Kaddarar Zuciya Book 2 Complete JIddah Barkum

Author :  Jiddah Barkum Category :  Read Hausa Novels

Chapter   7 / 40

18K to 21K   out of 117.5K words

Inteesar ta zaro ido, “ni?” “eh, ki haife shi, in huta.” Inteesar ta fashe da dariya, “kaiii! wa ya ganni da ciki? inna lillahi!” Dariya suka saka su biyun.

A daidai lokacin… sai suka ji takun sauka daga staircase. Inteesar ta haɗiye dariyarta, ta gyara zamanta. Nana kuwa… har yanzu murmushin yana kan fuskarta. Umar ne, sanye yake da grey coloured kaftan mai sauƙi, agogon hannunsa ya yi matching da takalmansa, ya sauko yana gyara cuff ɗin hannunsa. Inteesar ta kalleshi, “Yaya… ina kwana.” Ya yi murmushi, “morning, Intee, how are you doing? kin tashi lafiya?” Ta gyada kai, “alhamdulillah.” “good,” ya amsa cikin gamsuwa. Sannan idanunsa suka koma kan Nana, “wife.” Nana ta ɗaga kai, “na’am Babe.” “zan fita, Khalid yana jirana, za mu je mu duba construction site ɗin, engineer ya ce an kusa kammalawa so we need to be there.” Nana ta buɗe baki, “Babe… breakfast fa?” Umar ya ɗan yi murmushi, “kin manta yau Monday, ina azumi.” Nana ta buga goshinta da tafin hannunta, “Allah! na manta.” Inteesar ta yi murmushi tana kallonsu. Umar ya matso kusa da Nana, ya sunkuya kaɗan, “bye.” Sai ya ɗan kalli cikinta, “please… don’t do what I cannot do.” Nana ta yi ƙaramin murmushi, “alright dear, take care.” Ya gyada kai, “in sha Allah.” Sai ya juya, ya wuce kusa da Inteesar ya fita, ƙofar ta rufe a bayansa.

Inteesar kuwa… ta sauke kanta ƙasa a hankali. Nana ta yi shiru na wasu daƙiƙu tana kallon Inteesar, sai kuma ta miƙa hannu zuwa drawer ɗin da ke gefen carpet ɗin, ta buɗe shi a hankali, ta ciro wani ƙaramin littafi mai kyau, mai murfi mai launin cream da zinari mai laushi a gefe. Ba diary ba ne sosai, ba kuma memo ba, ya yi kama da wani ƙaramin journal da aka tsara cikin tsari na musamman. Ta riƙe shi na ɗan lokaci kafin ta miƙa wa Inteesar, “Princess…” Inteesar ta karɓa da mamaki, ta juya littafin tana kallonsa, “nawa ne wannan?” Nana ta yi murmushi kawai, “naki ne.” Inteesar ta ɗan ɗaga gira, “na buɗe?” Da ta kai hannu kan murfin… sai Nana ta yi saurin cewa, “a’a.” Inteesar ta tsaya, ta ɗago ta kalleta. Nana ta yi wani sassanyan murmushi mai cike da natsuwa, “karki buɗe yanzu.” Inteesar ta zaro ido cikin wasa, “to yaushe zan buɗe?” Nana ta jingina da pillow ɗin bayanta, ta shafa cikinta a hankali, “ki bari… …sai ranar da na haihu.” Inteesar ta yi murmushi. Nana ta ci gaba da cewa, “idan mun dawo gida… …baby yana wajanki, ni kuma ina barci saboda gajiyar haihuwa…” ta yi dariya kaɗan, “a lokacin ne za ki buɗe.” Inteesar ta rungume littafin a ƙirjinta, “toh shikenan.” Ta yi dariya cikin wasa, “Allah ya kaimu, Allah ya sa ma ki haihu yau ɗin nan.” Ta ɗan ɗaga littafin, “kinga kenan… …zuwa dare zan buɗe shi.” Ta matso kusa da Nana kamar yarinya, “wallahi na matsu, in ji me kika ɓoye a ciki.” Nana ta yi ƙaramar dariya, amma ba ta amsa ba, ta dai ci gaba da kallon Inteesar cikin wani irin kallo mai cike da ƙauna… kallon da kamar yana ƙoƙarin haddace fuskarta. Inteesar ba ta lura da hakan ba, ta rungume ƙaramin littafin cikin walwala, “i promise, ba zan buɗe shi ba har sai lokacin da kika ce.” Nana ta gyada kai cikin nutsuwa, “good girl.” Sai ta miƙa hannu… ta shafa gefen kumatun Inteesar a hankali, “…na gode.” Inteesar ta yi murmushi, “saboda me?” Nana ta ɗan yi shiru, sai ta ce cikin ƙaramar murya, “saboda komai.” Inteesar ta yi dariya, “Yaya Nana, kina bani mamaki yau.” Nana ta yi murmushi kawai, ba ta ƙara cewa komai ba.

A daidai lokacin ne wayar Nana ta yi ringing, “Small Mum ❤️” sunan ya bayyana a saman screen ɗin. Nana ta ɗan yi murmushi, murmushin da ya tsaya iya lips ɗinta, ba irin murmushin da yake fitowa daga cikin zuciya ba. A hankali ta ɗan sace kallon Inteesar ta gefen ido, ta ga wayarta take ɗan dannawa, sai ta ja numfashi, ta yi sliding ta ɗaga kiran, ta kai wayar kunnenta, “assalamu alaikum Ummie.” Daga ɗayan ɓangaren… muryar Hajiya Maimuna ta amsa cikin nutsuwa, “wa alaikumus salam, Nana… yaya kike?” Nana ta yi murmushi, “alhamdulillah, lafiya lau.” “ya jikinki?” Nana ta shafa cikinta a hankali, “alhamdulillah, da sauƙi sosai.” Hajiya Maimuna ta ce, “toh Allah ya sauƙaƙa, Allah ya raba lafiya.” Nana ta amsa da ladabi, “ameen ya Rabb.”

Inteesar kuwa… har yanzu idonta na kan wayarta, sai dai kunnuwanta… na ɗan kamo hirar, ba wai tana saurare da gangan ba, sai dai muryar Ummie tana fita fili. Na ɗan lokaci… sai Hajiya Maimuna ta yi shiru, daga bisani kuma… ta sake magana, sai dai… a wannan karon… muryarta ta sauya, “Nana…” Nana ta amsa, “na’am Ummie.” “haukanki har ya kai wannan matakin ne?” Nana ta ɗan haɗe gira, “Ummie?” Hajiya Maimuna ta ci gaba, “duk ’yan uwanki… sai da kika sake gayyato yarinyar nan.” Nana ta yi shiru. “kin san irin haukan da Umar yake yi a kanta, amma kika rufe ido… kamar ba ki san komai ba.” Nana ta ɗan gyara zamanta, “Ummie…” amma Hajiya Maimuna ba ta bari ta yi magana ba, “kika dawo da ita gidanki, bayan aurenta ya rushe… ba kya ganin hakan a matsayin barazana gareki?” ta sauke numfashi, “kina so ne a liƙa masa ita? ko?” Idanun Nana suka lumshe, ta san halin Ummie, idan ta fara magana cikin wannan yanayin… sai ta gama. “idan so kike ya aure ta…” muryar Hajiya Maimuna ta ƙara nauyi, “ai ga ki… ga ta nan, Nana… ki aura masa.” Kalmar ta sauka cikin falon kamar dutse.

Nana ta ɗaga idanunta, kai tsaye… suka sauka kan Inteesar. Tun da farko… Inteesar ba ta nuna komai ba, wayarta ce kawai a hannunta, amma… yadda yatsunta suka tsaya daga scrolling… ya nuna… ta ji komai. Ba tare da ta ɗaga kai ba… ta miƙe tsaye cikin nutsuwa, ba ta ce uffan ba, ba ta nuna fushi ba, ba ta nuna damuwa ba, kawai… ta juya, ta nufi stairs cikin takunta mai natsuwa. Nana ta bita da ido, zuciyarta ta yi nauyi, ta san… tabbas Inteesar ta ji komai. Da ta ɓace daga ganinta… Nana ta sake mayar da wayar kunnenta, ta sauke wani dogon numfashi, “wallahi Ummie… ba haka bane, ba abin da kike zato ba ne.” Ta yi shiru kaɗan, sannan ta ci gaba cikin nutsuwa, “yanzu… Yaya Umar ya ajiye komai, ya wuce wannan maganar tun da dadewa.” Ta sake kallon hanyar da Inteesar ta bi, sannan ta ce, “kuma ita Intee… wallahi… ta zo ne saboda na kira ta, saboda halin da nake ciki, saboda ta taimaka min, shi kaɗai.” Hajiya Maimuna ta yi shiru daga ɗaya ɓangaren, sai dai Nana ta san… har yanzu ba ta gamsu ba. Don haka cikin murya mai cike da girmamawa ta ƙara da cewa, “Ummie… don Allah… ki daina wannan tunanin kinji, ba na so… …ta ji kamar ta zama nauyi a gidan nan.” Falon ya sake yin shiru, sai ƙar AC da ke kaɗawa cikin sanyi. Nana kuwa… har yanzu tana riƙe da wayar a kunnenta, amma zuciyarta… na bin Inteesar ne, domin ta san… wasu kalmomi… ko da mutum bai yi kuka ba… suna iya barin tabo a zuciya.

Bayan wayar ta katse… Nana ta sauke numfashi a hankali, ta ɗan lumshe idanunta na wasu daƙiƙu kafin ta miƙe tsaye. A hankali ta fara takawa zuwa ɗakin Inteesar. Da ta isa bakin ƙofar… ta yi sallama a hankali, “assalamu alaikum.” Ba ta ji amsa ba, ta tura ƙofar cikin nutsuwa. Dakin babu kowa, sai dai… ta ji sautin ruwan shower daga bathroom, alamar Inteesar tana wanka. Nana ta yi murmushi kaɗan, ta ƙarasa bakin gado, ta zauna cikin tana jiranta. Kusan mintuna goma suka wuce, sai ƙofar bathroom ta buɗe. Inteesar ta fito sanye da farin towel da ta ɗaure daga ƙirji zuwa ƙasa, ƙananan digon ruwa na saukowa daga gashinta zuwa kafaɗunta. Da ta ɗago… sai ta hangi Nana zaune bakin gadonta, ta tsaya cak, “Yaya Nana?” ta yi dariya, “lafiya?” ta ƙarasa gare ta, ta zauna kusa da ita, “ko dai…” ta ɗan taɓa cikinta cikin wasa, “…labour ne ya zo? mu tafi asibiti?” Nana ta fashe da dariya, “eh mana, shi ne na zo na kira ki.” Inteesar ta haɗa baki, “kai! kar ki tsoratani.” Duk suka yi dariya. Dariyar ta lafa… sai Nana ta kama hannun Inteesar cikin nata, ta shafa bayan hannunta a hankali, “Intee… karki damu da abin da Ummie ta faɗa, kin san halinta.” Ta yi shiru na ɗan lokaci, “Daddy… da Abbana ma… haƙuri suke yi da ita, saboda haka… kada ki saka maganarta a ranki, kin ji?” Inteesar ta tsaya tana kallon Nana, sai wani ƙaramin murmushi ya bayyana a fuskarta, ta matse hannun Nana cikin nata, “ai… Yaya Nana… na saba.” Nana ta haɗe gira kaɗan. Inteesar ta yi murmushi, “mutane suna faɗar abubuwa da yawa, ba duk abin da mutum ya ji ba ne ya kamata ya ɗauka ya zaunar a zuciya.” Ta ɗan yi dariya, “ki kwantar da hankalinki, wallahi… ba na fushi, ba kuma zan taɓa yin fushi da Ummie ba.” Ta ɗora kanta kaɗan a kafaɗar Nana, “ina mata uzuri.” Nana ba ta ce komai ba, sai ta ci gaba da kallon Inteesar, a zuciyarta kuwa… ta san Princess nata tana murmushi ne kawai, amma… akwai wasu kalmomi da ko mutum bai nuna ba… sai sun bar wani ɗan tabo a zuciya. Ta ja Inteesar jikinta, ta rungume ta a hankali.

*Daren ranar*

Daren ya yi tsit, shiru irin na ƙarshen dare ya mamaye gidan gaba ɗaya, sai ƙar AC mai taushi da kuma iska da ke bugun labulen ɗakuna. A cikin ɗakinta kuwa… Inteesar tana zaune kan sallayarta, ta gama idar da sallar Tahajjud da Wutri kenan. Ta jingina bayanta da wardrobe da ke gefen gadonta, idanunta a lumshe, yatsunta na jan tasbaha cikin nutsuwa, bakinta kuwa… zikiri yake yi cikin sanyin murya, “subhanallahi wa bihamdihi… subhanallahil azeem…” tun da ta tashi wajen ƙarfe biyu da rabi na dare… ba ta sake samun barci ba, ta yi ta juyi kan gado, har daga ƙarshe… sai ta miƙe, ta yi alwala, ta tsaya gaban Ubangijinta. Yanzu kuma… zikiri kawai take yi. Sai dai… a cikin zuciyarta… akwai wani irin rashin natsuwa da ba ta san dalilinsa ba. Ta buɗe idanunta a hankali, ta kalli agogon bangon ɗakin, 3:20 AM.

A dai-dai lokacin… ƙar knocking ta katse shirun ɗakin. Inteesar ta buɗe idanunta a hankali, gabanta ya faɗi, da sauri ta ɗaga kanta ta kalli agogon bango, “a wannan lokacin?” kafin ta yi wani tunani… sai aka sake knocking, amma wannan karon ya fi na farko ƙarfi kaɗan, sai kuma wata murya ta fito daga bayan ƙofar, “Inteesar…” muryar Yaya Umar ce. Da jin yanayin muryarsa… gabanta ya sake faɗuwa, ba muryar mutum mai nutsuwa ba ce, muryar ce ta mutum da ke ƙoƙarin danne tashin hankali. Inteesar ta miƙe tsaye da sauri, “na… na’am, Yaya…” ta faɗa cikin ruɗani, ba tare da ta tsaya gyara komai ba… ta ƙarasa bakin ƙofar, ta buɗe ta da sauri. Ƙofar ta buɗe… idanunta suka sauka kan Umar. Sanye yake cikin farin T-shirt da baƙin wando na bacci, sumarsa ta ɗan hargitse, fuskarsa ta sauya gaba ɗaya, ba irin nutsuwar da ta saba gani a tattare da shi ba. A karon farko… ta ga damuwa ƙarara a idanunsa, numfashinsa ma yana fita da sauri. Inteesar ta ji gabanta ya ƙara faɗuwa, “Yayaa…” ta furta cikin rawar murya, “lafi…” har ta fara tambayar lafiyarsa… sai ya katse ta, “mu je.” ya faɗa cikin gaggawa, “Nana… she’s bleeding.” ya haɗiye yawu, “I think… she’s in labour.”

Ai kafin ya gama rufe bakinsa… Inteesar ta riga ta fice da gudu, ko silifas ba ta tsaya ɗauka ba, ta riƙe gefen doguwar rigarta da hannu ɗaya, ta nufi corridor ɗin da zai kai ɗakin Nana cikin sauri. Umar ya tsaya na ɗan daƙiƙa yana kallon yadda take gudu, sai shi ma ya bi bayanta cikin sauri. Corridor ɗin ya yi tsit, sai sautin takunsu kaɗai ke amsawa a cikin gidan. Da suka isa bakin ƙofar ɗakin… ƙofar a buɗe take. Inteesar ce ta fara shiga, abin da idanunta suka gani… ya sa zuciyarta ta buga. Nana na zaune bakin gado, hannunta ɗaya na riƙe da cikinta sosai, ɗaya hannun kuma ta dafe gefen gadon, fuskarta ta cika da zufa, numfashinta yana fita a hankali. A gefen ƙafunta kuwa… ga ɗigon jini ya sauka kan farin tiles ɗin ɗakin. Inteesar ta zaro ido, “Yaya Nana!” ta ƙarasa da sauri ta durƙusa a gabanta, ta kamo hannunta, hannun ya yi sanyi, “Yaya Nana… ki kalle ni.” Nana ta buɗe idanunta a hankali, da ta ga Inteesar… sai ta yi murmushi mai rauni, “Intee…” ta furta da ƙyar, “kada ki tsorata…” wata irin azaba ta sake ratsa cikinta, ta runtse idanunta, numfashinta ya ɗauke na wasu daƙiƙu, “innalillah…” ta furta cikin wahala. Inteesar ta ji hawaye sun cika mata idanu, amma ta haɗiye su, ba lokacin kuka ba ne, ta matse hannun Nana cikin ƙarfi, “Yaya Nana… kada ki damu, in sha Allah komai zai tafi lafiya.”

A bayansu… Umar ya riga ya ɗauko hospital bag ɗin da suka gama shiryawa tare da Inteesar jiya da dare, ya ɗauki key ɗin mota daga kan dressing table, ya juya ya kalli Inteesar, muryarsa har yanzu cike take da damuwa, “Intee… za ki iya taimaka min mu kai ta mota?” Inteesar ta gyada kai cikin gaggawa, “eh, Yaya.” Ta miƙa hannayenta, a hankali ta taimaka wa Nana ta tashi daga bakin gadon. Da Nana ta tsaya… sai ta ɗan karkata saboda wani sabon ciwo da ya ratsa ta, da sauri Umar ya ƙaraso, ya riƙe ta daga ɗaya gefen, Inteesar kuma ta riƙe ta daga ɗayan gefen. A hankali… cikin kulawa… suka fara fito da ita daga ɗakin, yayin da zuciyar kowane ɗayansu… ke bugawa da fatan abu ɗaya kawai, Allah ya sauƙaƙa.

Sorry for the typos not edited

*KADDARAR ZUCIYA*

*CHAPTER SEVENTY-TWO: 72*

*NANA ASEEYAH 💔*

*JIDDAH BARKUM*

A hankali… suka fito daga cikin ɗakin. Inteesar na riƙe da Nana ta gefen dama, Umar kuma na riƙe da ita ta ɗayan gefen. Kowane taku da Nana za ta yi… sai ta ɗan tsaya, numfashinta yana fita da ƙyar. Lokaci zuwa lokaci kuma… wani irin ciwo mai ƙarfi yana tasowa daga ƙasan cikinta har zuwa bayanta, sai ta matse hannun Umar da ƙarfi, ta runtse idanunta, “innalillahi…” ta furta cikin wahala. Umar ya ɗan sunkuyar da kansa gare ta, “ki yi numfashi, Wife…” ya faɗa cikin murya mai laushi, duk da tashin hankalin da yake ƙoƙarin ɓoyewa, “almost there…” Inteesar kuwa… ta ci gaba da shafa bayan Nana cikin tausasawa, “in sha Allah komai zai yi sauƙi, Yaya Nana.”

Da ƙyar suka isa compound din gidan. Da maigadin ya hango su… sai ya yi saurin buɗe ƙofar, fuskarsa ta nuna tsantsar ruɗani. Umar ya buɗe ƙofar bayan motar cikin sauri, shi da Inteesar suka taimaka wa Nana ta shiga. Saboda yanayin cikinta… sai suka zaunar da ita a back seat domin ta sami isasshen wuri. Inteesar ta shiga ta zauna kusa da ita, ta rungumo hannunta cikin nata. Umar kuwa… ya zagaya ya shiga mazaunin driver, ya ajiye hospital bag ɗin a kujerar gaban motar, ya ɗaura seat belt ɗinsa. Kafin ya kunna motar… sai ya ɗan waiwayo baya, idanunsa suka sauka kan Nana, “Wife…” ta buɗe idanunta da ƙyar, “ki daure, okay?” ta yi masa ƙaramin nod. Maigadin ya buɗe babban gate ɗin gidan gaba ɗaya, “Allah ya raba lafiya, Alhaji.” ya faɗa cikin ruɗani. Umar ya ɗaga masa hannu kaɗan, “ameen.” Sai ya taka accelerator, motar ta fice daga compound cikin sauri.

Kasancewar ƙarshen dare ne… hanyoyin Abuja sun yi shiru, fitilun titi ne kawai ke haskaka kwalta, ba cunkoso, ba hayaniyar motoci, sai motoci kaɗan da ke wucewa lokaci zuwa lokaci. Cikin motar kuwa… shiru ne ya mamaye komai, sai ƙar engine, da kuma numfashin Nana da ke sauyawa lokaci zuwa lokaci. Wani sabon contraction ya taso, Nana ta matse hannun Inteesar sosai, har sai da Inteesar ta ji zafin matsewar, “ahh…” Nana ta saki wata ƙaramar ƙara. Inteesar ta matsa kusa da ita, ta kamo fuskarta a hankali, “Yaya Nana… ki kalle ni.” Nana ta buɗe idanunta cikin wahala, “ina nan.” Inteesar ta yi murmushi, duk da hawayen da ke neman cika idanunta, “ki yi numfashi… in… out.” Nana ta bi umarninta, ta ja numfashi a hankali, ta sake fitar da shi. Umar kuwa… hannunsa ɗaya na kan steering, amma idanunsa suna yawan kallon rear-view mirror. Duk lokacin da ya ga ciwo ya kama Nana… sai zuciyarsa ta matse. Ya ƙara saurin motar cikin kulawa, ba gudun da zai jefa rayuwarsu cikin haɗari ba… amma gudun da zai kai su cikin lokaci. Ya ɗan lumshe idanunsa na daƙiƙa guda, “ya Allah… ka sauƙaƙa mata.” Inteesar ta amsa da ƙaramar murya, “ameen.”

Mintuna goma sha biyar kacal… suka iso harabar babban asibitin. Tun kafin motar ta tsaya sosai… wasu nurses biyu da ward attendant suka fito da wheelchair cikin gaggawa. Umar ya fito daga motar da sauri, ya buɗe ƙofar bayan motar, Inteesar ta fara sauka, sannan ta taimaka wa Nana. Nurses ɗin suka karɓe ta cikin ƙwarewa, “ma’am, relax, we’ve got you.” ɗaya daga cikinsu ta faɗa cikin kwantar da hankali. A hankali suka zaunar da Nana a wheelchair. Umar ya ɗauki hospital bag, Inteesar kuma ta ci gaba da riƙe hannun Nana har zuwa ƙofar shiga. Da suka isa… wata nurse ta tsaya gabansu, “sir… only one person can follow her to the labour ward.” Umar da Inteesar suka kalli juna lokaci guda, dukansu suna son kasancewa tare da ita, amma ƙa’idar asibitin… ƙa’ida ce. Nana ta ɗaga kanta da ƙyar, idanunta suka sauka kan Inteesar, ta miƙo mata hannu, “Intee…” ta kira cikin raunin murya. Inteesar ta matso da sauri,

7 / 40