Author : Jiddah Barkum Category : Read Hausa Novels
tana yaba girkin lokaci zuwa lokaci. “Wallahi Princess... kin iya girki sosai. Umar ya yi sa’a.”
Inteesar ta sunkuyar da kai cikin kunya. “Anty...” ta faɗa tana dariya.
Cikin hirar ne Anty Sameera ta fara ba ta labarin abin da zai kaita Katsina daga nan. “Kin san za a yi taro a gidanmu. Bangaren mahaifiyarmu ne za a yi taron. Na zo ne zan ƙarasa gyaran passport dina, daga nan zan wuce Katsina.”
Da sauri Inteesar ta ce, “Dama Yaya Umar ya bar ni in je nima.”
Anty Sameera ta yi murmushi. “To ki tambaye shi mana. Yanzu kin yi aure. Ya kamata idan akwai irin waɗannan abubuwa kina zuwa wajen dangin mahaifiyarki. Mu ma fa muna da hakki a kanki.”
Inteesar ta gyada kai. “In Sha Allah Anty.”
A dai-dai lokacin ne suka ji ana buɗe ƙofar falon. Yasmeen ce ta dawo daga makaranta. Da ta ga Anty Sameera, fuskarta ta washe. “Antyyy!” ta ƙarasa da sauri ta rungume ta.
Anty Sameera ta yi dariya. “Yar makaranta. Ya school?” “Alhamdulillah.”
Suka gaisa cikin mutunci, sannan Yasmeen ta shiga ta sauya kaya kafin ta dawo, suka ci gaba da hira tare.
⸻
*Bayan sallar Isha...*
Inteesar da Anty Sameera suna zaune a ɗakinta. Hirar ta ƙi ƙarewa.
Can Anty Sameera ta tsaya tana kallon Inteesar daga sama har ƙasa. Sai ta ɗan matso kusa da ita. “Princess...”
Inteesar ta amsa da murmushi. “Na’am Anty?”
Anty Sameera ta ɗan taɓa kumatunta. “Ni dai na ga kin ƙara kyau. Kuma...” ta ɗan lumshe ido tana sake kallonta, “kin yi kiba. Kin kuma sake haske.”
Sai ta ɗan karkatar da kai. “Ko dai... ciki ne da ke?”
Inteesar ta zaro ido. “Kai Antyyy!” ta turo baki cikin shagwaɓa. “Wallahi ni ban da komai.”
Anty Sameera ta yi dariya. “To shikenan. Za mu gani,” ta faɗa tana murmushi.
Sai ta ɗan yi shiru kafin ta ce, “Amma yanzu kam, ya kamata ki tafi ɗakin mijinki. Tun da na zo kina nan. Kar ya ga rashin hankalina a matsayina na uwa.”
Inteesar ta fashe da dariya. “Anty ai... shi kaɗai yake kwana a ɗakinsa. Ni kuma a nan nake kwana,” ta faɗa zuciyarta ɗaya, kamar tana magana ne kan abu mafi sauƙi a duniya. “Ko ban je ba, ba zai ce komai ba. Wallahi... Yaya Umar ai ko kwana muka yi a zaune babu ruwansa,” ta ƙarasa tana yar dariya.
Anty Sameera kuwa, ta hangame baki. Ta tsaya cak tana kallon Inteesar, kamar ta ji wani abu da ba taɓa tsammani ba. Na wasu daƙiƙu ba ta ce komai ba, sai kawai idanunta dake bin Inteesar cikin mugun mamaki.
“Me kika ce?” ta tambaya a hankali.
Inteesar ta ɗan yi dariya. “Na ce ai... shi a ɗakinsa yake kwana. Ni kuma a nawa. Tun ranar da na zo... haka muke.”
Shiru. Wani irin shiru mai nauyi ya rufe ɗakin.
Anty Sameera ta jingina bayanta da headboard. Idanunta suna kan Inteesar. A hankali ta ce, “Wait... ke da Umar... ba kwa kwana tare?”
Inteesar ta girgiza kai a nutse. “A’a. Ai Anty, shi ma bai taɓa cewa na kwana ba.”
Anty Sameera ta sauke numfashi. A zuciyarta kuwa tambayoyi ne suka fara taruwa. Tun yaushe? Me ya sa Umar zai zuba mata ido haka? Ko akwai wata matsala tsakaninsu? Ta san Umar sosai. Ta kuma san irin haukan son da yake wa Inteesar, sai dai idan akwai wani babban dalili.
Ta sake kallon Inteesar. Ta ga yadda take magana cikin rashin sanin cewa abin da ta faɗa ya girgiza ta gaba ɗaya. Sai ta haɗe rai, ta dubi Inteesar.
“Ashe dai ba ki da hankali.”
Inteesar ta ɗago a hankali tana kallonta.
Anty Sameera ta ci gaba da magana cikin tsananin takaici. “Wallahi na san daga ke ne. Ke ce nan da kanki za ki dinga ƙin zuwa ɗakin mijinki.”
Ta dafa goshinta. “Ke yanzu saboda rashin hankali sai an riƙa cewa ki je wajen mijinki?” Ta girgiza kai cikin takaici. “To bari ki ji. Kin san cewa duk daren da mace ta ƙi zuwa wajen mijinta ba tare da wani uzuri na shari’a ba, tana iya faɗawa cikin babban laifi? Ke kina zaune kina ɗauka abin wasa ne.”
Inteesar ta yi shiru. Ba ta iya cewa komai ba. Sai kallon Anty Sameera kawai take yi, idanunta cike da ruɗani.
Anty Sameera ta ƙanƙance ido. “Yanzu tashi. Ki shiga ki yi wanka. Wallahi kafin takaicinki ya sa na miki shegen duka a daren nan.”
Da sauri Inteesar ta miƙe. Ta fara tafiya a hankali tana jan ƙafafunta.
“Go,” Anty Sameera ta faɗa da ƙarfi.
Inteesar ta juya ta kalle ta. “Anty Sameera...”
Kafin ta ƙarasa magana, Anty Sameera ta zabura. “Kin tsaya kina kallona?”
Da sauri Inteesar ta shige toilet ta rufe ƙofa.
⸻
*Mintuna ashirin suka wuce, sai talatin. Har yanzu ba ta fito ba.*
Anty Sameera ta tashi ta nufi ƙofar toilet ɗin. Ta buga ƙofar sau biyu. “Inteesar.” Shiru.
Ta sake bugawa. “Wallahi idan na shigo ciki... ranki zai ɓaci.”
Da sauri ƙofar ta buɗe. Inteesar ta fito, kanta a ƙasa, idanunta sun yi ja saboda kuka.
Anty Sameera ta kama hannunta ba tare da ta ce komai ba. Ta ja ta har gaban mirror. Ta ɗauki body lotion. “Shafa.”
Inteesar ta karba ta fara shafawa.
Da ta gama, Anty Sameera ta buɗe jakarta. Ta ciro wani ƙaramin kwali mai kyau. Ta buɗe shi. A ciki akwai wata ƙaramar farar roba. Ta buɗe robar, ta ɗauko wasu ƙananan capsules guda uku. Ta miƙa mata. “Karɓi.”
Inteesar ta karɓa ba tare da tambaya ba. Ta haɗiye su da ruwa. Ta san Anty Sameera tana mata wasa sosai amma she’s no nonsense. Kuma ta san idan ta yi mata gardama, ba za ta ji daɗi ba.
Anty Sameera ta sake buɗe jakarta. Ta ciro wata kwalba mai ƙamshi, ta wata hadaddiyar khumra da kuma scented body oil mai ɗa sheƙi. Ta zuba kaɗan a tafin hannunta. “Matso ni ko na mangare ki.”
Da kanta ta fara shafa mata a wuyanta, hannayenta da sauran wajen da ya bayyana. Ƙamshin ya cika ɗakin da wani irin daɗin ƙamshi mai nutsuwa.
Daga nan ta nufi wardrobe. Ta tsaya tana kallon kayan Inteesar na wasu daƙiƙu. A ƙarshe ta zaro wata doguwar luxury net sleep gown mai launin ivory white, an yi ta da silk mai laushi kamar ruwa. Gefen hannayenta da ƙasan rigar an yi musu ado da French Chantilly lace mai launin silver, yayin da ƙananan Swarovski crystals ke walƙiya a gefen wuyanta da cuffs ɗinta cikin nutsuwa. Rigar tana da dogon zubi mai matuƙar kyau.
Ta miƙa mata. “Cire towel ɗin nan. Ki saka wannan.”
Jikin Inteesar har yanzu rawa yake yi. A hankali ta karɓi rigar, ta tsaya tana kallon rigar kamar za ta yi magana.
“Ba zaki saka ba?” Anty Sameera ta buga mata tsawa. Da sauri ta saka ta.
Anty Sameera ta sake ɗaukar wasu turarukanta, ta fara fesawa mata a dukkan jikinta har ya fara hawa kanta.
Sai ta zauna bayanta. Ta ɗauki comb. A hankali ta fara gyara mata gashinta, ba tare da gaggawa ba, kamar uwa tana shiryawa ’yarta ranar aurenta.
Daga nan ta ɗaure mata gashin cikin wani ƙaramin neat bun. Ta ɗan ja baya, ta tsaya tana kallonta na wasu daƙiƙu. Sai murmushi ya bayyana a fuskarta. “Subhanallah... har kinyi kyau.”
Inteesar ta sunkuyar da kai. Kunyar da take ji ta haɗu da tsoro da kuma wani sabon abu da zuciyarta ba ta iya fassarawa.
Anty Sameera ta ɗauko wani hijabi mai laushi har ƙasa. “Saka.” Ta jira har ta gama, sannan ta gyara mata shi da kanta
Ta dafa kafaɗarta.
“Yanzu...”
“Ki kama hanya ki tafi ɗakin mijinki.”
Sai ta ɗan tsuke fuska.
“Dan ubanki kuma wallahi idan na ji wani abu saɓanin abin da nake tunani za ki sha mamaki.”
Ta ɗan taɓa goshinta.
“Tunda ke shashasha ce wacce ba ta san abin da ke mata ciwo ba.”
Inteesar ta ji wani irin motsin rai ya tokare mata maƙoshi.
Hawaye suka sake cikowa idanunta.
Ta kasa cewa komai. Sai kawai ta gyada kai.
“Wuce ki tafi, kuma ina tsaye ina kalloki har ki shiga,” Anty Sameera ta faɗa.
Ta buɗe ƙofar ɗakin.
Ta fara tafiya.
Kowace taku da take yi, sai zuciyarta ta ƙara bugawa.
Hawayenta kuwa suna ci gaba da gangarowa.
Har ta iso bakin ƙofar ɗakin Yaya Umar.
Ta tsaya.
Ta ɗora hannunta a kan ƙirjinta. Numfashinta ya yi nauyi.
Ta share hawayen da bayan hannunta.
Ta ɗaga hannu cikin rawar jiki...
Ta fara buga ƙofar a hankali.
Sorry for the typos not edited
KADDARAR ZUCIYA
CHAPTER NINETY-THREE: 93
THE PROMISE OF GENTLENESS
JIDDAAH BARKUM
———-
This page is completely dedicated to Oumawwab nd Nrzaynerv love you guys bigg time😍😁💕——
Inteesar ta tsaya a bakin ƙofar ɗakin Yaya Umar. Hannunta na rawa, ta sake share hawayenta da bayan hannu. Numfashinta kuwa kamar wanda ta yi gudun kilomita. Ta ɗaga hannu a hankali, ta buga ƙofar sau biyu.
Shiru. Babu amsa.
Ta lumshe idanunta. “Ko ya yi barci ne?” ta faɗa a ranta. Ta sake buga ƙofar. Har yanzu shiru. Ta haɗiye yawu, ta waiwayo baya kamar wacce take tunanin komawa ɗakinta.
“Ai idan na koma… Anty Sameera za ta kashe ni.”
Ta cije lips ɗinta. A hankali ta sake ɗaga hannu. Kafin ta buga karo na uku, sai ta ji muryarsa daga cikin ɗakin.
“Come in, Princess.”
Numfashinta ya tsaya. “Ta yaya ya san nazo?” Jikinta ya yi sanyi gaba ɗaya. Ta dafe ƙirjinta, a hankali ta murɗa handle ɗin ƙofar. Ta buɗe ƙofar kaɗan, ta leƙa ciki.
Yaya Umar yana zaune a ƙaramin sofa da ke gefen window. Sanye yake da farin T-shirt mai sauƙi da black joggers. Laptop ne a cinyarsa, amma tun kafin ta shigo sosai, ya riga ya ɗaga kansa yana kallonta. Idanunsu suka haɗu.
Inteesar ta yi saurin sauke kanta. Ta shiga cikin ɗakin a hankali, ta rufe ƙofar cikin nutsuwa, amma ba ta matsa sosai ba. Ta tsaya bakin ƙofar, kanta a ƙasa, yatsunta suna ta murza gefen hijabinta.
Yaya Umar ya cire idanunsa daga laptop ɗin gaba ɗaya. Ya rufe shi, ya ajiye shi a gefe. Duk hankalinsa ya koma kanta. Ya lura da jajayen idanunta, ya lura da yadda hannayenta ke rawa, da kuma ƙamshin turaren da ya cika ɗakin. A hankali ya miƙe tsaye.
“Princess…” ya kira cikin sanyin murya. “Lafiya?”
Inteesar ta buɗe baki, ta sake rufewa. Ta kasa magana. Ya ɗan matsa kusa da ita, amma ya tsaya da tazarar da ba za ta firgita ba.
“Me ya faru?” ya sake tambaya.
Inteesar ta haɗiye yawu. “Anty Sameera ce…” ta faɗa cikin ƙaramar murya.
Ya ɗan haɗe gira. “Me ta yi?”
Inteesar ta ƙara sunkuyar da kanta. “Ta… ta yi shiru, ta sake gwadawa. “Ta ce… ta ce idan ban zo ɗakinka ba…” Sai ta kasa ƙarasa maganar, kunyar ta hana ta.
Yaya Umar ya tsaya yana kallonta na wasu daƙiƙu. Sai wani ƙaramin murmushi ya bayyana a gefen lips ɗinsa. A ransa ya ce, “Anty Sameera… Ashe ke kika turo ta, ai dama na sani.” Ya sauke numfashi a hankali kafin ya ce, “Shi ya sa kika zo?”
Inteesar ta gyada kai kaɗan. Har yanzu ba ta iya kallonsa ba. Yaya Umar ya shafa gefen goshinsa, sai ya yi murmushi mai laushi.
“Princess… Ki daina tsorona.” Muryarsa cike take da natsuwa. “Ba zan taɓa tilasta miki wani abu ba,” ya faɗa a hankali.
Inteesar ta ɗan cije lips ɗinta. A karon farko tun shigowarta, ta ɗan ɗaga idanunta ta kalle shi. Ta ga gaskiya a cikin idanunsa; ba ta ga fushi ba, ba ta ga wani buri a tattare da shi ba, sai kawai natsuwa da kulawa.
Yaya Umar ya nuna mata sofa da hannunsa. “Zo, ki zauna.”
Inteesar ta tsaya na wasu daƙiƙu kafin a hankali ta ƙarasa. Ta zauna a gefen sofa, amma ta bar babban tazara a tsakaninsu. Yaya Umar ya lura da hakan, sai kawai ya yi murmushi a ransa. Ya tashi, ya koma ɗayan sofa ɗin ya zauna.
Ya ɗauki remote, ya kashe AC ɗin da yake mata sanyi, sannan ya ɗauki blanket mai laushi daga gefen gadonsa ya miƙa mata. “Ga wannan, kar ki ji sanyi.”
Inteesar ta karɓa, ta ɗago ta kalle shi. “Nagode…” ta faɗa cikin sanyin murya.
“You’re welcome,” ya amsa.
Sai shiru ya ratsa tsakaninsu. Amma a wannan karon, ba irin shiru mai tsoro ba ne; shiru ne da ke fara gina wata sabuwar amana a tsakaninsu.
A hankali Yaya Umar ya koma kan sofa ɗin da yake zaune. Ya ɗauki laptop ɗinsa, ya buɗe shi, ya ci gaba da aikin da yake yi cikin nutsuwa.
Inteesar kuwa ta ɗan gyara zamanta, a hankali ta kwanta a kan sofa ɗin da yake kusa da window. Ta janyo duvet ɗin har ya rufe jikinta, sai dai idanunsa na ɗan leƙen shi ta gefen ido. Shi kuwa, duk da cewa idanunsa suna kan laptop ɗin, lokaci zuwa lokaci yana ɗan ɗagowa yana kallon inda take. Da zarar idanunsu suka kusan haɗuwa, Inteesar sai ta yi saurin rufe idanunta kamar tana barci.
A zuciyarta kuwa, tunani ne ya fara yawo: “Ko dai na gwada na sake roƙonsa? Wataƙila yanzu zai yarda. Ai ba gidan Daddy zan je ba… Taron gidan Anty su Sameera ne.”
Ta yi shiru na wasu daƙiƙu, sai ta tattara ƙarfin hali. A hankali ta tashi kaɗan daga kwanciyar, ta zauna. Motsinta ya sa Umar ya ɗago daga laptop ɗinsa. Ya kalle ta cikin nutsuwa.
“Do you need anything?” ya tambaya cikin murya mai laushi.
Inteesar ta sunkuyar da kai, hannunta har yanzu riƙe da gefen duvet ɗin. “Dama…” ta fara, sai ta yi shiru ta kasa ƙarasawa.
Umar bai katse ta ba. Ya ci gaba da kallonta cikin haƙuri.
Inteesar ta sake haɗiye yawu. “Za a yi taro… a gidansu Anty Sameera, a can Katsina.” Ta ɗan tsaya kafin ta ci gaba cikin murya mai cike da roƙo. “Shi ne… ina so nima na je.”
Shiru ya ratsa ɗakin. Yaya Umar bai yi gaggawar ba ta amsa ba. Ya rufe laptop ɗin a hankali, ya ɗora shi kan table, sannan ya zuba mata waɗancan lumsashshun idanunsa da suka saba rikita zuciyarta. Na wasu daƙiƙu bai ce komai ba. Sai daga ƙarshe ya buɗe baki cikin sanyin murya.
“Kin manta sharadina na zuwa Katsina ne?”
Inteesar ta ɗago kai da sauri, idanunsu suka sauka cikin nasa. Sai ta ɗan turo baki, ta langwaɓe kanta gefe cikin shagwaɓar da ita kanta ba ta san ta yi ba.
“Ba gidan Daddy nace ba… Taron gidan su Anty Sameera ne. Kuma… ba zan dade ba,” ta ƙarasa tana kallonsa da idanu masu cike da roƙo.
Yaya Umar ya ci gaba da kallonta ba tare da ya ko lumshe ido ba, kamar yana jin daɗin kallon yadda take ƙoƙarin lallashinsa. Sai wani ɗan ƙaramin murmushi ya ɓuya a gefen lips ɗinsa, amma bai bari ta gani ba.
A hankali ya ce, “Ehh… Still dai, Katsina ne.” Ya ɗan jingina bayansa da sofa. “Ba za ki je ko’ina ba, sai kin cika sharadin da na gindaya,” ya faɗa cikin natsuwa, ba tare da ya ɗaga murya ba, ba tare da ya nuna fushi ba.
Sai kawai ya sake ɗaukar laptop ɗinsa, ya buɗe shi, ya maida hankalinsa kan aikin da yake yi. Alamar magana ta ƙare.
Inteesar ta tsaya tana kallonsa. Ta turo baki sosai, ta haɗe hannayenta a ƙirji. “Dama na sani ba zai bari ba…” ta faɗa ƙasa-ƙasa cikin shagwaɓa. “Mutum sai taurin kai,” ta ƙarasa tana mita a hankali, tana tabbatar da cewa ba zai ji ba.
Sai ta juyo gefe tana ƙara rungume duvet ɗinta, fuskarta cike da ƙorafi. Shi kuwa Yaya Umar bai ɗago ba, sai dai a can gefen lips ɗinsa, wani siririn murmushi ya bayyana saboda ya ji komai.
Inteesar ta juya gefe tana ƙara rungume duvet ɗinta. Bayan wasu daƙiƙu, wata zuciyar ta fara raɗa mata: “Maybe… ai idan an yi a daren yau, ƙila ma ki samu ciki nan take. Sai ya cika alƙawarinsa.”
Ta yi shiru, ta lumshe idanunta kamar tana son gaskata abin da zuciyar tata ke faɗa, sai ta sake buɗe su. A hankali ta ɗaga kanta, ta kalli Umar. Har yanzu yana zaune cikin nutsuwa, idanunsa suna kan laptop, yatsunsa na motsi a kan keyboard kamar ba shi da wata damuwa a duniya.
Inteesar ta ci gaba da kallonsa. Tunani ya fara yawo a zuciyarta. “Ko na tambaye shi? Ko kuwa na haƙura da zuwa Katsina?”
Sai ba zato ba tsammani, hoton Daddy ya faɗo mata a zuciya. Fuskarsa, murmushinsa, yadda yake kiranta da “Princess ɗina.” Idanunsa suka fara ɗan cika da hawaye. Ta tuna Khalil, ta tuna Mommy Haleema, ta tuna Aamaan. “Wayyo… yaushe rabona da ganinsu?” Ta haɗiye wani abu da ya tsaya mata a maƙoshi, zuciyarta ta cika da ƙewarsu.
Ba ta ma san lokacin da kalmomin suka kuɓuce daga bakinta ba. “Toh…” ta fara cikin ƙaramar murya.
Umar ya ɗan ɗago kai daga laptop ɗinsa, ya kalle ta.
“Yaya…” ta kira cikin kunya. “Zan iya samun ciki…” ta ɗan tsaya saboda kunya, “…yanzu?”
Daƙiƙa ɗaya… biyu… uku… Shiru ya mamaye ɗakin. Yaya Umar ya tsaya cak. Idanunsu suka sauka a kanta kamar bai tabbatar da abin da ya ji ba.
“Me kika ce?” ya tambaya cikin sanyin murya.
Inteesar ta ji gabanta ya faɗi. Sai a lokacin ta gane abin da ta furta. Da sauri ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta. “Wayyoo Allah na…” ta furta cikin jin kunya. “Ni… ba haka nake nufi ba…” Ta kasa ƙarasa maganar. Kunyar da ta ji ta sa har ta so ta nutse cikin duvet ɗin da take rungume da shi.
Yaya Umar ya ci gaba da kallon ta cikin wani shegen murmushi yana taune lips ɗinsa. A hankali ya taso daga inda yake zaune, ya ƙaraso gabanta. Ya ɗan janye duvet ɗin da take ɓoye fuskarta da shi. Da sauri Inteesar ta sunkuyar da kanta, ta kifa goshinta a kan gwiwowinta saboda tsananin kunya.
Murmushi ya ƙara faɗaɗa a fuskar Umar. Ya durƙusa a gabanta, a hankali ya kama hannayenta,