Author : Jiddah Barkum Category : Read Hausa Novels
da kai cikin ladabi, “yaya ina kwana.” ya amsa cikin fara’a, “sannu da zuwa.” ta ɗan gyada kai.
Hashim ya yi murmushi, “Aamaan fa?” tambayar tasa zuciyar Inteesar ta ɗan buga, ta yi murmushi mai rauni, “yana gida. in sha Allah za a kawo shi nan gaba.” Hashim ya gyada kai, “Allah ya kaimu.” “ameen.” daga nan… suka shiga mota, Hashim ya zauna a driver’s seat, Umar a gaba, Inteesar kuma a baya. Motar ta fara tafiya.
…
Bayan sun fita daga airport… Umar da Inteesar… dukansu sukayi shiru. Hashim bai ɗauki hanyar da suka saba bi ba, ba hanyar gidan Nana ba ce, ba hanyar da duk lokacin da suka dawo daga airport… sukan bi zuwa gida ba. Sabuwar hanya ya kama. Umar ya kalli wajen window, Inteesar ma ta ɗago kai ta kalli hanya. Zuciyoyinsu suka buga lokaci guda, ba wanda ya ce komai, amma dukansu sun fahimta. An rufe wannan babin. Babin Nana… ya zama tarihi. Allah sarki rayuwa… shikenan fa...
——
Kasancewar Hashim yana cikin motar… shi ne ya rage nauyin shirun. Yana ta hira da Umar, jefi-jefi, game da aiki. Umar ma yana amsawa cikin nutsuwa. Amma Inteesar… tun bayan gaisuwar da suka yi… ba ta sake cewa ko kalma ɗaya ba, sai kallon titi kawai take yi ta window, tana bin gine-ginen Abuja da ido, amma ba su take gani ba, tunaninta… yana wani wuri daban.
Har suka iso ƙofar sabon gidan. Hashim ya rage gudun motar, a hankali ya tsaya a bakin babban gate ɗin da ya yi tsaye cikin ƙasaita. Umar ya sauka ya bude gate din. Gidan ya kasance babu maigadi a lokacin. Tsohon maigadinsu na da, tun rasuwar Nana da suka tafi Katsina, Umar ya sallame shi tare da bashi hakkinsa, da niyyar idan sun dawo gaba ɗaya zai sake nemansa.
Yayin da zuciyar Inteesar ta sake bugawa, domin ta fahimci… daga wannan ƙofar da za ta shiga… sabuwar rayuwarta za ta fara. Bayan Hashim ya yi musu sallama… ya shiga motarsa, a hankali ya fita daga compound ɗin, gate ɗin ya sake rufewa. Shiru ya mamaye wajen, sai Inteesar da Umar kaɗai.
Inteesar tana tsaye a tsakiyar compound ɗin, idanuwanta suna yawo a kan gidan, komai sabo ne, komai ya yi mata baƙo. Ta ji wani irin nauyi ya sauka a zuciyarta. A hankali Umar ya ƙaraso bakin ƙofar gidan, ya saka key, ya buɗe ƙofar, ya ɗan juyo ya kalleta, bai ce komai ba, sai kawai ya matsa gefe, alamar ta shiga.
Inteesar ta ja numfashi, ta taka ƙafarta ta farko cikin gidan a hankali, kamar wacce take tsoron taɓa wani abu. Da ta shiga… Umar ya zagaya bayan gidan inda changing over din nepa yake ya kunna wuta. Nan take… haske ya mamaye ko’ina. Falon ya bayyana cikin ƙawa da tsari, manyan sofas masu launin cream, luxury center table, soft carpet mai laushi, golden wall lights, manyan curtains masu tsananin kyau. Komai ya yi tsaf, komai ya yi shiru. Ya dawo, ya rufe ƙofar gidan.
Inteesar kuwa… ta zauna a hankali a kan ɗaya daga cikin sofas, ta haɗa yatsun hannayenta, tana ta wasa da su cikin rashin sanin abun yi, kanta a sunkuye. Shiru ya sake dawowa. Umar ya tsaya yana kallonta na wasu daƙiƙu, sai ya ce cikin sanyin murya, “ki shiga ɗaki… ki huta.” Inteesar ta ɗan ɗago kai, ta kalle shi, sannan ta ce cikin muryar da ba ta da ƙarfi, “ai… ban san ina ne ɗakina ba.” Umar ya tsaya yana kallonta, na ɗan lokaci bai ce komai ba, sai daga ƙarshe ya ce, “follow me.” ta miƙe cikin nutsuwa, ta bi bayansa. Suka haura stairs ɗin gidan, mataki bayan mataki, har suka isa sama. Suka bi wani dogon corridor mai cike da hotunan bango da fitilu masu haske. A ƙarshe… ya tsaya a bakin wata ƙofa, ya buɗe ta a hankali, sannan ya ɗan matsa gefe, ya kalle ta, “this is your room.” Inteesar ta ɗan gyada kai, ba ta ce komai ba. Umar ya ba ta hanya, ta shiga, shi kuma ya ja ƙofar, ya rufe mata a hankali.
…
Inteesar ta tsaya cak, idanuwanta suka fara yawo cikin ɗakin. Bedroom ɗin ya yi kyau matuƙa. Babban king-size bed ne a tsakiya, an yi masa shimfiɗa da farin bedsheet mai laushi, golden pillows suna jere gwanin shaawa. A gefe akwai dressing table mai babban mirror, shoe rack, sai waje ajiye jakunkuna. A gefe akwai doguwar sofa, a gefenta akwai centre table mai kyau, sai wardrobe dinta, soft rug a ƙasan gadon. Ƙamshin air freshener da turare ya cika ɗakin, komai yana da tsari, komai yana nuna an shirya ɗakin ne domin ta.
A hankali ta ƙarasa bakin gadon, ta zauna, ta haɗa hannayenta biyu ƙarƙashin haɓarta, ta yi tagumi. Sai hawayenta suka fara zuba ba tare da ta sani ba. Ba wani abu take ta tunani ba… sai kalma guda, “yau… ni ce matar Yaya Umar.” Tun lokacin da aka fara maganar auren… har aka ɗaura. A zuciyarta… kamar wasa ne, kamar mafarki ne. Amma yanzu… da ta tsinci kanta a cikin wannan gidan… daga ita… sai shi. A karon farko… ta ji gaskiyar abin ta bugi zuciyarta. Sabbin hawaye suka sake gangaro mata, ta share su da bayan hannunta.
A hankali ta miƙe tsaye, ta cire lafayar jikinta, ta ninke ta da kyau, ta ajiye ta a gefe, sannan ta cire atamfar da ke jikinta, ta nufi toilet.
… da ta buɗe ƙofar toilet ɗin… sai ta tsaya. Komai yana nan cikin tsari. Bathroom ɗin yana ta sheƙi, manyan mirrors, glass shower cubicle, white fluffy towels. A kan shelf kuwa… an jera mata duk abin da take amfani da su. Body wash, shower gel, body scrub, exfoliating sponge, black soap, moisturizing soap, face cleanser, face scrub, toothbrush sabo, toothpaste, mouthwash, hair shampoo, hair conditioner, leave-in cream, combs. Komai sabo, komai an tanade shi ne saboda ita.
Inteesar ta daɗe tana kallon kayan, sai ta sauke numfashi. A hankali ta shiga, ta kunna shower, ruwan ɗumi ya fara zuba, ta yi wanka cikin nutsuwa, ta wanke jikinta, ta yi brush. Bayan ta gama… ta ɗaure towel a jikinta, ta fito daga bathroom ɗin. Da ta tsaya bakin ƙofar… sai ta yi shiru na wasu daƙiƙu, kamar tana jin nauyin fitowa. Daga ƙarshe… ta taka zuwa bakin gadon, ta jingina bayanta. Amma kafafuwanta suna ƙasa. Ba ta da ƙarfin tunanin komai. Gajiyar kwanakin baya, kuka, tunani, sabuwar rayuwa… duk suka haɗu a kanta. Bai wuce mintuna biyar ba… bacci mai nauyi ya ɗauke ta.
———
Yaya Umar bai sake zama ba. Da ya tabbatar Inteesar tana cikin ɗakinta, ya ɗauki key ɗin mota ya fita. Kai tsaye wani babban supermarket ya nufa. Ba wai ya shiga ya ɗauki abubuwa kawai ba… a hankali yake bi shelf ɗaya bayan ɗaya, yana tunanin duk abin da zai iya zama buƙatar Inteesar.
Ya ɗauki rice, ya dauki kayan abinci rice, spaghetti, macaroni, couscous da sauran kayan masarufi, daga nan sai kayan tea da su junk’s food irinsu, cornflakes, golden morn, oats. Daga nan sai ya dauki bottled water, fruit juice, soft drinks. Ya tsaya wajen vegetables, fresh tomatoes, scotch bonnet, bell peppers, onions, carrots, cabbage, lettuce, cucumber, green beans, spring onions, parsley, coriander. Sannan ya wuce wajen nama, jan nama, kazar gida, frozen chicken, minced meat, kifi, shrimps. Sai ya tsaya ya ɗauki butter, cheese, mayonnaise, ketchup, spices iri-iri, seasoning cubes, cooking oil, olive oil, da sauran kayan girki. Hatta kayan tsaftace gida bai manta ba, detergent, disinfectant, air freshener, kitchen towels, tissue, garbage bags, dishwashing liquid. Komai ya siya, ba don yana son cika gidan da kaya ba… sai don ba ya son ta nemi wani abu ta rasa.
Daga supermarket ɗin kuma… wani sanannen eatery ya tsaya, ya saya musu abincin. Rice, grilled chicken, salad, da chilled drinks.
Karfe biyu daidai na rana motarsa ta dawo kofar gidan. Bai shiga ciki ba, ya tsaya a wani masallaci na kusa ya gabatar da sallah, sannan ya karaso daidai kofar gate din. A wannan karon ma, sai da ya fito da kansa daga motar, ya tura katakon gate din ya bude shi gaba ɗaya, sannan ya dawo ya shigo da motar cikin harabar gidan. Ya sake fitowa ya rufe gate din da kyau, sannan ya fara kwashe ledojin kayan abincin daki-daki yana shigar da su cikin falon, ya dawo. Ya dauko babban takeaway din abincinsu ya shigo da shi, sannan ya maida kofar falon ya rufe ta ruf.
Bayan ya ajiye ledojin takeaway din a kan dining table, ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, sannan ya haura sama zuwa dakinsa. Jikinsa duk ya yi tsami, don haka ya rage kayan jikinsa ya shiga bandaki ya sako sanyayyen wanka. Ko mai bai shafa ba ya zura farar jallabiya kawai, sannan ya juyo ya dawo ƙasa zuwa falon.
Sai a lokacin ya tsaya dadi-daki yana karewa falon kallo. Komai yana nan yadda suka bar shi tun sassafe da suka shigo gidan, babu abin da aka taɓa. Wannan ya ba shi tabbacin cewa tun lokacin da Inteesar ta haura sama, ba ta sake tako kafar ta ƙasa ba. Umar ya ajiye wayarsa a kan sofa, ya dauki daya ledar takeaway ya sake nufar stairs. Takun takalminsa yana fita a nutse har ya isa daidai kofar dakinta. Ya tsaya na wasu dakiku, sannan ya daga hannunsa ya yi knocking a hankali.
Shiru ya ji babu alamun amsa. Ya ɗan daddale handle din kofar, luckily sai ya ji ta a bude ba ta rufe ba. Ya tura kofar kaɗan tare da tura kansa ciki. Daga nan bakin kofar, idanunsa suka hango ta. Takure a kan gadon, daga gani ba da shiri baccin ya dauketa ba, rabin jikinta ne kawai ke saman gadon, yayin da kafafuwanta ke ƙasa. Gaba daya yanayin ya nuna kishingida kawai ta yi da niyyar hutu, ba ta san sanda barci ya yi awon gaba da ita ba.
Kamar wanda ake sarrafawa da remote control, Umar ya tsinci kansa da kasa janye idanunsa daga gare ta. Gashin kanta a baje a kan pillow, jikinta daure yake da towel kaɗai tun daga saman kirjinta. Saboda yanayin baccin, towel din ya ɗan zame ƙasa kaɗan kusa daga kirjinta, yadda take sauke numfashi a hankali sai ya ba wa kirjinta damar yin sama da kasa a natse.
Wani irin abu ya daki ƙirjin Umar, nan take cikin mugun sauri ya dauke idanunsa gaba ɗaya daga kanta, da sauri ya ajiye ledar takeaway din hannunsa a kan wani stool dake kusa dashi, bai sake ko kallon inda take ba, ya juya da sauri ya fice daga dakin, ya jawo mata kofar.
Sorry for the typos not edited
*KADDARAR ZUCIYA*
*CHAPTER EIGHTY-THREE: 83*
*A HOUSE OF SILENCE*
*JIDDAH BARKUM*
*_*___
Saukowarsa ƙasa ke da wuya, Umar ya tsinci kansa da kasa zama a gu guda. Ya dinga gidaddaba a tsakar falon, sanyin fargaba da bugun zuciya suna gauraye da janyewar numfashinsa. Hoton yadda ya ganta a kwance— cikin wancan yanayin tana barci cikin kwanciyar hankali— ya ki bace masa a rai. Ya dafe goshinsa da hannunsa na dama, yana jin yadda wani sashe na zuciyarsa ke tunatar da shi matsayinsa a halin yanzu, shi din mutumin da ke kokarin gina sabuwar yarda da amana tsakaninsu.
Ya juyo ya kalli ledojin abincin da ya ajiye a kan table, sai ya taka a hankali ya zauna a dining din ya fara bude abincin.
Bayan kamar 30mins Inteesar ta fara motsawa a hankali. Sanyin AC din dakin ya ratsa ta, wanda hakan ya sa ta farka daga nauyin barcin da ya kwashe ta. Ta bude idanunta a hankali tana kallon ceiling din dakin, kafin ta juya ta zauna sosai a kan gadon. Lokacin da ta kalli agogon bango, ta ga har uku da rabi ta gota.
Ta miƙe da sauri tana kokarin gyara daurin towel dinta, tana mamakin yadda barci ya kwashe ta a hakan. Tana juyawa domin ta tashi ta nemi kayan da zata sa, sai idanunta suka sauka a kan ledar eatery din da ke ajiye a kan stool din kusa da kofa.
Gabanta ya faɗi. Ta san tabbas ba ta shigo da wannan ledar ba. Kuma a gidan nan, babu kowa sai... Yaya Umar.
Wata irin kunya da fargaba suka mamaye ta lokaci guda. Ta dafe kumatunta, tambayoyi suna mata yawo a kai: shin yaushe ya shigo? Kuma a wani yanayi ya ganta?
Ta sake duban kanta ta cikin mirror, nan take gabanta ya sake tsananta faɗuwa da ta ga ashe towel ɗin ma ya sauka ƙasa sosai, kirjinta daga sama sama, gashi nan visible. With a racing heart, ta hanzarta damƙe shi da sauri ta sake matse daurin. Tana jin kamar har yanzu idanun Yaya Umar na kanta, wani irin intense embarrassment ya ziyarce ta.
Swiftly, ta miƙe ta nufi wardrobe ɗinta ta buɗe ta janyo wata sanyayyiyar free-size gown ta zura ta sama, without even thinking of putting on a bra. Her only priority at that moment was to get out of that towel.
Ta tura lallausan gashin kanta cikin hula, sannan ta ƙarasa gaban mirror ta fesa mata daddadan turare. Ta juya ta koma toilet tayi alwala, tayi zuhr prayer bayan ta idar ta ninke hijab din ta tashi.
Sai a lokacin ne ta tuna rabonta da abinci tun jiya da dare a gida. Ta kalli stool ɗin nan, ta ƙarasa ta ɗauko ledar takeaway ɗin, sannan ta dawo kan sofa ta zauna ta daura abincin a kan table din gabanta.
Ta yi "Bismillah" sannan ta fara cin abincin very gently. After eating just a few bites, ta ajiye saboda zuciyarta ba ta sake gaba ɗaya ba, tana ta tunanin ko a wanne yanayi Yaya Umar ya ganta. Sai kuma ta turo baki, “kawai sai mutum ya dinga shiga dakin mutane babu sallama.”
Ta koma kan gado ta sake kwanciya, sai tunaninta ya tafi kan baby Aamaan.
Da sauri ta dauko handbag dinta da ke kan bedside, ta buɗe ta zaro wayarta ta danna kiran Mommy. Once, twice... no answer. She tried for the third time, amma mommy bata daga ba, amsa daya ce, no answer. Ta turo baki cike da shagwaba kamar Mommy na kallonta.
Shortly after, aka kira sallar la'asar. Ta miƙe ta gabatar da sallah tare da yin adkhar ɗin yamma. Kawai sai ta ji ta gaji, wannan kwanciya kwanciya. Ta nufi wardrobe da niyyar ta gyara ta, amma tana budewa sai ta ga, everything was neatly arranged, looking perfectly organized.
Ta koma kan sofa ta zauna a hankali. Har yanzu shiru ne ya mamaye gidan. Ta sauke wata siririyar ajiyar zuciya. Sannan ta ɗauki wayarta da ke kan center table. Ba tare da wani tunani mai yawa ba… ta danna number Humaira.
Wayar ta fara ringing. Humaira na ta dariya tun kafin ta yi magana. Wayar na kan loudspeaker saboda tana ta faman dariya, “amaryaaaa…” ta ja sunan da wata irin sigar tsokana, “ba kya laifi fa.”
Inteesar ta yi wani ƙaramin tsaki, “mtsssw. ke matsalata dake kenan. na kira ki ne mu ɗan yi magana ki rage min zaman shiru… …amma kin fara wannan shirmen naki.”
Humaira ta ƙara ƙyalƙyalewa da dariya, “lallai ma, Intee. a kai ki gidan miji yau… …amma har kin fara neman wanda zai debe miki kewa.”
Inteesar ta zaro ido, “Humaira! wai kina da hankali kuwa?” Humaira ta ƙi tsayawa, “ai ni ban ce komai ba. kawai na ga after just few hours…”
Inteesar ta yi dariya kaɗan duk da ta yi ƙoƙarin ɓoye ta, “kanki da matsala wallahi.” Humaira ta yi saurin cafewa, “aha! kin yi dariya! I finally got you.” Inteesar ta girgiza kai, “ki rabu da ni.”
Humaira ta sake rage murya cikin sigar tsokana, “ko dai… …Yaya Umar ya barki ne ya je sayo miki kajin amarci kika ji gidan ya yi miki shiru?” Inteesar ta yi shiru. Shirun nata ya sa Humaira ta ƙara dariya, “wai da gaske? Intee! don't tell me kina missing him already.”
Inteesar ta turo baki, “kin gama? ko akwai sauran abubuwan da za ki ƙirƙiro?” Humaira ta ce, “wallahi idan ni ce… …ina ganin idan na yi aure… …first one week… …I won't even know where my phone is.” ta fashe da dariya, “no calls. no chats. no social media. ni da mijina kawai. having the best moment of our lives.”
Inteesar ta girgiza kai tana murmushi, “you are not serious, Humaira.” “Hajiya Amarya kenan.” Inteesar ta girgiza kai tana dariya, “kinga ni dai… …sai anjima dan idan na kira ki ma ba amfani.”
Humaira ta yi saurin cewa, “why? Yaya Umar zai kwace wayar ne?” Inteesar ta yi murmushi, “saboda idan na ci gaba da sauraren shirme irin naki… …zan fara nadamar da na kira ki.”
Humaira ta fashe da wata irin dariya mai ƙarfi, “Allah ya ƙara muku zaman lafiya. sai dai ki sani… daga yau… …duk lokacin da na kira ki… …ba zan ce Inteesar ba. Gimbiyar yaa Umar zan riƙa ce miki.”
Inteesar ta dafe goshinta, “oh God. this girl! kin cika surutu.” Humaira ta yi murmushi, “and you love me for it.” Inteesar ta lumshe ido tana murmushi a hankali, “maybe… just a little.” Humaira ta yi ihu da farin ciki, “I knew it!” dariyar Humaira ta cika wayar. Ita ma Inteesar… ba tare da ta shirya ba… ta tsinci kanta tana dariya. A karo na farko tun bayan shigowarta gidan… wata yar ƙaramar dariya ta kuɓuce mata, dariyar da ta ɗan rage mata nauyin da ke kan zuciyarta.
—————
*Four Weeks Later…*
Kwanaki sun ja. Rana ta koma mako. Mako kuma ya koma wata. Cikin ƙiftawar ido… aure ya cika sati huɗu. Amma duk da haka… a gidan nan har yanzu komai yana tafiya ne cikin wani irin shiru.
Tun ranar da Inteesar ta shigo