umar da fargabar kalaman Mommy sun rurrita mata wani irin ƙarfin gwiwa da ba ta taɓa sanin tana da shi ba.

Cikin idanuwan da suka yi luff saboda shauƙi, ta sa hannayenta ta fara ɓalle buttons na rigarsa. Ta tura hannunta kai tsaye kan lallausan gashin ƙirjinsa, tana shafawa a hankali.

Ta canza musu position gaba ɗaya cikin salon da ya firgita shi kansa Umar. Ta tura shi baya ya koma ya kwanta daram a kan gadon, sannan ta haye samansa, ta zauna a kan cinyoyinsa.

Umar ya saki wani nannauyan nishi mai zafi gami da lumshe idanunsa. Hannayensa suka sauka a kan cinyoyinta yana matsewa saboda tsananin daɗi.

Inteesar ta sunkuya gaba ɗaya a kan ƙirjinsa. Wannan karon ita ce ke da iko da komai. Ta fara gudanar da zazzafan

34 / 40