Kaddarar Zuciya Book 2 Complete JIddah Barkum

Author :  Jiddah Barkum Category :  Read Hausa Novels

Chapter   3 / 40

6K to 9K   out of 117.5K words

kamar shi ma yana da wani kaso a abin da ya faru…

Faisal ya jingina da kujera, ya sauke numfashi mai nauyi, tun farko yana ganin Inteesar tana son Aliyu, amma bai taɓa tunanin… soyayyar ta kai wannan matakin ba, har mutum ya karya amanar mahaifinsa, har mutum ya kasa samun nutsuwa tsawon watanni, ya girgiza kai a hankali, “subhanallah…”

Mommy Haleema kuwa… ta kasa ƙara zama, ta miƙe a hankali, ta ƙarasa inda Inteesar take, ta durƙusa, ta kamo kafaɗarta, “Fateema…” Inteesar ta ƙara fashewa da kuka, “Mommy… na yi laifi… na san na yi laifi…” Mommy Haleema ta rungume ta sosai, ta manna kanta a ƙirjinta, kamar yadda take yi tun tana yarinya, “shhh… ya isa, ki daina kuka.” Amma Inteesar ta kasa tsayawa, “Mommy… ban taɓa samun nutsuwa ba… kullum sai na tuna Daddy… kullum sai na ji kamar na cuce shi…” Mommy Haleema ta lumshe idanunta, ita ma hawayenta suka gangaro, ta sumbaci goshin Inteesar, “ki yi shiru ya isa hakaa.” Falon ya sake nutsuwa, sai sautin kukansu kaɗai yake tashi. A wannan lokacin… Alhaji Kabeeru ya ɗaga kansa a hankali, ya kalli ɗiyarsa da ke rungume a jikin Mommy Haleema, sai ya kalli Aliyu da yake durƙushe yana kuka, ya ja wani dogon numfashi, kafin ya buɗe baki… don ya yi magana karo na farko tun bayan bayyana gaskiyar. Ya lumshe idanunsa na wasu daƙiƙu, kamar yana ƙoƙarin tattara kalmomin da zuciyarsa ta kasa furtawa. Da ya buɗe idanunsa… sai suka sauka kan Inteesar, har yanzu tana rungume a jikin Mommy Haleema, kukanta ya ragu, amma hawaye suna ci gaba da gangaro mata. Daddy ya kira sunanta, “Fateema…” muryarsa ta yi laushi. Inteesar ta ɗago kanta da ƙyar, “na’am… Daddy…” ta kasa kallonsa cikin ido, kai tsaye ta maida idanunta ƙasa. Daddy ya yi shiru na wasu daƙiƙu, kafin ya ce, “ki zo nan.” Mommy Haleema ta shafa bayanta a hankali, “je wajen Daddy.” Inteesar ta share hawayenta, a hankali ta matsa, ta sake durƙusawa a gaban mahaifinta, kanta a sunkuye, hannayenta na rawa. Alhaji Kabeeru ya dube ta na ɗan lokaci, sai ya miƙa hannu, ya ɗaga haɓarta cikin tausasawa, ya tilasta idanunta su haɗu da nasa, “dube ni.” Da ƙyar Inteesar ta ɗago, idanunta sun yi ja, sun kumbura, sun gaji da kuka. Daddy ya ci gaba da kallonta, na wasu daƙiƙu… ba tare da ya ce komai ba, sai ya ce cikin sanyin murya, “kin san abin da ya fi ciwo a zuciyata?” Inteesar ta girgiza kai cikin kuka, “a’a… Daddy…” ya sauke numfashi, “ba kuɗin nan ba ne.” Falon ya yi tsit. Daddy ya ci gaba, “ba miliyan goma sha bakwai ba ne.” Ya ɗora hannunsa a kanta, “abin da ya fi karya min zuciya… shi ne… yadda kika raina kanki saboda soyayya.” Inteesar ta fashe da sabon kuka, “Daddy…” ya ɗaga hannu, ya dakatar da ita, “a’a, ki saurare ni.” Ta yi shiru, hawayenta kaɗai suke zuba. Daddy ya ci gaba, “tun kina ƙarama… na koya miki abu guda, mutum zai iya rasa kuɗinsa, zai iya rasa dukiyarsa, zai iya rasa komai, amma… kada ya taɓa rasa mutuncinsa.” Ya nuna ƙirjinta, “ke kuma… saboda soyayya… kin karya amanar da ke tsakaninmu.” Inteesar ta girgiza kai, “Daddy wallahi—” “na sani,” ya katse ta cikin nutsuwa, “na san ba saboda mugunta kika yi ba, na san ba saboda son kuɗi kika yi ba, na san saboda kina son Aliyu ne.” Ya ɗan yi shiru, sai ya ce, “amma hakan bai sa abin ya zama daidai ba.” Inteesar ta rufe fuskarta da hannayenta, kukanta ya sake ƙaruwa, “ka yafe min Daddy… wallahi ba zan sake ba… ka yafe min…” Daddy ya jawo ta, ya rungume ta, kamar yadda yake yi tun tana yarinya, ya manna hannunsa a bayanta, “na san kina cikin nadama, tun da kika furta gaskiya… na ga nadamar a idanunki.” Ya shafa kanta, “amma ki tuna wannan darasi har ƙarshen rayuwarki, kada soyayya ta taɓa sa ki rasa kanki, kada soyayya ta taɓa sa ki karya amanarki, kada soyayya taɓa sa ki raina darajarki.” Inteesar ta ƙara fashewa da kuka, ta ƙara manne masa, “Daddy… na yi kuskure… ka yafe min…” ya lumshe ido, ya shafa bayanta, “na ya yafe miki.”

Kalmar ta sauka cikin falon kamar ruwa a kan wuta. Mommy Haleema ta sauke numfashin da ta daɗe tana riƙewa, Humaira ta share hawayenta, Khalil ya lumshe ido, Faisal ya sunkuyar da kansa. Aliyu kuwa… sai ya ƙara rushewa, domin ya fahimci cewa… mutumin da ya fi cutarwa a wannan labarin… ba shi kaɗai ba ne, har Inteesar ma ta sha wahala saboda shi. Daddy ya saki Inteesar a hankali, ta koma ta zauna kusa da Mommy Haleema, ya juya idanunsa kan Aliyu. Tun farkon zaman… Aliyu bai taɓa ɗaga kansa ba, har yanzu yana durƙushe, kai a ƙasa, hawaye na sauka ba ƙaƙautawa. Daddy ya kira sunansa, “Aliyu.” Da sauri ya amsa, “na’am Daddy…” “ka ɗago.” Aliyu ya ɗago a hankali, idanunsa sun kumbura, fuskarsa ta rame. Daddy ya ci gaba da kallonsa, na wasu daƙiƙu, sai ya ce, “yanzu… ka san girman abin da wannan yarinya ta yi maka?” Aliyu ya kasa magana, hawayensa suka sake zuba. Daddy ya nuna Inteesar, “ta yi wa ubanta ƙarya, ta rasa kwanciyar hankali tsawon watanni, saboda kai.” Aliyu ya dafe ƙirjinsa, “Daddy… na sani… na yi mata babban laifi…” Daddy bai katse shi ba, ya ci gaba, “ka san abin da ya fi bani mamaki?” Aliyu ya girgiza kai. Daddy ya ce, “ba taɓa zuwa ta faɗa mini gaskiya ba, ba saboda tana jin daɗin abin da ta yi ba, saboda tana tsoron kada na tsane ka.” Aliyu ya runtse idanunsa da ƙarfi, wani sabon kuka ya ƙwace masa, “I failed her… I failed the only person who truly loved me.” Daddy ya kalle shi cikin natsuwa, sai ya juya ya kalli sauran ’ya’yansa, “Abubakar.” “na’am Daddy.” “tun farko ka ce an gama.” “eh Daddy.” Ya juya ya kalli Mommy, “ke ma kince ba za ki ba da auren ba.” Mommy Haleema ta gyada kai, “eh.” Daddy ya jinjina kansa, “sai dai…” ya yi shiru, kalaman suka sa kowa ya ɗago kai, “sai dai… a gidana… ba zan taɓa yanke hukunci ba… ba tare da na ji bakin wanda abin ya fi shafa ba.” Ya juya idanunsa a hankali… suka sauka kan Inteesar.

Alhaji Kabeeru ya ci gaba da kallon Inteesar, idanunsa cike da tausayi, amma kuma cike da hikimar uba. A hankali ya kira sunanta, “Fateema…” Inteesar ta ɗago kanta cikin hawaye, “na’am… Daddy.” Ya yi shiru na wasu daƙiƙu, kafin ya ce, “tun kina ƙarama… ban taɓa tilasta miki abin da ba kya so ba.” Ta ci gaba da kallonsa. Ya ci gaba, “lokacin makaranta… na bar ki kika zaɓi abin da kike so, lokacin jami’a… na bar ki kika zaɓi abin da kike so, saboda na yi imani… rayuwarki… ke za ki amfana sama da kowa.” Ya sauke numfashi, “shi ya sa… ko da ni ne uba… ba zan taɓa tilasta miki aure ba.” Falon ya sake yin tsit, kowa ya mayar da hankalinsa gaba ɗaya kan Daddy. Daddy ya yi magana cikin laushi, “yanzu ba na tambayarki a matsayin Alƙali, ba na tambayarki a matsayin shugaban gida, ina tambayarki ne… a matsayin ubanki.” Ya nuna ƙirjinsa, “uban da yake son farin cikinki.” Sabbin hawaye suka sake gangaro wa Inteesar. Daddy ya ci gaba, “ba wanda zai matsa miki, ba wanda zai tsorata ki, ba wanda zai yi fushi da amsar da za ki bayar.” Ya yi shiru, sai ya ce, “idan kika ce… ba kya son Aliyu, a yau… maganar nan za ta ƙare har abada.” Aliyu ya ji gabansa ya faɗi, numfashinsa ya tsaya. Daddy ya ci gaba, “amma… idan har yanzu kina sonsa… ki faɗa min, idan har yanzu kina son ki aure shi… ki faɗa min.” Falon ya yi difff, kowa yayi shiru, babu wanda ya motsa, har agogon bango kamar ya daina bugawa. Daddy ya sake maimaitawa, “Fateema… har yanzu kina son Aliyu? Har yanzu kina son ki aure shi?”

Tambayar ta sauka cikin zuciyar Inteesar, ta kasa motsi, ta kasa magana, sai hawaye. A hankali… ta ɗaga idanunta, a karon farko… tun bayan saukowarta daga bene… idanunta suka haɗu da na Aliyu. Shi ma… tun farko idanunsa suna kanta, bai taɓa ɗauke su ba. Da suka haɗu… zuciyar Aliyu ta buga da wani irin ƙarfi, bai yi magana ba, bai motsa ba, amma idanunsa… sun faɗi duk abin da bakinsa ya kasa furtawa, nadama, kunya, soyayya, tsoro, roƙo. Kamar suna cewa… “don Allah… kada ki rufe mini ƙofar zuciyarki, ki ba ni dama guda ɗaya, na san na cuce ki… na san ban cancanci gafararki ba… amma wallahi ina son ki.” Sabbin hawaye suka cika idanunsa, a hankali ya girgiza kansa, ba alamar musun tambayar Daddy ba, alamar roƙo ce, tsantsar roƙo, kamar zuciyarsa tana durƙusawa a gabanta. Inteesar ta ci gaba da kallonsa, lokaci ya tsaya a gare ta. Ta tuna ranar da ya fara kiranta… “babygirl”, ta tuna ranar da ya durƙusa ya roƙi aurenta, ta tuna yadda yake kula da ita, ta tuna yadda take jin babu wani namiji irinsa. Sai kuma… ta tuna screenshots ɗin, “she will endure… mansion… seventeen million…” kowace kalma… kamar wuƙa ce. Ta sake jin yadda zuciyarta ta karye a ranar da ta karanta su, ta tuna yadda ta yi kuka ita kaɗai, ta tuna yadda ta kasa cin abinci, ta tuna yadda ta kasa kallonsa, ta tuna yadda ta rasa amincewa da duk abin da yake faɗa. Sai ta sake kallonsa, yana kuka, yana neman gafara, yana kallonta da idanun da suka cika da fargabar rasa ta. Zuciyarta ta yi wani irin rauni, amma… raunin da ke cikinta… ya fi ƙarfin soyayyar da take ji. Daddy ya sake katse shirun, “Fateema… har yanzu kina son shi? Har yanzu kina son ki aure Aliyu?” Inteesar ta lumshe idanunta a hankali, ta ja dogon numfashi, hawayenta suka ci gaba da sauka, jikinta yana rawa, da ƙyar ta buɗe baki, muryarta ta fito a raunane, “…Daddy…” ta tsaya, ta haɗiye wani abu mai ɗaci, sannan… a hankali… ta girgiza kanta, “a’a.” Sabbin hawaye suka sake zubo mata, ta sake girgiza kanta, da ƙyar ta furta, “…ba zan iya ba, Daddy.” Kalmar ta fito ne kamar an ciro ta daga cikin zuciyarta. Aliyu ya ji kamar wani abu ya tsaya masa a ƙirji, numfashinsa ya ɗauke. Inteesar ta ci gaba cikin kuka, “wallahi… har yanzu… ina…” ta kasa ƙarasa, ta dafe ƙirjinta, “har yanzu… ina…” ta sake fashewa da kuka, “amma… ba zan iya aurensa ba, Daddy, ba zan iya ba… ba zan iya sake yarda ba… ba zan iya rayuwa da wannan ciwon ba…” ta rufe fuskarta da hannayenta, kukanta ya mamaye falon. Aliyu kuwa… kamar duniya ta tsaya masa, ya lumshe idanunsa a hankali, wani zafan hawaye suka gangaro masa, bai yi magana ba, bai yi ƙoƙarin kare kansa ba, domin a wannan karon… ya fahimci cewa akwai raunuka… waɗanda “yi haƙuri” kaɗai… ba ya warkar da su. Falon ya sake yin tsit, sai sautin kukansu biyu kaɗai… na Aliyu, da Inteesar. Zukata biyu… masu ƙaunar juna, amma… waɗanda ciwon da aka yi musu… ya fi ƙarfin soyayyar da ke tsakaninsu. A hankali… Alhaji Kabeeru ya sauke wani dogon numfashi, ba tare da ya sake kallon kowa ba… ya miƙe tsaye, kujerar da yake zaune ta yi ƙaramar ƙara yayin da ya tashi, kowa ya bi shi da ido, babu wanda ya ce komai. Fuskarsa ta nuna gajiyawar da ba ta jiki ba… gajiyawar zuciya ce. Ya tsaya na ɗan daƙiƙu yana kallon Inteesar da har yanzu take durƙushe tana kuka, sai ya juya cikin nutsuwa, ba tare da ya furta ko kalma ɗaya ba… ya nufi stairs, takunsa a hankali suke sauka kan matattakalar, amma kowace taka… sai ta yi kamar tana bugawa a zuciyar waɗanda suke falon. Mommy Haleema ta share hawayen da ke gefen idanunta, ta matso kusa da Inteesar, a hankali ta kama kafaɗarta, “zo, yar albarka…” Inteesar ba ta motsa ba, kawai tana kuka. Mommy Haleema ta sake dafa bayanta cikin taushin murya, “mu je sama.” Da ƙyar Inteesar ta miƙe tsaye, jikinta babu ƙarfi, kamar wacce ta kwashe kwanaki ba ta ci komai ba. Mommy Haleema ta riƙe hannunta sosai, kamar yadda uwa ke riƙe da ƙaramin yaro, Humaira ta yi saurin matsowa, ba tare da ta yi magana ba… ta kama ɗayan hannun Inteesar, suka fara hawa stairs ɗin a hankali. Inteesar ba ta waiwayo ba, ba ta sake kallon Aliyu ba, kai tsaye suka bi bayan Daddy, har suka ɓace daga idanun mutanen falon…

Falon ya rage da shiru mai nauyi, babu wanda ya ce uffan, sai sautin agogon bango, tick… tick… tick… Aliyu yana tsaye a inda yake, kai a sunkuye, idanunsa sun yi jajur saboda kuka, hannayensa biyu suna rataye a gefensa. Abubakar ya ci gaba da kallonsa, na wasu daƙiƙu… babu wanda ya motsa. Daga ƙarshe… ya sauke numfashi, ya ce cikin murya mai sanyi… amma mai nuna ƙarshen magana, “I think… this is over.” Aliyu bai ɗaga kai ba, kawai ya lumshe idanunsa. Abubakar ya ci gaba, “you can take your leave.” Kalmar ta fito ba tare da tsawa ba, amma ta fi kowace irin tsawa zafi. Aliyu ya haɗiye wani abu mai ɗaci, ba ya da sauran abin faɗa, ba ya da abin kare kansa. A hankali… ya juya, ya fara tafiya, kanshi a sunkuye, kafafunsa suna masa nauyi, kamar ba shi ke tafiya ba… kamar ana jan jikinsa ne. Ya isa bakin ƙofa, ya buɗe ta, ya fita, har yanzu bai waiwayo ba, har ya wuce ledar kuɗin da ke kan kasan falon, babu wani abu da yake gani a wannan lokacin, sai kalma guda ɗaya da take ta maimaituwa a cikin zuciyarsa, “ba zan iya aurensa ba… ba zan iya ba…” kalamanta suna sake-sake amsawa a kunnuwansa, kowace maimaitawa… sai zuciyarsa ta ƙara fashewa…

Abubakar ya kalli ledar kuɗin, ya sunkuya, ya ɗauke ta, ba tare da ya ce komai ba… ya bi bayan Aliyu. A waje… Aliyu ya shiga motarsa, ya zauna a kujerar direba, amma bai kunna motar ba, hannayensa biyu suna kan steering, idanunsa a rufe, sabbin hawaye suka sake zubo masa. A wannan lokacin… Abubakar ya iso, ba tare da ya buga window ba… kai tsaye ya buɗe ƙofar back seat, ya ajiye ledar kuɗin cikin nutsuwa, ya rufe ƙofar. Ya kalli Aliyu ta cikin glass ɗin motar, ba ya jin daɗin halin da yake ciki, amma… a matsayinsa na ɗan’uwa… ba zai iya fifita tausayin Aliyu a kan ƙanwarsa ba. A hankali… ya juya, ya nufi cikin gidan. Aliyu ya ci gaba da zama a cikin motar, shi kaɗai, shiru. Cikin gidan kuma… Abubakar ya rufe ƙofar a bayansa, kamar yadda aka rufe babi ɗaya na rayuwa… ba tare da wanda ya san ko za a sake buɗe shi ba.

*KADDAR ZUCIYA*

*CHAPTER SIXTY-EIGHT: 68*

*THE HARD DAYS*

*THREE WEEKS LATER*

*JIDDAH BARKUM*

Makonni uku… kwanaki ashirin da ɗaya. Lokaci kaɗan ne a kalandar rayuwa, amma ga zuciyar mutum… wani lokacin kwanaki uku ma kan zama kamar shekaru. Tun bayan rushewar auren Inteesar da Aliyu… rayuwa ba ta tsaya ba, rana tana fitowa kamar yadda ta saba, dare yana komawa safe, mutane suna ci gaba da harkokinsu, sai dai… akwai wasu raunuka da lokaci kaɗai ba ya isa ya warkar da su.

Labarin fasa auren ya bazu cikin dangi da abokan arziki, na kusa da gidan Alhaji Kabeeru… sun san cewa akwai wani babban abu da ya faru, amma ba kowa aka faɗa wa cikakken dalilin ba, sai iyalan gida kaɗai, da kuma kaɗan daga cikin waɗanda lamarin ya shafa kai tsaye. Sauran mutane kuwa… abin da suka sani kawai shi ne… “an fasa auren.” Wasu suka ce kaddara ce, wasu suka ce wata rashin fahimta ce, wasu kuma suka yi ta ƙoƙarin gano abin da ya faru. Amma gidan Alhaji Kabeeru… ya zaɓi yin shiru, domin wasu labarai… darajarsu tana cikin rashin fitarsu bakin gida.

A cikin gidan kuma… komai ya fara komawa yadda yake a hankali. Alhaji Kabeeru ya koma harkokinshi na yau da kullum, Abubakar da sauran yayyen Inteesar suka koma harkokinsu. Sai dai… akwai abu guda da bai dawo yadda yake ba, Inteesar. Ba ta ƙara yin kuka kamar kwanakin farko ba, ba ta sake killace kanta a ɗaki ba, ta koma zama a falo, ta koma taimaka wa Mommy Haleema, ta koma cin abinci tare da iyalinta. Har ma… wani lokacin… ana iya jin dariyarta. Amma… waɗanda suka santa tun tana ƙarama… sun san cewa ba ita ce dariyar Inteesar ta gaske ba. Murmushi take yi… domin Daddy ya daina damuwa, dariya take yi… domin Mommy Haleema ta samu kwanciyar hankali, tana nuna kamar komai ya wuce… domin kada yayyenta su ci gaba da ɗora wa kansu laifi. Amma idan dare ya yi… ta kasance ita kaɗai a cikin ɗakinta… sai ta zauna na wasu mintuna cikin shiru, ba kuka, ba magana, sai kallon sararin ɗakinta, kamar zuciyarta tana ƙoƙarin koyon rayuwa daga farko.

Wataƙila… abin da ya fi taimaka mata cikin makonnin uku da suka wuce… shi ne kasancewar Humaira. Tun bayan abin da ya faru… Humaira ta tattara kayanta ta dawo gidan Alhaji Kabeeru, ba don wata matsala ba, sai don ta ƙi barin Inteesar ita kaɗai. Tun safe suke fita tare, suna yawo, suna siyayya, suna hira, wani lokaci ma su tsaya su sha ice cream ko su sha coffee kafin su dawo gida. Ba wai hakan ya goge ciwon da ke zuciyar Inteesar ba… sai dai… yana taimaka mata ta tuna cewa har yanzu akwai rayuwa a gabanta. Kuma yau ma… haka suka yi. Tun bayan sallar laasar suka fita, Humaira ta nace sai sun je Katsina City Park, wai Inteesar ta gaji da zama a gida. Da fari ta ƙi, amma da ƙyar Humaira ta lallashe ta, har suka yi yawo, suka ɗauki hotuna, suka yi dariya. Ko da kuwa… dariyar ba ta fito daga can ƙasan

3 / 40