Kaddarar Zuciya Book 2 Complete JIddah Barkum

Author :  Jiddah Barkum Category :  Read Hausa Novels

Chapter   10 / 40

27K to 30K   out of 117.5K words

gida… baby zai riƙa kwana a ɗakina… ke kuma ki riƙa hutawa a naki…” ta sake fashewa da kuka, ta share hawayenta da hannayenta biyu, sannan ta kalli fuskar Nana, da wata irin murya mai karya zuciya ta ce, “kinga ko… sun saka miki likkafani, so suke su tafi da ke, so suke su binne ki. ki tashi mana… ki gaya musu ba ki mutu ba… Yaya Nana… don Allah… ki buɗe ido…”

Amma… ba amsa, ba motsi, ba numfashi, sai shiru, shirun da ya tabbatar da cewa… Nana ta riga ta amsa kiran Mahaliccinta. Duk wanda yake cikin ɗakin… hawaye kawai yake yi, ko mazan da suke bakin ɗakin suna jiran su ɗauketa… sun kasa ɓoye nasu. A wannan lokacin ne… Yaya Abubakar ya shigo, da ƙyar ya buɗe baki, “an gama…” ya faɗa cikin sanyin murya, “a fito da ita.” kalmar ta sauka kamar an jefa dutse a cikin zuciyar kowa.

Inteesar ta ƙara rungume Nana, ta sake fashewa da kuka, “don Allah… kada ku tafi da ita… kada ku rufe min ita.” Yaya Abubakar ya lumshe idanunsa, ya ƙarasa wajen Umar, ya kamo hannunsa, a hankali… ya ɗaga shi daga gaban Nana. Sannan ya juya zuwa Inteesar, ya riƙe hannunta, ta yi ƙoƙarin ƙwacewa, “don Allah… ku bar ni… ina son na zauna da Yaya Nana…” amma… a hankali ya janyota zuwa bayansa, Mommy ta riƙeta. Da suka ba da wuri… wata dattijuwa ta matso, cikin nutsuwa… ta saukar da farin zanin likkafani… ya rufe fuskar Nana Aseeyah. A karo na ƙarshe… fuskarta ta ɓace daga idanun waɗanda suke sonta. Sai wani sabon kuka ya sake tashi a cikin ɗakin. Wasu maza suka shigo, suka durƙusa, a hankali… suka ɗaga nakarat da take kwance a ciki, suka fice da ita zuwa waje… domin a yi mata sallar jana’iza… kafin a raka ta zuwa makwancinta na ƙarshe.

Gidan ya yi tsit tamkar babu rai a cikinsa bayan an fita da gawar Nana Aseeyah zuwa makabarta. Wani irin shiru ne ya mamaye ko’ina, shirun da ba na rashin mutane ba ne… sai na babban rashin da aka yi. Kowa ya yi shiru, kowa yana cikin alhini.

Inteesar kuwa… tana kwance ne a jikin Mommy Haleema, idanunta sun kumbura saboda yawan kuka, jikinta babu ƙarfi, kamar an cire mata duk wata dama ta motsi.

Kwatsam… sai wani siririn kuka ya ratsa cikin gidan, kukan jariri, kukan da ya karya shirun da ya mamaye gidan. Inteesar ta buɗe idanunta da sauri, ta miƙe zaune zumbur, ta fara wara ido tana duban ko’ina, numfashinta ya fara sauri. Sai ta juya ta kalli Mommy Haleema, “Mommy…” muryarta ta fito cikin rawar jiki, “kukan baby nake ji?” Mommy Haleema ta lumshe idanunta, sabbin hawaye suka cika mata ido, a hankali ta gyaɗa kai, “ehh Intee… baby ɗin Nana ne, alhamdulillah… an samu nasarar cire shi bayan rasuwar Nana.”

Da jin haka… Inteesar ba ta jira ƙarin bayani ba, ta miƙe tsaye da sauri, ta nufi ɗakin da take jin kukan jaririn. Da ta shiga… sai ta hango Hajiya Kaltume zaune bakin gado, jaririn yana rungume a jikinta, feeding bottle na hannunta, tana ƙoƙarin ba shi madara. Amma yaron ya ƙi karɓa, sai kuka yake yi, yana jujjuya kansa, kamar yana neman wani abu da bai samu ba.

Inteesar ta ƙarasa da sauri, ba tare da ta ce komai ba… ta miƙa hannu. Hajiya Kaltume ta miƙa mata jaririn. Da ya sauka a hannunta… sai ya yi shiru, kukan ya tsaya, ya lafa a jikinta. Ta kwantar da kansa a ƙirjinta ya fara sauke ajiyar zuciya a hankali, kamar ya samu mafakar da yake nema. Wani sabon kuka ya ƙwace wa Inteesar, ta ƙara matse shi a jikinta, sannan ta ɗan ɗago shi, ta fara kallon ko ina a jikinsa. Allah sarki… blue baby suit ɗin nan da ta ce shi za a saka masa ranar da za a haife shi… shi ne har yanzu ke jikinsa. Ta sumbaci goshinsa a hankali, hawayenta suka fara zuba a kansa, ta goge su da sauri, kamar ba ta son ko digo ɗaya ya taɓa shi. Sai ta ɗaga kai ta kalli Hajiya Kaltume, “Mama… ya ci wani abu?” Hajiya Kaltume ta ɗaga feeding bottle ɗin, ta girgiza kai, “a’a, tun ɗazu nake ƙoƙarin ba shi, ya ƙi karɓa.” Inteesar ta sake kallon jaririn, ta matse shi a ƙirjinta, sai ta durƙusa a gaban Hajiya Kaltume, hawayenta suka sake gangarowa, “Mama…” ta yi shiru, ta haɗiye wani irin kuka, da ƙyar ta sake magana, “…dan Allah… ku bar ni na shayar da shi.”

Shiru ya sauka a ɗakin. Hajiya Kaltume ta zuba mata ido, kamar ba ta tabbatar da abin da ta ji ba. Mommy Haleema ma da ta biyo bayanta ta tsaya tana kallonta. Kowa ya yi shiru. Inteesar kuwa… ta sake rungume jaririn, ta lumshe idanunta, cikin wata murya mai cike da rauni ta ce, “na yi wa Yaya Nana alƙawari… na ce zan kula da baby, ba zan bari ya ji babu mahaifiyarsa ba, ko da ita ta tafi… …amanarta tana hannuna.” ta sumbaci goshin jaririn karo na biyu, hawayenta na ci gaba da zuba, “dan Allah Mama… ku bar ni…”

Mommy Haleema da tun ɗazu take tsaye bakin ƙofa tana kallon abin da ke faruwa cikin hawaye, ta ƙarasa shigowa ɗakin a hankali, ta zauna kusa da Hajiya Kaltume, su biyun suka zuba wa Inteesar ido cikin tausayi. Shiru ya mamaye ɗakin, sai sautin numfashin jaririn da yake kwance a jikin Inteesar, da kuma sheshsheƙar kukanta. Hajiya Kaltume ta sauke ajiyar zuciya, a hankali ta miƙa hannu ta dafa kafaɗar Inteesar, “Intee…” ta kira cikin sanyin murya. Inteesar ta ɗago idanunta da suka kumbura saboda kuka. Hajiya Kaltume ta share mata wasu hawaye da suka gangaro, “ba zai yiwu ki shayar da shi ba, ’yata. har yanzu ke budurwa ce, ko matar aure ma, ba ya halatta ta shayar da wani yaro ba sai da izinin mijinta.” ta sake shafa kanta cikin lallashi, “bare ke da ba ki ma yi aure ba, ki yi haƙuri, ’kinji. in sha Allah za mu samu mafita, amma yanzu… ki kwantar da hankalinki. ki ci gaba da yi wa Nana addu’a, hakan ne ya fi amfani gare ta yanzu, addu’arki take buƙata.”

Inteesar ta runtse idanunta, ta goge hawayenta da bayan hannunta, na wasu daƙiƙu ba ta ce komai ba, sai daga ƙarshe ta ɗaga kai a hankali, cikin murya mai rauni ta ce, “to Mama…” ta yi shiru, sannan ta sake kallon ƙaramin jaririn da ke kwance a jikinta, “amma… za a bar yaron a wajena ko? zan riƙe shi, zan iya.” muryarta ta sake rawa, “Yaya Nana ta ce min…” ta kasa ƙarasa maganar, kukan ya sake ƙwace mata, da ƙyar ta haɗiye shi, “…ta ce idan mun dawo daga asibiti… …ni zan riƙa riƙe baby a ɗakina.” ta matse jaririn a ƙirjinta, sai ta fashe da wani irin kuka mai karya zuciya, “ita kuma… ta girgiza kai cikin rashin yarda, “…ita kuma za ta kwanta tana barci.” ta ɗago idanunta sama, kamar har yanzu ba ta yarda da abin da ya faru ba, “ban san… ban san ashe mutuwa za ta yi ba…” da wannan kalmar… ta sake rushewa gaba ɗaya, ta rungume jaririn sosai, kukanta ya cika ɗakin. Mommy Haleema da Hajiya Kaltume kuwa… ba su sake iya danne nasu hawayen ba, su ma suka fashe da kuka, domin a wannan lokacin… ba Inteesar kaɗai ce ta rasa Nana ba… kowacce mace da ke cikin ɗakin… ta rasa wani ɓangare na zuciyarta.

Yaya Umar kuwa… tun daga makabarta kallon komai yake, gashi dai an binne Nana kamar dai da gaske kenan ta rasu, ta tafi ta barshi ta fiya ta har abada. Bai sake zubar da hawaye ba, hawayen kaɗan da suka zubo masa a asibiti… su ne kaɗai. Amma duk wanda ya kalle shi… sai ya san cewa zuciyarsa ta fi ta mai kuka ciwo. Idanunsa gaba ɗaya sun sauya launi, sun yi jajur… kamar ba nasa ba, sai wani irin nauyin numfashi da yake fitowa daga ƙirjinsa, kamar zuciyarsa na ƙoƙarin fashewa.

Yaya Abubakar ne ke riƙe da hannunsa tun daga wajen makabarta, da suka iso gida… bai kai shi wajen da ake karɓar gaisuwa ba, kai tsaye… ya shigo da shi cikin gidan, ya nufi ɓangarensa. Da suka shiga ɗakin… ya kai shi har bakin gadonsa, ya zaunar da shi a hankali, shi kuma ya tsaya a gabansa. Na wasu daƙiƙu… bai ce komai ba, sai kallonsa da yake yi cikin tausayi. Daga ƙarshe… ya kira cikin sanyin murya, “Umar…” a hankali… Umar ya ɗago kansa, idanunsa suka sauka kan Yaya Abubakar, shiru. Yaya Abubakar ya matso kusa da shi, ya dafa kafaɗarsa, sannan cikin murya mai rawa ya ce, “yi kuka, Umar…” ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya sake maimaitawa, “yi kuka… ka fitar da abin da ke cikin zuciyarka, kayi kukaaa.” kamar mutumin da yake jiran wani ya ba shi izini… nan take… Umar ya fashe da wani irin kuka, kuka mai ƙarfi, jikinsa ya fara karkarwa, numfashinsa yana tsinkewa, kamar zuciyarsa ce take fita tare da kowace sauti da yake yi. Yaya Abubakar ya matsa kusa da shi, ya rungume shi, ya jawo kansa ya ɗora a kafaɗarsa, bai ce masa komai ba, bai hana shi kuka ba, ya bar shi… ya yi kuka, kukan da ya kasaye tun samun labarin mutuwar. Sai da ya yi mai yawa… har ƙarfinsa ya fara ƙarewa, a hankali… numfashinsa ya fara sauyawa, jikinsa ya yi laushi. Yaya Abubakar ya ɗan janye shi, ya kira shi a tausashe, “Umar…” ba amsa. Ya sake kiran sunansa, har yanzu… shiru. Da ya duba fuskarsa sosai… sai ya fahimta, bacci ne ya ɗauke shi, ba baccin kwanciyar hankali ba… baccin gajiyar zuciya. A hankali… ya taimaka masa, ya kwantar da bayansa a kan gadon, ya gyara masa matashin kai, ya lulluba masa bargo, sannan ya tsaya daga gefen gadon… yana kallonsa cike da tausayi. Tun suna yara… Umar shi ne mafi ƙarfin zuciya a cikinsu, shi ne wanda ba ya tsoro, shi ne wanda ba ƙaramin abu ne yake girgiza shi ba, ko lokacin da suke cikin wata matsala… shi ne yake ƙarfafa sauran. Amma yau… a cikin yini ɗaya kacal… duba yanda ya sauya gaba ɗaya, kamar ba Umar ɗin da ya sani ba. Wata ƙwalla ta gangaro daga idon Yaya Abubakar, ya goge ta da sauri, ya sake kallonsa karo na ƙarshe, sannan cikin sanyin jiki… ya juya, ya fita daga ɗakin, a hankali… ya janyo masa ƙofar, ya bar shi kaɗai… da kuma rayuwar da ba za ta ƙara zama iri ɗaya ba.

Sorry for the typos not edited ✍️

*KADDARAR ZUCIYA*

*CHAPTER SEVENTY-FIVE: 75*

*A CHILD BETWEEN 2 HEARTS*

*JIDDAH BARKUM*

Abdallah…

Sunan da Yaya Abubakar ya zaɓa masa kenan lokacin da aka yi masa huɗuba, sunan mahaifin Yaya Umar. Kowa ya yi shiru lokacin da aka ambaci sunan, domin ya dawo musu da tarihin mutumin kirki da ya rayu da mutunci, kamar yadda aka yi addu’ar Allah ya sa ƙaramin Abdallah ya gaji halayensa.

Kasancewar sunan mahaifin Umar ne sai ake yi masa laƙabi da Aamaan.

Cikin ikon Allah, daga baya aka samu ya karɓi madara. Mommy Haleema ta sake yi masa wanka da ruwan ɗumi, ta shafe jikinsa da mai, sannan ta naɗe shi cikin wasu kaya masu laushi na jarirai. Ya kwanta cikin gadon jaririnsa yana barci cikin kwanciyar hankali… fuskar nan tasa cike da natsuwa, kamar ba shi da ko wace irin damuwa a duniya.

Inteesar kuwa… tun bayan da ta karɓe shi a hannunta, zuciyarta ta manne da shi gaba ɗaya. Ba ta iya matsawa daga inda yake, duk wanda ya ɗauki jaririn… idanunta suna binsa ne har sai an dawo mata da shi. Ko yanzu ma… da ƙyar Mommy Haleema ta lallashe ta ajiye shi domin ya huta. Tun da ta rungume shi… kamar wani abu a cikin zuciyarta yake gaya mata cewa kada ta sake shi, kamar wani zai zo ya ƙwace mata amanar Yaya Nana. Sai da ta tabbatar ya yi barci sosai sannan ta sake kwantar da shi, amma har ta ja baya… idanunta na kansa.



Wajen ƙarfe biyar na yamma… Alhaji Kabeeru ya ɗaga kansa ya dubi Yaya Abubakar, “ina Umar?” Yaya Abubakar ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya amsa, “yana ɗakinsa Daddy.” Daddy ya sauke numfashi a hankali, “ka je ka duba shi.” “to Daddy.” Yaya Abubakar ya miƙe, da sauri ya nufi cikin gidan, kai tsaye ɓangaren Umar ya dosa. Ya isa bakin ƙofar ɗakin, ya yi sallama sannan ya tura ƙofar. Ɗakin ya ɗan yi duhu, hasken yamma kaɗai ne ke ratsawa ta labule, fitilar kuma a kashe take. Ya kai hannu ya kunna maɓallin wuta, nan take haske ya mamaye ɗakin. Idanunsa suka sauka kan Umar. Har yanzu… yana kwance a yadda ya bar shi, ko juyawa bai yi ba, ko canja ɓangaren da mutum kan yi idan ya gaji. Wani irin faɗuwa zuciyar Yaya Abubakar ta yi. Da sauri ya ƙarasa kusa da gadon, ya dafa kafaɗarsa, “Umar…” shiru. Ya sake girgiza shi kaɗan, “Umar!” har yanzu… shiru. Gaban Yaya Abubakar ya faɗi. Da hannu mai rawa ya kai yatsunsa wuyan Umar yana laluben bugun numfashinsa. Da ya ji bugun yana da matuƙar rauni… zuciyarsa ta yi wani mugun tsalle. Bai tsaya ɓata lokaci ba, da gudu ya fita daga ɗakin, “Yaaya Adam! Khalil! Hashim!” muryarsa ta cika gidan. Cikin firgici suka ruga zuwa wajensa, “me ya faru?” “Umar!” kalma ɗaya kawai ya iya furtawa. Ba wanda ya sake tambaya. Da sauri suka shiga ɗakin. Adam ya durƙusa ya duba Umar, fuskarsa ta sauya, “mu tafi da shi asibiti, yanzu!” nan take suka ɗaga shi cikin gaggawa, suka fito da shi daga ɗakin, kai tsaye suka nufi mota. A cikin ƴan daƙiƙu kaɗan… motar ta fice daga gidan da gudu.

Gidan ya sake rikicewa, kuka ya sake tashi, wasu na kuka saboda Nana… wasu kuma saboda tsoron kada su sake rasa Umar. Mommy Haleema ta dafe ƙirjinta, Inteesar kuwa ta rungume ƙaramin Abdallah sosai, hawaye na sake gangaro mata, “ya Allah…” kawai ta iya furtawa, “kada ka ƙara gwada mu da wani sabon rashi…”

Da gaggawa aka karɓi Umar zuwa emergency unit, inda likitoci da nurses suka fara ba shi agajin gaggawa. A waje kuwa… hankalin ƴan’uwansa ya kai matuƙar tashi. Kowa ka kalla… fuskarsa cike take da tashin hankali. Ba a jima da dawowa daga jana’izar Nana ba, har yanzu ma ba su gama hawaye ba… sai ga wata sabuwar jarabawa ta sake faɗowa kansu. Yaya Adam yana kai-komo a bakin ƙofar emergency, Khalil ya dafe kansa, Hashim kuwa ya kasa zama wuri guda. Kowannensu addu’a kawai yake yi a zuciyarsa, “ya Allah… kada ka sake jarabtar mu.”

Bayan kusan mintuna ashirin… ƙofar emergency ta buɗe. Likitan da ke kula da Umar ya fito, ya dubi mutanen da ke tsaye a gabansa kafin ya ce, “who is the eldest among you? waye babba a cikinku?” dukkansu suka juya suka kalli Yaya Adam. A hankali ya matso gaba, “I am.” Likitan ya yi masa alamar ya biyo shi, “okay… come with me.” ba tare da ya ce komai ba, Yaya Adam ya bi bayansa har cikin office ɗinsa. Likitan ya zauna, ya buɗe file ɗin Umar da ke gabansa, sannan ya ɗaga kai ya kalli Adam, “did you know your brother has been receiving treatment for heart failure for almost a year now? ka san ɗan’uwanka yana karɓar maganin ciwon zuciya kusan shekara ɗaya kenan?” Yaya Adam ya zaro ido cikin matuƙar mamaki, “what?” ya girgiza kansa da sauri, “no, doctor… I had no idea.” Likitan ya ɗan yi shiru kafin ya ci gaba, “he has been coming here regularly for his medications and follow-up appointments, his condition has been managed with treatment, but… yana zuwa nan akai-akai akan maganinsa yana kuma zuwa ana sake dubashi, halin da yake ciki ana tare da magani…” ya tsaya na ɗan lokaci, “…his heart is very weak, zuciyarsa ta yi rauni sosai.”

Yaya Adam ya kasa magana, gabansa ya faɗi. Tunda yake da Umar… bai taɓa jin yana fama da wata matsalar zuciya ba, bai taɓa ganin yana shan magani a gida ba, ballantana ya san cewa kusan shekara guda kenan yana karɓar magani a ɓoye. Likitan ya lura da mamakin da ke kan fuskarsa, sai ya ɗan gyara zamansa, “right now… his condition has worsened, a halin yanzu halin da yake ciki ya baci. he suffered a severe emotional shock, and with someone who already has heart failure, that kind of stress can be very dangerous, ya samu firgita kuma ga wanda yake da ciwo irin wannan, hakan ba ƙaramin hatsari ba ne a gare shi.” ya haɗa hannayensa a kan tebur, “from now on, you all have to be very careful, daga yanzu yana da kyau ku kula sosai. keep him away from anything that could trigger emotional distress, sai ku kula da dukkan abinda zai daga masa hankali. he must take his medications consistently, kuma dole ya dage da shan magungunansa. and most importantly… abinda ya fi komai muhimmanci…” ya kalli Adam kai tsaye, “he needs peace of mind, yana buƙatar kwanciyar hankali. because if this continues… saboda idan haka ya ci gaba…” ya ɗan sauke numfashi, “…the next attack may be far more serious, abinda zai faru zai fi wannan tashin hankali.”

Kalaman likitan suka sauka a zuciyar Yaya Adam kamar an ɗora masa dutse. Ya sunkuyar da kansa, a hankali ya furta, “in sha Allah, doctor… we’ll do everything we can to take care of him.” amma a zuciyarsa… tambaya guda ce ta kasa barinsa, ta yaya Umar ya ɓoye musu irin wannan babban sirrin tsawon kusan shekara ɗaya…?

Daga ƙarshe likitan ya rufe file ɗin da ke gabansa, sannan ya dubi Yaya Adam, “we’ve given him the necessary injections and medications, if everything remains stable, you should be able to take

10 / 40