Kaddarar Zuciya Book 2 Complete JIddah Barkum

Author :  Jiddah Barkum Category :  Read Hausa Novels

Chapter   1 / 40

1 to 3K   out of 117.5K words

*KADDAR ZUCIYA*

*CHAPTER SIXTY-FIVE: 65*

*THE DENIAL*

*JIDDAH BARKUM*

Aliyu ya tsaya a wurin kamar an dasa shi, motar Yaya Abubakar ta ci gaba da tafiya har ta ɓace daga ganinsa, amma shi bai motsa ba. Ledar kuɗin tana hannunsa, yatsunsa sun matse ta sosai har takardar ledar ta fara lanƙwashewa, numfashinsa ya yi nauyi. A hankali ya buɗe ledar, idanunsa suka sake sauka kan bundles ɗin kuɗin, da aka dawo masa da shi. Auren da ya ɗauka babu abin da zai iya tsayawa a gabansa… an ce masa an fasa. Ya haɗiye yawu da ƙyar, a hankali ya furta, kamar yana magana da kansa, “…mansion.” Ya yi shiru, “…seventeen million.” Numfashinsa ya sake nauyewa, sai kalma ta ƙarshe ta dawo masa, “…Aisha.” Wani irin sanyi ya ratsa bayansa, ya girgiza kai a hankali, “a’a… wannan ba zai yiwu ba.” Sai kuma ya tsaya cak, idanunsa suka buɗe sosai, kamar walƙiya ce ta ratsa masa ƙwaƙwalwa. Ranar… ranar da ya je gidan Alhaji Kabeeru, ranar da ya ba Inteesar wayarsa kafin ya fita masallaci, da ya dawo ya tarar tana cikin wani yanayi da bai gane ba. Hannunsa ya kai bakin bakinsa, muryarsa ta fito a raunane, “does that mean…” ya haɗiye yawu, “…Inteesar checked my phone… ranar da na tafi sallah?” Gabansa ya faɗi da wani irin ƙarfi, da sauri ya dafe bakinsa, “la ilaha illallah…” A karon farko cikin shekaru… ya ji tsoro na gaske, ba tsoron rasa kuɗi ba, ba tsoron mutunci ba, tsoron rasa Inteesar, tsoron abin da ta karanta, tsoron abin da iyalinta suka sani, tsoron abin da yake jiransa.

Da sauri ya juya ya koma cikin office, receptionist ta yi saurin miƙewa, “sir…” bai ko kalleta ba, kai tsaye office dinsa ya nufa, ya shiga, ƙofar ta rufe da ƙarfi a bayansa. Ya tsaya tsakiyar office ɗin yana sauke numfashi, idanunsa suka fara yawo cikin ɗakin, komai ya zama kamar ba nasa ba. Ya kama gefen table, ya runtse idanunsa, “Intee…” kalmar ta kuɓuce masa. Sai ya buɗe idanunsa da sauri, ya ɗauki key ɗin motarsa, ya sake ɗaukar ledar kuɗin, ya fito. Staff ɗinsa suna ta magana, “are you alright, sir? Sir…” babu wanda ya samu amsa, kowa ya bi shi da kallo, ba su taɓa ganin Aliyu cikin irin wannan yanayin ba. Ya shiga motarsa, ya kunna engine, ba tare da wani tunani ba… kai tsaye ya nufi gidan Alhaji Kabeeru.

Da ya isa ƙofar gidan… ya yi horn, mai gadi ya buɗe gate kamar yadda ya saba yi a duk lokacin da ya gan shi, “ranka ya dade sannu da zuwa.” Aliyu ya ɗaga masa kai kawai, ya shiga cikin compound. Amma kafin ya kashe engine… sai ya ji zuciyarsa ta tsinke. Wannan gidan… gidan da yake shigowa kullum cikin walwala, gidan da yake jin kamar gidansu ne, yau… sai ya ji kamar yana shirin shiga kotu ne domin a yanke masa hukunci. Ya zauna cikin motar na wasu daƙiƙu, hannayensa biyu suna kan steering, bugun zuciyarsa yana ƙara sauri. Ya lumshe idanunsa, ya ja dogon numfashi, sai ya furta a hankali, “ya Allah…” ya buɗe idanunsa, ya ɗauki ledar kuɗin, ya fito daga motar. Kowanne taku da yake yi… sai gabansa ya ƙara faɗuwa.

A hankali ya tura ƙofar falon, “assalamu alaikum…” muryarsa ba kamar kullum ba ce, ta rasa kwarin da ta saba ɗauka. Falon ya yi tsit. Inteesar tana kwance a kan sofa, idonta a lumshe, ba barci take yi ba, ba kuka take yi ba, kawai… tayi shiru a tunani. Humaira tana zaune a kujerar dining tana fuskantar falon, Khalil da Faisal ma suna nan, kowa akwai abin da yake yi, amma babu wanda yake magana. Da jin sallamarsa… Humaira ta ɗaga kai, da ta ga Aliyu… nan take ta miƙe tsaye, fuskarta ta haɗe, ta kalle shi daga sama har ƙasa, “lafiya, malam?” ta faɗa cikin murya mai sanyi, amma mai cike da suka, “za ka shigo mana gida haka kawai?” Aliyu ya tsaya, bai san abin da zai fara cewa ba. Humaira ta yi wani ɗan murmushi na takaici, “ko abin da ka fara ne ka zo ka ƙarasa?” Kafin Aliyu ya buɗe baki… Faisal ya ɗaga kai da sauri, “Humaira.” Ta juya ta kalle shi, “what is this?” muryarsa ta yi tsauri, “kar na sake jin kina yin irin wannan magana.” Humaira ta cije leɓenta, ta watsa wa Aliyu wani mugun kallo, sannan ta juya ta koma ta zauna, amma yadda take girgiza ƙafarta ya nuna fushinta bai ragu ba ko kaɗan.

Tun daga sallamarsa ta farko… Inteesar ta buɗe idanunta, a hankali suka sauka kan Aliyu. Na ɗan daƙiƙu… idanunsu suka haɗu, Aliyu ya ji wani abu ya matse masa ƙirji. Waɗannan idanun… ba su da walwalar da ya sani, ba su da murmushin da yake gani duk lokacin da ta kira shi “mi amor.” Babu farin ciki, babu ƙauna, sai wani irin shiru mai karya zuciya. Inteesar ba ta ce masa komai ba, a hankali ta miƙe daga kan sofa, jikinta babu ƙarfi, ta juya, ta nufi stairs. Aliyu ya bi ta da ido, yana fatan… ko sau ɗaya za ta waiwayo, amma ba ta waiwayo ba, har ta ɓace daga ganinsa. Sai ya sauke idanunsa ƙasa, wannan shiru nata… ya fi masa zafi fiye da kowace magana.

A daidai lokacin… suka ji muryar Mommy Haleema daga kitchen, “hayaniyar me nake ji haka?” tana goge hannunta da ƙaramin towel ta fito zuwa falon. Da idanunta suka sauka kan Aliyu… ta tsaya turus. Na wasu daƙiƙu… ba ta motsa ba, ba ta yi magana ba, sai ta bi shi da kallo, daga takalmansa… zuwa ledar da ke hannunsa… har zuwa fuskarsa. Fuskarta ta canza a hankali, ba kallon surukin da take alfahari da shi ba ne, ba kallon mutumin da ta taɓa ba amanar ɗiyarta ba ne, kallo ne mai cike da takaici… da ciwon amanar da aka ci. Ta tsaya a gabansa cikin nutsuwa, ba yabo, ba fallasa, sai wani irin shiru mai nauyi da ya mamaye falon, wanda ya sa har Aliyu ya kasa gane wace kalma ce ta dace ya fara furtawa.

Aliyu ya buɗe baki sau biyu kamar zai yi magana, “Mommy… ni…” kalmar ta tsaya masa a maƙoshi. A karon farko tun da ya fara zuwa gidan nan… ya rasa abin cewa. Mommy Haleema ta ci gaba da kallonsa ba tare da ta ce komai ba, fuskarta babu fushi mai hayaniya, amma akwai wani irin natsuwa mai nauyi da ta fi kowace magana tsoro. A hankali ta ce, “lafiya dai?” Aliyu ya haɗiye yawu, yatsunsa suka ƙara matse ledar kuɗin da ke hannunsa, da ƙyar ya sami murya, “Yaya Abubakar…” ya tsaya, kamar kalmomin sun ƙi fitowa, “…ya kawo min kuɗi.” Mommy ta ci gaba da kallonsa, “ya ce…” Aliyu ya lumshe idanunsa na ɗan daƙiƙa, “…ya ce kuɗin auren Inteesar ya dawo min da su.” Shiru, ba Mommy ba, ba Faisal ba, ba Khalil ba, ba Humaira ba, babu wanda ya ce komai. Aliyu ya sake cewa cikin ruɗani, “Mommy… ban fahimta ba.” Ya ɗan ɗaga ledar kuɗin, “ya ce an fasa aure.” Numfashinsa ya yi nauyi, “ban san me ya faru ba.” Ya kalli Mommy cikin idanun da suka cika da damuwa, “wallahi ban san abin da yake faruwa ba.” Humaira ta yi wani ɗan murmushi mai cike da takaici, ta girgiza kai, “da gaske?” Faisal ya juya ya kalle ta, “Humaira.” Ta yi shiru, amma ta ci gaba da kallon Aliyu da idanu masu cike da ɓacin rai. Mommy Haleema ta ɗauke idanunta daga Aliyu na wasu daƙiƙu, ta sauke numfashi a hankali, sannan ta sake kallonsa, “da gaske ba ka san me ya faru ba, Aliyu?” Aliyu ya yi saurin girgiza kai, “wallahi ban sani ba, Mommy, kawai Yaya Abubakar ya zo… ya dawo min da kuɗin nan… ya faɗi wasu maganganu da ban fahimta ba… shi ya sa na zo nan.” Mommy ta ɗan jinjina kai, “to.” Ta ɗauki mataki ɗaya ta ƙarasa kusa da shi, “ka tabbata kana son sanin abin da ya faru?” Aliyu ya amsa ba tare da wata-wata ba, “eh, Mommy, saboda wallahi… zuciyata ba ta cikin nutsuwa.” Mommy ta yi shiru na wasu daƙiƙu, sannan ta ce cikin murya mai sanyi, amma mai cike da nauyi, “to ka shirya jin gaskiyar da za ta iya sauya rayuwarka gaba ɗaya.”

Ba tare da ta ƙara wata magana ba… Mommy Haleema ta juya cikin nutsuwa, ta taka zuwa centre table da ke tsakiyar falon. Wayar Inteesar tana nan inda aka ajiye ta, ta miƙa hannu ta ɗauke ta. Na ɗan daƙiƙu ta tsaya tana kallon screen ɗin wayar, sannan ta juya ta dawo gaban Aliyu. Ba ta yi saurin miƙa masa wayar ba, sai da ta ɗaga idanunta ta kalle shi ido cikin ido, kallo ne mai cike da takaici… da ciwon amanar da ba taɓa tunanin za ta gani daga gare shi ba. A hankali… ta miƙa masa wayar, screen ɗin yana buɗe kai tsaye a daidai screenshots ɗin, “karanta.” Kalma ɗaya ce kawai ta faɗa. Aliyu ya ɗan yi jinkiri, gabansa ya sake faɗuwa, a hankali ya miƙa hannu, yatsunsa na rawa suka karɓi wayar. Mommy Haleema kuwa… ta ja baya kaɗan, ta haɗe hannayenta a ƙirji, ta tsaya tana kallonsa ba tare da ta ƙifta ido ba. Falon gaba ɗaya ya sake yin tsit, har ƙar numfashin Aliyu ake iya ji. Idanunsa suka sauka kan screenshot na farko, da ya fara karantawa… fuskarsa ta sauya nan take, jinin jikinsa kamar ya tsaya cak. Ya yi saurin scrolling zuwa na biyu, sai na uku, sai na huɗu, kowace kalma da idanunsa suke sauka a kanta… sai fuskarsa ta ƙara sauyawa, launin fuskarsa ya fara gushewa, lips ɗinsa suka fara rawa, numfashinsa ya rikice. Da ya kai ƙarshen screenshots ɗin… hannun da yake riƙe da wayar ya fara karkarwa sosai, ya sake komawa sama, ya sake karantawa, kamar yana fata idanunsa sun yi masa ƙarya, amma kalmomin suna nan yadda suka kasance, ba su canza ba. A hankali… ya sauke wayar daga gabansa, idanunsa suka cika da tsantsar ruɗani, ya ɗago ya kalli Mommy Haleema, sannan ya sake kallon Faisal, ya kalli Khalil, Humaira kuwa ta juya kai gefe cikin takaici. Aliyu ya ji wani irin nauyi ya sauka a kirjinsa, a hankali ya girgiza kai, muryarsa ta fito da ƙyar, “…Mommy…” ya haɗiye wani abu mai ɗaci, “wallahi… ba haka abin yake ba.”

Kafin Mommy Haleema ta sake cewa komai… sai suka ji wata murya daga bakin ƙofar falon, murya mai cike da iko… da kuma wani irin ƙarsashi, “to… ya abin yake?” Kowa ya juya lokaci guda. Yaya Abubakar ne, yana tsaye a bakin ƙofar falon, fuskarsa babu annuri, idanunsa kuwa… suna kan Aliyu, kai tsaye. Aliyu ya ji gabansa ya sake faɗuwa, ya kalli Abubakar, ya sake kallon Mommy, ya kalli Faisal, ya kalli Khalil, a ƙarshe idanunsa suka sauka ƙasa, ya haɗiye yawu da ƙyar. Na wasu daƙiƙu… babu wanda ya ce komai. Daga ƙarshe… Aliyu ya ɗaga kansa a hankali, “tabbas…” ya ɗan lumshe ido, “akwai Aisha.” Kalmar ta fito da ƙyar. Humaira ta yi wata yar dariyar takaici, “kai… yanzu ka fara faɗin gaskiya.” Faisal ya yi mata kallon kashedi, ta yi shiru. Aliyu ya ci gaba, “ba zan ce babu ita ba.” Ya sauke numfashi, “amma maganar ba yadda kuka ɗauka take ba.” Abubakar ya ci gaba da kallonsa ba tare da ya motsa ba, “ka ƙarasa.” Aliyu ya gyara tsayuwarsa, “ni da Aisha… mun taɓa shirin aure a baya, amma wasu dalilai suka sa abin bai yiwu ba.” Ya yi shiru na ɗan lokaci, “tun daga lokacin… ta ƙi yarda rayuwata ta ci gaba, duk inda na je neman aure… sai ta nemo hanyar lalata komai.” Mommy Haleema ta haɗe gira. Aliyu ya ci gaba da magana, “ta kan kira iyayen yarinyar… ko ta tura saƙonni… ko ta yi barazana, sau biyu… har an kusa ɗaura aure… amma abin ya rushe saboda ita.” Ya lumshe idanunsa, “da Inteesar ta shigo rayuwata… na fahimci ba zan iya rasa ta ba, shi ya sa… lokacin da Aisha ta sake fara barazana… …na biye mata a magana.” Khalil ya haɗe gira, “ka biye mata?” Aliyu ya gyada kai cikin kasala, “na yi hakan ne domin in kwantar mata da hankali, in cire hankalinta daga kan Inteesar, na yi tunanin idan ta ga kamar inteesar ta fi sona maimakon son da nake mata… za ta daina neman hanyar cutar da Inteesar.” Ya ɗaga idanunsa ya kalli Mommy Haleema, “wallahi… ban taɓa nufin abin da na rubuta ba, na yi kuskure, babban kuskure, amma zuciyata… zuciyata ba taɓa daina son Inteesar ba, bazan iya cutar da ita ba.”

Kafin wani daga cikin waɗanda ke falon ya samu damar cewa komai… Mommy Haleema ta yi saurin ɗaga hannu, “ya isa.” Muryarta ba ta da ƙarfi, amma cike take da yanke hukunci. Kowa ya yi shiru, ta ɗauki mataki ɗaya gaba, idanunta suna kallon Aliyu kai tsaye, “to… idan haka abin yake… wannan kaɗai ma ya isa.” Aliyu ya ɗago kansa da sauri, “Mommy…” ta katse shi da hannu, “a’a, ka bari na gama.” Ta ja dogon numfashi, “idan har akwai wata mace da take bin rayuwarka… har tana yi wa duk matar da ka nema barazana… har tana lalata maka maganar aure… har ka kai matsayin da za ka riƙa biye mata saboda tsoro… to ba za mu yi wasa da rayuwar yarinyarmu ba.” Aliyu ya yi saurin girgiza kai, “Mommy, wallahi ba—” “Aliyu.” Ta sake katse shi, muryarta ta ƙara yin sanyi, amma ta fi ta da farko nauyi, “ka saurare ni, ni uwa ce, kuma abin farko da zan fara dubawa shi ne lafiyar ɗiyata.” Ta matsa kusa da shi, “ba zan kai Inteesar cikin gidan da za ta riƙa rayuwa cikin tsoron wata mace ba, ba zan kai ta gidan da za ta dinga waiwayen ko yau wace irin barazana za ta sake fitowa ba, ba zan kai ta wajen da za ta riƙa fafatawa da tsohuwar soyayya ko tsohuwar matsala ba.” Ta girgiza kai, “a’a, ba zan yi hakan ba.” Aliyu ya ji kalamanta suna shiga zuciyarsa ɗaya bayan ɗaya, ya yi saurin cewa cikin rawar murya, “Mommy… na rantse da Allah… Aisha ba komai ba ce a wurina, tun shekaru da suka wuce komai ya ƙare, Inteesar ce kaɗai nake so.” Mommy ta dubi idanunsa na wasu daƙiƙu, sannan ta ce cikin natsuwa, “ko da haka ne… har yanzu matsalar tana nan.” Ta nuna shi da yatsa, “saboda kai da kanka ka faɗa mana cewa tana bin duk inda ka je neman aure, to wa zai tabbatar min cewa gobe ba za ta sake dawowa ta tayar da hankalin Inteesar ba?” Aliyu ya buɗe baki, ya rasa amsa. Mommy ta ci gaba, “Aliyu… ba zan yi caca da rayuwar ɗiyata ba.” Ta jinjina kai a hankali, “saboda haka… a gare ni… wannan magana ta isa ta sa a dakatar da maganar auren nan.” Falon ya sake yin tsit. Aliyu kuwa… ya ji kamar an zare masa wani sashe na zuciyarsa. Ya buɗe baki da ƙyar, “Mommy… don Allah… kada ku hukunta ni saboda kuskuren da ban taɓa nufin zai cutar da Inteesar ba.” Amma a wannan karon… fuskar Mommy Haleema ta nuna masa cewa… ba ta shirya sauya matsayarta ba.

*KADDAR ZUCIYA*

*CHAPTER SIXTY-SIX: 66*

*THE HIDDEN TRUTH UNVEILED*

Jiddaah Barkum

Idanun Aliyu suna yawo daga kan Mommy Haleema zuwa Faisal, daga Faisal zuwa Khalil, daga Khalil zuwa Abubakar. Kowa yana kallonsa, amma ba kallon da ya saba gani ba ne, ba kallon mutunci ba, ba kallon suruki ba, kallo ne mai cike da takaici. Abubakar ya yi taku biyu gaba, ya tsaya daidai gaban Aliyu, fuskarsa babu hayaniya, babu ihu, amma nutsuwar da ke fuskarsa ta fi kowace irin faɗa tsoro. Ya ɗan sunkuyar da kai yana kallon Aliyu, “ka gama?” Aliyu ya haɗiye yawu, a hankali ya gyada kai, “…eh.” Abubakar ya jinjina kai kaɗan, “to, yanzu ni zan yi magana.” Khalil ya sauke numfashi, Humaira ma ta daina girgiza ƙafarta, har Mommy Haleema ta maida hankalinta gaba ɗaya kansu. Abubakar ya ci gaba cikin sanyin murya, “ko da duk abin da ka faɗa gaskiya ne…” ya nuna wayar da ke hannun Aliyu, “…abin da ka rubuta da hannunka ba ya gogewa.” Aliyu ya yi yunƙurin magana, “Yaya ni—” Abubakar ya ɗaga hannu, “na ce ka bari.” Nan take Aliyu ya yi shiru. Abubakar ya ci gaba, “ka raina ƙanwata, ka raina iyayena, ka raina gidanmu, ka kuma karya amana da yardar da muka yi maka.” Aliyu ya girgiza kai da sauri, “wallahi ban taɓa nufin—” “ban gama ba,” Abubakar ya katse shi, muryarsa ta fara yin nauyi, “kai ne ka rubuta, kai ne ka tura, ba wani ya tilasta maka ba.” Ya yi shiru na wasu daƙiƙu, sannan ya dubi Aliyu kai tsaye, “no matter what… ko mene ne dalilinka… auren tsakaninka da Inteesar…” ya tsaya, kowanne mutum a falon yana jiran kalmar da za ta biyo baya, sai ya furta cikin ƙarfi, “…ya ƙare.” Aliyu ya ji kamar wani ya bugi ƙirjinsa, numfashinsa ya tsaya. Abubakar ya ƙara da cewa, “and that… …is final.” Kalmar ta sauka cikin falon kamar dutse. Aliyu ya runtse idanunsa, ya girgiza kai cikin rawar murya, “a’a… don Allah…” ya yi taku ɗaya gaba, “ka bar ni in yi magana da Inteesar.” Abubakar ya girgiza kai, “ba za ka ganta ba, ba yau ba, ba yanzu ba.” Aliyu ya ƙara matsowa, “wallahi minti biyu kacal, in yi mata bayani, in roƙe ta.” Abubakar ya nuna masa ƙofar fita, “ka fita.” Aliyu ya sake girgiza kai, “Yaya… don Allah.” “na ce…” muryar Abubakar ta fita cikin tsawaaa, “KA FITA.” Falon ya sake yin shiru, har Humaira ta ji gabanta ya faɗi, ba don ta yafe masa ba, amma… a karon farko… ta ga Aliyu cikin wani irin hali da ba taɓa ganin irinsa ba. Khalil ya lumshe ido, Faisal ya dafe goshinsa, Mommy Haleema kuwa… ta tsaya kawai tana kallon

1 / 40