FARRAH HAUSA NOVELS COMPLETE BY M SHAKUR COMPLETE.doc

Author :  Maman Shakur Category :  Arewa Pen

Chapter   43 / 48

126K to 129K   out of 142.7K words

gidana ko Mami ko minti biyu bai karaba bacci ya kwasheshi ajikin Mami tadade tanamai massage tana kallonshi harcikin ranta karamai addu a take Allah ya tsareshi yakuma kareshi.
[12/21, 11:07 PM] +2347066933957>?p?: Bayan na sanar musu cewar na gama na sauko na daya a dayan set din cushion din domin bana son na tsaya a kusa da inda ya zauna dazun yayi zaton ko na taba mashi waya, babu mai iya sanin farincikina sai Allah da ya amince min na girka wannan breakfast a yau na shirya komai ba tare da sanin kowa ba, balle a gane cewar ban iya ba. Ummiter ce ta fara saukowa jikinta sanye da tufafin bachi wando da riga ta nade kanta da wani abun da nake kyautata zaton tawul ne. Alhaji Bashir ne na biyu sannan Hajiya Jamila, a duk lokacin da muka hada ido harara take aiko min da ita, mijinta kam ban da murmushi babu abun da yake, ba na ce ina ganinshi kullum ba balle na ba da shaidar kyakkyawan murmushin sake fita tsakanin kumatunshi amman tabbas tsakanin jiya da na fara bashi labarina zuwa yau na lura nishadin shi dabam yake.

 Kin cire na ki ko?

 Aa ban zuba ba

 Ke da girki, mu da fara ci zo ki zuba na ki mana

Na dauki plate din da yake nan na bude cooler na zuba, na sake daukar dayan na zuba dankali da kwai, sannan na dauka zan tafi.

 Tea fa?

Na juyo na kalleshi sai kuma na kalli Hajiya Jamila wacce ta hade min fuska.

 Aa wannan ya isa

Ban jira ya sake cewa wani abu ba na fito falon da saurina, kamin na karasa bq na tsaya na dandana abinci domin tun a cikin yawuna ya tsinke, saranda na yi ina fidda ido waje, anyi ba'ayi ba kenan ni kaina ban taba cin girki marar dadi irin wannan gashi dai be nuna ba kuma ga rashin dadi wani gurin ma kamar gishiri ya zarce.

 Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un

Na fada cikin tashin hankali, da gudu na karasa bq din a waje na aje plates din hannuna na dawo da gudu zuwa main house din jikina har mazari yake, ala ala nake idan ba su ci ba ina shiga cikin falon muryar Hajiya Jamila ta dira a kunne

 Ni gaskiya ba zan iya cin wannan abincin ba

Ummiter kuma sai kwasar dariya take, tsaye na yi jikin kofar falon irin yadda yara suke idan sun yi laifi fuskana na bayyana rashin jindadin abun da na aikata, sai suka dago suna dubana, Alhaji Bashir da fuskarsa take sake har yanzu ya ce.

 Zahra karaso mana

Kamar ance karasa ki jr ga ajalinki haka na ji, sai na samu kaina da kara matsawa baya na kwalla sharrr daman can haka nake zarar zan aikata laifi to kuka ne zai biyo baya tun kam ayi min hukunci.

 Dan iskanci kin san baki iya girki ba kika karba kika yi? Shi wannan abinci mai kama da guba da kika girka mana so kike mu ci mu mutu ne?

Na girgiza kai daga inda nake tsaye, sai Alhaji Bashir yayi alama da na zo da hannu, cikin karfin hali na taka na karasa gurin ina mai tsananin jin kunya taya mace kamar ni ace ban iya girki ba, ai da kunya ba ma karama ba.

 Kiriniya bata barki kin tsaya kin ko yi girki ba ko Zahra?

Na sauke kai na kasa ina jin sautin murmushinsa.

 Video da kika gani a waya suna tsallaken time ne ke kuma kin yi amfani da yadda suke kika girka mana wannan ba ki yi la'akari da haka ba

Wata kunya ce ta kama ni, ya aka yi ya san na dauki wayar har na duba?ko dai akwai camera a falon da kitchen din ne? Wata kila Hajiya Jamila ta boye min ne saboda na saki jiki na aikata wani abun ta gani, wannan maganar da mijinta yayi ya tabbatar min da akwai camera a falon ba kamar yadda Hajiya Jamila tace min a waje kawai aka saka camerar tsaron ba. Yanayin yadda muryarsa ke fita ya isa ya karantar da ni cewar ranshi be bace ba, musamman da na daga kai na kalli fuskarsa sai na yi arba da murmushi irin na mazan dake da kokarin fin karfin zuciyarsu ko da an musu ba daidai ba su kasa nunawa. Ummiter kallon mamaki take min tana yi ma Alhaji Bashir sai kuma ta kalli Hajiya Jamila da ta kusa mutuwa tsaye.

 Ba ki iya girki ba Zahra?

Ya tambaya, sai na daga masa kai ina dan turo baki ji nake kamar ya muzantani a bainar nasi.

 Ya kamata ki koya ko dan gaba, maza suna son mace da ta iya girki misali irina ina son mace mai girki kala kala, kuma ya kamata ki koyi amfani da wasu abubuwan like wannan dankali akwai inda ake soya shi ba sai an saka cikin ruwan mai ba, Wife ina tunanin catering school zamu nema mata what do you think?

Ya karasa yana kallonta wata uwar harara da ta jefo masa ni kaina sai da na nemi natsuwata na rasa, Ummiter kam abun da take nema ne ya bude mata kofa wato gulma har bakin Alhaji Bashir dake motsi kallon take balle kuma reaction dina da na Hajiya Jamila.

 Hubby ina son magana da kai

Tana fadar haka ta mike tsaye har wani hura hanci take kallo daya zaka yi mata ka fahimci ranta a bace yake, daman kuma na lura da hakan tun a jiya.

 Okay gani nan shigowa

Amsa mata yake amman idonshi akai yake kamar zata wulgar da kujerar data zauna haka ta jata baya ta bar dinning a matukar fusace, a take na karanci jindadi a fuskar Ummiter sai kallona take da mamaki.

 Ummiter shiga kitchen ki shirya mana wani abun da zamu ci

 Okay dan'uwana Yayana

Ya mike tsaye tare da jan kujerar a baya a hankali ta sauka dinning din ta shiga kitchen.

 Zauna

Yayi min nuna da kujerar da Hajiya Jamila ta tashi.

 Yallabai...

Ban karasa fadar abun da zan fada ba ya daga min hannu.

 Ki ce Bashir idan yayi miki nauyi ki kira da Mr Bashir

Sai da na ji faduwar gaba for no reason.

 Hajiya Jamila zata iya fada, tace kar na sake kebewa da kai

Murmushi yayi ya dauki dankalin ya kai bakinshi.

 Ina ta karanta abubuwa akanki, har yanzu akwai kurciya da wauta irin ta yan auta a tare da ke, taya Jamila zata yi miki magana cewar karki sake kebewa da mijinta kuma ki fada min? Dazun ma zuciyarki bata raya miki da sanina na bar wayata akan kujera ba? Ba ki yi mamakin wayar babu password ba? I expect ki dauka ki duba wani abu kuma kin yi

Risinawa na yi kasa ina kuka.

 Wallahi ba bincike na yi maka ba video kawai na duba na abinci

Da hannu yayi alama da na tashi tsaye.

 Kina tauye kanki kuma ba ki iya tsayawa ki yi tunani Mai Kyau kamin aikata abu, ya kamata ki fito kai tsaye ki fada min ban iya girki ba, daman na saka ran haka yara irin da basa jin magana ba komai suka iya ba, sai kuka da shagwaba, i wonder how mijinki ya iya zama da ke?

Yanayin yadda ya karashe maganar ya nuna tambaya yake da neman sani, sai na share hawayena.

 Daman ai ya saba da halina tun a gida

 Shi Abiey?

 Aa Deen

Yayi murmushi.

 Shi ma kin taba masa kenan? Zauna ki tsakura min ya kuka kare da Abiey?

Na kalli hanyar stairs yan hanjin cikina na kadawa ba dan tsoron Hajiya Jamila ba sai dan gudun bacin rai, kallon stairs din yayi ya kalleni

 Look Zahra daga Jamila har abun da yake karkashinta iko na ne mallakina na ne, saboda haka ki natsu kuma ki bi duk umarnin da zan baki wata kila hakan zai goge shafukan laifukan da kike da su a gurina

Zaunawa na yi idona na kanshi irin na marasa gaskiya.

 Waya ce na ni wani abu? Wani laifin aka ce na maka? Ko kuma na aikata cikin rashin sani ne?

Kallona yake yana zagaye fuskata da idonshi can ya sauke gurin bakina yana kallon lips dina.

 Fada min ya kuke kare da Abiey? Ina son sani abubuwa akanki, saboda ina son zuciyata kara natsuwa da ke

Na ware hannuna ina tabawa sai idonshi ya koma gurin tsiraran yatsun hannuna.

-Gudu muka rika yi ina ta kiranshi amman be juyo ba kuma ba tsaya min ba har sai da ya ji na fara kuka, na fadi a gurin ina ta kiran Babana da Mama sannan Abiey ya dawo ya kama hannuna yace

 Ki tashi mu gudu mana, bana tunanin a nigeria muke fa, duba wannan dajin babu kowa babu haske, kuma tafiyar da na yi be wuce daga nan zuwa can ba ina nemanki sai hango ki na yi a tare da matar nan amman duba gudun da muke amman har yanzu ba mu kai gurin mutane ban ga alamar titi ba

Kuka na fara yi domin na gaji sosai.

 Ni ba zan iya gudi ba na gaji da yawa

 Haka zaki daure waya ce ki kawo mu nan, tun da nake a rayuwata ban taba shiga hatsari irin wannan

 Ai kai ka kawo mu kai ka yi min dinki da baka dinka min wannan lace din ba da yanzu ina can gida ina bachina, amman kai ka dinka min ka kuma ka kawo nan

 Laifin ki ke kika ji maganar iyaye ki ai, da kin ji maganarsu da duk haka be faru ba

 To waya ce na bijire musu ba kai ba, kai ka dinka min kaya kuma ka dauko ni ka kawo gurin bikin aljana Allah ka dai ya sani gaskiya wata kila kai ma aljanin ne

 Amman da na kawo ki ai na ce ki tashi mu tafi kika ki ko? Kuma da kin fada min cewar Mamanki ta hana ki zuwa ba zan yarda na kawo ki ba, gashi nan abun da kika ja mana ai

Na fisge hannuna.

 Abiey mu ga kafarka

Tsaki yayi ya mike tsaye ya fara tafiya, sai na saka kuka ina ihu idan na yi ihun sai murta ta amsa amo, da sauri ya dawo ya fara kokarin rufe min baki.

 Ki yi shiru Zahra karki ja mana wata matsalar haba, kina jin yadda muryarki take amsawa kin san ba a duniyar mutane muke ba

 Ban yarda da kai ba, mu ga kafanka

Ya daga wandonshi da sauri ya haska kafar da wayarshi, farar fata na gani irin ta mutane amman ban gansu ba har sai da na kai hannu na taba, ban ji gashi irin wanda na ji a gurin wacan yarinyar Aljanar mai kafafuwan doki ba, hakan kuma be kara gamsar da ni ba sai da na dankara mashi kwanta har sai da yayi kara.

 Miye haka?

 Tabbatarwa na yi, yanzu me zan fadawa Mama? Kuma na san Deen sai ya kusa kashe ni idan na koma gidan

Na fada cikin kuka ina tuna irin azabar da Deen yake ba ni idan ya ga na tsaya da wani balle kuma ace na bi namiji na shiga motarshi. Ya sake kama hannuna.

 Yi hakuri ta so mu tafi

Na mike tsaye muka cigaba da tafiya cikin tsoro yana rike da hannuna gam.

 Karki juya, ba a son tafiya ana juyawa

Da dukan alama shi ma tsoron be gama fita cikinshi ba, idan ba haka ba taya zai ce min wai kar na waige ba a son waige idan ana tafiya. Kyalkyalewa na yi da dariya sai yayi saurin sakin hannuna.

 Zahra ke ce?

Ina jin haka na san tsoro yake ji sai dariyar ta kara taho min.

 Ban taba ganin namiji mai tsoro ba irinka, ashe ma kai matsora ci ne

 It's not funny Zahra baki da hankali ashe, now i understand why ake dukanki a gidanku taya zaki fara mana dariya muna cikin wannan halin

 Haka ka wuce ni fiuuuuuu kamar iska

Na nuna yadda yake gudun ina cigaba da dariya, sai gashi shi ma yana dariyar, tafiya muka cigaba da yi har muka gaji muka samu gindin wani ice muka zauna ni da shi, sai ya jinginar da wayar tsakiyar mu nan tsoron ya sake dawo min.

 Ka kira waya mana ka fadawa Babanka ko Ammy, ni tsoro nake ji

 Network din ya dauke ai, da tun kamin ki fada na kira

 Yanzu ya zamu yi?

 Waya sani kin janyo mu kin kawo a nan, Allah yasa idan kika koma gida ayi miki shegen doka

 Kai ma Allah yasa idan ka koma Babanka yayi maka shegen duka

Ya kalleni.

 Da ace Babana zai doke ni ko ya hukunta idan na yi masa laifi da zan fi kowa farinciki da jindadin haka

 Saboda?

 Saboda mahaifina ba kamar mahaifinki ba ne, ni nawa mahaifin babu ruwanshi da ni, idan na ci ko ban ci ba, ba damuwarshi ba ne idan wani abun zai same na fadi na mutu ma ba zai damu ba

 Ka masa laifi ne?

 Ban masa laifin komai ba domin na tashi ban san wani abu soyayyar mahaifi ba, ko riga daya be taba siya min na saka ba, a gidan Ammy na bude ido ita ce uwata ita ce ubana, ita take hukunta ni idan na yi laifi kuma ita take cilasta min zuwa gidan mahaifina daga ita sai matarshi ta uku Anty Amarya ita ma tana so na sosai kuma tana nuna min kulawa tana neman duk wata hanya da zata shirya tsakanina da mahaifina

 Fada kuka yi?

 Ba mu yi fada ba Zahra, ko da na bude ido haka na samu kaina cikin tsanar mahaifina ban san dalili ba, amman abun nan yana min ciwo sosai, amman kin yi dace ba kamar ni ba Babanki yana son ki

 Ka fini sa'a domin kai ka ga mahaifinka, ni kuma ban san nawa uban ba, Mama ta fada min tun ina ciki ya rasu ban taba ganinshi ba sai a hoto, sai abokin shi na sani wanda shi yake auren Mama ta a yanzu

Kamin na karasa maganar hawaye regen regen sauko min yake, domin ni ma ina da wannan tabon na rashin sanin mahaifin ko sau daya ban taba jin muryarshi ba, balle na yi rayuwa da shi.

 Allah ya mishi Rahma

 Ameen

Na share hawayen sai ya rika kaina yana kokarin kwantar da ni kan kafadarshi na buge masa hannu.

 Kai wai miyasa kake taba ni be kamata ba fa, ni dai ba yar iska ba ce

 Ni kuma dan iska ne ga iskanci nan rubuce a goshina, daga taimako, ai gashi nan kin jefa mu cikin wannan halin

 Ai nima bana son taimakonka daga yau, ba ni ba kai daman ba san haka za a fada min a gida, kuma zan fada musu cewar sace ni ka yi?

 Ya aka yi na sace ki? Ai babu wanda ya gan ni gidanku kuma ban san hanyar gidanku ba

Ina ganin ya mike tsaye ni ma na tashi sai ya dauki wayarsa ya matsa daga kusa da ni, binsa na yi da saurina.

 Kin ce ba ni ba ke

Ban sake ce masa komai ban kuma daina binsa ba, har muka samu wani fili muka zauna a guri ni dai kamin wani lokaci bachi yayi gaba da ni, ban farka sai da safe ina bude ido na zabura na tashi zaune ina waige waige can na hango shi zaune yana ta daga waya sama da alama network yake nema, da sauri na tashi na karasa inda yake zaune.

 Ka kira gida ne?

 Network din ne sai ya kawo ya dauke gurin nan ba network daman ke na ke jiran ki farka mu tafi

Na waiga ina kallon ko'ina na dajin, irin dajin nan ne mai kama da tsohuwar gona idan an cire amfanin gonar babu komai a ciki sai haki da ciyayi.

 Abiey a ina ka kawo ni?

 Ya za'ayi na sani? Ki kabe kanki akwai kasa

Na kabe dogon gashina da ya gama hautsinewa saboda wahala dankwalin da mayafin ma ban san inda suke ba daga ni sai doguwar rigar lace din da aka dinka min jiya, kama hanya muka yi muna ta tafiya cikina sai kukan yunwa yake min ga gajiya, daker da tsudin goshi muka fara hango mutane, kamin mu karasa gurinsu na yi kuka har Abiey ya gaji da ba ni hakuri ya saka min ido.
Mutanen kauyen mutane masu karamci da son mutane sosai sai da suka fara ba mu abinci da ruwa, Abiey yayi fir shi ba zai ci ba, ni kan na zauna kamar a gidan mu na kwashi tuwona na ci na koshi ba wani kyama na sha ruwa sannan suka ba mu guri muka yi na yi sallah, bayan na gama na dawo kusa da shi na zauna.

 Abiey ka je ka yi sallah?
 Na yi sallah tun a inda muka kwana na yi taimama a gurin na yi sallah, yanzu kuma na kira Ammy na fada mata muna garin Bagar (Fake name)

 Ya aka yi ka san sunan garin?

 Mutanen garin suka fada min, kuma na yi browsing na gani

 To yanzu tafiya zamu yi?

 Aa a nan zamu jira su har su zo

 Amman dan Allah idan mun koma gida ka je gidan mu kace musu sace ni ka yi ka ji?

Ya wara ido yana dariya.

 Na saka kaina a bala'i kenan? Ya aka yi ma muka zo nan? Ko ina motata?

 Waya sani, ashe kenan wannan yarinyar da muka bi tafiyar da ta yi da ni har mun iso nan kenan? Kai kuma ya aka yi ka zo?

 Shi ne abun tambayar ai

Na waige

43 / 48