Kaddarar Zuciya Book 2 Complete JIddah Barkum

Author :  Jiddah Barkum Category :  Read Hausa Novels

Chapter   38 / 40

111K to 114K   out of 117.5K words

na kare lafiyarku gaba ɗayanku.”

Haka zaman gidan ya ci gaba da kasancewa cike da tsaftatacciyar soyayya, kulawa, da barkwanci tsakanin Yaya Umar da Inteesar. Kulawar da yake mata ta zame mata wata sabuwar fitila da ke ƙara haskaka zamantakewarsu.

Sorry for the typos not edited

*KADDARAR ZUCIYA*

*CHAPTER ONE HUNDRED: 100*

*THE GREATEST LOST*

*JIDDAAH BARKUM*

———

Bayan labarin cikin Inteesar ya tabbata, rayuwarsu ta sake ɗaukar wani sabon salo mai cike da tsaftatacciyar soyayya, tattali, da zallar ƙauna. A wannan karon kuwa, kulawar da Yaya Umar yake ba ta zarce komai da kowa ya sani a baya.

To amma fa, laulayin cikin ya fara tsananta matuƙa.

Tun daga safe har dare, Inteesar ke cikin jiki ba lallai ba. Wani lokacin ko ruwa ba ta iya sha sai ya fito. Abincin da take so da safe, idan yamma ta yi ko ƙamshinsa ba ta iya jurewa. Wani lokacin kuma, ba zato ba tsammani sai ta nemi wani abu na daban gaba ɗaya.

Da zarar ta ce tana so, ko dare ne, ko ruwan sama ake yi kamar za a fasa sama, Yaya Umar zai fita ya nemo mata. Saboda shi, ba ya kallon wahalar da zai sha ko kadan. Abin da yake gani kawai shi ne lafiyar matarsa da jaririnsu.

Sai dai, akwai wani abu guda ɗaya da Inteesar ba ta sani ba.

Duk lokacin da Umar ya ga tana amai, ko kuma ta rame saboda laulayi, zuciyarsa sai ta koma shekaru baya. Sai ya tuna da Nana, ya tuna da ranar da ta rasa ranta sakamakon matsalar ciki. Tunawa da wannan rana shi ne babban abin da yake ƙara dagula masa hankali da haifar masa da matsananciyar fargaba.

Saboda haka, ko office ma ya daina zuwa yadda ya saba. Ya ɗauki hutu ya mayar da hankalinsa gaba ɗaya kan Inteesar.

Kusan kullum yana gida tare da ita. Shi yake mata komai, shi yake lallashinta ta ci wani abu ko da kaɗan ne, kuma shi yake zama kusa da ita idan ta kasa barci. Wani lokacin ma sai ya zauna yana kallonta kawai, yana gode wa Allah cikin zuciyarsa, yana kuma roƙonsa kada ya sake gwada shi da wani irin ciwon rabuwa.

Cikin ikon Allah, bayan watanni suka ci gaba da ja, laulayin ya fara raguwa a hankali. Inteesar ta fara samun sauƙi, fuskarta ta sake yin haske, murmushinta ya fara dawowa, cikinta kuma ya ci gaba da girma cikin ƙoshin lafiya, har zuwa lokacin da ya kai watanni takwas cif.

A daidai wannan lokacin ne aka fara gudanar da shirye-shiryen bikin Humaira da Yaya Abubakar.

Wata rana da yamma, suna zaune a falon gidansu. Inteesar tana kwance rabin jikinta a kan lallausar kujerar sofa, Yaya Umar kuwa yana zaune kusa da ita. Ya zuba gyaɗa cikin ƙaramin bowl, yana barewa yana saka mata a baki ɗaya bayan ɗaya, ita kuma tana ci cikin kasala.

Can sai ta yi wani dogon ajiyar zuciya, ta turo baki gaba tare da yin ƙwafa. “Hmm!”

Umar ya ɗago ya kalle ta. “Lafiya kuwa, Jewel?”

Ta sake yin wata ƙwafar. “Wallahi ba lafiya ba.”

Ya ɗan matsa kusa da ita cikin kulawa. “Me ya faru kuma?”

Ta nuna cikinta. “Sai su yi aure yanzu?”

Umar ya ɗaga gira guda. “Hmm?”

“Ɗan Allah...” ta sake turo baki, “…ba za su iya jira na haihu ba ne?”

Umar ya kasa magana saboda mamaki, ita kuwa ta ci gaba: “Duk abin da za a yi, sai a yi bayan na haihu mana.”

Umar ya haɗe gira yana ƙoƙarin danne dariyar da ke cin sa. “Me ya sa?”

Ta zaro ido gaba ɗaya. “Me ya sa?”

Ta nuna fuskarta. “Kalli hancina fa!” sai ta dafa hancinta. “Ya kumbura!” Ta kuma shafa kumatunta. “Ga fuskata...” Ta nuna cikinta. “Ga wannan babban cikin! Ta ina zan yi kyau a bikin?” ta ƙarasa maganar kamar za ta fashe da kuka.

Umar bai ƙara jurewa ba, sai ya fashe da wata dariya sosai mai fitowa daga ciki.

Inteesar ta zuba masa ido cike da mamaki. “Yayaaa!”

Ya ci gaba da dariyar yana gyara zamansa.

Ta fara shagwaɓa gaba ɗaya. “Ka daina dariya mana! Ni da gaske nake yi!”

Ya dafe cikinsa saboda dariya. “Wai kina nufin, su fasa aurensu saboda ke?”

Ta turo baki. “Eh mana! Su jira ni. Ni ma ina son na yi kyau, ba zan je da wannan hancin ba!”

Umar ya sake fashewa da dariya har sai da hawayen dariya suka cika masa ido. Inteesar kuwa ta fara ƙoƙarin kuka na gaske.

Da sauri Umar ya matsa kusa da ita, ya jawota cikin jikinsa ya rungume ta sosai. “Sorry...” ya sumbaci goshinta. “Sorry, my wife.”

Ta ci gaba da turo baki tana lafe jiki. Bai sake dariya ba, ya ɗaga haɓarta cikin taushi.

“Listen to me, Jewel.”

Ta kalle shi da idanunta da suka targaɗe da ƙwalla.

“Yanzu saboda ke, sai Humaira da Abubakar su fasa aure har sai kin haihu?”

Ta yi shiru tana kallo.

Ya yi murmushi mai matukar sanyi da kashe jiki. “My stubborn wife... ki yi haƙuri, kin ji? Fatanmu kawai Allah Ya sauke ki lafiya. In yaso idan ya haihu sai kiyi wani biki da kike so.”

Inteesar ta yi shiru na wasu daƙiƙu, daga ƙarshe sai ta lafa a ƙirjinsa ta sauke nauyaya ajiyar zuciya. “To... amma fa, idan na fito ban yi kyau ba, laifinka ne.”

Umar ya yi dariya a hankali, ya sumbaci goshinta guda. “Wallahi ke ko yaushe kina da kyau. Kuma a wurina, ba wata mace da taɓa yin kyau kamar Jewel ɗina.”

Nan take kunyarta ta bayyana, ta ɓoye fuskarta a faɗaɗen ƙirjinsa. Shi kuma ya ƙara rungume ta tsam, yana shafa bayanta cikin taushi. A zuciyarsa kuwa, yana ci gaba da gode wa Allah, saboda duk wata wahala da take sha a cikinsu na yanzu, ya san ƙarshenta zai kasance zallar farin ciki da albarka ne.

*A cikin haka kuwa...*

Lokacin biki ya sake matsowa. Saura kwana uku kacal a ɗaura auren Humaira da Yaya Abubakar.

Saboda haka, Umar da Inteesar suka tattara kayansu suka koma Katsina domin halartar bikin.

Tun kafin su isa gidan Alhaji Kabeeru, gidan ya riga ya ɗauki harama. Dangin nesa da na kusa sun fara saukowa ɗaya bayan ɗaya. Kusan babu ɗakin da ba a cika da baƙi ba.

Hayaniyar yara, kamshin girki, dariyar mata, da shirye-shiryen biki, su ne suka mamaye gidan gaba ɗaya.

Duk wanda ya ga Inteesar, sai ya tsaya yana kallonta da murmushi. Kowa yana yi mata addu’a. Wasu ma har tausayi suke ji saboda girman cikin da ke jikinta. Cikinta ya yi girma sosai, har idan mutum bai sani ba sai ya rantse yara biyu ne ke cikinsa. Alhali guda ɗaya ne.

Saboda yawan baƙi, Inteesar ma ba ta samu damar sauka a tsohon ɗakinta ba. Ita da Umar aka ware musu wani ɗaki daban domin samun nutsuwa.

*...*

Ana gobe za a fara shagulgulan bikin. Inteesar tana tsaye gaban madubi. A jikinta ɗaya daga cikin dogayen gowns ɗin da aka ɗinka mata ne na shirin biki. Ta juya dama, ta juya hagu, sai ta haɗe fuska.

“Ka kalla mana, Yaya Umar,” ta faɗa tana banka masa harara ta cikin madubin.

“Kalli yadda gown ɗin nan ya matse ni.” Ta dafa cikinta. “Wallahi idan na fita da wannan, mutane dariya za su yi min.”

Umar, wanda yake zaune yana duba waya, ya ɗago kai. Ya kalleta na wasu daƙiƙu, sai ya ajiye wayar gaba ɗaya. Ya miƙe. A hankali ya ƙaraso bayanta. Ba tare da ya ce komai ba, ya zagaye ta da hannayensa biyu. Ya rungume cikinta daga baya, sannan ya ɗora haɓarsa a kafaɗarta. Su biyun suka haɗa ido ta cikin madubin.

“Wayye zai miki dariya, Jewel?” ya tambaya cikin sanyin murya. “Ba dai a cikin gidan nan ba, bare kuma a wajen bikin.”

Inteesar ta ci gaba da turo baki.

Ya yi murmushi. “Babu wata mace da ta fi matata kyau a duk wajen taron nan.” Ya shafa cikinta cikin taushi. “Kuma wannan cikin, ba ya rage miki kyau. Sai ma ya ƙara fito da kwarjini da annurin da Allah Ya ba ki.”

Inteesar ta yi ƙoƙarin kau da kanta. “Rai kake son kashe min zuciya da kalaman nan.” ta faɗa cikin shagwaɓa. “Saboda ka san idan ka fara faɗa min irin waɗannan maganganun, ba zan iya ci gaba da faɗa da kai ba.”

Umar ya yi dariya a hankali. “Saboda gaskiya nake faɗa miki, My Wife.” Ya sunkuya ya sumbaci kuncinta.

“Yanzu dai, ki cire kayan nan. Ki huta. Na riga na haɗa miki ruwan wanka mai ɗumi.”

Inteesar ta kalle shi ta yi murmushi. “Wai kai yaushe ka zama nurse ne?”

Ya ɗaga gira. “Tun ranar da aka ce kina ɗauke da Little Miracle.”

Dukansu suka yi dariya.

*Washegari...*

Ranar ɗaurin auren Humaira da Yaya Abubakar ta waye cikin annashuwa. Tun safe gidan ya cika da mutane. Baƙi daga sassa daban-daban, ’yan uwa, abokan arziki, da maƙwabta. Kowa yana ta hidimar da ta dace da shi. Mata na ta kai-komo, maza na karɓar baƙi. Yara kuwa, sun mamaye ko’ina da gudu da dariya.

Ko da yake Umar ya hana Inteesar shiga kowace irin wahala, bai hana ta zama tare da mata ba. Inda take zaune, sai ta zama kamar sarauniya. Kowa na zuwa ya gaishe ta. Ana yi mata addu’a, ana mata fatan sauƙin haihuwa.

“Allah Ya sauke ki lafiya.”

“Ameen.”

“Allah Ya ba ki haihuwa mai albarka.”

“Ameen.”

Inteesar kuwa, murmushi kawai take yi. Tana amsa addu’o’in da zuciya ɗaya.

*Alhamdulillah...*

An ɗaura auren Humaira da Yaya Abubakar lafiya. An gudanar da dukkan al’adun bikin cikin farin ciki. Komai ya tafi yadda aka tsara.

*Da dare...*

Bayan baƙi sun fara watsewa, Umar ya dawo gida. A gajiye yake, amma farin cikin da ke kan fuskarsa ya fi gajiyar da ya yi.

Da ya shiga dakin, sai ya tsaya. Inteesar ce kwance a kan doguwar kujera. Ta naɗe ƙafafunta, ta jingina bayanta. Alamar gajiya ta bayyana ƙarara a fuskarta.

Ba tare da ya ce komai ba, ya ƙarasa kusa da ita. Ya zauna a ƙasa. A hankali ya ɗaga ƙafafunta, ya ɗora su a kan cinyarsa, sannan ya fara matsa mata su cikin taushi.

“Sannu da ƙoƙari, Jewel,” ya faɗa yana kallonta. “Na san kin gaji sosai.”

Inteesar ta buɗe idanunta kaɗan. Ta yi murmushi. “Na gaji sosai.” Ta sauke numfashi. “Amma, na yi farin ciki. Alhamdulillah. Allah Ya nuna mana ranar.”

Ta ɗan yi shiru. Sannan ta ce, “Allah Ya ba Humaira da Yaya Abubakar zaman lafiya, da zuri’a ɗayyiba.”

“Ameen.” Umar ya amsa cikin nutsuwa. “Ameen summa Ameen.”

Ya shafa cikinta a hankali ya yi murmushi. “Yanzu kuma, mu ne muke jiran namu albishir.”

Inteesar ta sauke hannunta a kan nasa. Ta haɗa yatsunsu, ta lumshe idanunta cikin nutsuwa. A hankali ta ce, “In Sha Allah, Allah Ya ƙara mana lafiya.”

Umar ya sunkuya ya sumbaci goshinta. “Ameen, My Jewel. Allah Ya nuna mana ranar cikin farin ciki, ba tare da wata damuwa ba.”

Dakin ya yi shiru. Sai sanyin AC da bugun zuciyoyi biyu masu jiran zuwan ƙaramin baƙonsu. Ba su san cewa kaddara tana shirin sake buɗe musu wani sabon shafi na rayuwa ba.

*Daren ranar ya yi tsit.*

Hayaniyar bikin da ta mamaye gidan tun safe ta lafa gaba ɗaya. Ba a jin komai sai sanyin iska da ke ratsawa ta labulen ɗakin da kuma sautin AC mai laushi.

Sai dai, Inteesar sam ta kasa samun barci. Ko da ta lumshe idanunta, sai ta sake buɗewa. Wani irin tsoro ne da ba ta san dalilinsa ba ya mamaye zuciyarta. Gabanta na ta faɗuwa.

Ta juya a hankali, sai ta sake juyawa. A ƙarshe, sai ta firgita ba zato ba tsammani.

Yaya Umar, wanda ke rungume da ita cikin barci, ya farka a gigice.

“Jewel...” ya kira cikin damuwa. “Lafiya kuwa?”

Inteesar ta kalli fuskarsa. Idanunta sun cika da damuwa. A hankali ta girgiza kai.

“Ban sani ba, Yayaaa.”

Ya ɗago ya jingina da headboard ɗin gadon. “Me kike ji?”

Ta sauke numfashi. “Na kasa barci. Kuma... gabana yana ta faɗuwa. Wallahi ban san me yake damuna ba.”

Umar ya ji zuciyarsa ta ƙara bugawa. Sai dai bai nuna mata ba. Ya matsa kusa da ita, ya kamo hannunta. Ya fara tofa mata addu’o’in kariya.

“A’udhu bi kalimatillahit-tammati min sharri ma khalaq...” ya ci gaba da karanta ayoyin kariya cikin nutsuwa.

Inteesar ta lumshe idanunta tana sauraren muryarsa. Wata irin nutsuwa ta fara sauka a zuciyarta.

Ya yi tunanin ya ce ta tashi su yi nafila. Amma da ya tuna yadda ƙafafunta suka kumbura tun da yamma, da kuma irin gajiyar da ta sha a bikin, sai ya fasa. Maimakon haka, ya ce cikin sanyin murya,

“Ki ci gaba da yin addu’a. Ki yawaita istigfari. Allah ba Ya taɓa wulakanta bawan da Ya dogara da Shi.”

Inteesar ta gyada kai. “To.”

Sai suka yi shiru. Ita tana ta addu’a a hankali. Shi kuma yana ci gaba da tofa mata addu’a.

Can, ba tare da ta ankara ba, barci ya ɗauke ta. Umar ya sauke numfashi. Ya shafa kanta a hankali. Sai shi ma barci ya ɗauke shi.

*Da misalin ƙarfe uku na dare...*

Akayi Knocking dakin. Ya buɗe idanunsa a hankali. Da farko ya yi tunanin mafarki yake yi. Sai aka sake bugun ƙofar. A wannan karon da ɗan ƙarfi.

Umar ya juya ya kalli Inteesar. Barcinta ya yi nisa. A hankali ya zare jikinsa daga nata. Ya gyara mata pillow. Ya lulluɓe ta da duvet sosai. Ya tabbatar ba ta farka ba. Sai ya ɗauko farar jallabiyarsa ya saka cikin gaggawa, ya nufi ƙofar.

Da ya buɗe, Mommy Haleema ce tsaye a wajen. Fuskarta ta canza gaba ɗaya. Idanunta cike da firgici. Numfashinta na fita da ƙyar.

Da ta ga Umar, sai ta yi magana cikin ƙasa-ƙasa don kada Inteesar ta ji.

“Umar... Daddynku ne, ya faɗi a toilet.” Muryarta ta karye.

“Ka yi maza. Mu kai shi asibiti. Kuma...” ta kalli cikin ɗakin, “kar Princess ta ji. Don Allah, kar ka tashe ta yanzu.”

Amma kafin ta ƙarasa maganar, tuni Umar ya wuce ta da gudu. Hankalinsa ya tashi gaba ɗaya. Ya nufi ɓangaren Daddy da sauri.

*A gigice...*

Umar ya ƙarasa ɓangaren Daddy. Da ya shiga toilet ɗin, sai gabansa ya faɗi.

Alhaji Kabeeru ne kwance a ƙasa. Jikinsa ya yi sanyi. Idanunsa a lumshe. Ko motsi ba ya yi. Ko numfashinsa ma da ƙyar ake iya hangowa.

“Daddy!” Umar ya kira cikin firgici yana durƙusawa a gabansa. Ya girgiza shi a hankali. “Daddy... Daddy!”

Shiru. Babu amsa.

Hannunsa ya kai kan bugun zuciyarsa. Yana jin bugun, amma a raunane. Ba tare da ya ƙara ɓata lokaci ba, ya sunkuya ya ɗauke Daddy a kafaɗarsa. Duk da nauyin jikinsa, ko kaɗan bai ji ba saboda tashin hankalin da yake ciki.

Da sauri ya fito da shi daga cikin gidan.

Mommy Haleema kuwa, tuni ta fito tana kuka. Ta ɗauko key ɗin mota. “Hanzarta Umar!” ta faɗa cikin rawar murya. “Kada mu ɓata lokaci.”

Ya gyada kai. Ya nufi compound cikin sauri. Da ya isa, sai ya ɗora Daddy a kujerar baya ta motarsa cikin kulawa.

A daidai lokacin kuma, Mommy Haleema ta juya da gudu zuwa ɓangaren da mazan gidan suka sauka. Ta dinga bugun ƙofar cikin tashin hankali.

“Adam! Salim! Ku buɗe ƙofa! Da sauri!”

Ba a jima ba, ƙofar ta buɗe. Yaya Adam ya fito da sauri, fuskarsa cike da damuwa.

“Mommy, lafiya?”

Hawaye suka cika idanunta. “Daddynku... ya faɗi.”

Kalmar kawai ta isa. Babu wanda ya ƙara tambayar wani abu.

Salim ya fito a guje. Faruq ma ya fito. A daidai lokacin, Abdul suka fito daga ɗakinsu. Jaafar da Alamin ma suka fito cikin firgici. Khalil kuwa, da ya zo bikin daga France, shima yana cikin gidan. Ya fito yana sa rigarsa cikin gaggawa.

“Wai me ya faru?”

Adam ya juya gare su. “Daddy ne. Mu tafi yanzu.”

Nan take, kowa ya watse. Wasu suka nufi motocinsu, wasu suka shiga motar Umar. Babu wanda ya sake magana. Sai tashin hankali, da kuma addu’o’in da suke yi a zuciyarsu.

Mommy Haleema ta zauna kusa da Alhaji Kabeeru tana riƙe da hannunsa. Hawayenta na zuba ba tare da ta sani ba.

“Ya Allah, kada Ka ɗauke mini shi. Kada Ka bar Princess ta tashi ta tarar da wannan labarin.”

Umar ya tada motar cikin sauri. Adam ya bi bayansu da tasa motar. Sauran yayyen ma suka biyo a baya.

Cikin dare, jerin motocin ya fice daga gidan Alhaji Kabeeru da gudu. Kowa cikin tashin hankali. Kowa cikin addu’a. Kuma zuciyar kowa tana roƙon Allah abu ɗaya ne kawai, Allah Ya ceci shugaban gidansu kafin su isa asibiti.

*Da ƙarfe biyar saura na asubah...*

Ƙofar Emergency ta buɗe a hankali. Likitan da ya fito, fuskarsa babu walwala. Fuskarsa cike take da gajiya da kuma wani irin tausayin da ba ya buƙatar fassara.

Kafin ma ya yi magana, duk wanda yake tsaye a wajen ya miƙe. Yaya Abubakar ma anyi waya dashi ya zo. Kowa ya tashi lokaci guda. Idanunsu suna kallon likitan kamar suna jiran ya ce musu komai zai yi kyau.

Likitan ya sauke numfashi. Sannan ya ce cikin sanyin murya,

“…I’m so sorry.”

Kalmar ta tsaya a iska. Babu wanda ya fahimta nan take.

Sai ya ƙara da cewa, “We did everything we could, but we lost him.”

Shiru. Wani irin shiru. Kamar duniya ta tsaya. Kamar lokaci ya daina tafiya.

Umar ya zuba masa ido. “Doctor... me kake nufi?” Muryarsa ta yi rauni.

Likitan ya runtse idanunsa na ɗan lokaci. “Allah Ya yi masa rasuwa.”

Kalmar ta sauka kamar wata babbar dutse.

“A’a!” Mommy Haleema ta yi ihu. Ta dafe ƙirjinta. “Karya kake! Alhaji! Alhaji!!”

Ta ruga zuwa ƙofar Emergency. Nurses suka yi saurin tare ta. Ta fashe da kuka. Kukan da ya fito daga cikin zuciya.

“Ka bar ni in gan shi! Alhaji!!”

Adam ya dafe bango. Ƙafafunsa suka kasa ɗaukar nauyinsa. Ya zame ya zauna a ƙasa. Idanunsa suka cika da hawaye. Mutumin da bai saba kuka ba, sai hawaye suka fara saukowa a fuskarsa.

Abubakar ya juya baya. Ya dafe bakinsa. Kukansa ya ƙi fitowa. Sai jikinsa

38 / 40