Author : Jiddah Barkum Category : Read Hausa Novels
zuciyar Inteesar ba, amma ta yi ƙoƙari, saboda waɗanda suke sonta, saboda kanta, saboda rayuwar da dole ne ta ci gaba.
Bayan sun gama zagayawa Katsina City Park… Humaira ta ja hannun Inteesar, “Intee zo mana, ina son mu ɗauki hoto a wajen fountain.” Inteesar ta ɗan yi murmushi, “ke dai hotuna kawai I think kinada aljanun hoto.” Humaira ta ɗaga gira, “eh mana, idan kika tsufa zan riƙa nuna miki.” Inteesar ta ɗan yi dariya, suka tsaya. Humaira ta miƙa wayarta ga wani matashi da yake tsaye kusa da su, “excuse me… please za ka ɗauka mana picture?” Matashin ya yi murmushi cikin ladabi, “sure.” Ya karɓi wayar, ya ɗaukar musu hotuna da dama. Da yayi daya sai Inteesar ta janye, Humaira is okay mana amma Humaira ta sake janyo ta tana sake canja musu pose. Da ya gama… ya dawo ya miƙa musu wayar. Humaira ta duba, “wow, nagode sosai.” “babu komai,” ya amsa cikin murmushi, ya juya zai tafi, sai kamar ya tuna wani abu, ya sake juyowa, “sorry for interrupting…” idanunsa suka sauka kan Inteesar, “amma… na ga kamar your face looks familiar, kina Nile University ko?” Inteesar ta ji zuciyarta ta buga, nan take… murmushin da ke kan fuskarta ya ɓace, ta matse wayarta, ta ja mataki ɗaya baya ba tare da ta sani ba. Humaira ta lura. Matashin ya ci gaba cikin ladabi, “actually… ina ganin na taɓa ganinki a wani waje cikin Nile university but I can’t remember inane specifically, shi ya sa na tambaya.” Inteesar ta girgiza kai cikin sauri, “…a’a… ka yi kuskure.” Muryarta ta fito ƙasa-ƙasa, ba ta jira ya sake magana ba, ta kama hannun Humaira, “mu tafi.” Humaira ta kalli saurayin, ta yi masa murmushin girmamawa, “thank you.” Suka juya suka fara tafiya, matashin ya tsaya yana kallonsu cikin mamaki, sai kawai ya girgiza kai, ya ci gaba da tafiyarsa…
Bayan sun ɗan yi nisa… Humaira ta kalli Inteesar, “Intee… me ye sa kikace bake bace?” Inteesar ta ci gaba da tafiya, ba ta amsa ba. Humaira ta sake tambaya, “mutumin fa bai yi miki komai ba, kawai ya tambaya ne kamar ya sanki ne meyesa zakice aa.” Inteesar ta tsaya, ta sauke numfashi a hankali, da ƙyar ta ce, “…na sani.” Sai ta haɗiye wani abu mai ɗaci, “…amma yanzu… ina jin tsoro idan wani namiji ya tsaya yana magana da ni.” Humaira ta tsaya cak. Inteesar ta yi murmushi… amma murmushin ya cika da ciwo, “…ba don shi ba… ni ce… har yanzu zuciyata ba ta warke ba.” Humaira ba ta ƙara tambaya ba, kawai… ta kamo hannunta, suka ci gaba da tafiya wajen da suka ajiye mota.
Humaira ta tura ƙofar falon da sallama, “assalamu alaikum…” muryarta ta fito cike da gajiya, “wa alaikumus salam…” Mommy Haleema da Khalil suka amsa a tare. Humaira ta sauke numfashi, “wallahi na gaji.” Kai tsaye ta faɗa kan doguwar kujera, “ni ma.” Inteesar ta bi bayanta, ta zauna tana shafa ƙafunta, yawo da suka yi a Katsina City Park ya nuna aikinsa. Mommy Haleema ta ɗago tana murmushi, “kun dawo kenan?” Humaira ta yi wata irin fuskar wahala, “Mommy, wallahi yau Inteesar ta wahalar da ni.” Inteesar ta zaro ido, “ni?” Humaira ta nuna ta, “eh ke, da farko kin ce ba kya son fita, da muka je kuma… …ke ce kika ce sai mun zagaya park ɗin sau biyu.” Inteesar ta ɗan yi dariya, “ni dai ban tilasta miki ba.” “haba!” Humaira ta buɗe baki, “har ice cream ma sai da kika ce sai mun jira flavour ɗin strawberry.” Inteesar ta yi dariyar da ta sa Mommy Haleema ta ɗan tsaya kallonta, tun bayan makonnin nan… irin wannan dariyar ba ta cika fitowa ba. Khalil kuwa yana zaune yana cin shinkafar da Mommy Haleema ta ajiye masa, ya kalli su yana murmushi, “an sha yawo.” Humaira ta kalleshi, “Yaya Khaly don’t say anything.” Ta faɗa tana turo baki. Khalil ya ɗaga hannayensa, “ni kuma me na yi?” Idanunsa suka sauka kan wata babbar leda da Inteesar ta ajiye kusa da ƙafarta, ya ɗan matsa gaba, “to… bari na ga me kuka siya.” Yana miƙa hannu… cak! Inteesar ta yi saurin janye ledar, ta rungume ta a ƙirjinta, “wallahi ba za ka ci ba.” Khalil ya zaro ido, “ni kuma?” “eh kai.” Mommy Haleema ta ɓoye murmushinta. Khalil ya turo baki, “ni zaku hadewa, kai sabida kunada abun duniya, nima fa a cikinku nake.” Humaira ta yi dariya, “eh, munji a cikin kake amma mai kai rahoto.” Khalil ya haɗe gira, “rahoto kuma?” Inteesar ta ɗago, “da farko ma… da za mu fita… …sai da ka je ka faɗa wa Yaya Abubakar.” Humaira ta amsa da sauri, “exactly!” Inteesar ta kwaikwayi muryar Abubakar daidai yadda yake magana, “Humaira… Inteesar… two hours kacal zan ba ku, duk abin da za ku yi ku dawo gida.” Duk suna fashe da dariya. Humaira ta ɗaga hannu sama, “wallahi na san Khalil ne ya kai mu gaba, yayaya Yaya Abubakar ya san zamu fita bayan baya gidannn.” Khalil ya kama ƙirji, “astaghfirullah, ni? Ni zan kai gulma?” Inteesar ta turo baki, “eh kai, shi ya sa yanzu kuma kake son ka ci abin da muka saya?” Ta girgiza kai, “a’a, punishment ne.” Khalil ya yi dariya, “to me kuka siya ma?” Humaira ta rungume ledar ita ma, “sirri ne, kuma ba za ka sani ba, ko kaɗan.” Khalil ya miƙe daga kujerarsa yana son ƙwace ledar, “in ba haka ba zan bincika da kaina.” Humaira ta yi ihu tana dariya, “Mommyyy! Ga Khalil nan!” Inteesar ta yi saurin tashi tana riƙe da ledar, “wallahi idan ka taɓa ta… …ko chocolate ɗaya ba za ka gani ba.” Khalil ya tsaya yana kallon su, sai ya girgiza kai, “na gane, tun da Inteesar ta fara murmushi… …ni ne first victim.” Falon ya kaure da dariya, har Mommy Haleema ta kasa riƙe nata, ta girgiza kai tana kallon ’ya’yanta, “Allah ya shiryaku.” Inteesar ta kalli Humaira, suka haɗa ido, ba tare da sun shirya ba… suka sake fashewa da dariya. A wannan karon… dariyar ta fito ne daga zuciya. Kuma Mommy Haleema… ta lumshe idanunta a hankali, ta yi shukar godiya cikin ranta, “alhamdulillah… ko da ba ta warke gaba ɗaya ba… ta fara sake koyon yadda ake murmushi.”
Dariyar da ta cika falon ta ɗan lafa a hankali. Khalil ya sake komawa kan plate ɗinsa yana ci yana girgiza kai, “wallahi dai ba zan sake bari ku fita ba, zaku sani ba, dai ni kuka maida munafuki, na daga yanzu ko compound kuka fito sai na faɗa masa.” Humaira ta harare shi, “ka fara tambayar Yaya Abubakar permission tukunna.” Falon ya sake kaurewa da ɗan dariya. A dai-dai lokacin… Shemau ta leƙo daga bakin kitchen, fuskarta ɗauke da murmushi, ta kalli su ɗaya bayan ɗaya, “sannunku da zuwa, yauwa…” Humaira da Inteesar suka amsa a tare. Shemau ta sake cewa, “a kawo muku abinci ne?” Humaira ta dafa cikinta tana dariya, “ni fa… …I am full.” Ta kalli Inteesar, “sai dai ko Intee.” Inteesar ta ɗago ta kalli Shemau, murmushi mai laushi ya bayyana a fuskarta, “wallahi duk mun ƙoshi.” Ta ɗan yi shiru kafin ta ƙara da cewa, “maybe anjima kafin mu kwanta za mu ci, thank you.” Ta ƙarasa cikin murmushi. Shemau ta gyada kai cikin jin daɗi, “toh shi kenan.” Shemau ta yi musu murmushi kafin ta juya ta koma kitchen. Mommy Haleema ta bi bayanta da kallo, sannan idanunta suka dawo kan Inteesar, ta tsaya tana kallon murmushin da ke kan fuskar ɗiyarta, ba shi da faɗi kamar na da, amma… ya fi shiru da kuka. A zuciyarta ta yi addu’a a hankali, “ya Allah… kamar yadda ka fara dawo mini da murmushinta… ka gama warkar da zuciyarta.”
Mommy Haleema ta ci gaba da kallon Inteesar cikin murmushi, sai ta ɗan gyara zamanta kafin ta ce, “daughter.” Inteesar ta ɗago kanta, “na’am Mommy.” Mommy Haleema ta yi murmushi, “Nana ta kira Daddy ɗazu.” Humaira ta juya tana kallonta, “me take cewa?” Mommy Haleema ta ci gaba, “tana neman izini… …ki je ki ɗan zauna da ita na wasu kwanaki.” Inteesar tayi murmushi. Mommy Haleema ta gyada kai, “kin san ta shiga watan haihuwa, ko wani lokaci naƙuda na iya kamata, shi ya sa take son ta samu wani a kusa da ita.” Humaira ta yi murmushi. Mommy Haleema ta ci gaba, “da farko ma… Umar ya ce kawai ta dawo gida ta haihu, sabida shima yana fita office, kada ya bar ta ita kaɗai duk da Maryam tana zuwa kullum.” Sai ta yi ɗan murmushi, “amma ai kun san Abba.” Humaira ta yi dariya, “eh mana, ba zai yarda ba.” Mommy Haleema ta gyada kai, “haka ya ce, gwamma ta haihu a gidanta, mijinta yana tare da ita, saidai a samu wanda zai je.” Da aka faɗa mata abinda abbanta yace… “sai ta ce… …idan Inteesar za ta zo ta ɗan zauna da ita… zata fi son haka.” Inteesar ta yi shiru, wani irin taushi ya ratsa zuciyarta, Nana… tun bayan abin da ya faru… ba su samu damar zama tare ba, ba ta son su yi wata magana da zata daga mata hankali ga ciki a jikinta. Humaira ta yi saurin cewa, “wallahi Mommy ta je, hakan ma zai ɗan sauya mata yanayi.” Khalil ya amsa da sauri, “ni ma haka nake gani, can za ta samu abin da zai ɗan ɗebe mata kewa.” Mommy Haleema ta sake kallon Inteesar, “ni dai na ce na faɗa miki, amma… Daddy ma yace ki je kawai.” Inteesar ta yi shiru na wasu daƙiƙu, sai ta ɗan yi murmushi, “ni ba damuwa Mommy, zan je.” Mommy Haleema ta sauke numfashi cikin jin daɗi, “Allah ya miki albarka.” Humaira kuwa ta yi tsalle daga inda take zaune, “yesss!” sai ta rungumi Inteesar, “wallahi na san Yaya Nana za ta yi murna sosai, duk ta fi sonki a kusa da ita.” Inteesar ta yi dariya a hankali, “ke ma ai za ki zo.” Humaira ta ɗan ɗaga gira, “to ai dole, a na buga waya ta haihu zamu taho Abuja, no time to waste aiii.” Falon ya sake cika da annashuwa, ba wanda ya lura… cewa a karon farko cikin makonni uku… Inteesar ta yi dariya ba tare da tilasta kanta ba. Kuma a zuciyar Mommy Haleema… ta yi fatan wannan tafiyar zuwa wajen Nana… za ta zama wata sabuwar ƙofa ta cikakkiyar warkewar ɗiyarta.
Daren ranar… bayan Mommy Haleema ta gaya wa Inteesar maganar tafiya Abuja… gidan ya yi shiru, ɗaya bayan ɗaya… kowa ya nufi ɗakinsa domin hutawa. A ɗakin Inteesar kuwa… hasken fitilun ɗakin ya cika ko ina, suitcase ɗinta yana buɗe a gefen gado, Humaira ce ke ta saka mata kaya cikin tsari, wani lokaci ta naɗe hijabi, wani lokaci ta gyara wata rigar. Inteesar kuwa… tun da suka shigo ɗakin… ba ta yi magana sosai ba, zaune take a bakin gadonta, ta jingina bayanta da headboard, idanunta suna kallon wani wuri… amma ba da gaske take ganin abin da ke gabanta ba, tunani take, tunani mai nauyi, tunani da ya daɗe yana cinye zuciyarta. Wayarta tana gefenta, screen ɗinta ya sake haskawa, number ce da ba suna. Wayar ta fara ringing, Inteesar ba ta ko kalli screen ɗin ba, kamar ba ita ake kira ba, ta yi shiru, har kiran ya katse. Bayan wasu daƙiƙu… sai ya sake shigowa, wayar ta sake ringing, har yanzu… ba ta motsa ba. Humaira ta ɗaga kai daga inda take shirya kaya, ta lura… ba wannan ne karo na farko ba. A hankali ta taso, ta ƙaraso bakin gadon, da ta ga yadda Inteesar ta yi nisa cikin tunani… a hankali… ta dafa kafaɗarta, “Intee…” Inteesar ta firgita, kamar wacce aka taso daga mafarki, ta ɗago kai da sauri. Kafin Humaira ta ce komai… Inteesar ta yi maza ta share hawayen da ba ta ma san suna zuba ba. Humaira ta tsaya tana kallonta, ta lura… ba sabon kuka ba ne, tun da daɗewa take yi, sai dai yau ne ta gan shi. Cikin sanyin murya ta ce, “…tunaninsa kike yi ko?” Inteesar ta lumshe idanunta, ta sauke kanta ƙasa, ba ta ce komai ba, shirunta… shi ne amsar. Humaira ta sauke numfashi, sai ta ɗauki wayar daga gefen gadon, ta nuna mata screen ɗin, “gashi nan… an sake kira.” Inteesar ko kallon wayar ba ta yi ba, ta girgiza kai kaɗan, “…ba zan ɗauka ba.” Humaira tayi silencing, sai ta maida wayar kan gadon, ta zauna kusa da Inteesar. Na wasu daƙiƙu… ba ta yi magana ba, sai ta tambaya cikin murya ƙasa-ƙasa, “to… me ya sa ba ki yi blocking ɗinsa ba?” Inteesar ta ci gaba da kallon ƙasa, ta yi shiru, ba ta ba da amsa ba. Humaira ta ɗan matsa kusa da ita, muryarta ta ƙara yin laushi, kusan rada take, “…har yanzu kina sonsa ko?” Kalmar… ta karya katangar da Inteesar take ƙoƙarin ginawa tun kwanaki. Numfashinta ya rikice, leɓunanta suka fara rawa, ta yi ƙoƙarin haɗiye kukanta, amma ta kasa. A hankali… ta jinjina kai, sau ɗaya, sai hawaye suka fara zubo mata ɗaya bayan ɗaya. Da ƙyar ta buɗe baki, muryarta ta fito a raunane, “…ban sani ba…” ta tsaya, ta rufe idanunta, sabbin hawaye suka sake gangaro mata, “…ban san ta yaya zan daina sonsa ba.” Kalmar ta fito ne da wata irin karyewar zuciya, “…na yi ƙoƙari…” ta dafe ƙirjinta, “…wallahi na yi ƙoƙari… ina gaya wa kaina kullum… …cewa bai cancance ni ba.” Ta girgiza kai cikin kuka, “…amma idan na kwanta… …sai na tuna shi… idan na tashi… …sai na tuna shi… idan wayata ta yi ringing… …zuciyata sai ta yi fatan… …shi ne…” ta yi saurin girgiza kai, “…sai kuma na tuna… …abubuwan da ya faɗa… …sai zuciyata ta sake karyewa.” Ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta, kukanta ya ƙwace mata gaba ɗaya, “…na gaji Humaira… …na gaji… …ina son in daina sonsa… …amma ban san yadda ake yi ba.” Humaira ta ji hawaye sun cika mata ido, ba ta ce komai ba, domin ta san… akwai ciwukan da kalmomi ba sa iya warkarwa. A hankali… ta matsa kusa da Inteesar, ta rungume ta sosai, ta bar ta tana kuka a kafaɗarta, ta bar ta tana zubar da duk abin da zuciyarta ta daɗe tana riƙewa. Cikin ɗakin… yayi shiru baa jin komai, sai sautin kukan Inteesar… da kuma hannun Humaira… da ke shafa bayanta cikin shiru.
Shiru ya sake mamaye dakin, Humaira har yanzu tana rungume da Inteesar, kukan da ya daɗe yana taruwa a zuciyarta… da alama ya ɗan sauka, sai dai ciwon… har yanzu yana nan. Bayan wasu mintuna… a hankali Inteesar ta ɗago kanta daga kafaɗar Humaira, idanunta sun kumbura, fuskarta ta yi ja saboda yawan kuka, ba ta ce komai ba, kawai… ta share hawayen da suka rage a fuskarta da bayan hannunta, sai ta miƙe tsaye cikin nutsuwa. Humaira ta bi ta da ido, kai tsaye… ta nufi bathroom, ƙofar ta rufe a hankali. Humaira ta ci gaba da kallon ƙofar, ta sauke wani dogon numfashi, ta jingina bayanta da headboard ɗin gadon, ta lumshe idanunta, “ya Allah… ka sauƙaƙa mata.”
Kusan mintuna ashirin bayan haka… ƙofar bathroom ta buɗe, Inteesar ta fito, towel fari ne a ɗaure a jikinta, ruwan da ta yi wanka da shi har yanzu yana sauka daga gashinta zuwa kafaɗunta, fuskarta ta yi sanyi, amma ba sanyi irin na farin ciki ba, sanyi irin na mutum da ya yi kuka har ya gaji. Ba tare da ta ce uffan ba… ta ƙarasa gaban wardrobe, ta buɗe shi a hankali, ta ɗauko doguwar rigar baccinta mai launin royal blue, ta sa ta cikin nutsuwa, sannan ta ɗauko hula mai laushi, ta rufe kanta, ta ƙarasa gaban mirror ta shafa turare kaɗan. Da ta gama… ta kashe babban hasken ɗakin, sai bedside lamp kaɗai ya rage yana haskawa da ɗan haske mai laushi. A hankali… ta ƙarasa bakin gadonta, ta ɗaga duvet, ta shige cikinsa, ta kwanta ta juya gefe, ta lumshe idanunta, sai leɓunanta suka fara motsi cikin sanyi, ta fara karanta addu’ar kwanciya, “bismika Allahumma amūtu wa aḥyā…” muryarta ba ta fita sosai ba, sai dai kowace kalma… ta fito ne daga zuciyar da ta gaji. Da ta gama… ta ɗan buɗe idanunta, ta kalli ceiling na ɗan lokaci, sai ta lumshe su a hankali. A karo na farko cikin daren… ba hawaye ne suka sauko ba, sai wata doguwar ajiyar zuciya. Humaira da ke kwance a ɗayan gefen gadon… ta juya ta kalle ta, ta tabbatar Inteesar ta yi barci ne kawai saboda gajiya… ba don zuciyarta ta samu salama ba. Humaira ta kashe bedside lamp ɗin, dukkan ɗakin ya nutse cikin duhu, sai yayyafar ruwan saman da ake yi a waje… da kuma shiru… mai cike da abubuwan da ba a faɗa ba.
*KADDARAR ZUCIYA*
*CHAPTER SIXTY-NINE: 69*
*A STEP FORWARD*
*JIDDAH BARKUM*
Wayewar garin ta zo cikin wani irin nutsuwa, yayyafin ruwan saman da aka yi cikin daren jiya ya bar iska mai sanyi tana ratsa bishiyoyin gidan Alhaji Kabeeru, komai ya yi tsaf. Tsuntsaye na ta ƙananan waƙoƙinsu daga saman bishiyoyi, harabar gidan kuma ta kasance cikin natsuwa irin ta safiyar Lahadi…
A ɗakin Inteesar kuwa… ta riga ta gama shiryawa. Sanye take cikin wata kyakkyawar baƙar designer abaya mai yalwar gaske, wadda aka kawata da duwatsu masu ƙyalli na Swarovski a gefen hannaye da bakin mayafinta, da zarar hasken ya bugi kayan, ƙananan duwatsun suna kyalli cikin nutsuwa ba tare da hayaniya ba. Veil ɗinta baƙi ne mai laushi, an naɗe shi cikin tsari irin yanda matan larabawa ke nade mayafi. Turaren da ta shafa yana ƙamshi a hankali, ba mai yawa ba… sai dai irin ƙamshin da yake bayyana tsafta da nutsuwa. Ta tsaya a gaban mirror na wasu daƙiƙu, ta kalli kanta, sannan… a hankali… ta yi murmushi. Ba murmushin farin ciki ba, ba murmushin warkewa ba, murmushi ne da take koyawa kanta, domin Daddy, domin Mommy, domin waɗanda suke rayuwa cikin damuwa saboda ita. A