Kaddarar Zuciya Book 2 Complete JIddah Barkum

Author :  Jiddah Barkum Category :  Read Hausa Novels

Chapter   11 / 40

30K to 33K   out of 117.5K words

him home in about an hour, mun riga mun ba shi allurai da magungunan da yake buƙata, idan komai ya ci gaba da tafiya lafiya, cikin kusan awa ɗaya za ku iya tafiya da shi gida.” ya ɗan yi shiru kafin ya sake kallon Yaya Adam da muhimmanci, “but please… don’t leave him alone, he needs all of you now more than ever, amma don Allah… kada ku bar shi shi kaɗai, yana buƙatar ku a wannan lokacin fiye da kowane lokaci. support him, talk to him, encourage him, and make sure he doesn’t carry this grief alone, ku kasance tare da shi, ku riƙa yi masa magana, ku ƙarfafa masa gwiwa, kuma ku tabbatar bai ɗauki wannan baƙin cikin shi kaɗai ba. his recovery depends not only on the medications… but also on the love and care he receives from the people around him, warkewarsa ba magunguna kaɗai suka dogara da ita ba… tana kuma dogara ne da ƙauna da kulawar da zai samu daga mutanen da ke kewaye da shi.” Yaya Adam ya gyada kai a hankali, “in sha Allah, doctor… we’ll take good care of him.” likitan ya ɗan yi murmushi, sannan ya ce, “that’s all I wanted to hear.” daga nan Yaya Adam ya yi masa godiya, sannan ya fito daga office ɗin… zuciyarsa cike da damuwa fiye da yadda ya shiga.

Bayan an sallamo Umar daga asibiti… labarin cewa yana fama da ciwon zuciya kusan shekara ɗaya ya girgiza kowa. Babu wanda ya taɓa zargin hakan. Kowa ya zuba masa ido cikin tausayi. Yaya Adam, Abubakar, Khalil da Hashim duk sun yi mamakin yadda ya ɓoye musu irin wannan babban sirrin. Daddy kuwa… sai ya lumshe idanunsa ya sauke ajiyar zuciya. A ƙarshe… kowa ya yi masa fatan samun lafiya. Tun daga wannan ranar… ba wanda yake barinsa shi kaɗai, ana kula da shi tamkar ƙaramin yaro, duk abin da zai faranta masa rai ake yi, ba wanda yake son ya sake shiga damuwa.



Kwanaki bakwai da rasuwar Nana suka shuɗe. Gidan da kwanaki kaɗan da suka wuce yake cike da jama’a da kuka… yanzu ya fara yin shiru. Kowa ya fara shirin komawa gidansa, masu zuwa gaisuwa ma sun ragu. Sai dai… shirun gidan ya fi kowace hayaniya ciwo. Ko’ina ka kalla… sai ka tuna Nana, ƙamshinta, dariyarta, muryarta, da kuma ƙaramin Abdallah Aamaan da yake kwance yana barci ba tare da sanin irin gibin da mutuwarta ta bari ba.



A wani sashe na gidan… Hajiya Maimuna ta kebe da Hajiya Kaltume, mahaifiyar Nana. Dukkansu suna zaune a kan kujerun gadon ɗakin da suka sauka tunda suka zo gidan. Shiru ne ya ɗan ratsa tsakaninsu. Daga ƙarshe… Hajiya Maimuna ta sauke numfashi, ta dubi Hajiya Kaltume, “anty Kaltum…” Hajiya Kaltume ta ɗago kanta, “na’am Maimuna.” ta ɗan yi shiru kafin ta ce, “yanzu ya za a yi da Abdallah?” idanun Hajiya Kaltume suka sauka kan jaririn da yake barci cikin carry cot ɗinsa, wani irin tausayinsa ya cika mata zuciya, ta shafa gefen fuskarta a hankali, “zan so na tafi da shi.” ta faɗa cikin sanyin murya, “shi kaɗai ya rage min daga Nana.” ta haɗiye kukanta, “sai dai…” ba ta ƙarasa ba. Hajiya Maimuna ta haɗe gira, “sai dai me?” Hajiya Kaltume ta kalleta, “ba ni kaɗai ba ce da iko a kansa.” ta sauke numfashi, “mahaifinsa yana nan, ba zai yiwu in ɗauke shi ba tare da yardarsa ba.” Hajiya Maimuna ta ƙanƙance idanu, “kina nufin… za ki bar musu ɗan ne?” Hajiya Kaltume ta gyada kai a hankali, “ba sai abin da Umar ya yanke ba.”

Sai fuskar Hajiya Maimuna ta canza, ta ja dogon numfashi, “subhanallah. anty Kaltum… har yanzu kina kallon lamarin nan da wannan idon?” Hajiya Kaltume ta ɗan ɗago gira, “wane lamari?” Hajiya Maimuna ta matsa kusa da ita, “kashe miki ’ya.” kamar wadda aka doka… Hajiya Kaltume ta tsaya cak, ta zuba mata ido, “kashe min ’ya? kamar ya Maimuna?” Hajiya Maimuna ta yi murmushin da babu daɗi a ciki, “eh mana. toh… Umar ya saka son Inteesar a gaba, ba yau ba, ba jiya ba, ke ba ki gani ba ne? bai taɓa yi wa Nana ƙara a kan haka ba.” ta girgiza kai, “amma Nana… saboda haƙurinta, saboda kyakkyawar zuciyarta, sai ta dinga rufe ido, suna ci mata fuska.” Hajiya Kaltume ta buɗe baki za ta yi magana… sai Hajiya Maimuna ta ɗaga hannu, “a’a, ki bari na gama.” ta ci gaba cikin ɗacin rai, “kin ga abin da ya kashe Nana ko? likitoci ma sun ce hawan jini, toh me ya jawo mata hawan jinin? ba damuwa ba ce? ba tunani ba ne? ba tashin hankali ba ne?” ta buga ƙirjinta, “kuma ita wannan Inteesar… wai kina ganin ba ta son Umar? wallahi sonsa take, bari ki gani, na faɗa miki tun yanzu. ba daɗewa ba… za ki ji an ce sun yi aure. yanzu dai Nana ta ba su waje, sai ta fake da wai tana kula da Abdallah.” ta nuna inda jaririn yake, “kin ga yadda ta manne da yaron nan? ke kina ɗauka ƙauna ce? a’a, duk makirci ne, uwar ce ke kitsawa, yaron zai zama hanyar shiga, daga ƙarshe… a ce ai saboda yana buƙatar uwa, sai a ɗaura musu aure.”

Shiru ya mamaye wajen, na wasu daƙiƙu… Hajiya Kaltume ba ta ce komai ba, kawai… ta ci gaba da kallon Hajiya Maimuna, idanunta cike da mamaki. Daga ƙarshe… ta ja numfashi a hankali, “Maimuna…” ta kira sunanta cikin nutsuwa, “wannan da kika faɗa… magana ce mai nauyi.” ta girgiza kai, “ban ga abin da zai sa in zargi Umar ba, ko Inteesar, musamman a irin wannan lokacin.” ta ɗan yi shiru, hawayenta suka cika idanunta, “na rasa ’ya ta, amma ba zan ɗora wa wani laifin da ban gani ba.” ta shafa hawayen da suka zubo, “mutuwa… alƙawari ce daga Allah, idan lokacin bawa ya yi… ko ya yi me… ba zai tsallake ta ba.” ta kalli Hajiya Maimuna kai tsaye, “don Allah… kada mu bari baƙin ciki ya sa mu yi hukunci a kan mutane ba tare da hujja ba. kuma… game da Abdallah…” ta juya ta kalli inda jaririn yake, “shi yanzu amanar Umar ne, ni kakarsa ce, ba zan taɓa raba ɗa da mahaifinsa ba, matuƙar mahaifin yana raye, yana kuma son ɗansa.” Hajiya Maimuna ta tabe baki, ba ta gamsu ba, amma ta san… a yau… ba za ta iya sauya tunanin Hajiya Kaltume ba.

*KADDARAR ZUCIYA*

*CHAPTER SEVENTY-SIX: 76*

*THE DIARY*

*JIDDAH BARKUM*

Daddy ya dubi Umar cikin tausayi. Na ɗan lokaci bai ce komai ba, sai daga bisani ya sauke numfashi a hankali, “saboda halin da kake ciki…” ya ɗan dakata, “ina ganin ya kamata ka rubuta hutu a wajen aikinka.” ya ci gaba cikin nutsuwa, “ba zan iya tafiya Katsina in bar ka a nan kai kaɗai ba.” ya girgiza kai, “a’a. za ka bi mu Katsina, ka huta, ka samu kwanciyar hankali. in sha Allah… idan lokaci ya yi, idan Allah ya kawo sauƙi… daga baya sai ka dawo bakin aikinka.”

Umar ya ɗan sunkuyar da kansa, “to Daddy. duk hukuncin da ka yanke… …ni mai biyayya ne a gare ka.” wani ɗan murmushi mai rauni ya bayyana a fuskar Daddy, “Allah ya yi maka albarka.” ya faɗa cikin alfahari, “Allah ya ƙara maka haƙuri.” sai ya sake kallon Umar karo na biyu. A wannan karon… tambaya ɗaya ce a zuciyarsa, “maganar Abdallah fa?” ya tambaya cikin natsuwa, “a matsayinka na mahaifinsa… me ka yanke a kansa? za ka bar Hajiya Kaltume ta tafi da shi ne… ko kuma ya ya kake ganin za a yi?”

Nan take… Umar ya sunkuyar da kansa, ya daɗe bai ce komai ba, kalmomin sun tsaya masa a maƙoshi. A zuciyarsa… ba zai iya rabuwa da ɗansa ba, shi ne kaɗai abin da Nana ta bari masa, amma kuma… ya kasa cewa haka a fili. Daddy ya zuba masa ido, bai jira ya yi magana ba, tun kafin Umar ya buɗe baki… ya riga ya fahimci abin da ke cikin zuciyarsa. Nan take… wani tsohon al’amari ya dawo masa cikin ƙwaƙwalwa. Ranar da Hajiya Fateema ta rasu bayan ta haifi Inteesar… ’yan uwanta ma sun so su tafi da jaririyar, amma shi… ya ƙi, ya ce ba zai iya rabuwa da amanar matarsa ba. Yau… ga Umar ma yana cikin irin wannan yanayin. A hankali Daddy ya jinjina kai, “toh shikenan.” ya faɗa cikin fahimta, “Abdallah zai zauna tare da kai.” ya ɗan yi murmushi, “Inteesar tana nan, Haleema ma tana nan, za su kula da shi, in sha Allah.”

Umar ya ɗago kansa, wata irin nutsuwa ta sauka a zuciyarsa, “nagode Daddy.” ya faɗa cikin sanyin murya. Daddy bai amsa ba, kawai… ya ci gaba da kallon Umar, kallo mai cike da tausayi… da fahimta… domin shi kaɗai ya san irin ciwon da Umar yake ɗauke da shi, saboda shi ma… wata rana… ya taɓa tsayawa a daidai wannan gurbin.

*Bayan watanni shida da rasuwar Nana Aseeyah*

Rayuwa ta ci gaba, lokaci kuwa… bai taɓa jiran kowa ba. A hankali… raɗaɗin rasuwar Nana Aseeyah ya fara lafawa a zukatan mutane, ba wai sun manta da ita ba… sai dai rayuwa ta tilasta musu ci gaba. Amma… ba kowa ne ya warke ba.

Umar musamman… har yanzu bai dawo Umar ɗin da aka sani ba. Ya ƙara zama mutum mai tsananin shiru, ba ya yawan magana, ba ya yawan dariya, murmushinsa ma ya zama baƙo. Duk lokacin da ya samu kansa shi kaɗai… sai ya zuba wa sararin samaniya ido, ko ya zauna yana tunani na dogon lokaci. Wani lokacin ma… hawaye sukan cika masa idanu ba tare da ya sani ba. Sai Yaya Abubakar ya kan lura, saboda haka kullum yana ƙoƙarin cire shi daga cikin wannan yanayin. Wani lokaci ya kai shi yawo, wani lokaci su tafi gym, wani lokaci kuma su fita kallon ƙwallo… ko ma su shiga fili su buga ƙwallon tare. Kasancewarsa a Katsina tare da iyali… ya rage masa kaɗaici fiye da lokacin da yake Abuja. Sai dai… har yanzu akwai wani gurbi a zuciyarsa da babu wanda ya iya cikewa.

A wani ɓangaren kuma… Aamaan ya fara girma, yaron ya fara wayo, ya fara gane mutane, kuma ya samu kulawar da ko wane jariri yake buƙatar samu. Mommy Haleema… da Inteesar… su ne suka maye masa gurbin uwa. Sai dai… a wurin Aamaan… Inteesar ce mahaifiyarsa, ita kaɗai yake nema idan ya farka, ita kaɗai yake natsuwa a jikinta. Ko Umar wani lokacin idan ya karɓe shi… sai ya fara kuka, amma da zarar Inteesar ta karɓe shi… nan take yake yin shiru. Ita ce ke ba shi abinci, ita ce ke masa wanka, ita ce ke canza masa kaya, a ƙirjinta yake kwanciya har barci ya ɗauke shi, ita ce ke goya shi. Duk abin da uwa take yi wa ɗanta… Inteesar ce take yi wa Abdallah. Har mutane da yawa idan suka gan su tare… wadanda basu santa ba sukan ɗauka itace ta haifi yaron, ta kan yi murmushi kawai ha tare da wani bayani ba.



Wata rana da dare… gidan ya yi tsit, kowa ya kwanta. Inteesar tana kwance kan gadonta, Abdallah kuwa… yana kwance a ƙirjinta cikin nutsuwa, numfashinsa kaɗai ake ji yana fita a hankali, barci mai daɗi yake yi. Amma ita… barcin ya ƙi zuwa. Ta zuba wa silin ɗakin ido, tunani kala-kala na yawo a zuciyarta. Ba tare da ta shirya ba… sai wani abu ya faɗo mata, diary… diary ɗin Nana. Nan take zuciyarta ta buga. Tun ranar da Nana ta ba ta amanar diary ɗin… ba ta sake ko taɓa shi ba, ko dubawa ma ba ta yi ba. A hankali… ta sauke Abdallah daga ƙirjinta, ta kwantar da shi cikin kulawa a kan gadon, ta saka masa pillow a bayansa, ta kuma saka wani a gabansa. Ta san halinsa, da zarar ya farka bai gan ta kusa da shi ba… kuka zai fashe da shi. Da ta tabbatar yana barci sosai… sai ta sauko daga gadon ba tare da ta yi ƙara ba, ta nufi trolley ɗinta. Tun ranar da ta dawo daga Abuja… ba ta sake buɗe shi ba. Ta durƙusa a gabansa, a hankali ta buɗe zip ɗin, sai kuma ta sake buɗe wani ƙaramin zip da ke can ƙasa. Nan take… diary ɗin ya bayyana, har yanzu yana nan… yadda Nana ta ba ta shi. Inteesar ta tsaya tana kallonsa na wasu daƙiƙu, kafin ta miƙa hannu… ta ɗauke shi cikin kulawa, ta rufe trolley ɗin, ta mayar da shi yadda yake. Sannan… ta koma ta zauna a kan sofa, diary ɗin na hannunta, ta shafa murfinsa a hankali, numfashinta ya yi nauyi. Da ƙyar… ta buɗe shafin farko… hannunta na rawa… ta buɗe diary ɗin a hankali.

Shafi na farko… a saman takardar da rubutun Nana mai kyau ta fara bayyana, “bismillahir rahmanir rahim…” da idanunta suka sauka kan rubutun… numfashinta ya tsaya, kamar tana jin muryar Nana ce da kanta. Ta ɗaga hannunta a hankali ta shafi rubutun, hawaye suka cika mata ido, sannan ta fara karantawa…

“My angel… Inteesar…”

“idan kina karanta wannan diary… to hakan na nufin ban samu damar dawowa gare ku ba.”

Nan take… Inteesar ta dafe bakinta, “wai me yasa kika rubuta haka Yaya Nana…” ta girgiza kai cikin rashin yarda, hawayenta suka soma zuba ɗaya bayan ɗaya. Ta ci gaba da karantawa.

“na san za ki yi kuka, na san za ki yi fushi da ni, na san za ki ce na yi miki alƙawari zan dawo da baby… ki yi haƙuri angel… wallahi ban karya miki alƙawari da gangan ba, Allah ne ya fi son in dawo gare shi.”

Da jin wannan… Inteesar ta rufe diary ɗin da sauri, ta dafe ƙirjinta, “Yaya Nana…” ta fashe da wani irin kuka, kukan da ya fito daga can ƙasan zuciyarta. Ta jingina kanta da bayan kujera, sai da ta yi kuka mai tsawo… kafin ta sake buɗe diary ɗin.

“ki kula da baby na, duk abinda na haifa na baki, halak malak…”

“ba na jin tsoron barinsa… saboda na san yana hannun wacce ta fi ni son shi… ke. tun kafin a haife shi na san ke ce za ki zama komai a gare shi. ki riƙe shi kamar ɗanki, ki koya masa addini, ki koya masa mutunci, ki gaya masa mahaifiyarsa tana sonsa… ko da bai taɓa ganina ba.”

Inteesar ta sake fashewa da kuka, ta rungume diary ɗin a ƙirjinta, “na yi miki alƙawari…” ta furta cikin kuka, “wallahi zan riƙe shi kamar ɗana, ba zai taɓa kukan rashin uwa ba.” sai ta share hawayenta, ta ci gaba.

Rubutun ya ɗan tsaya… sai wani sabon layi, da alama… Nana ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta rubuta shi, “Intee… akwai wata amana kuma…” Inteesar ta lumshe ido, ta ci gaba da karantawa.

“ba baby kaɗai zan bar miki ba… akwai wani mutum… da yake buƙatar kulawa fiye da yadda yake nunawa. Umar.”

Da ganin sunan… Inteesar ta tsaya, ta lumshe ido, numfashinta ya fara nauyi.

“Tun kafin na aure shi… na san yana ɗauke da wani ciwo a zuciyarsa. ba ciwon da ido yake gani ba ne… ciwo ne da yake ɓoyewa da murmushi, da shiru, da ‘alhamdulillah’. na yi shekaru ina ƙoƙarin zama maganinsa… ban san ko na yi nasara ba.”

Inteesar ta girgiza kai, “a’a…” ta furta a hankali, hawaye suka sake zubo mata.

“idan Allah ya ƙaddara kika karanta wannan… ina da roƙo guda ɗaya. idan har kin ga maganin wannan ciwon… don Allah… ki taimaka ki ba shi. kada ki bar shi ya sake rayuwa shi kaɗai da wannan ciwon. domin Umar… ba ya iya faɗin abin da yake ji, sai ya binne komai a cikin zuciyarsa.”

Inteesar ta dafe bakinta, kuka ya sake ƙwace mata.

“kada ki yi tunanin ina ɗora miki wani nauyi. a’a… ina roƙonki ne saboda na san irin zuciyar da Allah ya baki. ki kula da shi… kamar yadda za ki kula da ɗan’uwanki. ki tuna masa cewa har yanzu akwai mutanen da suke sonsa… duk lokacin da kika ga ya sake yin shiru… ko kuma ya manta da kansa… ki tuna masa cewa har yanzu rayuwa tana da dalilin da zai ci gaba da rayuwa.”

Inteesar ta kasa ci gaba da karantawa, diary ɗin ya zame daga hannunta ya faɗi ƙasa, ta rufe fuskarta da hannayenta biyu, ta rushe da kuka, “Yaya Nana… me yasa kika bar ni da wannan amanar…” ta durƙusa ƙasa, kukan da take yi ya cika ɗakin. A ɗayan gefen gadon… Aamaan ya ɗan motsa cikin barcinsa, kamar ya ji muryarta. Inteesar ta share hawayenta da sauri, ta ɗauke shi ta rungume shi a ƙirjinta, sai ta sake ɗaukar diary ɗin, ta rufe ba tare da ta ci gaba da karantawa ba. Ta runtse idanunta, cikin kuka… ta yi magana da muryar da ita kaɗai da Allah suka ji, “…na yi miki alƙawari Yaya Nana. zan riƙe Abdallah. zan yi masa duk abin da uwa za ta yi masa… …amma…” ta yi shiru, sabbin hawaye suka sake zubo mata, “…game da Yaya Umar… Allah ka ba ni ikon cika amanar da ta bar min… domin ban san ta ya ya zan yi ba…”

Daren ya yi wa Inteesar tsawo matuƙa. Tun bayan da ta rufe diary ɗin Nana ta mayar da shi cikin trolley, ta koma ta kwanta… amma bacci ya ƙi zuwa. Duk lokacin da ta lumshe idanunta, kalmomin Nana ne suke dawo mata ɗaya bayan ɗaya, “ki kula da baby… ki taimaka wa Umar… addu’arki nake buƙata…” hawayenta suka ƙi tsayawa. Sai da asuba ta ketare kafin idanunta suka ɗan lulluɓe na ƴan mintuna.



Da gari ya waye… Inteesar ta tashi kamar ba ita ce ta kwana cikin kuka ba. Ta yi alwala, ta

11 / 40